Wednesday, 16 July 2025

TARIHIN UNGUWAR AYAGI

TARIHIN UNGUWAR AYAGI

Wallafar

COMRADE AUWAL ZAKARI AYAGI

(Barden Ayagi)

Haqqin Mallaka (M)

Auwal Zakari Ayagi (Barden Ayagi)

Lambar Waya:     07038775781

Bugu Na Xaya     2025/1446

TSARAWA DA BUGAWA

Al-Azmiyya Islamic Foundation: No. 313 Al’Mustapha House Kadawa Western Bypass AL’EEMAAN Medicine Store Building, Adjacent to Gwarzo Road Kano.

E-mail: auwalzakari@gmail.com

www.sautulazimiyya.blogspot.co.uk/

GSM:  07038775781, 08023615685


SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan Littafi ga marigayi Sarkin Ayagi na Shida (6) Mal. Abdulqadir Salihu Ayagi (Labaran), da Mahaifiyarsa Malama Bikisu Muhammad Allah ya gafarta musu, Amin.

TA’ALIQI

Da sunan Allah Mai yawan Rahma Mai yawa jin qai. Tsira da Aminci su qara tabbata ga fiyayyen halitta

Abdulrashid Baba Ayagi

 (Sarkin Ayagi)

GODIYA

Da sunan Allah mai yawan Rahama Mai Jin qai, tsira da aminci su qara tabbata ga shugaban halitta ga shugaban halitta Annabin rahma, Allah ya qara yarda a gareshi.

Bayan haka ina godiya ga Allah madaukakin sarki da ya ba ni ikon rubuta wannan qaramin littafi na: TARIHIN UNGUWAR AYAGI

Godiya mai tarin yawa ga Malam Abdulrrashi Baba Ayagi (Sarkin Ayagi na Bakwai (7) da Wazirin Ayagi Ma’ajin Masarauta, Alh. Abdallah Sani Rabi’u, Xan Masanin Ayagi, Daraktan Ilimi da Ayyuka, Mal. Hadi Tijjani Abubakar, da Shatiman Ayagi Sharif Ibrahim Abdullahi, da Mallam Kabiru Sani Ayagi da sauran jama’ar da suka ba ni kwarin gwiwa wajen ganin na wallafa wannan littafi.

Allah ya saka wa kowa da alheri Amin.

Auwal Zakari Muhammad Ayagi

      (Barden Ayagi)

5 ga Zulhijja 1445= 1/6/2025


ABUBUWAN DA KE CIKI

Sadaukarwa…………………..………………… 2

Godoiya………………………………………… 3

Ta’aliqi…………………………………………. 4

Abubuwan da ke ciki…………………………… 5

Gabatarwa …………………………………........ 6

Babi Na Farko:

GABATARWA

Da sunan Allah mai rahama mai jin qai, tsira da aminci su qara tabbata ga shugaban halitta Annabin rahama salallahu alaihi wasallam.

Na yunqura wajen rubuta wannan littafi, sakamakon wani bawan Allah da ya yi min magana ta waya cewa; yana so ya yi rubutu akan tarihin Unguwar Ayagi, bayan ya kamala Digirinsa na Farko a Jami’a, amma ya yi bincike a yanar gizo-gizo (Internet) bai samu wani bayani gamsashshe ba, kuma ya nemi bayanai daga mutane, amma babu wani rubutaccen tarihi da zai kafa hujja da shi.

Sai na ga dacewar in samar da tarihi sahihi da za a iya dogaro da shi game da tarihin wannan unguiwa ta Ayagi, cikin sauqi sai na samu rubutaccen tarihi da masarautar Ayagi ta samar a cikin kundin masarautar, sai nayi amfani da shi da kuma sauran bayanan da na samu daga dattijai da masana na unguwar wajen rubuta wannan littafi. 

Wassalamu Alaikum

Auwal Zakari Muhammad Ayagi

 (Barden Ayagi) 9 ga Zulhijja 1445= 5/6/2025

UNGUWAR AYAGI

Unguwar Ayagi daxaxxiyar Unguwa ce daga cikin Unguwannin da suke a cikin qaramar Hukumar Dala dake cikin Kwaryar Birnin Kano Nigeria, Unguwa ce mai tsohon tarihi, da take da Sarautar Sarki, maimakon Mai’unguwa.

Unguwar Ayagi ta yi iyaka da unguwannin ‘Yan-Muruci, da Mararraba, da Baqin-Ruwa, da Kabuga-Aisami, da Mai-Aduwa, da Unguwar Qofar Kabuga wato titin Malam Aminu Kano, da kuma Unguwannin Sani-Mainagge, da Xandago, da Warure, da Dausayi, da Gyaranya dakuma Takalmawa.

Unguwar ta kafu ne tin zamani Sarkin Kano Sulaimanu, kuma a zamanin Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo wanda ya mulki Jihar Kano daga Shekara ta 1819 zuwa Shekara ta 1846, ya daxa tabbatar da Unguwar da Sarautarta.

IYAKOKIN UNGUWAR AYAGI A ZAMANIN BAYA

A wancan lokaci Qasar Ayagi ta faro ne daga bakin Jakara har zuwa bakin Dutsen Goron-Dutse, don haka idan ka auna za kaga cewa gidan Sarkin Ayagi shi ne tsakiya tsakanin Jakara zuwa Gwauron Dutse.

IYAKOKIN UNGUWAR AYAGI A YAU

A yauzu kuwa wannan unguwa ta yi iyaka da unguwanni kamar haka:

Gabas: tayi iyaka da Unguwar ‘Yan-Muruci.

Arewa: tayi iyaka da Unguwannin Mararraba, da Baqin-Ruwa, da Mai’aduwa da kuma Kabuga-Aisami.

Yamma: kuwa tayi iyaka da Qofar Kabuga wato titin Malam Aminu Kano.

Kudu: kuma tayi iyaka da unguwannin Sani-Mainagge, Xandago, Warure, Dausayi, Gyaranya da Takalmawa.

ASALIN KALMAR AYAGI

Wasu suna ganin kalmar Ayagi kalma ce daga yaren Mallanci da ta hauhawa daga kalmomi guda biyu wato “aya” da “gi”, “aya” tana nufin: ‘malam’ “gi” kuma tana nufin: ‘ya zo’, wato Mallam ya zo

A wani bayanin kuma, kalmar ‘Ayagi’ ta samo asali ne daga yaren Nufanci wadda take nufin Beyerabe ko Yarabawa da suke gaya wa almajiran Malam Nasiru Jatau da suke tare da shi.

Kasancewar unguwar Ayagi ce wuri na farko da Yarabawa (Xaliban Mallam Nasiru Jatau) suka fara sauka, shi ya sa ake kiranta da wannan sunan, kamar yadda ake kiran wasu Unguwanni da dama da wasu qabilu suka fara zama a jihar Kano, Misali:

1.      Zangon Bare-bari: (ta kasance wajen zaman Kanuri).

2.      Tudun Nufawa: (ta kasance wajen zaman kabilar Nupe)

3.      Dambazau: (ta kasance wajen zaman Fulani na farko)

4.      Yolawa: (ta kasance wajen zaman mutanen Yola da suka sauka a Kano).

5.      Agadasawa: (ta kasance wajen zaman mutanen Agadez ta jamhuriyar Nijar), da dai sauransu.

Amma zance mafi inganci mafi shahara shi ne: “a yagi yamma da gari a ba shi wadda ta fito ne daga bakin Sarkin Kano Sulaimanu, kuma Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya tabbatar wa da Mallam Nasiru Jatau, dalilin wannan ne ma ake ce masa Sarkin Ayagi, kuma har yake aiwatar da aikin Sarauta kamar yin shari’a da jivintar haraji na wannan vangare; da kuma sa shi a kason fada kamar bayi da abubuwan amfani, inda ake aiko masa da shi duk lokacin da hakan ta samu.

MALAM NASIRU JATAU XAN MALAM MAHMUDU XAN MALAM ABDULKARIMI

In za ayi batun tarihin Unguwar ta Ayagi ta yau, to dole sai an ambaci Sarkin Ayagi na farko wato Malam Nasiru Jatau xan Malam Mahmudu xan Mallam Abdulkarimi, wanda asalin sa mutumin garin Tumbuktu ne ta qasar Mali.

Mallam Muhammadu Nasiru Jatau ya shigo Najeriya ne a dalilin yaxa addinin Musulunci ya fara sauka a qasar Zariya kuma har ma suka zauna na xan wani lokaci a Zariyan tare da barin wasu iyalansa a can.

Daga nan suka wuce har qasar Ilori da Ogbomosho don yaxa addinin Musulunci tun kafin bayyanar jihadin Shehu Xan Fodiyo (R.T.A.). A lokacin da suka sami labarin bayyanar jihadin Shehu Xan Fodiyo sai suka haxe da su. Ta haka ne Allah Tabaraka wa Ta’ala ya haxa Muhammaadu Nasiru Jatau da Malam Ibrahim Dabo dalilin neman ilimi da ilimantarwa. Inda suka zama aminan juna. Tun kafin Malam Ibrahim Dabo ya zama Sarkin Kano.

DAWOWAR MALAM NASIRU JATAU ZUWA GIDA AREWA

Bayan Malam Nasiru Jatau ya yi shekaru da dama inda yake zaune ya na ba da ilimi yana kasuwanci, sai ya ga ya kamata ya dawo gida Arewa; da ya dawo ya fara zama ne a qasar Zariya, lokacin sarki Muhammadu Makau wanda yayi sarautar Zaria daga 1808 zuwa 1821, wanda a lokacin sa ne sarakunan Fulani masu cin gashin kansu suka fara sarautar Qasar Zaria.

Amma sai Sarkin na Zariya ya ce da shi Malam! Zariya ba ta kamace ka da zama ba, Kano ya kamata ka koma. Da Malam Nasiru Jatau ya ji wannan bayani daga Sarki, sai ya shirya ya taho Kano ya baro wasu daga cikin iyalansa a can Zariya, suna nan ana cewa da su Mallawa.

Malam Muhammadu Nasiru Jatau dai sun fara zama ne a nan Kano a unguwar da ake cewa da ita Kwakwatawa a yau, wannan unguwa kuma ta sami wannan suna ne saboda wata irin riga da ake cewa da iata Kwakwata da wannan zuriya ta Muhammadu Jatau suke sayarwa a lokacin baya, inda ya zauna yana ba da ilimi. Almajiransa na can Ilori da Ogomosho suka biyo shi don ci gaba da xaukar karatu a wajensa.

A lokacin da Allah ya bai wa Sarki Sulaimanu sarautar Kano sai ya yi niyyar shigar da Malam Muhammadu Jatau cikin masarautarsa, saboda yadda ya sami labarin ilimi, taqawa da jarumtar Muhammadu Jatau a wurin amininsa Malam Ibrahim Dabo. Amma shi Muhammadu Jatau ya fi son ci gaba da tafiye-tafiyen da suka saba yi na yaxa addinin Musulunci tare da ilimantarwa musamman yadda wasu daga cikin xalibansa suka biyo shi nan Kano daga can qasar Ilori da Ogbomosho inda suka ci gaba da karatu a wajensa, ban da waxanda ya bari a can.

Amma duk da haka sai mai martaba sarkin Kano Sulaimanu ya yanka masa wannan qasar ta Ayagi yamma da kasuwar Kurmi daga bakin Jakara har zuwa Kabuga ya ce sai ka dinga yago mutanenka (Daga nan aka samo asalin sunan Ayagi) kana dawo wa da su nan, kuma ya yi masa Sarkin Ayagi sannan ya sanya shi xaya daga cikin mutune uku da suka zamo wakilansa a Fuskar Yamma, wato:

1.      Xan-kududdfi,

2.      Muahammadu Jatau,

3.      Malam Yusufu

Tun kafin a yanka unguwanni a Kano, kamar yadda suke a halin yanzu[1].

Ana cikin wannan lokaci sai Allah ya yi wa Mallam Sulaimanu rasuwa, inda aka bai wa Malam Ibrahim Dabo sarautar Kano a shekara 1819. Kasancewar Mallam Ibrahim Dabo ya zama sarkin Kano shi ne ya qara tabbatar da wannan matsayi na Sarkin Ayagi har ma ya sa aka samo ciyawa da aka sani da da sunan ‘dashi’ aka kewaye wannan gida na sarkin Ayagi da ita. Kuma aka yi bukkoki (15) a ciki shi ma ya jaddadawa Muhammadu Nasiru Jatau cewa ya dinga yago mutanensa daga Kwakwatawa yana dawowa da su nan.

A lokacin da mai martaba Malam Sulaimanu ya yanka wa Malam Jatau wannan qasa ta Ayagi ta haxa da unguwanni masu yawa sama da waxanda suke kewaye da ita a yanzu, tun kafin a yanka unguwanni a shekara ta 1926[2].

ASALIN MU MUTANEN IRAQI NE KAKANNIN MU SU KA ZO DAGA MALI

Mun sami labari daga Malam Hadi Tijjani Abubakar daga babban shehin nan na garin Sabo-Ibadan daga babban shehin nan na garin Ofa a qasar Oshigbo Malam Alfa Juma inda yake cewa da Malam Qassim[3]: “Malam Qasim ka ga mutane a nan suna ganin mu Yarabawa ne, amma asalinmu mu ba Yarabawa ba ne, asalinmu mu mutanen Iraqi ne, kakanninmu ne suka zo suka zauna a Mali, sannan kuma suka shigo qasar Nijeriya daga nan ne har suka shigo nan Oshigbo don kasuwanci da ba da ilimi, da suka nufi tashi sai suka bar wasu iyalan nasu a nan suka tafi da wasu waxanda suka zauna a Kano”. Alfa Juma ya ce da Malam Qassim, “Ka san Shehi Malam Mijin-yawa[4] na Kano?” Sai ya ce da shi; “ba Bajimi xan Aika ba”? Sai ya ce: “shi fa, to mahaifiyarsa jininmu xaya da ita asalinmu mutanen Iraqi ne, daga Iraqi kakanninmu suka zo Mali”.

ALAKAR SARKIN KANO IBRAHIM DABO DA MALLAM NASIRU JATAU

Kamar yadda ya inganta Malam Nasiru Jatau yana da cikakken aminci tsakaninsa da Malam Ibrahim Dabo tun suna yawon neman ilimi, da ba da ilimi da yaqi don tabbatar da addinin Musulunci, kamar yadda muka ambata a baya. Don haka lokcin da Malam Ibrahim Dabo ya zama Sarki; sai shi ma ya nemi da ya jawo Malam Nasiru Jatau kusa da shi don ya taimaka masa a tafi da harkar sarauta saboda amanarsa da ya sani da kuma iliminsa, amma Malam Nasiru Jatau nan ma ya ce a’a shi dai ya fi so a bar shi ya zauna da xalibansa ya ci gaba da ba su ilimi.

Da Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya xebe qauna daga Malam Nasiru Jatau ya matso kusa da shi a fada, sai ya tabbatar masa da wurin da Sarkin Sulaimanu ya ce: a yagi yamma da da gari a ba shi. A inda Sarkin Kano Malam Dabo, ya sa aka kewaye gidan da ganuwa da wata ciyawa ‘dashi’, tare da bukkoki goma sha biyar (15) inda ya zauna a ciki tare da masallaci da makaranta wadda ake wa laqabi da (babban soro).

MASALLACI DA MAKARANTAR FARKO

A zamanin Sarkin Ayagi Malam Salihu xan Mal. Abdulqadir xan sarkin Ayagi Malam Nasiru Jatau, sai ya zama ana samun cikowar masu kawo qara da kuma cikowar masu xaukar karatu, kuma a al’adarsu sun saba sai sun gabatar da ba da karatu sannan suke zaman Shari’a, to sai ya ga ya kamata ya xau hanya mai sauqi don hutar da masu kawo qara, to shi ne sai ya ciru daga ba da karatu da yin limanci ya naxa almajirinsa kuma sirikinsa Malam Abubakar Lafiyagi da ya ci gaba da ba da karatu da yin limanci, bayan ya shafe shekaru (38) yana sarautar Ayagi da alqalanci da ba da karatu da kuma limanci. Sannan Sarkin Ayagi Malam Salihu ya shagala da sarauta da kuma yanke hukuncin masu kawo qara. A wannan lokaci duk shari’ar da sarkin Ayagi ya yanke hukunci a kanta ta ko gaban Sarki aka je; ba ya tashinta sai dai ya tabbatar da ita, wanda yake ganin kamar bai yarda da shari’ar ba ya fuskanci hukuncin fadar Kano.

Dangane da Masallaci da soron Makaranta kuwa, Sarkin Kano Malam Dabo da kansa ya fitar da Masallaci da Makaranta, inda aka nemi Malam Ci-gero[5] ya fitar da mihrabi, bisa ilhama an ce da suka tsaya ya yi musu nuni sai da suka hango hasumiyar Xakin Allah (Ka’abah).

Daga baya a lokacin Sarkin Ayagi Malam Salihu, aminsa Malam Muhammadu Kwalayi[6] ya nemi da Sarkin Ayagi Malam Salihu da ya ba shi damar gina Masallacin, maimakon zankwayen[7] da aka yi hijabi da rufi da shi. Sarkin Ayagi Malam Salihu ya ce masa: “Masallaci ai xakin Allah ne, ni ma ina so in gina soro na” haka kuwa aka yi Malam Kwalayi yana gina Masallaci; shi kuma Sarkin Ayagi Malam Salihu yana gina soron Makarantarsa, a ka kammala lokaci guda.[8]

 GIDAN SARKIN AYAGI

Gidan Sarkin Ayagi wanda yake a tsakiyar unguwar Ayagi, an kafa shi ne tun zamanin Mai Martaba Sarkin Kano Mallam Sulaimanu a shekara ta 1814. Kuma Sarkin Ayagi na farko wato Mallam Muhammadu Nasiru Jatau xan Mallam Mahmudu xan Mallam Abdulkarimi xan Abdullahil Iraqi shi ya afara zama a cikinsa, (kamar yadda muka ambata abaya).

Kamar yadda mai girma Sarkin Ayagi Inuwa xan Sarkin Ayagi Salihu (I) xan Mallam Abdulqadir xan Sarkin Ayagi na farko Mallam Muhammadu Nasiru Jatau ya bayyana tarihin kafuwar wannan gida na Sarkin Ayagi a wata hira ta musamman da aka yi da shi a shekarar 1975.[9]

Haka kuma akwai rubutattun bayanai da aka samu a kundin Sarkin Ayagi Inuwa waxanda suke nan a halin yanzu, kuma suke xauke da cikakken tarihin wannan gida na Sarkin Ayagi kamar yadda za mu bayyana shi kamar haka:

Zuriyar Sarkin Ayagi Muhammadu Nasiru Jatau sun zo Kano ne daga garin Tumbuktu na qasar Mali a zamanin Sarkin Kano Yaji.[10] Kasancewar sun zo daga qasar Mali, shi ya sa ma ake cewa da su Mallawa. Duk da cewa asalinsu Larabawa ne na qasar Iraqi. To abin da ya fito da su daga qasarsu ta asali shi ne aikin yaxa Addinin Musulunci ta hanyar ilimantarwa bisa tafarkin Sufanci tare da gudanar da kasuwanci tsakanin qasa da qasa gari da gari.

Kamar yadda yake rubuce a tarihin shigowar addinin Musulunci Afrika ta yamma, cewar addinin Musulunci ya shigo Afrika ta yamma ne; ta hanyar Mayaqa, Sufaye da ‘yan Kasuwa.[11]

JERIN SARAKUNAN AYAGI

1.               Malam Muhammadu Nasiru Jatau - xan Malam Mahmudu xan Abdulkarimi xan Abdullahi Al-Iraqi – shi ne sarkin Ayagi na farko daga shekarar (1819 - 1852), inda ya samu shekaru (33) yana mulki haxi da limanci da ba da karatu da yanke hukunci.

2.               Sarkin Ayagi Malam Salihu jikan sarkin Ayagi Malam Nasiru Jatau wanda ya fara mulki bayan rasuwar kakansa Malam Nasiru a shekarar (1852 – 1896) wato ya yi shekaru (44) shi ma yana mulki gami da ba da karatu da limanci da yanke hukunci. A shekaru shida na qarshen mulkinsa ya dakko almajirinsa kuma sirikinsa Malam Abubakar Lafiyagi ya ba shi limanci da bayar da karatu, shi kuma ya ci gaba harkokin mulki da hukunci.

3.               Sarkin Ayagi Malam Ibrahim xan Sarkin Ayagi Malam Salihu ya fara mulkin Ayagi bayan rasuwar mahaifinsa sarkin Ayagi Salihu a shekarar (1896 – 1930) inda ya sami shekaru (34) yana sarautar Ayagi.

4.               Sarkin Ayagi Muhammadu Inuwa xan sarkin Ayagi Salihu. Ya fara mulkin wannan unguwa bayan rasuwar yayansa sarkin Ayagi Ibrahim a shekarar (1930 – 1978) inda ya sami shekaru (48) yana sarautar Ayagi. A lokacinsa ne aka fitar da wasu sabbin unguwanni a garin Kano kaf. Inda wani Bature da ake ce masa Buga-House ya karkasa unguwannin Kano. Inda Ayagi take da Sarki kuma Mai Unguwa. Wannan ne ya sa Sarkin Ayagi Inuwa da ransa ya ayyana sirikinsa kuma babban hadiminsa Mal. Sulaimanu Tereta[12] a matsayin mai unguwar Ayagi, bayan rasuwar Mal Sulaimanu Tereta ya ayyana qaramin xansa Alh. Baba Agwa a matsayin mai unguwa shi ma, shi kuma sarkin Ayagi Inuwa yana nan a Sarkinsa na Ayagi. 

5.               Sarkin Ayagi kuma Mai Unguwar Ayagi Alhaji Salihu Inuwa (Alh. Baba Agwa) xan Sarkin Ayagi Muhammadu Inuwa. Dalilin kiransa da ‘Baba Agwa’ mahaifinsa Muhammadu Inuwa ya sa masa sunan mahaifinsa Salihu, sai Yarabawa masu kawo goro daga kurmi suka tambaye shi ya ya sunan xan autan nan naka? Sai ya ce sunan mahaifina ne, sai suka ce: ‘Baba Agwa’ wato da Hausa ‘Baba Babba’ daga nan wannan suna ya bi shi. Alhaji Salihu ya fara mulkin Ayagi bayan rasuwar mahaifinsa Sarkin Ayagi Muhammadu Inuwa daga shekarar (1978 – July 2008) inda ya sami shekaru (30) yana mulkin Ayagi.

6.               Sarkin Ayagi Abdulqadir Salihu Inuwa ya fara sarautar Ayagi bayan rasuwar mahaifinsa Alhaji Salihu Inuwa (Alhaji Baba Agwa) a shekarar (August 2008, – March 2024) ya sami shekaru goma sha shida (16) yana sarautar Ayagi.

7.      Sarkin Ayagi Mal. Abdurrashid Baba Ayagi, Sarkin Ayagi na (7) ya hau sarautar Ayagi yana da shekaru 42 da haihuwa, kafin ya zama Sarkin Ayagi ya riqe hakimci na wamban Ayagi kuma shugaban Majalisar Sarkin Ayagi, a wannan masarauta ta Ayagi. Malam Abdurrashid ya hau sarautar Ayagi a ranar Litinin 8 ga watan Aprilu 2024 wanda ya yi daidai da 28 ga Ramadan 1445.

MASARAUTAR AYAGI DA HAKIMANTA

Sarkin Ayagi na Shida (6) Abdulqadir Salihu Inuwa wanda ya mulki sarautar Ayagi bayan rasuwar mahaifinsa Alhaji Salihu Inuwa (Alh. Baba Agwa) a shekarar (2008 – 2024) wanda ya sami shekaru (16) yana sarautar Ayagi, ya yi kokari wajen zamanantar da Masarautar ta Ayagi. Inda ya samar da Kundin Tsarin Mulkin masarautar, tare da naxa mata Hakimai.

JERIN HAKIMAN MASARAUTAR SARKIN AYAGI

Ga jerin sunayen Hakiman da sarautun su, wadanda suke a kan karagar hakimcin har zuwa wannan shekara ta 2025:

1. Galadiman Ayagi Mallam Khamisu Hussaini Ayagi

2. Wamban Ayagi, Shugaban Majalisa kuma Wakilin Ayagi Mallam Al-hassan Baba Ayagi

3. Wazirin Ayagi, Xan Majalisa, Ma’ajin Masarauta, Alh. Abdallah Sani Rabi’u

4. Xan Masanin Ayagi, Daraktan Ilimi da Ayyuka, Mal. Hadi Tijjani Abubakar

5. Walin Ayagi Sharif Lawan Ali

6. Qa’idus Shurafa’u, Maga-takardar walwala da jin daxi, Sharif Bashir Ahmad Ayagi

7. Makaman Ayagi, Xan Majalisa, Matimakin Sakatare, Mal. Hussaini Baba Ayagi

8. Ciroman Ayagi Xan Majalisa, Mai Binciken kuxi, Alh. Mubarak Xanjuma Sani

9. Turakin Ayagi, Xan Majalisa, Tijjani Abubakar

10. Barden Ayagi, xan Majalisa, Mai Ba Da Shawara kan Harkokin Addini, Comrade Auwal Zakari Ayagi

11. Shatiman Ayagi, Sharif Ibrahim Abdullahi

12. Madakin Ayagi, Sulaiman Sulaiman Magaji

13. San Turaki, Sagiru Xanjuma Sani

14. Matawallen Ayagi Xan Majalisa, Misbahu Ibrahm Khalil

15. Sardaunan Ayagi, Abdurrazaq Baba Ayagi

16. Tafidan Ayagi, Xan Majalisa, Najibullahi Salman Ayagi

17. Xan Buran Ayagi, Basiru Kabiru Sani

18. Xan Darman Ayagi, Abdulhadi Hassan Sani

19. Xan Isan Ayagi, Umar Aliyu Zakari

20. Maji-Daxin Ayagi, Mudassir Nazifi Imam

21. Sarkin Fulanin Ayagi, Mustafa Shehu Musa

22. Xan Goruban Ayagi, Mahmud Garba Isa

23. Xan Adalan Ayagi, Aliyu Ibrahim Garba

24. Zannan Ayagi, Saifullahi Sani Hashim

25. Magajin Ayagi, Khalifa Tijjani Adam

26. Falakin Ayagi, Muhammad Shu’aibu Abubakar

27. Garkuwar Ayagi, Shugabar Mata, Hajiya Hassana Baba Ayagi.

LIMANCI A MASALLACIN SARKIN AYAGI

Maganar limanci a wannan gida na Sarkin Ayagi kuwa, kamar yadda muka bayyana a baya cewar sarkin Ayagi na farko wato Malam Nasiru Jatau shi ne limamin masallacin gidansa na farko har qarshen rayuwarsa. Kamar yadda yake bisa tsarin Daular Usmaniyya sarkinku shi ne Limamin ku kuma Alqalinsu.

Bayan rasuwarsa kuma magajinsa wato sarkin Ayagi Salihu (I) wanda ya fara sarauta a shekarar 1852 zwa 1896 shi ma shi ne ya ci gaba da ba da ilimi, shari’a da kuma limanci, sai a qarshen rayuwarsa ne ya ga dacewar ya yi na’ibi a sakamakon yadda ayyuka suke ta qara yi masa yawa ga kuma girma, shi ne sarkin Ayagi Salihu (I) ya naxa na’ibi a limanci da ba da ilimi. Wanda ya naxa na’ibin kuwa shi ne babban Almajirinsa:

1.               Malam Abubakar Lafiyagi wanda ya yi fice wajen girmamawa da biyayya a gare shi, sannan kuma sarkin Ayagi Salihu Na I ya aura masa xiyarsa Halimatu. Malam Abubakar Lafiyagi ya ci gaba da limanci a wannan masallaci na gidan Sarkin Ayagi har qarshen rayuwarsa.

Bayan rasuwarsa a lokacin shi ma sarkin Ayagi Salihu na I ya rasu, sai magajinsa Sarkin Ayagi Ibrahim ya naxa:

2.               Malam Muhammadu wanda xa ne ga Malam Abubakar Lafiyagi a matsayin liman. Bayan rasuwar Malam Muhammadu a lokacin shi ma sarkin Ayagi Ibrahim ya rasu. Sai sarkin Ayagi Inuwa ya naxa:

3.               Malam Muhammadu Inuwa wanda aka fi sani da suna (Malam Me-keke) kasancewar ya fi cancanta a lokacin duk da cewa shi ba xa ne ga Malam Muhammadu ba. Bayan rasuwar Malam Me-keke wanda tun kafin rasuwarsa ya yi nuni da Mallam Abubakar da aka fi sani da (Malam Yarwa) wanda xan-xan uwansa ne kuma sirikinsa ne, sai sarkin Ayagi Salihu na II, Alhaji Baba Agwa ya naxa:

4.               Malam Abubakar Yahaya (Mal. Yarwa) a matsayin Liman. Bayan rasuwar Malam Yarwa wanda shi ma ya yi nuni da xansa Malam Auwalu sai sarkin Ayagi Abdulqadir (Labaran) ya naxa:

5.               Malam Auwalu Abubakar a matsayin liman. Wanda shi ne liman a halin yanzu.

Kuma duk wannan naxe-naxe na limanci an yi shi ne da sani da kuma izinin masarautar Kano.

Domin a lokacin baya duk abubuwan da masarautar Kano ta samu kamar bayi da dawakai da sauransu sai an aiko wa sarkin Ayagi nasa rabon.

Haka nan duk wani hukunci na shari’a da sarkin Ayagi ya yanke to haka Masarautar Kano za ta tabbatar da shi domin a lokacin har daga qasar Gwarzo ana kawo shari’a nan gidan sarkin Ayagi kuma a yi hukunci. Kamar yadda tarihi ya nuna sarkin Aygi ne ke kula da mahara da suke shigowa Kano tin daga qasar Gwarzo zuwa cikin gari a wancan lokaci ta wannan fuskar. (Don nan ne qarshen inda sarkin Yammawa wato Sarkin Qaraye yake karewa daga Mahara, ta yammacin Kano)

 Haka nan ba za mu manta da tsarin hawa na mai martaba Sarki lokacin da yake biyowa ta Qofar Galla inda yake tsaya wa don karvar gaisuwa daga Sarkin Ayagi saboda jaddada alaqa wadda take tsakani.

Haka wannan alaqa mai kyau ta zarce har zuwa wannan lokaci, domin kuwa har yanzu duk sallah qarama sai Masarautar Kano ta aiko da riga alkyabba, da sallah babba kuma rago a kawo wa Sarkin Ayagi shi kuma ya yi rakiya don bai wa Liman tun lokacin baya har zuwa wannan lokaci haka ake yi. Kamar yadda yake a al’adance domin wasu unguwanni ne ana cikin gari, limamansu maimartaba Sarki ne da kansa yake naxa musu rawani, kamar yadda ake naxa limamin Juma’a, kuma duk Sallah sai an aika musu da kayan al’ada, ranar gaisuwar Sallah su sako rigunan da aka aika musu, don su tabbatarwa da Sarki yaqo yazo, su kuma yi godiya ga Sarki.

Waxannan Limaman Unguwanni kuwa sune:

Limamin Galadanci, Limamin Ayagi, Limamin Jalli, Limamin Wudilawa, Limamin Yola da sauransu.

Tushen naxin Limancin Ayagi dam ace ko ragamar sarkin Ayagi ce mai ci ne, domin shi ne yake da alhakin zaven wanda zaiyi limanci a a wannan unguwa, shi ne yake bada jawabi a gaban maimartaba Sarki, a gabatar d ashi a yi masa naxi a kawoshi gaban sarki.

  

FITATTUN MUTANE YAN ASALIN UNGUWAR AYAGI

Unguwar Ayagi ta haifi fitattun mutane da suke taka rawa afannoni daban daban na rayuwa, ga wasu daga cikin na da da na uyanzu:

Vangaren Ilimi:

Wannan Unguwa ta yi fice wajen ilimin Addinin Musulunci kamar Karatun Alqur’ani, da Tafsiri, da Fiqhu musamman littafin Askari. Sannan wannan Unguwa ta yi fice a Madahu (Karatun Islamiyya), domin kuwa har yanzu ana karatun Ishiriniya duk ranar Takutaha, da aka fara tun lokacin Sarkin Ayagi Malam Salihu wanda Malama Hasana Mai Auduga ta assasa shi; kuma har yanzu ake aiwatar da wannan karatu na Ishiriniya a cikin wannan gida na Ayagi.

Akwai manyan Malamai a wannan Unguwa da sukayi fice a fannoni da dama, na da na yanzu, ga wasu daga cikin su kamar haka:

1.      Sarkin Ayagi Malam Nasiru Jatau: Wanda Shi ne yake limanci da ba da ilimi

2.      Sarkin Ayagi Malam Salihu: Shi ma shi ne yake yin limanci da ba da ilimi

3.      Limamin Ayagi Malam Abubakar Lafiyagi: limamin Unguwa na farko, da yake limanci da ba da ilimi. 

4.      Mahiru Sharif Bala: Babban Malami Mai Buga Alkur’ani da litattafan Addini, Qur’anin sa bugun warshu ya shahara a duniya.  

5.      Mal. Sani Salihu (Mal. Barau): Shi ma Babban Malami ne kuma xan kasuwa, mafatauci da da’awa, ya yi fatauchi a garuruwa da dama a kudancin xasar nan, har ya gina Babban Masallaci a garin Kabo, wanda Mallam Wada yake limanci a halin yanzu, haka zalika ya musuluntar da maguzawa da dama.

6.      Mallam Abdullahi xan Ringim: Shi ma babban melamine na azure da yake koyar da karatun Addini a kofar Jaji, jikin gidan Mal. Usaini mai Goro, wanda ayanzu jikansa Sharif Ibrahim (Shatiman Ayagi) shi ne ya gajeshi.  

7.      Malam Baqo Sufi:

8.      Malam Labaran:

9.      Shaik Kabiru Sani Salihu Ayagi: xa ne ga Mal. Sani Salihu, shi ne ya kafa Makarantar Sahatus-Sibyan Lil Tahfizul Qur’an a 1992, wacce take koyar da haddar Alqur’ani mai girma. Makarantar ta zama cibiyar koyon Ilimi ga al’umma.

10.  Mallam Yahaya Rabiu: Babban Malamin Alqur’ani ne da yake da tarin Almajirai.

11. Mallam Zakari Mai Ishiriniyya:

12. Khalifa Mal. Tijjani Na Mallam Shehu

13. Mal. Ya’u Labaran Kofar Jaji

14. Alaramma Mal. Salisu (Mal. Dogo)

15. Alaramma Mal. Gambon a Mal. Dogo

16. Alaramma Mal. Yahaya Rabiu

17. Alaramma Mal Yahaya (Dan Wanzam)

18. Mal. Hudu

19. Mallam Na Gulu

20. Mallam Isa Yan Balangu

21. Mal. Garba Xan Asabe

22. Mallam Ya’u Labaran Qofar Jaji

23. Mallam Halliru Ya’u Kofar Jaji

24.  Mal. Idris Baba

25. Shaik Tijjani Abubakar Namama

26. Mal. Habibu Khamis Baqo

27. Malla. Lawan (Dikkani)

28. Mal. Sharu Lawan (Dikkani)

29. Alhaji Ibrahim Uba Awade

30. Mallam Jatau na Mal. NazifiTijjani (Namama)

31. Alaramma Mal. Musa Jakara

32. Alaramma Mal. Muhammadu tawakkala

Vangaren Attajirai:

Kamar yadda yake babbar sana’ar wannan Unguwa ita ce fatauci, irin su fataucin goro, citta, manyan riguna, da xinki da sauransu. A cikin Attajiran wannan unguwa na da, da na yanzu akwai:

1.      Malam Muhammadu Kwalayi:

2.      Alhaji Salisu na Alhaji Abdulwahabi

3.      Alhaji Abdulwahabi Abubakar Lafiyagi

4.      Alhaji Falke

5.      Alhaji Nuhu: Wanda shi ne ya sabanta ginin masallaci da makarantar gidan Sarkin Ayagi.

6.      Mal. Usman Husaini Kumurya (Usmaniyya)

7.      Alhaji Usaini Mai Goro

8.      Alhaji Qassim Ayagi

9.      Alhaji Tanko Bala

10.  Alhaji Zakari Muhammad (Alh. Amasha)

11. Alhaji Ashafa

12. Alhaji Sharu Imam

13. Alhaji Maifate

14. Alhaji Xangu

15. Alh. Isma’il Mai Tsakiya

16. Alhaji Xalha Na Mal. Bawo

17. Alhaji Auwalu Xalha Ayagi

18.

Bangaren Ma’aikata da ‘Yan Boko:

Wannan Unguwa ta na da Manyan ‘yan boko da Manyan Ma’aikatan Gwamnati a matakin qasa da Jiha da Kananan Hukumomi, wasu daga ciki sun haxar da:

1.      Farfesa Ibrahim Ayagi (1940-2020): Wanda ya kasance masanin tattalin Arzikin, Malami kuma mai ra’ayin cigaban qasa, yayi fice a qasa baki daya, domin ya riqe muqamai da dama, ciki har da shugaban hukumar binciken tattalin arziqin qasa (NEIC) a zamanin Shugaba Obasanjo, shi ne wanda ya kafa makarantar Hassan Ibrahim Gwarzo a nan Kano.

2.      Farfesa Sani Musa Ayagi: Haifaffen Unguwar Ayagi ne,, kwararren Malami ne masani a fannin Tafsiri, Hadisi da Ilimin Qur’ani, shine Babban limamin Juma’a na tsohuwar Jami’ar Bayero (BUK) kuma Malami a Jami;ar.

3.      Barister Nura Ado Ayagi: Wanda yake kwararren lauya ne

4.      Farfesa Musbahu Tijjani Rabiu

5.      Dr Rabiu Tijjani Rabi’u

6.      Dr. Aminu Garba Aminu

7.      Dr. Musa Sani Aliyu

8.      Dr. Sunusi Ridwan Ayagi

9.      Dr. Mansur Sani Salihu

Vangaren Jarumta da ‘Yan Tauri;

1.      Jarmai Tagwai: wani jarumi ne da ya goge wajen yaqi, Wanda a gidansa ake ajiyar bayin da aka samo a wajen yaqi.

2.      Uba Sagi

3.      Mal. Maitama Gungun

4.      Baba Sa’idu

5.      Abdulmuminu Tankas

6.      Amadu Mai dawa (Baban Shamilo)

7.      Abdullahi Sungul

8.      Shamilo

9.      Bashir Emir (Tsoho Langel)

10. Ummarul Iya

11. Audu Toli

Vangaren ‘Yan siyasa;

1.      Alhji Baba Agwa Ayagi (Ya tava yin Kansila a zaven kai da ruwanka)

2.      Alhaji Musa Dindile: Babban Xan siya a NPC)

3.      Sunusi Musa Dindile: Babban Xan siyaya a PRP

4.      Alhji Aminu Dan-shila: Yayi kansila a Mazabar Goron Dutse)

5.      Auwalu Abdullahi Ayagi (Auwalu Wizi)

6.      Aminu Garba Ayagi (Yayi Kansila )

7.      Muhd Isma’il Lamin (Mimi) ya rike sakataren Ilimi na Dala

8.      Ali Ibrahim (Uba Chogi)

9.      Nura Ibrahim Ayagi yayi Kansila

10. AVM Ibrahim Umar (Rtd): ya rike babban darakatan ayyuka na musamman na gidan Gwamnati, sannan yanzu shi ne Kwamishina tsaro da ayuukan cikin gida na jihar Kano.

11. Khamis Bashir Bako: Maitamakawa Gwamna

12. Auwal Zakari Ayagi: Ya shugabanci Kwamitin Lafiya Jari na Karamar hukumar Dala.

13. Aliyu Zakari Ayagi

14. Alh. Muaikuxi Musa

Vangaren ‘Yan Gwagwarmaya:

Wannan Unguwa ta yi fice wajen ‘yan Gwagwarmaya, wato masu fafutukar samawa Alumma mafita, kaxan daga ciki sun haxa da:

1.         Comrade AA Haruna Ayagi: Sanannen ɗan rajin kare haƙƙin ɗan adam ne daga Ayagi, kuma yana riqe da mukamin Babban Darakta kuma shugaban Human Rights Network (HRNNigeria) na Qasa, kuma Lauya.

2.         Comrade Auwal Zakari Ayagi: Shine Mataimaki na Musamman kan kafofin sadarwa ga Mataimakin Shugaban Qungiyar Kwadago (NLC) na Qasa, kuma Shugaban Qungiyar Ma’aikatan Lafiya na Qasa

3.         Comrade Ibram Siba Ayagi

4.         Bulyaminu Zakariyya Hamisu (Abul-waqat Ayagi): shi ne ya kafa qungiyar Raudhatur- Rasool Ayagi, kuma marubucin litattafai, masani ilimin Addini da na zamani.

Vangaren Sha’irai Mawallafa da Mawaqa:

Wannan Unguwa ta yi fice masu yabon Manzon Allah da Mawakan zamani, kaxan daga ciki sun haxa da:

1.      Mallam Rufa’I Ibrahim Ayagi: Kwararren mawakin yabon Manzon Allah ne, ya shahara da wakarsa ta Fiyayye Abin Bege, da sauransu.

2.      Mallam Sani Yusuf Ayagi: (Nayako): Shi ma Sha’iri ne fitacce a Kano

3.      Mal. Faruk Ibrahim Ayagi: Shi ne Halifan Mal. Rufa’I Ayagi bayan rasuwarsa, ya dora a fagen bege kamar yadda yayansa ya rasu yana yi.

4.      Mal. Abdulmalik Ibrahim Mai Sharifiya: Fitaccen Sha’iri

5.      Mal. Xan Abai Na Madina: Fitaccen Sha’iri.

6.      Mal. Hamza Khamis Mai yabo: Fitaccen Sha’iri.

7.      Saddiq Usman Sale (Sadiq Zazzabi): Mawaqi ne kuma marubucin waqoqin Hausa, wanda aka sani da wakarsa ‘Yanzu Abuja tayi tsaf’ dan asalin Unguwar Ayagi ne, ya samu ilimi a makarantu daban daban.

8.      Isah Ayagi: Mawaki ne a Hausa wanda yake tashe,

Vangaren Dattawa:

Wannan Unguwa tana da Manyan Dattawa da sukayi fice, kamar haka:

1.      Malam mai Doki

2.      Sharu Amadu Mai Doki

3.      Alh. Alqasim Panda

4.      Alh. Xan Wanzam

5.      Alh. Tijja Lungun kwari

6.      Baba Dankali

7.      Alhaj. Siba Ayagi

8.      Alhaji Kassim Ayagi

9.      Mal. Bashir Siba

10. Alh. Rabiu na Me Goyo

11. Alhji. Ibrahim Madugu

12. Alhji Garba Wada

13. Alhj. Muhammadu Tsoho

14.

Vangaren Masu Sana’ar Hannu:

Wannan Unguwa tana da Manyan Dattawa da sukayi fice, kamar haka:

1.      Alh Audu Magini: Ya shahara a sana’ar Gini

2.      Alh. Musa Magini

3.      Mallam Ibrahim Kafinta: Yana cikin waxanyta suka koyi aiki a takanikal inda turawa suka koya musu, tin ana gudun Boko

4.      Alh. Ali Kafinta: Yana cikin waxanyta suka koyi aiki a takanikal inda turawa suka koya musu, tin ana gudun Boko

5.      Dabalo: Ya shahara a bangaren Pawa

6.      Alh. Musa Mai Qafa:

7.      Alh ya gyara Gashi

8.       Sarki dan tilli: ya shhara wajen Saukar Dabino a ciki da kewayen Unguwa

9.      Alhji Sale Magini:

10.

ABUBUWAN DA UNGUWAR AYAGI TA KEVANTA DA SU

Akwai abubuwan da wannan unguwa ta kevanta da su, kamar Masallatai, makarantun Buzu dana Allo, da makarantun Boko da na Islamiyya, zamu kawo wasu daga cikin su.

MASALLATAN UNGUWAR AYAGI

Akwai kimanin Masallatai 22, na Juma’a guda biyu, na Hamsu Salawat guda Ishirin (20) ga su kamar haka:

1. Masallacin juma’a na Mahiru Sharif Bala Gabari

2. Masallacin juma’a na Alhaji Shu’aibu Ali Gangaren Zango Ayagi

3. Masallacin gidan Sarkin Ayagi

4. Masallacin Alhaji Sani Nuhu Bila na cikin gidan Ayagi

5. Masallacin qofar Jaji

6. Masallacin Alhaji Mukhtari Mai-Fata

7. Masallacin Ziri

8. Masallacin Alhaji Uwaisu Nuhu ‘Yan-Balangu

9. Masallacin lungun Adoye na Malam Shahru Lawan Dukkali

10. Masallacin Qofar Adoye na Makarantar Sahatu

11. Masallacin Alhaji Sunusi Musa Dindile

12. Masallacin Rijiyar Wanki na Malam Xalladi

13. Masallacin Qwar Lawan Filin Mowa

14. Masallacin ‘Yar Chexi

15. Masallacin Dandali na Malam Yaro

16. Masallacin lungun Tsamiya

17. Masallacin Alhaji Sulen gidan Mai

18. Masallacin Aisami bayan Makarantar Warure Firamare

19. Masallacin Aisami na Alhaji Magaji Mai Gwanjo

20. Masallacin ‘Yan-hula na Alhaji Sani

21. Masallacin Alhaji Nasiru Musa

22. Masallacin gadar ‘Yar-Ai na Alaramma

 MAKARANTUN ALLO NA UNGUWAR AYAGI

A wannan Unguwa akwai Makarantun Allo kimanin guda Goma Sha Bakwai (17) na yanzu, da wasu kuma da suka shuxe, ga su kamar haka:

1.      Makarantar Mal. Tanko (Kofar Adoye Yanzu babu ita)

2.      Makarantar Mallam Na Gulu (‘Yar chexi )

3.      Makarantar Malam Yahya Rabi’u (Alhajin Makaranta)

4.      Makarantar Malam Mamman Mal Salisu Sabo

5.      Makarantar Malam Gambo na Malam Dogo

6.      Makarantar Malam Kabiru na Alhaji Sagiru Usman

7.      Makarantar Malam Yamani ‘Yar-cexi

8.      Makarantar Malam Yahya ‘Yan-Hula Tawakkala

9.      Makarantar Malam Xalladi (Mal Idris)

10. Makarantar Alaramma Malam Murtala

11. Makarantar gidan Alhaji Abdu Mai-leda

12. Makarantar gidan Alhaji Qassim lungun Mari

13. Makarantar Mahiru Sharif Bala

14. Makarantar jikin Warure Firamare

15. Makarantar Dandali

v Makarantun Islamiyyu a wannan Unguwa na rana guda Shida (6).

MAKARANTUN ISLAMIYYU NA RANA

Wannan Unguwa tana cikin Unguwanni na farko-farko da aka kafa Islamiyya, domin akwai Makarantar Islamiyya da Mallam Aminu Kano ya kafa da kansa a Jakara, in da yanzu Nurul Islam take, daga cikin Makarantun na Islamiyya na rana akwai su kamar haka:

1.   Makarantar Nurul Islam (safe) da (yamma) ta Malam Auwalu Hussaini da ke Jakara.

2.   Makarantar Sahatu (Safe) da (yamma) ta Liman Ustaz Kabiru Sani Salihu, da ke Gidan Alhaji Garba Wada Tawakkala.

3.   Makarantar Tarbiyyatul Aulad (safe) da (yamma) ta Malama Inna da ke tsakiyar Ayagi.

4.   Makarantar Tarbiyatul Aulad ta masallacin Alhaji Nasiru Musa (yamma) da ke Tawakkala.

5.   Makarantar Sanin Kwano Islamiyya (safe), (yamma) da (dare), dake Aisami.

MAKARANTUN DARE NA ISLAMIYYA

Makarantun dare na islamiyya a wannan Unguwa su ne kamar haka:

1.      Makarantar Banul Huda Islamiyya Jigawa.

2.      Makarantar Safiyya Ibrahim Islamiyya ‘Yan-kanbu.

3.      Makarantar Tarbiyatul Aulad Islamiyya lungu Kwari.

4.      Makarantar ‘Yar-Ai Islamiyya.

5.      Makarantar Majalisa.

6.      Makarantar Majalisa Gangaren Zango.

7.      Makarantar ‘Yar-chexi.

8.      Makarantar qofar gidan Alhaji Audu mai Leda.

9.      Makarantar Sharif Abba Sharif Aminu.

10. Makarantar Dala’ilu lungun Awaki Qofar Adoye.

11. Makarantar Dala’ilu lungun Kwari.

12. Makarantar Majalisa (manya) ta Alqur’ani.

13. Makarantar Rijiyar Wanki (manya) ta Alqur’ani.

14. Makarantar Masallacin Gidan Sarkin Ayagi Samari Alqur’ani da ilimi.

15. Makarantar Malam Habibu Khamis ta Ishiriniya.

16. Makarantar ‘Yan Hula Masallacin Na-Fatima (manya) Alqur’ani.

17. Masallacin Gangare Alqur’ani da ilimi.

MAKARANTUN BUZU

Makarantun buzu a wannan Unguwa su ne kamar haka:

1.      Makarantar Shehi Malam Shahru Lawan Dukkali (safe), da kuma Tafsirin Alqur’ani ranakun Alhamis da Juma’a da safe.

2.      Makarantar Malam Habibu Khamis (dare).

3.      Makarantar Malam Nazifi Tijjani Abubakar (dare).

4.      Makarantar Mahiru Sharif Bala (Ashafa) ranakun Alhamis da Juma’a da safe.

MAKARANTUN AZUMI

Karatuttuka da ake gabatarwa a Watan Azumi na Tafsiri da kuma Littafin Asshifa sune:.

1.   Tafsirin Alqur’ani na Khalifa Mal. Tijjani na Mal. Shahru.(dare).

2.   Tafsirin Alqur’ani na Ustaz Kabiru Sani Salihu (yamma).

3.   Tafsirni Alqur’ani na Malam Habibu Khamisu (yamma).

4.   Karatun Littafin Asshifa na Mal. Nazifi Tijjani Abubakar (rana).

MAKARANTUN MATAN AURE

Makarantun matan aure kuma Su ne kamar Haka:

1.   Makarantar Ummuhatul Mu’minat a (Sahatu) Asabar da Lahadi.

2.   Makarantar Malama Inna ranakun Alhamis da Juma’a (safe) da (yamma).

3.   Makarantar Nurul Islam ranakun Asabar da Lahadi (safe).

4.   Makarantar Raudhatus-Sayyidat karkashin jagorancin kungiyar Raudhatur-Rasul.

MAKARANTUN FIRAMARE

Makarantun Firamare na wannan Unguwa su ne:

1.      Warure Special Primary School (ta Gwamnati)

2.      Raudhatu Sahatus-Sibyan (Mai zaman kanta)

3.      Dalhat Primary School (Mai zaman kanta)

MAKARANTUN SAKANDARE

Makarantun Sakandare kuma na wannan Unguwa su ne:

1.      Makarantar “Collage Of Qur’anic Studies” ta Liman Ustaz Kabir Sani Salihu

2.      Makarantar “Nurul Islam Secondary School Ayagi”

3.      Makarantar “Kansakali Senior Secondary School Aisami.

4.      Makarantar “Dalhat Secondary School Ayagi.

Karatu na musamman (Extra Lesson) guda

Haka kuma akwai karatun ba da sahidar koyo da koyarwa, NCE a makarantar Aisami Asabar da Lahadi.

Kungiyoyi da suke Unguwar Ayagi:

1.      Ayagi United

2.      Ayagi New Generation

3.      Raudhatul-Rasool Ayagi

4.     

SUNAYEN LAYIKA DA LUNGUNA

Kasancewar wannan Unguwa ta Ayagi tana da fadin qasa domin tana da kimanin Gidaje har Guda….. , haka zalika tana da Layika da Lunguna masu tarin yawa, ga wasu daga ciki:

1.   

Babban Soro

2.   

Kwar-galla

3.   

Kar-Jaji

4.   

Ziri

5.   

Gangaren-Zango

6.   

Yach-chedi

7.   

Lungun Mari

8.   

Rijiyar Wanki

9.   

Gidan Makaranta

10.

Layin Sahatu

11.

‘yan Balangu

12.

Lungun Tsamiya

13.

Dandali

14.

‘Yanhula

15.

Aisami

16.

Lungun Gidan Awaki

17.

Jigawa

18.

Dakalin Xan kata

19.

Majalisa

20.

KAMMALAWA

Kamar yadda muka ji tarihin Unguwar Aygi, da tarihin Sarakunanta da Hakimanta da dai sauransu, za a iya qari ko ragi a dukkan wadannan bayanai, in samu wani canji a kowanne lokaci

Dafatan Allah Ta’ala zai datar damu, ya shiryar damu ya karamana tsoronsa da biyayya agareshi, ya karamana Lafiya da zaman Lafiya da kwanciyar hankali a Unguwarmu da sauran Unguwannnin da ke kewaye da mu, dama jiharmu baki xaya.

Allah ka kara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi Muhammad da ahalin gidansa da dukkan sahabbansa, da wadanda suka bishi da kyautatawa har zuwa ranar karshe.

Alhamdulillah.

MANAZARTA

-  Bahago, Alhaji Ahmad (1998) ‘Kano Ta Dabo Tumbin Giwa, Tarihin Unguwannin Kano Da Mazaunanata Da Gawuna Da Qofofin Gari’, Kano;  Munawwar Books Foundation.

-  Gwangwazo, Maje Ahmad (2001) ‘Kano Garin Albarka’ Indiana University.

-  Sarkin Ayagi Malam Muhammadu Inuwa (19/04/1976) Kassette: Hira da su Alhaji Xanjuma Sani Ayagi da wasu a Gidan Sarkin Ayagi Inuwa da ke Cikin Gidan Sarkin Ayagi, Kano.

-  Sarkin Ayagi Alhaji Salihu Inuwa (1985) Takarda da ya yi shifta Abdulqadir Salihu Inuwa yake rubutawa.

-  Malam Ahmadu Zakariyya Inuwa (2012) Hira da Abdurrashid Baba Ayagi a Soron Gidansu da ke Cikin Gidan Sarkin Ayagi, gidan Alh. Baba Zakari, Takardar da ya ba ni an rubutata

-  Xan Masanin Ayagi, Hadi xan Shehi Tijjani (Na-mama) xan Abubakar (Tagu) xan Salihu (i) xan Abdulqadir xan Muhammadu Nasiru Jatau xan Mahmudu xan Abdulkarimi xan Abdullahil-Iraqi, a wani rubutu da yayi (2025)

- Kundin Masarautar Ayagi, (2021)



[1] - Bahago, A,A, Kano Ta Dabo Tumbin Giwa Tarhin Kano Da Mazaunanta Da Ganuwa Da Qofofin Gari,

[2] - Littafin Bahago, A,A, Kano Ta Dabo Tumbin Giwa Tarhin Kano Da Mazaunanta Da Ganuwa Da Qofofin Gari,

[3] -Malam Qassim, almajirin Shehi Sani Auwalu ne a can Ibadan.

[4] - Babban Malami Shehu Abubakar Mijin-yawa, mahaifiyarsa ita ce Malama Ruqayya (Aika) yar Sarkin Ayagi Malam Salihu xan Mal. Abdulqadir xan Sarkin Ayagi Mal. Nasiru Jatau. Mahaifinsa kuma shi ne  Malam Muhammadu xan Abdullahi.

[5] - shi ne wanda aka fi sani da Wali Ci-gero yana daga cikin manyan waliyyai a nan garin kano, 

[6] - Muhammadu Kwalayi bafatake ne kuma Attajiri, wanda yake sayar da manyan riguna don kaisu garuruwa, gidan sa yana nan dab da gidan sarkin Ayagi kuma zuriyarsa har yanzu sunanan cikin Unguwar.

[7] - Jam’i ne na ‘zanko’ wato: tamkar dabino.

[8] - Sarkin Ayagi Malam Muhammadu Inuwa (19/04/1976) Kassette: Hira da su Alhaji Xanjuma Sani Ayagi da wasu a Gidan Sarkin Ayagi Inuwa  da ke Cikin Gidan Sarkin Ayagi, Kano.

[9] - Waxanda suka yi wannan hira da shi kuwa su ne: Alhaji Xanjuma Sani Ayagi, Alhaji Mukhtari Zakari Ayagi da (Dr) Auwalu Sulaiman Ayagi a gaban ‘yan uwanmu masu yawa kamar : Alh Kabiru Sani Ayagi, Alh. Salmanu Baba Ayagi, Nura Sulaiman Ayagi, da sauransu.

[10] - Sarkin Kano Yaji xan Daxi ya yi sarautar Kano a shekarar 1753 – 1768, sarki na 40 a sarakunan Kano kafin zuwan Fulani. Sarki ne mai nagarta kuma mai adalcimutum ne mai son zaman lafiya.

[11] - Al-islam Fi Nijeriya- Al-ilori S.A.A shafi na 39 zuwa shafi na 42.

[12] - Mal. Sulaimanu Tereta: asalinsa Sharifi ne mutumin garin Tudun Wada, Sarkin Ayagi Muhammadu Inuwa ya riqe shi xa, inda ya aura masa babbar xiyarsa Baba Iyan-Fura: ita suna ta ci na matar Sarkin Ayagi Salihu, sun haifi ‘ya’ya Goma (10).