Thursday, 6 October 2016

Azumin Tasua Da Ashura

AZUMIN TASUA DA ASHURA

Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Mafificin azumi bayan azumin Ramadana shine azumin watan Allah mai alfarma Almuharram.”  Ya cigaba da cewa mafificiyar sallah bayan sallar farilla ita ce sallar nafila cikin dare.[Muslim] 

Sheikh Usaymin ya ce, “Azumin watan Muharram wanda ya ke bayan Zulhajj wanda Sahabi Umar ya sa shi a farkon shekara ta musulunci, ya ce “wannan azumin shine mafifici bayan azumin Ramadan”.[ZadulMustaqani]

Da  a farkon musulunci azumin Tasu’a wajibi ne amma daga baya ya koma ba wajibi ba. Bayan an wajabta azumin Ramadana sai ya zama wanda ya so ya yi wanda bai yi ba bu laifi a gare shi.[Nisa'i]

Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Azumin Tasua yana kankare zunubin shekara.”[Muslim 1162]
Wata ruwayar manzon Allah umurni ya bayar da a yi azumin Tasua.”[Sahih Tirmizi]

Asalin Azumin Tasu'a manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya zo garin Madina ya taras da Yahudawa suna azumi ranar goma ga watan Muharram, da ya tambaye su dalilin yin azumin  sai suka ce a ranar ne Allah ya tserar da  Annabi Musa daga Fir’auna da rudunarsa. Sai manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “mu ne muka fiku cancanta ga Annabi Musa sai ya azumci wannan rana ya kuma umurci al’umma da su azumci wannan rana ta goma ga watan Muharram, kuma da ma kureshewa suna girmama wannan ranar.[Majmu'ul Fatawa 25/310-311]

Ranar goma ga watan Muharram ce Allah ya tserar  da Annabi musa  daga sharrin Fir’auna, kuma a dai goma ga watan ne Allah ya tserar da Annabi Nuhu da jama,arsa daga ruwan dufana sai su ka azumce ta saboda godiya ga Allah. [Fatahul Bari]

Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya azumci, azumin Ashura ya ce badi in Allah ya kai mu zan azumci Tasua wato tara ga watan Muharram. [Sharhu Muslim]

Yahudawa sun dauki ranar Ashura ranar farin ciki manzon Allah sallallahu alayhi wa,alihi wasallam ya ce “Ku kuma musulmai ku saba mu su ku yi azumi a wannan ranar.[Majma'ul Fatawa]

Ibn Abbas ya kasance yana yin azumin Tasu’a da Ashura ko yana cikin halin tafiya ne, sunnah ce yin azumin Tasu’a kamar yadda azumin Ashura yake Imamu Shafi,i da Ahmad bn Hambal sun kasance suna yin Azumin Tasu'a da Ashura  domin su saba wa Yahudawa su Yahudu goma ga muharram kawai suke yi basa yin tara, don haka ana bukatar ka da kayi Tasu'a da Ashura domin ka saba ma Yahudu. [Sharhu Muslim]

Ibn Taymiyyah ya ce, “sunnah ce mustahabbiya yin azuminTasu’a da Ashura ajere, yin guda biyun shine bin umurni Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam.[Majma'ul Fatawa]

Sheikh Usaymin ya ce yana da matukar mahimmanci yin azumin Tasu’a da Ashura wato azumin tara da goma ga watan muharram ya ce a karfafi  jama’a da su azumci wadannan ranaku, domin a wannan rana ce Allah Ya halaka Fir’auna Ya tserar da Annabi Musa. Usaymin ya qara da cewa wasu malaman ma suna ganin makaruhi ne  yin azumi daya ka bar daya suka ce idan ka yi Tasua ba, ka yi Ashura ba ko kayi Ashura ka qi yin Tasu’a baza ka sami cikakkun lada ba.[Sharhu Muntani'i]

Yin azumin Tasu’a da Ashura shi ne ya tabbata  amma yin azumin watan Muharram  baki dayansa bai tabbata ba ko yin wata sallah ta daban a ranar Ashura bai tabbata ba.[Irwa'ul Ghalil]