FALALAR GOMAN FARKON ZUL-HIJJA
Daga Auwal Zakari Ayagi Chairman Al'azmiyyah Islamic Foundation Kano
07038775781,08023615685, 08090987314, E-mail auwaizakari@gmail.com
Da sunan Allah mai yawan Rahama, Mai yawan jin kai, tsira da Aminci su kara tabbata ga fiyayyan halitta Annabin rahama, tare da saabbansa da iyalan gidansa, da duk masu binsa da kyautatawa har zuwa ranar Alkiyama.
Bayan haka sabo da ganin kusantowar watan da yake kunshe da manya manyan falaloli , da darajoji a kwanaki goma na farkonsa wato kwanaki Goman farkon watal zul hijja, naga yadace in dan dada tinatar da yanuwa almajirai mahimmanci, tare da girma da Allah ya yiwa ranakun tare da irin abubuwan daya dace mu aikata a ranakun don kara neman kusanci da Allah Subhanahu Wataala.
Dafan Allah ya amfanar damu, abin da aka gain na kuskure Allah ya yafe.
WADANNENE RANAKUN FARKON ZUL HIJJA
Ubangiji madaukakin sarki yana fada cikin alkur,ani mai girma cikin suratul fajar aya ta 1-3 INA RANSTUWA DA ALFIJIR, DA RANAKU GOMA, DA SHAF,I DA WUTIRI. Manyan malamai sunyi maganganu masu yawa akan wannan ayoyi, amma Abdullahi ibn Abbas Allah yakara yarda agareshi yace; Abin da Allah yake nufi da Alfijir shine sallar Asubahi, Darare goma kuwa sune goman zulhijjah, shafa,i kuma shine halitta, Wutiri kuma shine Allah Allah ya ambace su sune darare goma, domin ranaku ne Tara da dare goma, saboda girman da wadannan ranaku suke da shi har Allah{SWT}yayi ranstuwa dasu cikin littattafansa mai girma.
DAUKAKA DA DARAJOJIN RANAKU GOMA NA ZULHIJJA
Waddannan ranaku suna da matukar girma da daukaka domin an karbo Hadisi daga dan Abbas Allah ya kara yarda a gareshi, cewa shi ya ce Acikin goman farko na zulhajji Allah ya karbi tuban Annabi Adam (A.S). Cikinsa ne Annabi Ibrahim ya gina Kaaba, acikinsune Allah yayi munajati da Annabi Musa, harila yau acki aka saukarwa da Annabi Dawud gafara, aciki ranar Tarwiyya take, da ranar Arfat, da ranar layya, da kuma ranar Hajji.
An karbo daga Abi Said Alhudri (RTA) daga Manzon Allah (SAW) yace; “Sugaban watanni watan Ramadan, mafi girmansu kuma Zulhijja.
FALALAR WATAN ZULHIJJA
An karbo daga Jabir Allah ya kara yarda agareshi, daga Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam yace; Mafifitan Ranakun duniya Ranaku na Zuihijja Ankarbo daga Addau dan Rabia yace; Naji Sayyada Aisha (RTA) tace; Yakasance lokacin Annbi (SAW) wani mutum ya kasance idan watan Zulhijja ya kama sai ya wayigari yana Azumi sai wannan labari yariski Manzon Allah (SAW), Sai akazowa Annabi Alaihissalam da shi, ai yace dashi meyasa kake Azumtar wadannan ranaku?sai yace ya Maaikin Allah sun kasance ranakune na haduwa,kumaranakune na aikin hajji, sai nake so ubangiji ya hadani a cikin Adduoin da ake yi a ciki, sai Annabi Alaihissalam yaceda shi, ya tabbata ageka ko wacce rana da kai Azumikamar kayanta wuyaye dari ne,kayi hadaya da taguwa dai, kabayar da dawakai dari don daukaka Addinin Allah, amma kuma in ka Azumci ranar Arfa kamar ka yenta wuyaye dubu biyu ne, kayi hadaya da taguwa dubu biyu, kabaya da dawakai dubu biyu don Allah, kuma kamar ka Azumci shekarar da ta gabata ne da kuma shekara tagaba
Buhari da Muslim sn rawaito hadisi cewa Manzon Allah Alaihissalam yace; Babu wasu wadansu ranaku da Allah Yafi son Alheri acikinsu fiye da wadannan ranaku, ina nufin ranakun fakon Zulhijja, sai akace ya maaikin Allah ko jihadi ne? sai yace ko da jihadi ne, sai dai mutumin day a fita kansa da dukiyarsa, sannan bai dawo da komai ba
FALALAR AZUMTAR RANAR ARFA
Muslim ya rawaito cewa Manzon Allah Alaihissalam yace Azmin ranar Arfa yana kankare zunuban shekaru biyu da suka gabata da shekara ta gaba. An rawaito da sashin matan Manzon Allah cewa Manzo Alaihissalam ya kasance yana azumtar tara na zulhijja (Abu Dawud)
Azumtar wadannan ranaku yana da matukar mahimmanci kamar yadda mukaji daga bakin shugaba Alaihissalam musamman ranar Tara ga Zulhijja wato ranar ARFA kamar yanda yazo a hadisin Buhari da muslim daya gabata.
AIKATA AYYUKAN ALHERI
Haka zalika anaso a yawaita sauran ayyukan alheri, domin Allah ya matukar son ayyukan alheri a ranakun, kamar yawaita tasbihi, da salatin Annabi, sada zumunci, yawaita nafil fili, da istigifari, da karatun Alkurani, kyautatawa iyali, ziyarar marasa lafiya, farantawa iyaye, da kara biyayya agaresu , tufatar da muminai da ciyar dasu ko shayar dasu, musamman masu tsananin bukata, jinkan marayu, musamman shafa kansu da kyautatamusu, da sauran ayyukan alhei, amma ubangiji yafi son a yawaita kabarbari a wadannan ranaku musamman a salloli goma sha biyar, daga sallar azahar taranar zuwa sallar asubahi ta ranar uku ga sallah, domin Abdullah Ibn Abbas ya kasance yana bin kasuwa yana kabarbari don tunawa mutane kada su shagala.