Wednesday, 1 October 2014

Bayani kan Amosanin Ka

BAYANI AKAN AMOSANIN KA

Da farko dai ya kamata da kai da sauran masu karatu su fahimta cewa amosanin kai ba ciwo ba ne, wato ba cuta ba ce wadda wata kwayar cuta ke iya sa wa. Kamar matsalar saba ta sauran fatar jiki da wasu suke ganin kamar ciwo ne, amosani shi ma saba ce da kan faru a fatar kai wadda take karkashin suma. To idan tana barbashewa za a ga fari-fari na zuba kamar gari, musamman idan an zo taje kai ko kitso ko an zo yi wa mutum aski.

Bari mu fara dora bayanin a kan ita kanta fatar jiki tukuna, sa’annan ka gane cewa ba matsalar da za ka damu da ita ba ce sosai. Dama fatarmu canzawa take daga lokaci zuwa lokaci, kusan a ce wata-wata, dangane da irin abinci da muke ci da yanayin gari wato, zafi ko hunturu ko rani ko damin, da irin abin da muke shafa mata da kuma
yawan shekaru, wato tsufa ko kuruciya. Duka fatar kowa tana son abinci mai lafiya isasshe, mai dauke da sinadarin abinci mai gina jiki wato protein, wanda daga shi ne fatar kan sarrafa sinadaran keratin da collagen da elastin, wadanda su ne ginshikan ita kanta fatar. Sai kayan marmari masu dauke da bitaman masu sa fata sheki da
walwala. Akan iya samun wasu sinadaran a man da muke shafawa, wanda shi ma fata kan tsotse su idan an shafa. Don haka za ka ga fatar wadanda suka faye samun wadannan irin abinci da mai daban da ta wadanda ba su cika samun hakan ba kuma a iya cewa fatarsu ta fi lafiya kuma ta fi rashin nuna matsaloli.

Dangane da yanayi kuma wasu fatarsu ta fi son zafi, wasu kuma ta fi son yanayin danshi, a wasu kuma ta fi son yanayin sanyi. Babu fatar da ke son busasshen yanayi irin na hunturu. Misali, shi ya sa kusan kowa yakan samu matsalar fata a wannan lokaci, tun daga kaushi zuwa faso zuwa saba zuwa tsagewar lebe, zuwa waskane, har zuwa
amosanin ka.

To amma duk da cewa amosani ba ciwo ba ne, yana daya daga cikin abin da kan sa mutane da yawa damuwa musamman ma mata, don haka dole a saurari mai korafin wannan matsala.

Matsalar kan shafi kusan rabin mutanen duniya, ba bambanci a tsakanin jinsinan duniya. Wasu lokuta yakan sa kaikayi, mutum ya yi ta sosa kai, wanda wannan ma idan a cikin mutane ne sai
kunya ta fara kama shi. Idan ana sosawa kuma barbashin kan biyo kai a gan shi a saman suma ko a kafada.

A gaskiya babu abin da zai warkar da amosanin ka, tun da ba ciwo ba ne, sai dai abin da zai rage shi. Kamar yadda muka fada a baya, yanayin abinci da na wuri suna taimakawa, haka ma man wanke kai wadanda ga su nan birjik a kasuwanni da manyan shaguna ba sai a kyamis ba. Da mutum ya je ya ce a ba shi maganin shamfo na amosani za a ba shi mai kyau. Mutane da dama sun fi ganin amfanin wani wai shi head and shoulders fiye da sauran. A mafi yawan lokuta da an fara amfani da shi za a fara ganin saukin barbashewar suma da kuma kaikayi. Ba wai hana fatar marmashewa yake ba, a’a yakan ba fata laushin da ba za a san lokacin da ta canza ba, tunda dole ne duk bayan ’yan makonni sai ta sama ta marmashe ta karkashi ta tofo. Ka ga ke nan babu tabbas din idan ka daina amfani da shi
ba zai dawo ba.

Babu kanshin gaskiya game da cewa idan kurar kai ta mai amosani ta sauko ta shiga ido tana illa ga lafiyar idon.

BAYANI GAME DA CUTAR HAWAN JINI

Bayani akan CUTAR HAWAN JINI

Cutar Hawan jini ta yawaita matuka a cikin mutane harda al’umarmu ta jinsin bakaken fata, kuma tana jawo mana illoli masu yawa. Babban abin damuwa da bakin ciki shine, da yawa daga cikin al’umarmu basu da cikakken bayani game da wannan cuta; wasu kuma sun sani amma basa bada himma wajen neman magani.

MENENE CUTAR HAWAN JINI?
Ana cewa mutum ya kamu da wannan cuta ne idan an auna shi da na’urar awon karfin bugun jini (wato spygmomanometer) wadda ta nuna awon jininsa ya kai, ko ya wuce, dari da arba’in bisa casa’in (wato > 140/90mmHg) kuma awon ya dauwama a haka. Sai dai wannan adadi da aka ambata yana sabawa saboda bambancin shekaru, jinsi (wato namiji ko mace), halin da mutum yake ciki, da sauransu. A takaice dai, sai
an je asibiti za’a iya tabbatarma mutum ko yana da cutar ko baya da ita.

MENENE YAKE KAWO CUTAR?
Ta la’akari da yadda wanna cuta ke faruwa ga mutane, an raba wannan cuta zuwa gida biyu.

Kashi na farko - Sama da kashi casa’in (>90%) na mutane dake fama da wannan cuta, har yanzu ba’a san takamaiman dalilin da za’ace shi ya kawo masu wannan cuta ba sai dai akwai wasu abubuwa ko al’amura da aka alakanta ga faruwar wannan cuta ga wadannan mutane na kashin farko.
Wadannan abubuwan sun hada da:
· Yanayin kwayoyin halittar dan-adam, ma’ana ana iya gadon wannan cuta.
· Jinsin dan-adam (anfi samu a bakaken fata)
· Yawaita shan gishiri fiye da kima.
· Yawaita shan barasa (giya).
· Kibar jiki mai tsananin yawa.
· Rashin motsa jiki, da dai sauransu.

Kashi na biyu - A wannan bangare, an gano wasu cututtuka na musamman da suke kawo wannan cuta. Cututtukan sun hada da:
· Cututtukan dake shafar kodar mutum.
· Cututtukan dake shafar kwakwalwa.
· Wasu daga cikin magunguna na bature.
· Wasu cututtuka dake shafar jijiyoyin jini, da dai sauransu.

TA YAYA AKE GANE ALAMOMIN WANNAN CUTA?
Wasu daga cikin mutanen da suka kamu da wannan cuta basu da wasu alamomi da suke ji, wasu kuma sukan ji kamar yawan ciwon kai, fargabar zuciya, raguwar gani ko gani dishi-dishi. Wasu kuma suna zuwa asibiti ne da alamomi na illolin da cutar ta haifar musu (za’a yi bayani nan gaba). Wasu kuwa sai sunje asibiti dalilin wata cutar, wurin bincike sai a gano cewa suna da cutar hawan jini.
Karin bayani a nan shine, ba wai ance da mutum yaji yana fama da daya ko wasu daga cikin alamomin can na sama kawai sai yace ya kamu da cutar ba. Wannan kuskure ne. Mutum ya bari sai yaje an auna shi domin a tabbatar masa ko yana da cutar ko bashi da ita, domin tabbatacciyar hanyar sanin mutum ya kamu da cutar hawan jini ita ce ta auna jinin da na’urar asibiti.

ILLOLIN CUTAR HAWAN JINI.
Wannan matsaloli zasu iya faruwa ga wanda bai dade da kamuwa da cutar hawan jini ba ko kuma ga wanda ya dade da ita. Sun kunshi:
· Ciwon koda wanda zai iya jawowa ta daina aiki.
· Raguwar gani ko makancewar ido.
· Ciwon shanyewar wani bangare na jiki kamar rabin jiki (wato Paralysis).
· Ciwon zuciya, da dai sauransu.

Sai dai abinda ya kamata a fahimta game da wadannan matsaloli shine, ba cutar hawan jini kawai ke kawo suba. Za’a iya samun su ta wasu cututtuka kamar ciwon suga (wato Diabetes Mellitus) da sauransu. Wadannan illoli sun fi faruwa ga mutanen da suke da wannan cutar kuma basa shan magani ko kuma basa sha kamar yadda likita ya umarta.

MAGANIN CUTAR HAWAN JINI.
Akwai magunguna kala-kala da ake bayarwa ga masu wannan cuta. Suna yin amfani ne wajen tabbatar da daidaitar awon jini na mutum ta yadda ba zai yi yawa har ya kai ga samar da wadancan illoli da muka ambata ba. Wadannan magunguna za’a same su idan anje asibiti wajen likita.
Haka kuma kula da wadannan abubuwa da zamu zana wadanda ke da alaka da wannan cuta suna taimakawa matuka wajen kiyaye kai daga samun wannan cuta ko rage matsalolinta ga wadanda suke da cutar. Abubuwan sune:
· Barin shan barasa.
· Rage yawaita shan gishiri a abinci.
· Motsa jiki akai-akai.
· Rage kiba mai tsanani, ta hanyar rage yawaita cin abinci fiye da kima, rage cin man kitse, motsa jiki da sauransu.
· Yawaita cin kayan lambu da ababen marmari kamar su lemo, yalo, karas, alaiyahu, zogale, rama, da danginsu.

KAMMALAWA DA SHAWARWARI.
Tunda mun fahimci wani abu daga wannan cuta, kamar abubuwan da aka alakanta ta da su, matsalolin da take jawowa da sauransu, to ya kamata mu tashi haikan, mu nemi kariya daga gareta kamar yadda Allah (SWT) da ManzonSa suka umurta, ta kiyaye abubuwan da ke iya jawota.
Ba karamin kuskure neba ga mai wannan cuta ya ki shan magani, wato yace ya warke, domin ba shi jin alamomin ta. A yanzu babu wani magani da ke warkar da ita gaba daya har abada, sai dai a sami saukin da zai bada dammar rayuwa kamar yadda mai Lafiya yake yi. Tabbas, mun yi imani da bayanin Annabi Muhammadu (SAW) inda yake cewa “kowace cuta tana da magani”, amma muna fata Allah cikin rahamarSa zai fahimtar da likitoci maganin da zai warkar da ita nan gaba. Saboda haka sai a dauki wannan cuta a matsayin kaddara daga Allah, a kuma nemi lada daga wajenSa, a cigaba da shan magani domin a samu
rayuwa cikin kwanciyar hankali kamar kowa.
Kada mutum ya tsaya a zuwa kemis kawai ya ki zuwa asibiti. Illar wannan shine, za’a iya bada maganin da bai dace da mutum ba, ko kuma wanda zai iya kawo masa babbar matsala ga jiki.
A kuma lura, kada a tsaya a yi ta shan magunguna na gargajiya, a ki zuwa asibiti domin wadannan magunguna basu da tabbas, kuma za su iya taimakawa wajen kawo matsaloli da zasu shafi koda, hanta da sauran sassa na jiki.
A karshe ina tunatar damu game da fadin Allah Madaukakin Sarki a cikin surar bakara “…kada ku jefa kawunanku cikin halaka…”, wato mutum kiri- kiri ya zauna ya bari ciwo yayi masa illa ya ki shan magani, karshe a zo ayi ta wahala da jidali akan zuwa asibiti, sabanin inda mutum ya tashi tunda farko ya nemi magani. Muna yin addu’a duk wadanda basu da Lafiya, Allah Ya basu sauki. Masu Lafiya, Allah Ya kara kiyaye su, Amin summa Amin.