Wednesday, 21 June 2017

ALAMOMIN TASHIN ALKIYAMA

ALAMOMIN TASHIN AL-QIYAMA GUDA 138

Alqiyamah ta kusanto, ga wa su daga cikin Alamomin ta, wasu sun faru, wasu suna faruwa, wasu za su faru nan gaba.

1. Aiko Annabi (sallallahu-alaihi-wasallam) {ranar litinin, 21/Ramadan/0013bh daidai da 10/August/610m} yana shekara
Arba’in 40 da wata shida 6 da kwana goma sha biyu 12 lissafin wata/ shekara talatin da tara 39 wata uku 3 da kwana ishirin 20
2. Wafatin Manzon Allah (sallallahu-alaihi-wasallam) ranar litinin
12/rabi’ul-Auwal/11ah yana da shekara sittin da uku da kwana hu’du
3. Tsagewar wata
4. ‘Karewar Sahabbai
5. Bu’de Baitil-Maqdis
6. ‘Barkewar Annoba;- mai kama da ciwon dabbobi
7. Bayyanar fitintunu masu yawa
8. Bayyanar tashoshin tauraron ‘Dan Adam
9. Yaqin Siffaini
10. Bayyanar khawarij
11. Masu da’awar Annabta ta qarya
12. Yalwatar Arzi’ki;- Arzi’ki zai yalwata
13. Bayyanar wuta a Hijaz, dutse mai aman wuta
14. Ya’ki da turkawa
15. Bayyanar Azzalumai masu dukan babu dalili
16. Yawan zubar da jini;- kashe-kashe
17. ‘Dauke Amana;- ma su Amana za suyi ‘karanci
18. Koyi da Yahudu da Nasara
19. Baiwa za ta haifi uwargijiyar ta
20. Bayyanar masu shiga tsirara-tsirara (ba sa shiga ta addini)
21. Matsiya ta, Marasa takalma masu kiwon awaki, za su yi yin dogayen gine-gine
22. Yin Sallama ga wanda aka sani kawai;- mutane za su daina yi
wa mutum Sallama sai sun san shi
23. Ya’duwar kasuwanci;- ko ina zai zama kasuwa
24. Mata za suyi tarayya da mazan su a kasuwanci
25. Wasu tsirarun ‘yan kasuwa za su mamaye kasuwanci;- ya
zama ba ayi da kai sai da yardar su
26. Shaidar Zur
27. ‘Boye shaidar gaskiya
28. Yawan Rowa;- mutane za su zama marowata
29. Yanke zumunta
30. Munana maqotaka
31. Ya’duwar laifuffuka
32. Bayyanar jahilci
33. Amincewa maha’inci, da tuhumar mai Amana
34. Mutuwar Mutanen ‘kwarai da Ya’duwar lalatattu
35. Yaki Halal Yaki Haram
36. Rubda ciki akan Baitil-Mali (Asusun-gwamnati)
37. Mayar da dukiyar Amana ganimah
38. Rashin fitar da Zakkah da da’din rai;- mutum ya ga zakka kamar Asara Ce yayi
39. Yin Karatu dan Neman Abun duniya
40. Yi wa mata biyayya da sa’bawa Uwa
41. Fifita Abokai/’Kawaye akan iyaye
42. Hayaniya a masallatai
43. Mafi yawan shuwagabannin Al’ummah za su zama fasiqai
44. ‘Kas’kantattu za su zama manyan gari
45. Girmama mutum don tsoron sharrin sa
46. Za a halatta Zina
47. Halatta Alhariri ga Maza (sa Alhariri ga maza haramun ne,amma za ayi zamanin da za a halatta shi
48. Ya’duwar Kayan maye
49. Ka’de ka’de da raye-raye za su mamaye Al’ummah
50. Masifa da Bala’i za su yi yawa Har mutum ya dinga fatan mutuwa
51. Wani Zamani da mutum zai kwana Mumini ya wuni kafiri;-
saboda mafi yawan maganganu da aiyuka  ba sa kan Shari’ah
52. ‘Kawata Masallatai da yin gasar Hakan (kaji ana Masallacin mu yafi naku kyau)
53. ‘Kawata gidaje da yi musu kwalliya
54. Yawan Saukar Kwarankwatsa da Aradu
55. Yawan Rubuce-Rubuce;- Ya’duwar Rubutuce-Rubuce marasa amfani (jaridu da mujallu, da littafai da internet) ba a tunanin
amfanin rubutun kawai da an rubuta
56. Wanda suka ‘kware a ro’ko da ziga, su suka fi samun ku’di
57. Za shagala da karanta wasu abubuwa a bar Al’qur’ani
58. ‘Karancin Malaman fi’khu da yawan Gardawa
59. Neman Ilimi a wajen ‘kananan mutane;- ‘karamin Mutum
wanda ba ya aiki da ilimin sa
60. Yawan mutuwar ba-zata
61. Shugabancin Wawaye (kuma suna ganin kan su wayaiyu)
62. Lokaci zai dinga sauri
63. Banzaye za su mamaye kafafan ya’da labarai;- Mutumin da ba kowa ba, kuma bai zan komai ba, zai dinga magana kan
abubuwan da suka shafi Al’ummah
64. Ma’daukaki a duniya shine banza ‘dan banza;- kaga ana ta rububin wani wanda bai da amfanin komai saboda wani shirme
da yake Misali;- ‘Yan Bal da Mawa’ka
65. Mai da cikin masallatai Hanyoyi
66. Sadakin Aure zai yi tsada, sai kuma ya zo yai arha
67. Dawakai za su yi tsada sai kuma su zo su yi arha
68. Kasuwanci zai yi sau’ki (ta yadda zaka sai Abu ko ka sayar daga ‘dakin ka, ba tare da ka je ko ina ba) Misali;- yanar gizo
69. Kafiran duniya za su yi taron dangi akan musulmi
70. Mutane za su dinga gudun limanci a cikin Sallah (saboda ba cikakken Albashi)
71. Aukuwar Mafarkin Mumini (in Mumini yai mafarki sai Abu ya faru
72.Yawan ‘karaya
73. yawan gaba
74. Girgizar ‘kasa
75. Yawan Mata
76. ‘Karancin Maza
77. Aikata Sa’bo a fili
78. Mai da karatun Al’qur’ani hanyar Neman ku’di
79. ‘Kiba, mutane za su yi ta ‘kiba mai yawa
80. Bayyanar mutane masu yin shaida tun ba a tambaye su ba
81. Masu Bakance ba sa cikawa
82. Masu ‘karfi za su danne raunana
83.’Rashin Hukunci da Alqur’ani
84. Yawan rumawa da ‘karancin larabawa
85. Ya’duwar ku’di
86. ‘Kasa za ta fitar da taskokin ta
87. Za a dinga shafe halittar wasu mutane suna komawa wata Halitta daban
88. Tsagewar ‘kasa, ta ha’diye mutane
89. Wasu ‘kwarangwazai, duwatsun da ba a San su ba za sudinga fa’dowa mutane aka
90. Yawan ambaliyar ruwa
91. Ruwan ‘bala’i;- wanda ba ya fidda shuka ko tsirrai
92.wata fitina za ta’barke tsakanin larabawa Har ta kusa ‘karar da su
93. Bishiya za ta yi magana don taimakawa musulmi
94. Dutse zai magana don taimakawa musulmi
95. Ya’kin Musulmi da Yahudu
96. Kogin furat zai ‘kafe, a hango Dutsen Gwal a ciki
97. Zamanin da za a yiwa masu addini kallon ba wayayyu ba
98. ‘Kasashen larabawa za su samu ci-gaba mai yawa
99.Bayyanar wata Babbar fitina da zata shafi kowa
100. Bayyanar bakar fitina gama gari sai ta shafi kowa.
101 masifu za suyi yawa birni da kauye
102 Wani zamani zezo sujjada daya tafi duniya da abinda yake cikin ta, saboda karancin masu ibada,
103 Rigima akan ganin wata, saboda wata zai kumbura, ya dinka fitowa babba
104 za a dinka kaura ana komawa yankin Sham. Syria,
105 Yakin duniya tsakanin musulmi da Rumawa (Turawa)
106 Zaa bude yankin Qusdunsuniyya, karo na biyu, bayan na zamanin daular Usmaniyya
107 Zaa dena rabon gado, ( masu karfi su cinye na kanana)
108 Zaa dena farin ciki da samun ganima (saboda wadata tayi yawa)
109 Zaa koma amfani da makamai na gargajiya, saboda na zamani zasu dena amfani,
110 Zaa raya baitul Maqdis, bayan karbo shi daga yahudawa
111 Mutane zasu kauracewa Madina, idan shagala tayi yawa
112 Madina zata kore ashararai daga cikin ta, babu mai jin dadin zaman madina sai mumini
113 Duwatsu zasu gushe daga gurin su, saboda gine-gine na ci gaba.
114 Wani mutum zai fito daga yankin Qahdan na larabawa kuma mutane zasu bishi,
115 Bayyanar wani mutum mai suna Jah,Jah
116 Dabbobin dawa zasuyi magana irin ta mutane, kamar zaki da kura da makaman tansu
117 Tsumagiya ma zatayi magana,( Bulala)
118 Hancin takalmi zaiyi magana,
119 Jikin mutum zaiyi magana (kamar cinyarsa) ya bashi labarin abin da iyalansa suke aikayawa idan bayanan
120 Alkiyama baza ta tashiba sai anyi watsi da musulunci, ba karatu ba aiki.
121 Alkiyama baza ta tashi ba sai an dauke Alkur’ani mai girma
daga cikin takardu, da kirjin mahaddata,
122 Wata bataliyar mayaka zasu tunkari macca da niyar yaki, amma kasa zata hadiye su a hanya
123 Zaa kauracewa zuwa aikin hajji
124 Kabilar kuraishawa zasuyi kadan a duniya
125 Rushe kaabah ta hannun wani mutum daga yankin Habasha
126 Wata iska mai dadi zata dinga dauke ran muminai idan musifa tayi yawa
127 Zaa dinka yin ginai- ginai masu tsawo a Macca
128 Wasu tsinannun mutane, zasu dinka laantar magabata, (Masu zagin sahabbai)
129 Zaa sami kayan hawa na zamani,
130 Bayyanar Ma’hadi,

Manyan alamomi na tashin alkiyama wadanda suke kusa daf da tashin alkiyamaSune:
131: Bayyanar Dujal (babban balain da ake jira)
132: Saukowar Annabi Isah
133: Fitowar Yajuj da Majuj
134 Girgizar kasa (manya manya sau uku a duniya)
135: Hayaki da zai rufe duniya baki daya
136: Bayyanar wata dabba (am fadi kamaninta a hadisai)
137: Rana zata fito ta yamma
138: Wata wuta zata fito ta kora mutane, zuwa filin Mahshar.

ALLAH YA KAREMU DAGA MASIFUN DA SUKE CIKIN WANNAN RANA, YA ALLAH KA KARE MANA IMANINMU........Ameen