Wednesday, 13 March 2013

BAYANI AKAN MATAN DA AKA HARAMTA AURENSU



BAYANI AKAN MATAN DA AKA HARAMTA AURENSU
Matan da aka haramta aurensu sun kasu kasha biyu (2).

1.       Wadanda aka haramta aurensu na har abada.

2.       Wadanda aka haramta aurensu zuwa wani lokaci.

WADANDA AKA HARANTA AURENSU HARAMCI NA HAR ABADA

Matan da  aka haramta aurensu haramci na har abada sun kasu kashi 3

a)      Wadanda aka haramta aurensu ta hanyar dangantaka.

b)      Wadanda aka haramta aurensu ta hanyar shayarwa.

c)       Wadanda aka haramta aurensu ta hanyar Surukuta.

a)      WADANDA AKA HARAMTA AURENSU TA HANYAR DANGANTAKA

Wadanda aka haramta aurensu ta hanyar dangantakasun kasu kashi bakwai (7) :-

        I.            UWA KO MAHAIFIYA:- wannan ta hada da wadda ta haifi mutum, ko ta haifi mahaifin mutum, ko ta haifi mahaifiyar mutum wato kakar mutum ta wajen uwa ke nan, ko ta wajen uba zuwa abinda ya yi sama.

      II.            ‘YA:- “yard a mutum ya Haifa ko ya haifi mahaifinta ko kuma mahaifiyarta, wato jikar mutum kenan ta wajen “da ko “ya izuwa abinda ya yi kasa.

    III.            ‘YAR UWA:- Abin nufi anan shine , wadda ta ke uwa “daya uba “daya, kokuma uwa “daya uba kowa da nasa, ko uba “daya uwa kowa da tasa. (‘kanwar mutum ko yayaryasa kenan).

    IV.            GWAGGWANKA:- wannan itace ‘yar uwar mahaifi( ma’ana yayarsa ko ‘kanwarsa),ko ‘yar uwar kakan mutum na wajen uwa ko na wajen uba da abinda ya yi sama.

      V.            YAKUMBONKA:-  wannan itace  yar uwar mahaifiya( ma’ana yarta ko “kanwarta). ko ‘yar uwar kakar mutum ta wajen uwa ko ta wajen uba da abinda ya yi sama.

    VI.            ‘YAR DAN UWANKA:- wannan itace ‘yar  yayanka(wanka) ko kaninka wanda kuke uwa “daya uba “daya ko uwa daya uba kowa da nasa, ko uba “daya uwa kowa da tasa.

  VII.            ‘YAR ‘YAR UWARKA:- abin nufi shi ne  ‘yar ya ko kanwar mutum wadda suke uwa “daya uba “daya, kokuma uwa “daya uba kowa da nasa, ko uba “daya uwa kowa da tasa.

Wadannan sune kashi bakwai na matayen da aka haramta aurensu ga mutum,haranci na har abada ta hanyar dangantaka kamar yanda ya zo a cikin Alkurani, a cikin Suratun Nisa’I aya ta ashirin da uku(23).

b)      MATAN DA AKA HARAMTA AURENSU TA HANYAR SHAYARWA.

Wadanda aka haramta aurensu ta hanyar shayarwa su ma sun kasu kashi bakwa (7):-

        i.            BABARKA TA SHAYARWA:- ma’ana wacce ta shayar da mutum,ko kakar mutum ta shayarwa        zuwa abinda ya yi sama.

      ii.            YAR UWARKA TA SHAYARWA:-  Ma’ana wacce aka shayar da mutum tare da ita lokaci daya ko kuma lokuta  daban-daban. Matukar dai wadda ta shayar da ita, ita ta shayar da kai, haramun ne ka aure ta.

Wadannan sune haramcinsu ya tabbata a cikin AlKurani Mai Girma a cikin Suratul Nisa’I aya ta ashirin da uku (23).

    iii.            YARKA TA SHAYARWA:-  Abin nufi anan shine ,”yar da matar mutum ta shayar da ita, ta zama “yar mutum kenan ta shayarwa. Domin haka haramun ne ya aure ta.

     iv.            GWAGGWONKA TA SHAYARWA:- Abin nufi anan shine; Yar uwar mijin matar da ta shayar da mutum, ta zama gwaggwon mutum ta shayarwa. Domin haka ya zama haramun mutum ya aure ta.

       v.            YAKUMBONKA TA SHAYARWA:- ma’ana ‘yar uwar matar da ta shayar da mutum, ta zama yakumbon mutum kenan. Saboda haka haramun ne mutum ya aureta.

     vi.            ‘YAR ‘DAN UWANKA NA SHAYARWA:- wannan na  nufin ‘yar wanda aka shayar da mutum tare dashi ko jikarsa. To haramun ne ya aure ta.

   vii.            “YAR “YAR UWARKA TA SHAYARWA:- ma’ana yar wacce aka shayar da mutum tare da ita ko kuma jikarta itama haramun ne ya aureta.

Wadannan kuma haramcinsu ya tabbata ne  a Hadisin da Bukhari da Muslim su ka ruwaito shi. Wanda Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yake cewa: “ Shayarwa tana haramta abin da dangantaka take haramtawa”.

FADAKARWA

Malamai sun yi sabani a kan shayarwa da take haramta aure, amma zancen da ya fi inganci cikin zantuttukan malaman shine; haramcin baya tabbata sai in har yaron ya sha nonon sau biyar kuma ya shay a koshi ya saki . in an jima ko kuma wani lokaci na daban ya sake sha.sannan kuma ya zama lokacin ba zai iya cin wani abinci ya koshi ba sai nonon.

                Dadin dadawa , wannan haramcin ya takaita akansa  ne shi kadai da ya sha nonon. Baya hadawa da sauran danginsa ,kamar ‘kannensa ko yayyensa ko iyayensa. Su duk wannan haramcin bai shafesu ba.

WADANDA AKA HARAMTA AURENSU TA HANYAR SARAKUTA.

Matan da aka haramta su ta hanyar sarakuta su hudu ne(4):

                    i.            Mahaifiyar matar mutum ko kakarta: ta wajen uwa ce ko ta wajen uba da abinda ya yi sama, duk baya halatta mutum ya aure su.

                  ii.            Agolar mutum: abin nufi shine “yar matar mutum, wadda ta Haifa da wani mijin daban. Shin ta zo da ita gidansa ko bata zo da ita ba? Duk dai haramcin daya ne. Amma idan mutum bai sadu da uwar ba, “yar ta halatta ya aure ta.

                iii.            Matar ‘Dan Cikin Mutum Ko matar Jikansa: Sawaun na wajen “da ne ko na wajen “ya duk dai bai halatta ya aure taba.

                 iv.            Matar mahaifin mutum: Wannan ya hada da wanda ya haifi mutum ko kakansa na wajen uwa ko na wajen uba duk dai bai halatta a mutum ya auri matansu ba.kamar yadda ya zo a cikin Suratun Nisa’i, aya ta (23).

Duk wadannan suna haramta ne da zarar an daura aure, sai dai agola wadda ita sai an sadu da mahaifiyarta haramcin yake tabbata.

Wadannan da aka lissafa a sama sune suka haramta mutum ya aure su haramci na har abada , koda kuwa daga shi saisu ya rage a duniya.

BANGARE NA 2 WADANDA AKA HARAMTA AURENSU ZUWA WANI LOKACI

Matan da aka haramta aurensu zuwa wani lokaci su goma (10) ne gasu kamar haka:

        i.            Hada tsakanin “yan uwa guda biyu: wadanda suke uba daya uba daya, ko kuma wadanda suke uba daya , uwa kowa da tasa. Ko kuma uwa daya uba kowa da nasa. Saboda ayar da ta zo a cikin suratun Nisa’I aya ta (23).

      ii.            Hada mace da “yar uwar mahaifinta ko “yar uwar mahifiyarta: Saboda manzon Allah Sallallahu alayhi wa sallama yace:” Kada a auri mace a hada ta da “yar uwar mahaifinta. Ko “yar uwar mahaifiyarta.(Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi).

    iii.            Matar da take da aure: ba za’a sake daura mata wani auren ba,har sai idan sun rabu da mijinta sannan ta yi idda. Saboda ayar da ta zo a cikin suratun Nisa’I. Aya ta (24).

     iv.            Mace mai idda (ta saki) ko takaba( ta mutuwar miji): su ma wadannan ba za’a daura musu aure ba har sai sun gama idda ko takaba kamar yadda ya zo a aya ta (235) a cikin suratul bakara.

       v.            Matar da aka sake ta saki uku: Ba za’a sake daura mata aure da mijin da ya sake ta ba, har sai idan tayi wani auren da wani mijin daban ya sadu da ita. Saboda abinda ya zo a cikin suraratul Bakara aya ta (230) da kuma hadisin da  wata mata ta zo wurin Manzon Allah Sallahu alaihi wa sallama ta fadama sa cewa tana son ta koma wajen tsohon mijinta da ya sake ta saki uku (3) amma miji na biyun bai sadu da ita ba.Sai manzon Allah sallahu alaihi wa sallama yace:” A’a sam ba za ta koma wajen na farkon ba . har sai na biyun ya sadu da ita kamar yadda na farkon ya sadu ita.(Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi).

     vi.            Mace ta biya: Baya halatta mutum ya auri mace ta biyar (5) alhalin yana da mata hudu har sai sun rabu da wata ko kuma wata ta mutu daga cikin matan sa . kamar yadda ya zo a cikin Suratun Nisa’I aya ta uku(3).

   vii.            Auren mazinaciya: Wasu daga cikin fakihai suna ganin baya halatta mutum ya auri mazinaciya har sai ta tuba ta yi istibrai, hujjarsu kuwa ita ce aya ta uku a cikin Suratun Nur.

 viii.            Auren baiwa ga “da: Mafi yawancin malamai sun ce baya halatta ga “da auri baiwa said a sharudda guda biyu(2).

 (a)  Tsoron fadawa zina

 (b)  rashin samun wadatar auren “yar kamar yadda aya ta ashirin da biyar(25) a cikin suratun Nisa’I ta nuna.

     ix.            Mai harama da aikin hajji:  Mafi yawancin fakihai sun tafi akan cewa aure baya halatta ga mai harama da hajji.Saboda manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yace kada mai harama da hajji ya aura ko ya aurar.(Muslim ne ya ruwaito).

       x.            Auren macen da bata bin addinin sama:  Ma’ana wacce ba musulma ba, ba bayahudiya ba, ba kirista. To baya halatta ga musulmi ya aure ta har sai ta musulunta ko ta shiga addinin yadudanci mko kiristanci. Saboda ayar da take cikin suratul Bakara aya ta (221).

Wadannan sune wadanda aka haramta auren su amma ba haramci na har abada ba.Ma’ana da zarar matsalolin da lissafa sun gushe, to ya halatta a aure su. Wallahu ta’ala a’alam.

Wa Sallallahu wa sallama ala Nabiyyina Muhammadin wa ala ahlihi wa sahbihi wa man tabiahum bi ihsanin ila yaumiddin.

LITTAFAN NAZARI SUNE:

1.       AZZAWAJ NA DR. MUHAMMAD IBRAHIM HAFANAWI.

2.       MINHAJUL MUSLIM NA SHEIKH ABUBAKAR AL-JAZAIRI.