Tarihin Sayyidi Sheikh Abdulqadir Jilani, Mai Dariqar Qadiriyyah.
Daga Musbahu Bulyaminu Alqadiry
Lakabi da kuma Mahaifa
Ana yi mashi kinaya da Abu Muhammad da Muhyiddeen da kuma Gausul aazam da Alhasani da Alhusaini, da Jilani, ko gilani, ko geelaniy ko Algilani duka ana fada, Shine Muassasin Dariqar Qadiriyyah, An haife shi a cikin watan Ramadan a shekara ta 470 bayan hijira (1077-78 miladiyya) a yankin Farisa na Jilana (Iran), kudu da Tekun Caspian, Gudun mawar da ya bada ga sufanci da kuma addini da shuhurar shi har ake kiran shi da gausul aazam
*Iyali da Nasaba*
Daga cikin laqubban shi ana kiran shi da Alhasani Wal Husain, Sabida yana da nasaba da Annabi S'A'W ta wajen Mahaifin shi Sheikh Abu Saleh Musa (R,A)
Sheikh Abu Saleh Musa (R,A) wanda jikan Annabi (S'A'W) ne Ta Bangaren Sayyidina Hasan (R,A) Sheikh Abu Saleh Mutum ne mai tsoron Allah da qasqantar da kai da kuma hikimomi da dabarun tsara jihadi wannan dalilin ne ma yasa ake yi mashi laqabi da "Jangi doost"
Sannan kuma Sheikh Abdulqadir Jilani (R,A) Yana da dangantaka da Annabi (S'A'W) ta bangaren Mahaifiyar shi Sayyida Fatima (Ummul-Khair) (R,A) Wacca ita kuma Jikar Sayyidina Husaini ce, itama Macece Mai Tsoron Allah wanda hakan ne yasanya mahaifin Shehu Abdulqadir Abu Saleh ya auri ita Ummul khair din, Al'amarin auren nasu akwai al,ajabi Matuqa
*Auren Sayyidi Abu Saleh (Mahaifin Sidi Abdulqadir (R,A) da Sayyida Ummul-Khari (Mahaifiyar Sheikh Abdulqadir Jilani (R,A)*
Wata rana Abu Saleh Mahaifin Shehu Abdulqadir Jilani (R,A) yana tafiya gefen wata qorama ta ruwa sai yaga wani Apple (Tuffa) a gefen qoramar sai ya dauka yaci, bayan yaci se kuma ya shiga damuwa, ya fara tinanin cewa kada ace wannan apple na wani ne yaci wanda bai nemi izini ba kuma ba halal din shi bane sai ya tuna lokacin da kakan shi Annabi s,a,w "Sanda Annabi s,a,w yazo wucewa yaga wani dabino a kasa sai Annabi s,a,w yace badan yana jin tsoron kada ace dabinon sadaqa ne ba da ya dauka ya ci" nan take sai Abu Saleh Mahaifin Sheikh Abdulqadir Jilani (R,A) ya dimauce ya tafi neman mai wannan Apple, Yana ta shige da fice har ya iso wani lambu cike da Apple ya samu tabbacin cewa wannan apple da yaci daga wannan lambu yake se ya shiga ya tarar da mai wannan lambu mai suna Sayyidi Sheikh Abdullahi Sauma'e (R,A) sai Abu Saleh yaje ya nemi gafara wajen mai Wannan Apple Sayyidi Abdullahi Sauma'i na cin Apple din shi da yayi bada izini ba, da Sheikh Sauma'e yaga cewa Sayyidi Abu Sale ba kamar gama garin mutane yake ba sai yace zai yafe ma sheikh Abu Saleh Amma a bisa sharadin zai kular mashi da lambun shi na zuwa wani lokaci, sayyidi Abu Saleh ya Amince da hakan ya cigaba da kula da wannan lambu, bayan wani lokaci bayan Abu Saleh ya gama aikin da aka bashi sai Sheikh Abdullahi Sauma'e ya Sallame shi sannan ya sake kafa mashi wani sharadin cewa zai auri mashi diyar shi, Sheikh Sauma'e yace amma diyar tashi kurma ce Makauniya ce kuma gurguwa ce ba hannu ba qafafu, cikin girmamawa da biyayya Sayyidi Abu Saleh ya karbi wannan umarni na auren yar Sheikh Abdullahi Sauma'eh
A daren da sheikh Abu Saleh zai hadu da Amaryar shi a karo na farko yana shiga daki sai yaga wata irin kyakkyawar mata mai cikar kyawu kuma lafiyayyah da idon ta da hannayen ta da kafafun ta, sai ya fara tinanin ko dimuwa yayi ya shiga dakin da bashi bane, sai ga sheikh Abdullahi Sauma'e yace mashi maganar da ya fada mashi ta farko haka take wannan ce matar da nace zan aura ma yace nace maka makauniya ce sabida bata ganin kowa sai muharramin ta, nace maka kurma ce sabida bata jin duk wani abu da shari,a ta hana, sannan da nacema gurguwa ce ga hannu da qafafuwa ina nufin bata taba komai sai abinda shari,a tace ta taba hakanan bata taba fita daga gida ba a bisa sabama shari,a komai a bisa shari,a take yin shi, Wannan Shine auren Mahaifan Shehu Abdulqadir
A bisa wannan Martabar da darajar ne Mahaifin Shehu Abdulqadir Abu Saleh Alhasani (R,A) da Mahaifiyar shi Sayyida Ummul-khair Fatima Alhusain Sukayi aure, Wadannan Waliyyan Allahn Sune Mahaifan Sidi Abdulqadir Jilani Wanda ta tsatson sune aka sami wannan babban bawa Mai tsoron Allah mai matsayai da yawa Sarkin Waliyyai Maabocin Sirrika na boye da zahiri mai horo abi Allah mai hani da sabo, fitilar zamanai ginshiqin al,umma tauraron wulaya qashin bayan sufanci Wato Sayyidi Abdulqadir jilani (R,A)
Sayyidi Abdullahi Sauma'e Shine Kakan Shehu Abdukqadir na wajen Mahaifiya ya kasance Mutum ne mai tsoron Allah mai qasqantar da kai da kamewa mai tausayi da taimako
Sayyida Aisha Azzahida itace Gwaggon Shehu Abdulqadir baiwar Allah ce ta gari mai yawan tsoron Allah da haquri da ibada duka rayuwar ta ta tafi ne a ambaton Allah da ibada
*Busharorin da Akayi dashi Kafin Haihuwar shi*
(1) Sayyidu da'ifah Sayyidi Sheikh Junaidul Baghdadi (R,A) Ya Rayu Shekara dari biyu kafin Haihuwar Shehu Abdulqadir amma ya bada labarin zuwan shehu Abdulqadir fa abinda yake cewa
"Wata rana Junaidul baghdadi yana cikin halwa sai almajiran shi sukaji yana cewa "duga dugan shi na saman wuya na duga dugan shi na saman wuya na" bayan ya fito sai almajiran shi suke tambayar shi game da wadannan kalmomi da sukaji yana ta maimaitawa, se yace masu, haqiqa an sanar dani cewa akwai wani babban waliyyi da zaizo a qarshen qarni na biyar sunan shi zai zama Abdulqadir, inkiyar ahi itace Muhyiddeen, za,a haife shi a jilana sannan zai koma baghdad, Wata rana a bisa umarnin Ubangiji zaice Duga dugan shi na sama wuyayen kowane waliyyi, Junaid Yace ina cikin halwa shine shauqi ya jani na fadi wadancan kalmomi.
(2) Imam Hassan Askari Kafin Yayi Wafati ya bada Alkyabbar shi ga Imam Maaruful Kharki (R,A) sannan yace Shima Maaruful Kharki ya ba shehu Abdulqadir Jilani Ita, sheikh maaruful karki da yazo wafati sai ya bada alkyabbar ga junaidul baghdadi yace shima ya bada ta ga sheikh Abdulqadir jilani shima sheikh Junaidu da yazo wafati sai ya bada wannan alkyabba ga shehu Danuri (R,A) daga nan akayi ta bada wannan alkyabba har tazo kan shehu Abduqadir (R,A) a shekara ta 497 miladiyyah
(3) Sheikh Abubakar Bin Hawwar (R,A)
Shima ya rayu kafin Zuwan Shehu Abdulqadir Jilani kuma yana cikin manyan malaman baghdad, wata rana yana zaune a majalisin shi yana bada karatu sai akaji yana cewa akwai kudubai (Manyan Waliyyai) guda bakwai a baghdad sune kamar haka 1 Sheikh Maaruful kharki r,a 2 Sheikh Imam Ahmad bin hambal 3 Sheikh Bishiril hafi 4 Sheikh Mansur bn Amaar r,a 5 sheikh Junaidul bagdadi 6 Sheikh Sahl Altastari 7 Abdulqadir Jilani (R,A) sai cikin daliban shi wani yace munsan sauran mutanen guda 6 amma na cikob shiddan bamu san shi ba, sai sheikh Abubakar r,a yace Abdulqadir babban Waliyyin Allah ne da za,a haifa a qarshen qarni na shida kuma ba cikin garuruwan larabawa ba kuma zai koma bagdad da zama
(Bahjatul Asrar)
(4) Sheikh Khalil Balkhi (R,A) Babban Waliyin Allah ne ya rayu kafin haihuwar shehu Abdulqadir jilani (R,A) Wata rana yana zaune tare da daliban shi, sai yace wani babban Waliyyi zai bayyana a iraqi a qarshen qarni na 5 duniya zata haskaka da zuwan shi, zai zama gausin zamanin shi Halittun Allah zasuyi biyayya gare shi, shine sarkin dukkan waliyyan Allah
(Azkarul Abrar)
(5) Imam Muhammad bin Saeed Zanjani (R,A) ya kawo acikin littafin shi mai suna nuzhatul kawatir yace tun daga zamanin sheikh Abi Ali Hasan yasarajuwi (R,A) har zuwa zamanin shehu Abdulqadir (R,A) duk wani wali da akayi saida ya bada labarin zuwan Shehu Abdulqadir (R,A)
*Haihuwar Sheikh Abdulqadir Jilani (R,A)*
A Zance mafi inganci shine An haifi sheikh Abdulqadir jilani a wani waje da ake kira da neef, wanda wani yanki ne acikin jilana (Persia) a Mahamgar Imam Yaqoot Hamwi (R,A) an haifi Sheikh Abdulqadir Jilani (R,A) a wani waje da ake kira bashtir, masana tarihi dayawa sun tafi akan cewa da neef da bashtir duk guri daya ne mai suna daban daban tinda dai a jilana aka haife she kuma ance da neef din da bashtir din duk cikin jilana dinne, ana yima shehu Abdulqadir kinaya da Al-jilani sabida acan ne aka haife shi, shima da kanshi yana fada acikin qasidar shi ta gausiah yana cewa "Anal jilani Muhyideeni ismi"
Akwai maganganu guda biyu akan ranar haihuwar shehu Abdulqadir jilani (R,A)
Magana ta farko, ance anhaife shi ranar 1 ga watan ramadan a shekara ta 470 miladiyyah. Magana ta biyu kuma ance anhaife shi ne a dare na biyu acikin watan ramadan, yawancin malamai sunfi tafiya akan zance na biyu. Cewa a ranar ne aka haife shi Gausul aazam Wannan Haihuwa mai tarihi wadda aka shafe shekaru ana bada labarin ta tun kafin zuwan shi (R,A)
Abubuwan Al'ajabi da suka faru Awajen Haihuwar Sheikh Abdulqadir Jilani (R,A)
Lokacin haihuwar shi mahaifiyar shi ta kusa shekara 60 shekarun da mata basu fiye haihuwa ba, dalilin da yasa Shehu Abdulqadir ya zama ya samu sirrika da baye baye masu tarin yawa shine wata rana a daren miiraji Annabi s'a'w da zai hau kan buraqa ance wuyan shehu Abdulqadir ne ya taka a matsayin matakala, sawun kafar Annabi S'W'W yana nan ajikin wuayan shi har bayan wafatin shi, wannan ne dalilin shima ya zama babbar karama a gareshi domin duk wanda ya san shi yasan wannan tambari dake jikin shi.
A daren da aka haife shi ranar duka maza aka haifa a garin jilana, itama wannan karamar shi ce irin ta kakan shi Annabi S'A'W, anhaifi aqalla maza 1100 a daren kuma dukkan su sai da suka zama waliyyai
Kafin Haihuwar Shehu Abdulqadir Mahaifin shi Abu Saleh Yayi Mafarki da Annabi S'A'W Shugaba s,a,w Yace Mashi yakai dana Abu Saleh haqiqa Allah S,W,A ya azurta ka da da namiji wanda yake masoyi na kuma masoyin Ubangiji, matsayin shi acikin Waliyyai shine kamar matsayina acikin Annabawa. Ubangiji yayi ma iyayen shi bushara cewa zai zama sarkin Waliyyai kuma duk wanda suka muzanta shi zasu zama batattu, Labari ya karade gari cewa an haifi wani jariri wanda baya shan nono ko cin abinci da rana maana yana azumin watan ramadan, idan akayi hadari ko iska ko hazo a lokacin ramadan sai azo a tambaya aji shin Abdulqadir ya sha nono idan akace eh to se kowa yaci idan kuma akace a a to sai kowa ya miqe da axumi (R,A)
*Yarintar Sheikh Abdulqadir Jilani (R,A)*
Shehu Abdulqadir ba kamar sauran yara qanana bane, baiyi wasa irin na yarinta ba, kullun aikin shi shine ambaton Allah tin yana qarami sosai idan yaji yana so yaje ya hadu da abokan shi suyi wasan yara sai yaji wata murya tana cewa "taho gare ni ya kai maabocin daraja" da farko wannan murya tana razana shehu Abdulqadir idan yaji ta sai ya tafi wajen mahaifiyar shi ya zauna tare da ita, daga baya kuma ya saba da jin wannan murya har ta daina bashi tsoro, idan yaji wannan murya maimakon ya tafi wajen mahaifiyar shi se kawai ya tafi anbaton Allah
*Wafatin Mahaifin Sheikh Abdulqadir Jilani, Sheikh Abu Saleh Musa (R,A)*
Bayan Wafatin Sheikh Abu Saleh Mahaifin sheikh Abdulqadir Jilani (R,A) wanda ya rasu shehu Abdulqadir yana qarami sosai, sai kakan sheikh Abdulqadir Sheikh Abdullahi sauma'e ya ci gaba da tarbiyantar shi, ya ci gaba da kula dashi a bisa tarbiyyah mafi cikar kyau, ya dora shi a kan bautar Ubangiji da tarbiyya da hikima wanda dama shine ya hada auren mahaifan na sheikh Abdulqadir jilani (R,A)
*Farkon Shigar Sheikh Abdulqadir Makaranta*
Lokacin da shehu Abdulqadir ya kai shekara hudu sai mahaifiyar shi ta sanya shi makarantar cikin garin jilana haka yayi ta karatu har yakai wajen shekara goma, a lokacin ne sai shehu Abdulqadir ya fara ganin abubuwan al'ajabi duk sanda zai shiga makaranta sai yaga wani haske kamar qwayaye suna tafiya gaban shi suna cewa abada hanya ga waliyyin Allah
Sheikh Abdulrazak Aljilani dan shehu Abdulqadir ne na cikin shi, yana cewa antambayi shehu Abdulqadir a wani mataki ne ya fara ganin alamomin wulayar shi? Sai shehu Abdulqadir yace lokacin yana dan shekara 10 sanda wannan waqi,ar ta faru idan yazo makaranta yaji ana cewa abada hanya ga waliyyin Allah.
*Wafatin Sheikh Abdullahi Sauma'e Kakan Sheikh Abdulqadir na Wajen Mahaifiya*
Bayan Wafatin Sheikh Sauma'e Kakan Shehu Shehu Abdulqadir Wanda yake kula da tarbiyyar shi, sai nauyin shi ya koma kan mahaifiyar shi, mahaifiyar shi ta ci gaba da kula dashi bisa ilimantarwa fadakarwa sadaukarwa haquri da gaskiya da amana
*Tafiyar Sheikh Abdulqadir Jilani neman Ilimi Zuwa Baghdad*
Wata rana Shehu Abdulqadir yana tafiya wajen garin jilana lokacin yana dan qasa da shekara 18 sai yaga wata dabba a gaban shi yana binta a baya kawai sai yaji tana cewa ba don haka aka halicce ka ba kuma ba wannan ne aka umarce ka da kayi ba, sai shehu Abdulqadir ya koma gida ya fadama mahaifiyar shi abunda ya faru, nan take ya nemi izini domin tafiya baghdad, a lokacin mahaifiyar shi tana da shekaru wajen 80 lokacin da duk mahaifiya ke buqatar danta domin ya tallafa mata da ciyarwa da kula,, amma sabida neman yardar Ubangiji ita da kanta ta hada mashi kayayyakin shi tace ya tafi bagdad neman ilimi, tare da cewa kuma shine ke kula da ita a koda yaushe, ta zaunar dashi tayi mashi wasiyyah tayi mashi addu,o,i na musamman, a lokacin ana fama da yawan sace sace daga barayi acikin daji, amma duk da haka tace mashi komai zaiyi ta tabbatar da cewa yayi gaskiya aciki sannan tace mashi aifin shi ya bar masu dinari 80 shida dan uwan shi sayyidi Abu Ahmad Abdulkahi ta dauko dinari 40 ta qulle mashi ta qulle mashi su acikin riqar shi sannan ta sake yi mashi addu'a ta qara jaddada mashi cewa ya fadi gaskiya komai zai, yayi mata alqawali cewa zaiyi anfani da duk abunda ta fada mashi, nan take ta rugume shi tace jeka Allah ya tsare ka shine wanda zai taimake ka
Bayan sunyi bankwana ya tari ayari na zuwa baghdad ya bisu suka tafi, a nan ne daya daga cikin waqi,ar da duniya ta shaida ta faru, inda yan fashi suka tare su suka ce su kawo kudi bayan angama da kowa sai suka kalli shehu Abdulqadir wanda shine qarami duk cikin tawagar, cikin wasa da barkwanci sukace kai yaro kana da kudi sai yace eh ina da su sukace suna ina ya sa hannu aljihu ya fiddo wannan kudi ya basu, suka qirgaa sukaga dinari 40 sukace kai wani irin yaro ne kowa na boye kudin shi amma kai daga tambaya zaka fiddo, sai yace masu ai yayi ma mahaifiyar shi alqawali cewa komin rintsi bazai yi qarya ba zai fadi gaskiya, nan take yan fashin suka shiga mamaki har suka tuba wanda ance sune farkon Almajiran shehu Abdulqadir
*Shigar sheikh Abdulqadir Jilani garin baghdad*
Lokacin da shehu Ya shiga Bagadaza kusan babu sauran kudi a hannun shi sabida yanayin tsawon tafiya, duk guxirin ya qare a kan hanya, haka ya ci gaba da rayuwa cikin matsi da yunwa a garin baghdad, don haka ya fita wajen baghdad neman abinci na halal yana zuwa ya hadu da waliyyah da dama wanda suma duk abinda ya kawosu kenan, nan take ya juya ya koma bahgdad, yana tafiya ne ya hadu da wani bawan Allah daga jilana ya tambayi shehu Abdulqadir ko yasa wani yaro Abdulqadir daga jilana, yace mashi shine Abdulqadir bayan sun gaisa ya dauko wani dunqulen zinare ya bashi yace inji mahaifiyar shi, nan take shehu yaji dadi ya koma wajen waliyyan nan ya rabar masu da mafi yawa zinarennan sadaqa, haka yayi ta ciyar da mutane mabuqata
*Neman Ilimin Shehu Abdulqadir Jilani a Bagdaza*
Bayan Zuwan shi baghdad bai tsaya ba ya zarce neman makaranta har ya sami babbar makarantar nizamiyyah wanda ya samu manyan malamai kuma yayi ta maida hankali a fannin fiqhu da tafsir da sunnah da hadith da kuma arabic
Ya karanci ilimin fiqhun mazhabin hambaliyyah a qarqashin kulawar sheikh Abu Saeed Almakhzumi, Sannan ya karanci ilimin tafsir da hadith a wajen sheikh Abu ghalib Ahmad da Kuma Sheikh Abu Qasim Ali, sai ilimin larabci a wajen Sheikh Abu Zakariya Yahaya Tabrizi wanda shine shugaban nizamiyyah din.
*Qalubale da tsananin da Shehu Ya Shiga Awajen nemam ilimi a baghdad*
Haqiqa Shehu Abdulqadir ya hadu da jarabowoyi da qalubale da yawa a baghdad Shina Shehu Abdulqadir da kanshi yana fada cewa, wahalar da nasha a baghdad ba qarama bace, yace har takai ga cewa da zaa dora ma dutse ita da sai ya tarwatse, yana cewa idan tsanani ya same shi har yaji baya iya jurewa sai kawai ya kwanta a kan titi yana karana wadannan ayoyi na suratul Inshirah, aya ta 5 da ta 6
فَإِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا
إِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا
Sai yayi ta maimaitawa, yace idan yana karanta wannan ayoyi to yana samun nutsuwa da sauqi
Idan kuma aka tashi daga makaranta sai ya doshi cikin daji domin zikiri, zaiyi ta zikiri yana ambaton Allah har sai ya gaji, idan ya gaji sai ya tsaya ya huta kuma sai ya ci gaba kullun haka rayuwar take ba dare ba rana ba, ba zafi ba sanyi ba, ba ruwa ba iska ba. Idan yaji yunwa sai ya tafi gefen korama ya sami abinda zaici ko yayan itatuwa ko ganyeyyeki duk abinda ya samu sai ya ci, wata rana ansamu yunwa a baghdad mutane suna cin ganyaye da duk wani nau,in tsirrai, kowa yana fita neman abinci haka shima shehu yake fita neman abincin amma da yaje saiya dawo bai samo komai ba, sabida shi awajen shi bai halatta ba ace shi yaci abinci amma wani baici ba don haka da yazo zai dibi abu da yaga wani sai ya bar mashi shi ya diba kuma ya koma gida da yunwa sai da yayi kwanki bai ci abinci ba, Wata rana yana tafiya cikin wata kasuwa sabida tsananin jin yunwa har takai ga ya yanke jiki ya fadi kas, ya samu da qyar yaja jikin shi ya isa wajen wani masallaci na kauwar ya samu ya jingina da bangon masallacin bayan wani lokaci sai ga wani mutun ya shigo masallacinnan dauke da wata leda da abinci aciki, yazo ya bude yana ci a gaban shehu Abdulqadir
Zamu ci gaba Inshaallah.
Misbahu Bunyamin Alqariby.