TASIRIN AZUMI
GA LAFIYAR DAN ADAMNazarin Addini
Da Kimiyya
(Wanda Ya Tattara Bayanan Manyan Malamai Da
Likitocin Duniya)
Wallafar
Auwal Zakari
Ayagi
(Barden Ayagi)
2026
Hakkin Mallaka (M)
Auwal
Zakari Ayagi (Barden Ayagi)
Lambar Waya: 07038775781
Bugu Na daya 2026/1447
TSARAWA DA DAUKAR NAUYIN BUGAWA
Al-Azmiyya
Islamic Foundation:
No. 313 Al’Mustapha
House Kadawa Western Bypass AL’EEMAAN Medicine Store Building, Adjacent to Gwarzo Road Kano.
E-mail: auwalzakari@gmail.com
www.sautulazimiyya.blogspot.co.uk/
GSM: 07038775781, 08023615685
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan Littafi ga Babban
Malamina Jagorana Marigayi Ustaz Auwal Isa Yakasai (Rahimahullah) Allah
yajikansa Allah ya gafartamasa, Amin.
GODIYA
Da
sunan Allah mai yawan Rahama Mai Jin kai, Tsira da Aminci su kara tabbata ga
shugaban halitta Annabi Muhammad Tsira da Aminci su qara tabbata a gareshi da
ahalinsa da sahabbansa baki daya.
Da farko, ina mika godiya ta musamman ga
Allah Maɗaukakin
Sarki, wanda ya bani ikon kammala wannan littafi cikin aminci da nutsuwa. Shi
ne Mai baiwa bawa karfin tunani, hikima da nutsuwar zuciya, Ya kuma bayyana
masa abin da zai amfane shi da al’umma.
Ina mika godiya ta musamman ga Malam Salisu Abdul-Salisu, wanda ya
shafe shekaru da dama yana jagorantar faɗakarwa
a shafinsa na Zamantakewa dake manhajar Facebook, a dukkan watan Ramadan. Irin
wannan jajircewa da yake yi wajen yada ilimi da wayar da kan jama’a shi ne ya
kasance babban abin da ya karfafa gwiwata wajen rubuta wannan littafi. Allah Ya
saka masa da mafificin lada, Ya kara masa ilimi, dacewa da nisan kwana.
Ina gode wa malamai da masana da aka
ambata a cikin wannan littafi bisa irin gagarumar gudunmawar da suka bayar a
fagen ilimi. Rubuce-rubucensu da fassarar bayanan kimiyya da na addini su ne
ginshikan da wannan littafi ya dogara a kansu.
Godiya ta musamman ga Abokina Mal. Arabi
Sammani, da dan’uwana Imam Sani Zakariyya da sukai duba tare da gyare-gyare,
sai abokai, dalibai da dangi, waɗanda
a lokuta daban-daban suke ba ni shawara, goyon baya da addu’a. Hakan ya taimaka
matuka wajen saukaka wannan rubutu, da bincike da kuma tsara littafin yadda ya
kamata.
Ina kuma godewa masu karatu, waɗanda
su ne ginshikin dalilin rubuta wannan littafi. Idan aka sami kura-kurai a ciki,
ina roqon
a sanar da mu domin gyara. Idan kuwa aka samu daidai, ina roqon Allah Ya sanya
wannan aiki cikin abin da ake rubutawa a mizani na ranar sakamako.
Allah Ya sanya wannan littafi ya amfanar
da kowa, ya kuma zamo hanya ta qarin ilimi da tsaftace tunani.
Auwal Zakari
Muhammad Ayagi
(Barden Ayagi)
5 ga Zulhijja 1445= 1/6/2025
TA’ALIKI
Da sunan Allah Maɗaukaki, Mai yalwar rahama, Mai girman jin ƙai. Tsira da
amincin Allah su tabbata ga Shugaban halittu baki ɗaya, shugaban masu azumi, Annabi Muhammad (ﷺ), da iyalansa tsarkaka, da sahabbansa zaɓaɓɓu, da dukkan waɗanda suka bi sahunsu da kyautatawa har zuwa ranar
sakamako.
Bayan haka, hakika na karanta wannan littafi karatu na
tsanaki da zurfin nazari, tare da yin bitar abubuwan da ya ƙunsa dalla-dalla.
Sai na same shi littafi ne na musamman, wanda ya kebanta da irin rubuce-rubucen
da aka saba yi kan azumi, musamman ta fuskar haɗa ilimin addini da na zamani cikin tsari guda mai
ma’ana da armashi.
Marubucin ya yi kyakkyawan fashin baki wajen bayyana
tasirin azumi ga lafiyar ɗan Adam, ta
hanyar kawo bayanai na kimiyya na zamani tare da jingina su da ƙa’idojin Shari’a da fahimtar
malamai. Haka kuma, ya zurfafa bayani kan hukunce-hukuncen azumi, ya gabatar da
su cikin hikima, da tsari, da hujjoji masu ƙarfi.
Abin da ya ƙara wa littafin armashi shi ne irin
bajintar da marubucin ya nuna wajen saukar da kalmomi masu tsauri da ma’anoni na ilimi
zuwa harshen Hausa, cikin salo mai daɗi, mai sauƙin fahimta, ba tare da rage darajar ma’anar asali ba.
Wannan fasaha ta sa littafin ya zama abin dogaro ga malamai, ɗalibai, da masu neman ilimi gaba ɗaya.
A ƙarshe, ina ba da shawara mai ƙarfi, tare da
kwaxaitarwa, ga al’ummar Musulmi da su karanta wannan littafi, su zurfafa
fahimta a cikinsa, su yi aiki da abin da ya ƙunsa, domin samun alheri mai yawa a
addini, lafiya, da rayuwar yau da kullum.
Wassalāmu Alaikum wa Rahmatullāhi wa Barakātuh.
IMAM SANI ZAKARIYYA
Limamin Masallacin Juma’a Na Ibadur Rahaman Dake Tudun Yola GRA Kano
State
24/12/2025
TAKRĪR
Da sunan Allah Maɗaukaki, Mai yalwar rahama, Mai girman jin ƙai. Tsira da
amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (ﷺ) shugaban masu azumi, da iyalansa, da sahabbansa, da
dukkan masu bin tafarkinsa na gaskiya.
Bayan haka, hakika na karanta wannan littafi karatu na
fahimta da tantancewa, tare da yin bitar abubuwan da ke cikinsa a mahangar
ilimi da tsari. A yayin wannan nazari, na yi wasu gyare-gyare da shawarwari
domin ƙara inganta salo, daidaita lafazi, da kuma ƙarfafa ma’anoni, ta yadda
littafin zai fito cikin tsari mai armashi da sauƙin karantawa.
Na tarar da littafin yana ɗauke da muhimman bayanai da suka shafi azumi da
tasirinsa ga lafiyar ɗan Adam, inda
marubucin ya nuna ƙwazo wajen haɗa fahimtar addini da bayanan zamani cikin hikima da
daidaito. Haka kuma, littafin ya bi ƙa’idojin ilimi wajen gabatar da
hukunce-hukuncen azumi a addinance, tare da bincike a manyan litattafan addini.
Gyare-gyaren da aka yi sun ta’allaka ne kan inganta
lafazi, daidaita jimloli, da kuma tabbatar da cewa saƙon da ake son
isarwa ya fito a sarari, ba tare da rage ma’anar asali ba. Wannan ya ƙara wa littafin ƙima da dacewa da
amfani ga malamai, ɗalibai, da
al’umma gaba ɗaya.
A bisa haka, ina ganin littafin ya cancanci a fitar da
shi ga jama’a domin karantawa da amfana, musamman a wannan zamani da ake buƙatar ilimi mai haɗa addini da lafiya. Ina kuma roƙon Allah Ya sanya
wannan aiki ya zama abin alheri da lada ga marubucin da duk wanda ya amfana da
shi.
Wassalāmu Alaikum wa Rahmatullāhi wa Barakātuh.
Mal. Arabi
Sammani Tudun Nufawa
(12/01/2026)
TSOKACI
Littafin
“Tasirin Azumi ga Ɗan
Adam”
littafi ne mai matuqar muhimmanci da ya zo a kan lokaci, wanda ya haɗa
ilimin addini da na zamani cikin hikima da fahimta. Marubucin ya yi qoqari matuqa
wajen bayyana azumi ba kawai a matsayin ibada ba, har ma a matsayin wata babbar
hanya ta inganta lafiyar jiki, tunani da rayuwar ɗan
Adam.
Abin
da ya fi burge ni shi ne yadda littafin ya gina hujjoji bisa Alqur’ani,
Hadisai da kuma bayanan masana lafiya, yana nuna cikakken tasirin azumi ga
tsarin jiki, narkewar abinci, gyaran qwayoyin halitta da kuma tsarkake zuciya.
Wannan ya sa littafin ya zama abin amfana ga kowane musulmi, da ma wanda ba musulmi
ba, mai sha’awar fahimtar hikimar azumi.
A
tsawon shekaru, shafin zamantakewa
dake Facebook ya kasance dandali na ilimantarwa ga al’ummar musulmi a sassa
daban-daban na duniya, inda muke tattauna batutuwa da dama na addini, tarbiyya
da lafiya. Wannan maudu’i na Tasirin
Azumi ga Lafiyar Ɗan Adam
yana daga cikin muhimman jigogin da muke yawan bayyanawa, kuma wannan littafi
ya zo ya qara zurfafa fahimta tare da tattara bayanai a wuri guda.
Ina
yaba wa marubucin bisa wannan gagarumar gudunmawa, tare da fatan littafin zai
samu karɓuwa
sosai, ya kuma zama haske ga masu karatu wajen fahimtar azumi a matsayin ibada
da babbar ni’ima ga lafiyar ɗan Adam.
—
Salisu Abdul
ABUBUWAN DA KE CIKI
Sadaukarwa…………………………………
Jinjina/Yabo…………………………………
Godiya………………………………………
Ta’aliqi………………………………………
Taqrir
……..…………………………………
Tsokaci………………………………………
Abubuwan da ke ciki…………………………
Gabatarwa……………………………………
BABI NA 1: Muhimmancin Azumi A Addini Da
Kimiyya
§ Mahimmancin
Azumi a Addini……………
§ Mahimmancin
Azumi a Kimiyya …………
§ Dangantakar
Azumi a Addini da Kimiyya…
§ BABI NA 2: Ma’anar Azumi a
Musulunci
§ Ma’anar
azumi………………………….......
§ Dalilan
Wajibcin azumi……………………
§ Fa’idar
azumi ga ruhu………….....................
§ Hadisai
da suke nuna falalar azumi………....
§ Farlanta
azumin ramadan………....................
§ BABI NA 3: Nazarin Malaman
Musulunci da likitocin Duniya Kan Azumi da Lafiya
§ Nazarin
Malaman Musulunci……….............
§ Ibn
Taymiyyah Rahimahullah........................
§ Ibn
Qayyim Al-jawziyya…...........................
§ Imam
Ghazali …….......................................
§ Sheikh
Bin Baz…………………………….
§ Sheik
Yusuf Al-Qaradawi……………… …
§ Yin
azumi yana qara lafiya.............................................................
§ Nazarin
Likitocin kan tasirin azumi ga lafiya………....................
§ Rashin
Lafiyar da azumi ke yiwa amfani………...........................
§ Qarin
bayani kan ra’ayoyim masana da masu bincike……...........
§ Magance
manyan cututtuka ta hanyar azumi……….....................
§ Tasirin
azumi ga lafiya jiki da rage haxarin cututtuka……...........
§ BABI NA 4: Abubuwan Da Likitocin
Duniya Suka Gano
§ Dr.
Yoshinori Ohsumi ………......................................................
§ Dr.
Valter Longo ……....................................................................
§ Dr.
Mark Mattson – Lafiyar kwakwalwa…….…….…..................
§ Dr.
Jason Fung – Maganin ciwon suga da qiba……......................
§ Harvard
Medical School – Metabolic reset……….……...............
§ Mayo
Clinic USA – Detoxification da
cholesterol………..
§ WHO
– Shawarwari akan azumi………………………................
§ BABI NA 5: Yadda Azumi Ke Aiki A
Jiki (Scientific Mechanisms)
§ Autophagy
(Gyaran cells)……………………….……..................
§ Hormonal
reset……………….................
§ Kona
kitsen ciki (Fat burnning)…………
§ Tasirin
azumi ga hanta, koda, da zuciya………..…….....
§ Tasirin
azumi ga kwakwalwa da tunani………………....
§ BABI NA 6: Amfanin Azumi Ga
Cututtuka
§ Ciwon
suga (Type 2)…………………………………....
§ Ciwon
zuciya da Hawan Jini……………………….……
§ Ciwon
kiba…………………………………….…….…..
§ Cutar
Alzheimer da mantuwa…………………………....
§ Cututtukan
Borin Jiki da Daji……………..…….............
§ Lafiyar
Jiki da Tinani da qwaqwalwa…………….…….
§ Hutawar
hanji………..........................................................
§ Cutar
Shaye-shaye……….....................................................
§ Cutar
Damuwa………........................................................
§ Matsalolin
da kan iya samin mai azumi……….................
§ BABI NA 7: Cututtukan da basa
Bari a yi azumi
§ Ciwon
Suga………………………..…...............................
§ Ciwon
Qoda………………………...……….……..…...…
§ Ciwon
Qwaqwalwa………………………………..……
§ Ciwon
Gyambon Ciki mai tsanani………………...........
§ Tarin
Fuka da Ciwon Numfashi………………..….……
§ Ciwon
Hanta………........................................................
§ Ciwon
Zuciya……................................................................
§ Masu
Juna biyu da Masu Shayarwa………..........................
§ BABI NA 8: Kwatankwacin Azumin
Musulunci Da Intermittent Fasting (Azumin Likitanci)
§ Azumin
Musulunci………………………………….……....
§ Intermittent
Fasting (Azumin Likitanci)………………........
§ BABI NA 9: Hanyar Cin Abinci mai
lafiya yayin buxe Baki
§ Abincin
da ya fi dacewa wajen buxe baki…………………
§ Abincin
da ya kamata a guje masa………………...…........
§ Misalin
jadawalin cin abinci mai gina jiki……….…….......
§ Abincin
da yafi dacewa wajen Sahur…................................
§ BABI NA 10: Azumin Nafila
da ba na Watan Ramadan ba
§ Azumin
Litinin da Alhamis ……………………..…..….....
§ Azumin
Ranakun Haske………………………......….........
§ Azumin
Tasu’a da Ashura…………………….………...…
§ Azumin
Arfa………………………………….....…............
§ Azumin
watan Sha’aban…………………..……….............
§ Azumin
Annabi Dauda…………………………….............
§ Azumin
Sitti Shawwal………………….…....….................
§ Azumin
Gwauraye…………………………...….…............
§ Azumin
Watan Rajab…………………………..….…........
§ BABI NA 11
Hukuncin Azumin
‘Ya Mace
§ Azumin
mace mai Jini Haila da na Biqi………..…
§ Azumin
Mace Maishayarwa………….………..…
§ Azumin
ga Mace mai Jinin Rashin Lafiya ……..…
§ Azimin
Matar Aure……….……….……………...
§ Tsokaci
Ga Mai Karatu ……………………………………
§ Kammalawa
……………………………………....
§ Taqaitacce
tarihin Marubuci………………………
§ Manazarta
(References),………………… …….....
GABATARWA
Da sunan Allah, Mai Rahama
Mai Jin Qai. Tsira da amincin Allah su qara tabbata ga shugaban halitta, Annabin
rahama, (SAW) da ahalinsa da dukkan sahabbansa baki xaya.
Bayan haka, dalilin da ya sa
ni na rubuta wannan littafi shi ne: a duk shekara cikin watan Ramadan, Malam Salisu Abdul-Salisu yana
jagorantar wasu jerin faɗakarwa a shafinsa na
Facebook mai suna Zamantakewa.
Tun daga ranar 1 zuwa 30 ga watan Ramadan, yakan samar da jadawalin malamai da
masana a fannoni da dama, don su gabatar da darussa daban-daban.
A kowace shekara ni ma nakan
samu kaina cikin masu bada gudunmawa wajen faxakarwar, kuma galibi ana bani
dama ne in yi bayani mai taken “Tasirin Azumi ga Lafiyar xan Adam.”
Hakan ya kan saka ni yin bincike mai zurfi, domin na tattara bayanan da masana
kimiyya suka rubuta kan amfanin azumi ga lafiyar ɗan Adam, tare da abin da manyan malamai suka faɗa daga cikin littattafansu, da fatawoyinsu.
Daga qarshe ne na ga ya dace in haɗa waɗannan
muhimman bayanai cikin littafi guda xaya, domin amfanin al’umma, musamman ma
ganin irin tasirin azumi ga lafiya da kuma rawar da yake takawa wajen tsaftace
jiki da ruhin ɗan Adam.
Musani Azumi ibada ce daga
cikin ginshiqan Musulunci wand ya haɗa ruhi, da ɗabi’a, da kuma lafiyar jiki.
Tun Shekaru da dama, malamai na Musulunci sun yi rubuce-rubuce da bayanai akan
amfanin azumi ga jiki da zuciya. A yau, binciken kimiyya daga manyan likitoci,
cibiyoyin bincike, jami’o’i, da hukumomin lafiya na duniya sun tabbatar da
abubuwan da malamai suka yi ishara da shi tun asali.
Wannan littafi ya tattara
bayanai daga manyan malamai da manyan likitocin duniya, da cibiyoyin bincike.
littafin ya haɗa vangaren Addini da kuma na Kimiyya, ya kuma kawo hujjoji, da misalai, da
bayanai masu qarfi, domin musulmi ya fahimci cewa azumi ibada ce mai girma kuma
dabarun kara inganta lafiya.
Ina roqon Allah ya saka
wa Malam Salisu da alheri bisa irin faɗakarwa da wayar da kai da yake yi a wannan shafi. Ina kuma fatan Allah
Ya sanya wannan littafi ya zama hanya ta alheri ga mai karantawa, ya ilmantar
da su game da amfanin da azumi kanyi ga lafiyarsu, ya kuma qarfafi masu
karatun wajen kula da jikinsu da lafiyarsu. Domin kuwa Bahaushe ya ce: “Lafiya
uwar jiki.”
Duk wani kuskure da aka
hango a cikin littafin, ina roqon a sanar dani domin a gyara. Abin da kuwa ya zo daidai, Allah Ya karɓa ya sanya shi a mizanin alheri.
Auwal Zakari Muhammad Ayagi
(Barden Ayagi)
5 ga Zulhijja, 1445 H — 1/6/2025 M
BABI NA XAYA
MUHIMMANCIN AZUMI A ADDINI
DA KIMIYYA
Azumi babbar ibada ce da ta haɗa tsakanin gyaran ruhi, tsabtace zuciya, da inganta lafiyar jiki. Wannan
ya sa Musulunci ya sanya azumi cikin rukunan addini guda biyar, kuma kimiyya ta
tabbatar da hikimar da ke cikinsa ta fannoni da dama.
1. Muhimmancin Azumi a
Addini
a. Azumi ruku nine na
Musulunci
Allah Madaukakin Sarki ya yi umarni da yin azumi domin qarfafa biyayya, tsoron Allah
da tsaftar zuciya.
Kamar yadda (SWT) yake cewa:
﴿
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى
الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ﴾ [ البقرة: 183]
Ma’ana:
“Yã
ku waɗanda kuka yi
imani! An wajabta muku azumi, kamar yadda aka wajabta wa waɗanda suka gabaceku, domin ku zama masu
taqawa.” [1]
Wannan
ayar hujja ce mafi karfi da ta nuna cewa Azumin
watan Ramadan Wajibi ne ga duk Musulmi baligi, mai hankali,
wanda ba shi da uzuri.
Azumi
hanya ce da mutum ke miqa wuya ga Ubangiji ta hanyar nisantar sha’awa saboda
bin umarninsa.
b. Qarin Tsoron Allah (Taqawa)
Allah Ya bayyana cewa babban manufar azumi ita ce:
“ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ”
“Domin
ku samu taqawa.
Taqawa tana nufin tsoron Allah, tsarkake zuciya, aikata alheri da gujewa
zunubi. Azumi yana koyar da mutum juriya, haquri da duqufa ga ibada.
c. Karkatar da zuciya daga Duniya
zuwa Ibada
Lokacin azumi mutum kan rage yawan shagala, ya qara karatun Alqur’ani, da ibada da tunani
mai kyau. Wannan yana haifar da nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali.
d. Raunata Shaiɗan da qarfafar Ruhi
Annabi
(SAW) ya ce:
الصِيَامُ جُنَّةٌ
Ma’ana: Azumi Garkuwa ce: wato kariya ne ga bawa.
Manzon Allah ﷺ ya ce:
“Azumi garkuwa ne. don haka idan ɗayanku yana
azumi, kada ya yi magana ta batsa, kuma kada ya yi hayaniya ko faɗa. Idan wani ya
zage shi ko ya neme shi da faɗa, sai ya ce: Ni ina azumi ne.” [2]
Azumi yana zama garkuwa ne domin:
·
Yana kare Mutum daga Zunubi – ta hanyar rage sha’awa da fushi.
·
Yana kare Mutum daga Wutar Jahannama – idan aka yi shi da gaskiya da tsoron Allah.
·
Yana tarbiyyantar da Zuciya – domin yana
koya haquri, kunya da tsoron Allah.
Saboda
haka azumi ba hana ci da sha kawai ba ne kaxai, a’a tarbiyya ce ga zukatanmu
da halayen mu.
e. Koyi ne da Annabi (SAW) da Sahabbai
Annabi (SAW) ya yi azumci watan Ramadan, sannan ya yi Azumin Litinin da
Alhamis, da sauran ranakun da zamu kawosu a nan gaba. Wannan hujja ce kan
muhimmancinsa ga Musulmi.
2. MUHIMMANCIN
AZUMI A KIMIYYA
Kimiyya ta tabbatar da cewa azumi ba ibada ce kawai
ba, magani ne da yake tasiri ga jiki da kwakwalwa. Domin masana da dama da
cibiyoyin bincike irin su Dr. Yoshinori Ohsumi [3], Harvard Medical School, Dr. Valter Longo [4], da Cleveland Clinic [5] sun yi bincike da dama kan
azumi, kuma suka bayyana amfaninsa da dama, ga wasu daga cikin manyan amfaninsa
da binciken na su ya bayyana:
a. –
Tsabtace Jiki daga Guba (Autophagy): Dr. Yoshinori Ohsumi ya binciko cewa azumi hanya ce
da jiki ke kawar da tsofaffin kwayoyin cuta, da gubobi[6] da tarkacen da suke haifar
da cututtuka. Har sai da ya sami kyautar (Nobel Prize) saboda gano wannan
bayani da yayi a cikin binciken sa.
b. Rage qiba
da daidaita sinadaran jinni: Azumi yana taimakawa wajen, rage kitse mai haɗari (bad cholesterol) haka
nan yana qara kitse mara cutarwa (good cholesterol). Sannan yana daidaita sukarin
Jiki (glucose), domin yana taimaka wa masu ciwon suga, sannan yana rage qiba
cikin tsari mai kyau, batare da cutarwarba.
Don
haka masu son rage qiba ba sai sunyi amfani da wasu magungunma masu cutarwa ba,
muddin suka lazumci yin azumi, qibarsu zata ragu sannan jikin su zai qara
lafiya.
c. Gyaran kwakwalwa da qara
kaifinta: Azumi
yana qara yawan sinadarin (BDNF) ‘BDNF’
na nufin (Brain-Derived
Neurotrophic Factor): wato wani sinadari ne na (protein)
da kwakwalwa take samarwa, wanda ya ke taimaka wa qwayoyin halittar kwakwalwa
(neurons) su rayu, ya qarfafa
koyo da tunani,
ya inganta ma’ajiyar qwaqwalwa
(memory), da kuma gyaran kwakwalwar kanta
idan ta sami rauni.
A takaice: BDNF tamkar abincin
kwakwalwa ne domin yana waxannan ayyuka:
1.
Qara hankali da fahimta
2.
Inganta qwaqwalwa
3.
Rage damuwa (depression & anxiety)
4.
Kare kwakwalwa daga tsufa da
cututtuka
5.
Qarfafa sababbin qwayoyin kwakwalwa
(neurogenesis)
Abubuwan da su ke qara yawan BDNF
sun haɗar da:
·
Azumi Na Musulunci ko na Likita (Ramadan/ intermittent fasting)
·
Motsa jiki (exercise)
·
Karatu da tunani mai zurfi
·
Yin bacci mai kyau (cikin Nutsuwa
kuma mai yawa)
·
Cin abinci mai gina jiki, kamar kifi, gyaɗa, kwakwa, da kayan lambu da makamantan su)
Wannan
ya dace da Hadisin Annabi ﷺ:
da muka kawo abaya, da yake cewa: “Azumi garkuwa ce” wato garkuwa ga jiki, da
zuciya da kuma kwakwalwa.
d. Kare jiki
daga cututtuka masu tsawo (chronic diseases): Masu bincike sun tabbatar da cewa azumi na taimaka
wa masu waxannan cututtuka:
§
Ciwon zuciya
§
Ciwon Hawan jini
§
Cutar Mantuwa (Alzheimer)
§
Cutar Rawar Jiki (Parkinson)
§
Cutar kumburin Jiki (Inflammation)
§
Kiyaye hatsarin kamuwa da cutar daji (Cancer) a wasu matakai
e. Sake daidaita aikin jiki
da Gyaran tsarin narkewar abinci (Metabolic Reset): Metabolic reset: yana nufin lokacin da jiki ya daina dogaro da sukari wato (glucose) kaɗai, ya koma amfani da mai (fat) don samar da kuzari, hakan yana gyara yadda yake narkar
da abinci da sarrafa kuzari.
Yawanci hakan yana faruwa ne, a lokacin da ake yin azumi, ko
lokacin da aka rage cin abinci akai-akai, wato lokacin da ake yin intermittent
fasting.
Amfaninsa: yana rage qiba, yana daidaita sukarin cikin jini, yana rage
kumburi (inflammation), yana qara lafiyar kwakwalwa, yana qara BDNF, sannan
yana rage haɗarin kamuwa da cututtuka, kamar ciwon sukari da ciwon mantuwa.
Dangantakar Metabolic reset da Azumi: Azumi yana baiwa jiki damar hutawa daga cin abinci akai-akai, sannan yana
gyara kansa da kansa, kuma yana tsarkake shi jiki xin, sannan ya inganta aikin
da yake yi.
f. Tsawaita rayuwa (Longevity): Binciken Jami;ar Stanford da Jami’ar Harvard, ya
nuna cewa azumi yana taimaka wa tsawon rai, saboda yana rage yawan gubar da ke
jiki da rage matsa lamba ga kwayoyin halitta (wato kwayoyin halitta suna samu
suna hutawa).
3. DANGANTAKAR AZUMI A ADDINI DA KIMIYYA
§ Addinin Islama ya jaddada yin azumi, domin yana tsarkake
zuciya da qarawa mai yin sa kusanci da Allah.
§ Kimiyya kuma ta tabbatar da cewa wannan tsarkakewar
tana sake tsara jiki gaba ɗaya, daga kwakwalwa, jini, hanji har zuwa qwayoyin halitta.
§ Hakan ya nuna cewa hikimar da Allah Ya sa cikin azumi
ta wuce abin da ilimin ɗan Adam zai iya fahimta.
BABI NA BIYU
MA’ANAR AZUMI A MUSULUNCI
1. Ma’anar Azumi (As-Sawm): A shari’a, azumi
shi ne: “Kaucewa daga cin abinci, ko abin sha, ko kusantar iyali, tare da duk wani
abin da yake lalata azumi, tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana,
saboda girmama Allah.”
2. Dalilan Wajibcin Azumi: An
fara Azumin ne tun a zamanin al’ummomin Annabawan da suka gabaci Manzon Allah
(SAW).
Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana a
cikin Al-kur’ani cewa:
"يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡكُمُ
ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ"
“Ya ku
wadanda kuka yi imani, an farlanta muku yin azumi, kamar yadda aka farlanta shi
ga al’ummomin da suka gabace ku, tsammanin za ku samu jin tsoron Allah.” [7]
Wannan ya nuna cewa asalin
manufar azumi ita ce gyaran zuciya.
Malaman tarihin Musulunci sun bayyana
cewa gabanin manzancin Annabi Muhammadu ﷺ,
al’ummomin baya kan yi azumi ne a lokuta daban-daban, sannan yawan kwanakin da
suke yin azumin ya bambanta.
Alal misali, kafin a aiko Manzon Allah ﷺ
Yahudawa da Nasara har da Quraishawa masu bautar gumaka a lokacin sun kasance
suna azumtar ranar Ashura, 10 ga watan Muharram.
Azumi
na xaya daga shika-shikan Musulunci
Daga cikin shika-shikan Musulunci guda
biyar, Azumtar watan Ramadan xaya ne daga cikin su wato:
1.
Kalmar Shahada
2.
Sallah
3.
Azumin
watan Ramdan
4.
Zakka
5.
Aikin Hajji
Talakawa da mawadata sun yi tarayya a
cikin ukun Farko; ragowar biyun kuma (Zakka da Hajji) suka takaita ga mawadata
(wato waxanda Allah ya horewa).
Bisa koyarwar Addinin Islama, a watan
Ramadan, al’ummar Musulmi kan ninka yawan ayyukansu na alheri da neman kusanci
da Allah, babu dare, babu rana, saboda kwaxayin samun dacewa da falalar watan.
3. Fa’idar Azumi Ga Ruhi (Spiritual Benefits): Wannan
yana nuni da irin amfanin da azumi ke yi ga zukata, da ruhin xan Adam da kuma
kara masa kusanci da Allah. Ba wai iya jikin mutum kaɗai
kan samu wannan fa’ida ba, a’a har ma da gavvansa, da kuma yanda azumin ke qarfafa koyi da halaye
na gari, da tsoron Allah da tsaftace zuciya.
A
nan zamu fahimci fa’idodin azumi da suka haxa da:
§ Yana kawar da son zuciya
§ Yana daidaita zuciya da hankali
§ Yana inganta natsuwa
§ Yana sanya ɗa’a ga Allah
§ Yana Qara Taqawa
(Tsoron Allah)
§ Yana Qarfafa Ibada
§ Yana
tsarkake Zuciya Daga Hassada, Girman kai
§ Yana Qara Kusanci da
Allah
§ Yana
Gina Xabi’a da Halaye na Gari
§ Yana
Raunana Shaixan da qarfafa
ruhin xan Adam
4. Hadisai Da Suke Nuna Falalar Azumi
1. Kariya daga Zunubi da Wuta
Annabi ﷺ ya ce: الصِيامُ
الجُنَّة
“Azumi garkuwa ce.”Ma’ana:
“Azumi garkuwa ce (kariya ce daga zunubi da ayyukan da suke kaiwa ga wuta).” [8]
Wannan kalma ta garkuwa ta qunshi
ma’anonin addini da na lafiya. (Kamar yadda muka bayyana
a baya)
2. Tanadar Babbar qofa a Aljanna
ga masu Azumi kaxai: Ar-Rayyan
"إِنَّ
فِي الْجَنَّةِ بَابًا يُقَالُ لَهُ الرَّيَّانُ، يَدْخُلُ مِنْهُ الصَّائِمُونَ…"
Ma’ana:
“A cikin Aljanna akwai qofa da ake kira Ar-Rayyan; masu azumi ne za su shiga
ta…” [9]
Ita wannan qofa mai suna Ar-Rayyan an tanadeta ne a cikin Aljanna ga
masu Azumi su kaxai.
3- Nisanta Fuskar
Bawa Daga Wuta na Shekaru 70
مَنْ صَامَ يَوْمًا فِي سَبِيلِ اللَّهِ، بَاعَدَ اللَّهُ وَجْهَهُ عَنِ
النَّارِ سَبْعِينَ خَرِيفًا
Ma’ana: “Duk
wanda ya yi azumin rana guda saboda Allah, Allah zai nesanta fuskarsa daga wuta
na tsawon shekaru 70.” [10]
4. Sanya Tazara kamar Sama da qasa ga mai Azumi da wuta
مَنْ صَامَ
يَوْمًا فِي سَبِيلِ اللَّهِ، جَعَلَ اللَّهُ بَيْنَهُ وَبَيْنَ النَّارِ
خَنْدَقًا كَمَا بَيْنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ
Ma’ana:
“Wanda ya yi azumi saboda Allah, Allah zai sanya tazara kamar tsakanin sama da qasa tsakanin shi da wuta.” [11]
5. Azumi yana wanke zunubai
مَنْ صَامَ
رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا، غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ
Ma’ana: “Wanda ya azumci Ramadan cikin imani da neman lada,
an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa.” [12]
6. Qanshin Bakin
Mai Azumi Yafi na Turaren
Miski
وَخُلُوفُ فَمِ
الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ
Ma’ana:
“Qanshin bakin mai azumi ya fi kamshin miski a wurin
Allah.” [13]
7. Ladan Azumi Allah ne ya ke bayar da sha kai tsaye:
كُلُّ عَمَلِ ابْنِ آدَمَ لَهُ إِلَّا الصِّيَامَ، فَإِنَّهُ لِي وَأَنَا
أَجْزِي بِهِ
Ma’ana:
“Kowane aikin ɗan Adam na shi ne, sai dai azumi, domin shi nawa ne,
kuma Ni ne zan ba da ladansa.” [14]
8. Karvar Addu’ar mai yin Azumi
ثَلَاثَةٌ لَا
تُرَدُّ دَعْوَاتُهُمْ… وَالصَّائِمُ حَتَّى يُفْطِرَ
Ma’ana: “Mutane uku ba a mayar da addu’arsu ba… da mai
azumi, har ya buɗe baki.” [15]
9. Koyar da zuciya ladubba da kiyaye harshe
فَإِذَا كَانَ
يَوْمُ صَوْمِ أَحَدِكُمْ فَلَا يَرْفُثْ وَلَا يَصْخَبْ
Ma’ana: Idan
rana ta kasance ta azumin ɗayanku, to kada ya yi maganar batsa ko hayaniya.” [16]
Ibadar Azumi: Idan
watan ramadan ya tsaya, to ya wajaba akan ko wanne musulmai Maza da Mata,
baligai, masu lafiya, mazauna gida su yi azumi, ma'ana su kame bakinsu daga ci,
ko sha, ko saduwar aure daga fudowar alfijir har zuwa faxuwar rana, wanda kuma
ya kasance mara lafiya ko ya zamo matafiyi acikin kwanakin azumin ramadan, to
ya halatta a gare shi da ya sha azumin sa'annnan ya rama adadin kwanakin da ya
sha acikin kwanakin da ba na Ramadan ba.
Allah
(SWT) yace:
فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ ۖ وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوْ
عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أخْرَ،
Ma’ana: "Wanda ya
riski wata daga cikin ku, to sai ya azumce shi, wanda kuma ya zamo maras lafiya
ko matafiyi, to sai ya rama a kwanaki na daban..." [17]
Don
haka Kenan, Azumi ibada ce ta da qunshi kamewa daga ci, da sha, da kusantar
iyali. da sauran abubuwan da ke karya azumi tun daga fitowar alfijir zuwa faxuwar
rana.
Sharuxan Azumi: Yin
Azumin Ramadan farilla ne ga dukkan:
1.
Musulmi
2.
Baligi
3.
Mai Hankali
4.
Lafiyayye
5.
Mazaunin Gida.
Wanda ba Musulmi ba, ko qaramin yaro, ko
mara hankali, ko mara lafiya, ko matafiyi, waxannan bai zama wajibi a kan su ba.
Musulmin da suka cika waxannan sharuxxa
biyar, su kan shafe wata guda (kwanaki 29 ko 30) suna Azumin Ramadan, ya danganta
da yadda aka ga jinjirin watan Shawwal.
Farlanta
Azumin Ramadan: Bayan aiko Annabi Alaihissalam, an
farlanta Azumin Ramadan ne mataki-mataki, inda aka fara farlantawa a watan
Sha’aban na shekara ta biyu bayan Hijira.
An fara farlanta wa al’ummar Annabi
Muhammadﷺ
yin azumi ne tare da ba su zavi wanda zai iya ya yi, wanda azumin zai wahalar da
shi kuma, sai ya ciyar da miskini xaya a maimakon kowane azumi. Duk da haka an
fi kwadaitarwa a kan yin azumi.
Daga baya aka farlanta azumin ga duk
wanda ya halarci (Riski) watan Ramadan.
Imam Muslim sun ruwaito daga Salamata bn
Akwa’ cewa: Sahabban Manzon Allah ﷺ
sun kasance idan mutum ya so sai ya yi Azumin Ramadan, ko kuma ya ciyar (da
miskini) a maimakon kowane Azumi daya.
A
wata ruwaya ta Imam Muslim, daga baya an soke hukuncin da saukar ayar da ta 185
ta Suratul Baqara, da take cewa: “Duk wanda ya halarci watan (Ramadan) to ya
azumce shi’.”
فَمَن
شَهِدَ مِنكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ ۖ وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ
فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أخْرَ، [ البقرة: 185]
Ma’ana:
"Wanda ya riski wata daga cikin ku, to sai ya azumce shi, wanda kuma ya
zamo maras lafiya ko matafiyi, to sai ya rama a kwanaki na daban..." [18]
Hikimar Shari’a da Dalilin da ya sa Allah ya Wajabta
Azumi: Azumi ibada ce da Allah Ya ɗora wa
Musulmi domin gina zuciya, gyara halaye da qarfafa
dangantaka tsakanin bawa da Ubangijinsa. Duk wani abu da Allah Ya wajabta yana ɗauke da
hikima, ko da mutum bai gane ta a zahiri ba. Amma azumi na ɗaya daga
cikin ibadoji da aka fi bayyana hikimominsa a cikin Alqur’ani, Hadisi
da bayanan malamai.
1. Gina Taqawa da Tsoron Allah
Allah ya ce:
“An wajabta muku azumi kamar
yadda aka wajabta wa waɗanda suka gabace ku, domin ku samu taqawa.” (Tuba,
tsarkake zuciya, da nisantar zunubi)
Taqawa ita ce ginshiqin dukkan ayyukan Musulunci. Azumi yana koya wa mutum
juriya wajen barin abin da ya saba yi saboda Allah.
2. Daidaita Halaye (Moral Discipline): Azumi makaranta ce ta gina tarbiyya, yana horarwa tare
da koyawa mutane haquri da juriya da tausayi da xa’a da Nisantar maganganu
marasa amfani, da kuma kula da harshe da zuciya.
Annabi Salallahu Alaihi wa
sallam ya ce: “Wanda bai bar qarya da
aikinta ba, Allah ba ya buqatar barin cin
sa da barin shan sa.”
3. Tunatar da Musulmi Halin da Mabuqata ke ciki: Wata hikima mai girma da ke cikin azumi ita ce; mutum
ya ji irin wahalar da marasa qarfi ke fuskanta na yunwa da qishirwa, sai
zuciyarsa ta cika da tausayi, hakan yakan sanya shi ya yawaita sadaqa, sannan ya nisanci girman kai.
Azumi yana daxa qulla alaka
tsakanin masu hali da marasa qarfi, domin
masu qarfin suna xanxanar irin yanayin da marasa qarfin ke ji.
5. Hadaɗɗiyar Ibada ce da bata da Riya: Malamai sun ce: “Azumi ne kaɗai ibadar
da ba a iya ganin sahihancinsa a zahiri.” Domin tsoron Allah ne ginshikinsa,
kuma sirri ne a cikin zuciya, bawa yana yin shi ne domin Allah kaɗai, domin
baza a iya gane wanda baya yi ba, in ba shi ne ya fito fili ya ce baya yi ba. Saboda
wannan sirrin ibada, Allah ya ce:
“Azumi na wa ne, Ni ne kuma zan bada ladan sa.”
6. Raunana Shaidan da Qarfafa
Ruhin Musulmi: A lokacin azumi
ana xaure shaiɗanu, don haka ɗan Adam ya kan samu sauqin
yin ibada, ba tare da kasala ba, sa’anan zukata su na qara cika da
haske, kuma Ruhi yana samun qarfi da
nutsuwa.
Wannan shi ne ainihin horon ruhi da addini ke nufi.
7. Haɗa kan Musulmi Da Gwajin Imanin Bayi: Azumi yana haɗa kan dukkan Musulmi waje ɗaya, domin
kowannen su yana azumi a lokaci xaya, suna haxuwa a masallatai wajen jam’in
Sallah, yana gina zumunci da saka al’umma su kasance cikin ibada a lokaci guda,
wannan yana nuna cewa Musulunci addini ne na tsari.
Haka nan daga cikin manyan hikimomin azumi Allah yana gwada tsantsar Imanin
bayin sa ne, domin ya tantance masu tsayawa ga umarninSa ko akasin haka.
8. Sanya Bawa Cikin Rahama da Gafara: Ramadan lokaci ne da ake buɗe dukkan qofofin sama, a buɗe qofofin
rahama, sannan a rufe dukkan qofofin wuta,
Allah ta’ala yana gafara ga dukkan bayin da suka roqi gafararsa. Don haka ake
so bawa ya yi qoqari wajen
tsarkake kansa da kuma samun alfarma da garavasar wannan wata.
BABI NA UKU
NAZARIN MALAMAN MUSULUNCI DA
LIKITOCIN DUNIYA KAN AZUMI DA LAFIYA
·
Nazarin Malaman Musulunci
Kamar yadda mukaji dogon bayani game da Azimi, da
tarihin sa, da hukunce hukuncensa da falalarsa, duk da haka yana wajaba ne a
kan mutum mai cikakkiyar lafiya ta hankali da jiki, ba ya halatta ga mara
Cikakkaiyar lafiya ko kuma yaro karami.
Don haka ne yin azumi ya zama wani lamari ne na fixirar
halittar dukkan halittu masu jiki don samun cikakkiyar lafiyarsu, kuma duk wata
halitta mai jiki tana samun wani lokaci da jikin zai tilas ta mata dakatar da
cin abinci ko da kuwa ta hanyar rashin lafiya ne don samun hutu da annashuwa da
sabuwar rayuwa ga kwayoyin halittar jikin.
1. Ibn Taymiyyah (Rahimahullah)
Ya yi bayanin
cewa:
·
Cin abinci fiye da qima yana jawo cututtuka
·
Azumi yana ba jiki damar hutu
·
Yana rage “yawan jini” wato kuzarin (shaidan)
2. Ibn Qayyim Al-Jawziyya A cikin littafin Zadul
Ma’ad, ya ce:
·
Azumi yana kona gubobi
·
Yana inganta narkewar abinci
·
Yana rage qiba
·
Yana tsaftace jiki gaba ɗaya
3.
Imam Al-Ghazali Acikin littafin Ihya Ulumuddin, shi ma ya ce:
·
Azumi yana tsabtace zuciya
·
Yana rage nauyi da abinda ke cutar da ciki
·
Yana kara kaifin tunani (clarity of mind)
Wasu daga Malaman wannan Zamani
suma sunce wani abu game da azumi
Sheikh
Bin Baz: –
Ya bayyana cewa azumi:
·
Yana Rage qiba
·
Yana Daidaita jini
·
Yana Tsaftace jiki
·
Yana Kare mutum daga cututtukan cin abinci da yawa
Sheikh
Yusuf Al-Qardawi: Shi ma yace: “Azumi magani ne ga jiki da ruhi.”
Yin Azumi ya na Kara
Lafiya
Manyan Malamai masana suna cewa: "Ku yi azumi kwa yi lafiya".
Wannan na nuna fa'idar yin azumi ga lafiyar jiki, kuma ni'ima ce da Allah ya yi
wa xan adam da bai san iyakarta ba, don haka ne littafin Allah yake nuni da
cewa:
ُولِتَشْكُرُوا اللَّهَ عَلَى مَا هَدَاكُمْ
Ma’ana:
“Domin ku godewa Allah kan
abin da ya shiryar da ku...
[19]
Domin ba don ya shiryar da mu zuwa ga wannan hanyar
ta samun lafiya ba, da babu wani wanda zai iya shiryar da mu gare ta.
NAZARIN MANYAN LIKITOCI KAN TASIRIN
AZIMI GAME DA LAFIYA
ü
Karanta Cin Abinci Yana Sanya Hutun
Hanji
Cin abinci barkatai ne yake
sanya takurar ciki da sanya yawan maiqo da qiba sai su taso su toshe kirji ta
yadda huhu zai kasa numfasawa cikin annashuwa, don haka ne ma mutane da yawa
suke samun dama a lokacin azumi don su dawo da kansu daidai da tsara cikinsu da
rage qibarsu don samun sa'ida da walwalar jiki, ta hanyar qaranta cin abinci
don su samu hutun hanji.
Akwai bayanai masu yawa
na likitanci da suke nuna qarantuwar gubar da take a cikin abinci, da fitar ta
daga jikin mutum, a sakamakon yin azumi.
ü
Azumi Yana Taimakawa Wurin qona Sukari da
Maiqo
Azumi yana taimakawa
wurin qona sukari, da maiqo da yake cikin hanta da jini da fata, don samun
lafiyar zuciya. Akwai bayanai masu yawa da likitoci irin su; Dr. Mark P Mattson
[20], Dr. Casey Means [21], Micheal J. Angelos[22] da sauran manyan likitocin duniya suka
yi kan wannan lamarin da yake nuna matukar mahimmanci da wajabcin Azumi ga
rayuwar mutum.
ü
Yunwar Azimi Bata Illa Ga Jiki
Mutumin da yake
jahiltar sirrin jikinsa, sai ya dauka cewa, yunwa zata illata shi ne sakamakon
yin Azumi, alhalin bai san cewa, yana da ajiyayyen sukari da yake samun amfanin
jiki a matsayin gulokojin da aka ajiye a hantarsa wanda zai iya amfana daga
gare shi tsawon lokaci, sannan sai ya karkata ga ajiyayyun mai da yake jikinsa,
wannan shi ne sirrin da ya sanya zamu ga mutum yana iya amfani da ruwa har
kwanaki 40. Sai kuma jiki ya koma tara wasu sinadirai sakamakon hakan ya sake
amfani da su don gina gavovinsa da daidaita tsarin rayuwarsu a lokacin Azumi.
Sai dai duk da
muhimmancin Azumi ba a yarda kuma a wuce gona da iri wurin yunwata kai ba, don
haka daidaito shi ne abin nema. Dr. Valter Longo (USC, USA) da masu taimaka
masa sun kawo bayanai masu hadari ga jiki idan ya ci gaba da yunwatuwa tsawon
lokaci da ya wuce kwanki 30 – 40.
A nan ne zamu ga
hikimar shari'ar musulunci da ta yarda mutum ya yi azumi 30 ne kawai na
farilla, ko kwanaki 40 ga masu kaffara. Kuma ya sanya yin sahur a qarshen dare,
da buxe baki a farkon dare, ya kuma kwaxaitar dayin sahur xin, kamar yadda
Annbi (SAW) yake cewa: ‘kuyi sahur domin akwai albarki a cikin sahur’.
Lallai tafarkin Addinin
Manzon Allah Salallahu alaihi wa sallam ne kawai ya yi daidai da ilimi a wannan
fagen kamar yadda zamu iya gani.
ü
Rashin Lafiyar Da Azumi Kan Yi Wa Amfani
Manyan masana kimiyyar abinci da binke akan azumi
duk sun tabbatar da cewa; Azumi yana da muhimman abubuwa da babu wai magani da
yake da su da suka haxa da:
1.
Hutun jiki da
dawowa asalin kwayoyin halittarsa.
2.
Dakatar da
tsotsar sinadirai da suke ragewa a hanji da zubar da su, domin daxewar su a
jiki zai iya mayar da su guba.
3.
Dawo da
ayyukan gavobi da nishaxinsu da daidaita ayyukansu.
4.
Narkar da
sinadaran da suke qari ne a jiki da qona su.
5.
Dawowa da
rayuwar kwayoyin jiki da samartaka.
6.
Kiyaye
daidaiton karfin jiki.
7.
Gyara gavovin
narkar da abinci a jiki.
8.
Buxe kwakwalwa
da kara hazaka.
9.
Tsaftacewa da
tsarkake fata.
10.
Daidaita
bugawar jini da narkar da kitse.
Da sauran
abubuwa da za a kawo su anan gaba.
Karin Bayanai kan Ra’ayoyin Masana da Masu Bincike
Ga wasu bayanai kan ra’ayoyin wasu masana da masu
bincike sukayi game da (azumi), bisa nazari da tattaunawarsu a fannin ilimi,
zamantakewa da lafiyar jiki da tunani:
1. Dr.
Jon Holbrook: Ya yi nazari ne
akan azumi a matsayin wata hanyar tsarkakewa da daidaita zuciya da jiki. Ya
bayyana cewa azumi yana taimakawa wajen qaruwar hankali da natsuwa.
2.
John Dewey (1859-1952): Dewey (Masanin Falsafa ne da ilimin
zamantakewa) ya duba azumi ta fuskar ilimi da wayewar kai. Ya ce: “Azumi na koya
wa mutum kame kai, sarrafa sha’awa, da haɓaka
qwarewar hankali.”
ya haɗa shi da falsafar (experiential
learning): koyo ta hanyar aiki da tunani.
3.
Dr. Herbert M. Shelton (1895-1985): Shelton ya mayar da hankali ne kan
lafiyar jiki da azumi, inda ya nuna cewa azumi na rage qiba, inganta tsarin
narkewar abinci, da taimakawa jiki wajen tsaftace sinadarai da toxins.
4.
Dr Morgulis [23]: Morgulis ya mayar da hankali ne kan
azumi da falsafar rayuwa. Ya bayyana cewa azumi yana koya wa mutum daidaita buqatu
na jiki da na ruhi, yana qara
fahimtar da mai yinsa jinqai
ga wasu.
5.
Tattaunawar kimiyya da akayi a Ecosse
(Scortland): Tattaunawar ta
bayyana azumi a matsayin al’adar ɗabi’a da zamantakewa. Ana ganin azumi
yana karfafa haɗin kai da mutunci ga al’umma, kuma yana
inganta qaunar kai da
kula da lafiyar jiki da ruhi.
A taqaitaacciyar Fahimta
Duk da
bambance-bambancen a fannin nazarin waxannan masana falsafa, amma duk sun yarda
cewa azumi yana da tasiri mai yawa a:
1. Ruhi da taqawa
2. Lafiyar jiki
3. Natsuwa da
hankali
4. Inganta ɗabi’a da zamantakewa
ü Magance
Manyan Cututtuka Ta Hanyar yin Azumi
Kwararrun
likitoci har zuwa yau, sukan yi maganin manyan cututtuka ta hanyar yin Azumi.
Wannan ya na qara mana imani da dokokin da masana da dama suke cewa: "Uwar hanji ita ce gidan dukkan cuta,
kariya wato riga kafi ce babban magani".
§ “Uwar hanji ita ce gidan dukkan cuta” → Wannan magana tana nuni da cewa lafiyar hanji da
tsarin narkewar abinci yana da matuqar
muhimmanci wajen kare jiki daga cututtuka.
Masana kimiyya sun nuna cewa rashin
daidaito a hanji na iya haifar da matsaloli da dama kamar cututtukan zuciya, ciwon
suga (diabetes), da ciwon ciki da ake kira Basir.
§ “Kariya (riga kafi) ita ce babban
magani” → Wannan magana tana nuna mafin ingancin
magani shine rigakafi, wato kariya kafin cuta ta shiga jiki.
Wannan ma’anar tana da tushe a kimiyyar
zamani.
TASIRIN AZUMI AKAN LAFIYAR JIKI DA RAGE HAƊARIN WASU CUTUTTUKA
1)
Ciwon Sukari (Diabetes Type 2): Azumi na taimakawa wajen daidaita
matakin sugar a jini, yana rage insulin resistance. Masu ciwon suga (diabetes)
ana so su nemi shawarwarin likita kafin yin azumi, musamman idan suna amfani da
magunguna.
2)
Ciwon Zuciya da Hawan Jini: Azumi na rage kitse mara amfani (cholesterol),
da rage kitse mai xauke da kolostral da jinni wato (Low Density Lipoprotein LDL),
da rage wani nau’in mai (fat) a cikin jini wanda jiki ke amfani da shi don
samar da makamashi (Triglycerides,) da rage ciwon kumburi ko qonewar jiki (
inflammation), wanda ke kare zuciya. Yana Rage haɗari
musamman idan azumi ya hade da abinci mai kyau da motsa jiki
3)
Rage Qiba (Obesity): Azumi yana rage yawan (calories) wato
ma’auni na makamashin jiki. da rage kitsen jiki. Rage qiba na rage haɗarin ciwon zuciya, ciwon suga (diabetes), da ciwon
gavovi (arthritis).
4)
Ciwon Hanta da taruwar guba ko duka wasu
abubuwa masu cutarwa (Toxic Accumulation): Lokacin azumi, hanta da hanji na samun
hutu, wanda ke ingantawa da tsarkake jiki daga dukkan abubuwa masu cutarwa (detoxification).
5)
Ciwon Daji (Cancer) : Nazarin dabbobi da mutane suna nuna
cewa azumi na rage canjin sinadarinwajen haduwa da iskar (Oxcygen)
wato oxidative, da ciwon gajiya wato stress da lalacewal
sinadaran jiki (Cell) wato cell damage, wanda ke rage haɗarin ciwon daji, Ba magani bane, amma yana rage haɗari.
6)
Ciwon Ciki / Gastrointestinal Issues: Azumi yana baiwa hanji hutu, yana
inganta narkar da abinci (digestion da microbiome): Yana taimaka wajen rage
ciwon ciki da yawan acid wato acidity.
7)
Matsalolin Kwakwalwa (Cognitive
Health): Azumi yana qara sinadaran da ke taimakawa wajen
cigaban kwakwalwa (neurotrophic factors) kamar BDNF (an kawo cikakken bayanin
sa a baya), yana rage damuwa da stress. Yana taimakawa wajen qarfafa hankali da rage haɗarin lalacewar da ke shafar kwakwalwa (Alzheimer's dementia).
ü Wajibin
Lura Da Me Ake Ci
Mutumin da yake
son zaman lafiyarsa daram shi ne wanda zai lura da me yake ci, yaushe zai ci,
yaya zai ci, nawa zai ci, da sauran mas'aloli irin wannan.
Don haka Annabin
Rahama Alaihissalam ya karvi kyautar Mariya daga Mukaukis na Masar, amma ya
mayar da likitoci, yana mai ba shi amsa da cewar; Mu mutane ne da ba ma ci sai
mun ji yunwa, kuma idan muka ci ba ma cika ciki. Sai wannan ya zama wata fomula
mai daraja da likitocin Masar suka yi riko da ita a wancan lokaci suna mamakin
wannan hikimar, da suka yi amfani da ita wurin warkar da cututtukan da suka
addabi al'ummarsu.
BABI NA HUXU
ABUBUWAN DA LIKITOCIN DUNIYA
SUKA GANO
Manyan
likitocin duniya (International Medical
Experts) sunyi rubututtuka game da tasirin azumi ga lafiyar ɗan Adam.
1.
Dr. Yoshinori Ohsumi – Nobel Prize Winner (2016, Physiology &
Medicine) Shi ne masanin da ya gano autophagy, wato yadda jiki ke cin
tsofaffin qwayoyin
da suka lalace lokacin azumi.
Mene
ne Autophagy?
Autophagy hanya ce da jikin mutum ke cinye tsofaffin
qwayoyin da suka lalace, gubobi, cututtuka da tarkacen jiki domin sake gina
sabbin kwayoyin da suka fi qarfi.
Kalmar tana nufin:
Auto = kai Phagy
= ci
Wato “jiki ya na cinye kansa domin tsarkake kansa.”
Yadda
yake aiki
Lokacin da mutum yake azumi na sa’o’i 14–16 zuwa
sama, jiki yana shiga wani yanayi da ake kira:
Autophagy mechanism
§ Jiki
ya na fara la’akari da abubuwan da basu da amfani.
§ Ya
na tattara kwayoyin cuta, da guba, da tsoffin kwayoyin jiki, da tarkacen da ke
jawo cuta.
§ Sai
ya kone su ko sake sarrafa su ya mayar da su sabbi.
Fa’idojin
Autophagy
1. Kare cututtuka
Yana rage hatsarin kamuwa da:
§ Cutar
daji (cancer)
§ Cututtukan
qwqwalwa (Alzheimer da Parkinson)
§ Ciwon
zuciya
§ Ciwon
suga
§ Tsufa
da wuri
2.
Inganta lafiyar kwakwalwa: Yana qara
sinadarin BDNF, da ya ke qara
kaifin tunani ga qwaqwalwa.
3.
Rage qiba da kitse: Jiki ya na qona tsohon kitse don samar da ingantancen
makamashi.
4.
Gyaran qwayoyin jiki: Qwayoyin da suka lalace akan gyara su ko a
maye su da sabbi.
Wani babban abu shi ne, binciken Dr. Yoshinori
Ohsumi a 2016 kan autophagy wanda ya samu Nobel Prize, saboda wannan tsari shi
ne: “Sirrin tsawon rai” da asali na yadda azumi ke amfani jiki.
Abubuwar
da ke qara autophagy?
• Azumi (na
Musulunci ko Intermittent fasting)
• Rage cin
abinci mai yawa
• Wasannin
Motsa Jiki (Exersise)
• Rage amfani
da abinci mai kara kuzari sosai (carbohydrates)
Lokacin da mutum ya yi azumi, jiki ya na fara; gyara
qwayoyin
jiki, cinye guba da qwayoyin
da suka lalace, rage haɗarin cutar daji da kuma rage
tsufa (anti-aging)
Tasirin
da likitoci suka tabbatar:
·
Azumi yana tsabtace jiki daga tarkace marasa
amfani (toxins)
·
Yana sanya jiki ya samu sabbin qwayoyin lafiya
·
Yana hana qwayoyin
daji su haɓaka
2.
Dr. Valter Longo –
na University of Southern California qwararre a azumi
(Fasting Expert) Marubucin the Longevity Diet,
kuma ɗaya daga manyan masana a (fasting world-wide), ya
binciko tare da tabbatar da cewa yawaita azumi:
✔ Ya
na rage kitse da sukari (cholesterol & sugar), ya na kuma
rage qiba
✔
Ya na qara
tsawon rayuwa
✔
Ya na inganta garkuwar Jiki (immune system)
✔
Ya na rage haɗarin kamuwa da cututtuka, kamar:
– Ciwon zuciya
– Cututtukan qwaqwalwa (Alzheimer)
– Ciwon suga (Type 2)
– Cutar daji (Cancer)
Ya ce: “Fasting
is the most powerful natural medicine for the body.” Wato azumi ne
babban magani ga jiki.
3.
Dr, Mark Mattson –Na Johns
Hopkins University (Professor in Neuroscience). Masanin
kimiyar qwaqwalwa ne kuma xaya daga cikin mnyan a duniya kan azumi,ya kwashe
fiye da shekaru 30
yana bincike akan azumi, a qarshe ya
bayyana cewa:
ü Azumi
yana qara
qarfafa
kwakwalwa.
ü Yana
rage damuwa, matsanancin tunani, da mantuwa.
ü Yana
qara
sinadarin BDNF wanda ke sa kwakwalwa ta qara
basira.
Wannan ya siffanta yadda malamai suka ce: azumi yana nutsar da hankali da qara kaifin tunani.
4.
Dr. Jason Fung – Canada (World Renowned for Diabetes Reversal)
Likitan da ya fi shahara wajen maganin ciwon suga ta hanyar azumi.
Abubuwan
da ya tabbatar sune:
ü Azumi
yana rage (insulin resistance) wato jiki ya daina karbar sinadarin insulin
sosai.
ü Yana
dawo da lafiyar hanji
ü Yana
rage qiba ba tare da illa ba
ü Yana
ba jiki damar qona kitsen ciki (visceral
fat)
Ya tabbatar da cewa azumi na iya: kawar da ciwon
suga nau’in 2 (da kulawar likita)
5.
Harvard Medical School (USA): Binciken
su ya nuna cewa:
ü Azumi
yana rage kitse mara amfani (cholesterol LDL)
ü Yana
inganta bugawar jini (blood pressure)
ü Yana
rage haɗarin cukar varin jiki (stroke)
ü Yana
rage cuwon kumburin jiki (inflammatory diseases)
Harvard sun bayyana cewa: (“Intermittent fasting is one
of the most effective
ways to reset the body’s metabolism.”) wato
azumin Lokaci-lokaci xaya ne daga cikin hanyoyi mafi tsari don sake saita
tasrin narkar da abinci na jiki
6.
Mayo Clinic (USA – one of the top hospitals in the world) xaya
daga cikin manyan asibitici na duniya, sun tabbatar da cewa azumi:
·
Yana daidaita yawan jinin sugar
·
Yana rage qiba
·
Yana inganta lafiya gaba ɗaya
·
Yana taimakawa wajen kawar da guba mara kyau (detoxification)
7.
(World Health Organization WHO): wato qungiyar lafiya ta
duniya ta ce:
ü Azumi
yana da muhimmiyar rawa wajen rage kiba
ü Yana
rage cututtuka masu alaqa
da cin abinci fiye da qima
ü Yana
inganta juriya da qarfafa
rigakafi
Likitoci Na Tilastawa
wanda za a Yiwa Tiyata Yin Azumi
Haka nan
likitoci su kan tilastawa wanda za a yi wa wata babbar tiyatar aiki ko ba ta
hanji ba, su ce ya yi azumi kafin tiyatar, saboda a lokacin jiki ya samu ya
huta daga duk wata hayaniyar yau da kullum ta stress da sauransu. Sai an dora
mutum a teburin tiyata ne kawai ake sa masa ruwan sukari.
Ita kuma hanta
kan fito da abincin da ta tara (irinsu sinadaran (glycogen) (fatty acid) na
kitse) don jiki ya sarrafa su zuwa sukari wanda yake ba da kuzari na dan wani
lokaci don amfanin jiki, domin ita hantar ta fara shirin ajiye sabo.
Daidaiton
Maganaganun Malamai Dana Masana
Malamai tun daxaxɗe qarni sun ce: “Azumi yana kare jiki, yana
gyara zuciya, yana rage cututtuka.”
A yau, binciken likitocin duniya da manyan masana ya
tabbatar da haka.
BABI NA BIYAR
YADDA AZUMI KE AIKI A JIKI
(Scientific Mechanisms)
1.
Autophagy (Mun kawo Ma’anarsa a baya)
o
Jiki yana cinye gurvatattun cells
o
Yana samar da sabbin cells
o
Yana rage haɗarin
cutar daji
2.
Hormonal Reset: Hormonal Reset yana nufin jiki ya dawo da
daidaiton hormones (sinadaran da ke sarrafa yunwa, koshi, barci, kuzari da
kiba).
Yana faruwa ne saboda:
§ Azumi
§ Barci
mai kyau
§ Rage
damuwa
§ Motsa
jiki
§ Cin
abinci mai kyau
·
Amfaninsa:
§ Rage
kiba
§ Kara
kuzari
§ Inganta
barci
§ Rage
damuwa
§ Inganta
lafiyar jiki gaba ɗaya
3.
Fat Burning: Fat Burning a takaice shi ne:
Tsarin da jikin mutum ke qone kitsen da ya ajiye ya mayar da shi kuzari.
Wannan yana faruwa ne idan jiki ya rage samun abinci ko sukari, sai ya koma
amfani da ajiyayyen-kitse domin ya sami kuzari. Wannan shi ne asalin raguwar
kiba.
Fata Burning: Yana taimakawa kitsen ciki (visceral fat) da yake assasa ciwon zuciya ya qone
sosai.
4.
Ketosis: Ketosis yanayi ne da jiki ke shiga idan ya rasa
isasshen abinci masu qara kuzari (carbohydrates) daga abinci, sai ya fara qone
kitsen da ya ajiye domin samar da makamashi.
Muhimman
bayanai:
§ Jiki
na samar da ketones daga kitsen da aka kone.
§ Wannan
ke ba jiki kuzari lokacin da glucose ya yi qasa.
§ Ketosis
yana taimakawa wajen:
o
Rage qiba
o
Inganta kuzari
o
Inganta lafiyar zuciya da jini
o
Inganta metabolism
A takaice: Ketosis shi ne lokacin da jiki ya koma
amfani da kitsen da aka ajiye a matsayin makamashi saboda rashin carbohydrates.
–
Jiki yana canza makamashi daga sugar zuwa ketones
– Wannan yana kara kuzari da natsuwar kwakwalwa
Marasa Lafiyar Da Azumi
Kan Yi Wa Amfani
Wannan
shi ya sa a addinance da kuma a likitance ba kowa ne aka yarda ya yi Azumi ba.
Duk da haka kuma, akwai marasa lafiyar da azumi kan yi wa amfani sosai wadanda
su ma za muji amfanin Azumi a gare su.
Ilimin likitanci
ya tabbatar da cewa yin Azumi yana daga mafi muhimmancin hanyar da mutum zai
samu lafiya, kuma abu ne na tilas a rayuwar mutum ga wanda yake son lafiyarsa
ta inganta.
Barin Cin Abinci Na Wasu Kwanaki
Hikimar Allah
madaukakin sarki ta tabbatar da cewa hatta dabbobi suna barin cin abinci na
wasu kwanaki a shekara don samun dai-dai-to a rayuwarsu da lafiyar jikinsu,
masu dabbobin sukan dauke shi wani lokaci a matsayin rashin lafiya alhalin
lafiyar dabbobin kalau. Kaji hikimar ubangiji buwayi gagara misali.
Bincike ya nuna
cewa kowacce dabba tana da wani zango (marhala) da dole ne ta taqaita cin
abinci a cikinta don samun daidaito a lafiyar jikinta.
Likitoci Na Rubuta Wa
Mutum Yin Azumi
Waxansu za su yi
mamaki idan suka ji cewa a yanzu haka likitoci a fadin duniya har a qasashen da
babu addini sosai, suna iya rubuta wa mutum azumi domin kiyayewa ko magance
wasu matsaloli na rashin lafiya.
Wato maimakon su
ba mutum magani, sai su ba shi shawara cewa ya riqa yin azumi, kamar yadda
wasunsu kan ce mutum ya riqa yawan motsa jiki. Irin azumin da likitocin zamanin
nan suka fi rubutawa shi ne irin azumin Annabi Dawud (AS), wato mutum ya yi azumi
yau, gobe ya sha, wanda a likitance suke kira Intermittent Fasting.
5. Tasirin Azumi ga Hanta, Koda, Jini da Zuciya
a. Hanta (Liver)
Ø Azumi ya na taimakawa hanta wajen
tsarkake jini da fitar da guba.
Ø Yana rage kitsen da ke taruwa a hanta,
wanda ke taimakawa wajen hana ciwon hanta mai kitsen (fatty liver
disease).
Ø Lokacin azumi, hanta tana sarrafa
glycogen don samar da kuzari yayin da jiki ke rashin abinci.
b. Koda (Kidneys)
Ø Azumi yana taimakawa koda wajen daidaita
ruwa da sinadarai a jiki.
Ø Yana rage matsa lamba ga koda, wanda ke
taimakawa kuvucewa kamuwa da ciwon koda.
Ø Yana qarfafa tsaftar jini da fitar da abubuwa
marasa amfani daga jiki.
c. Jini (Blood)
Ø Azumi yana taimakawa wajen daidaita
glucose da cholesterol.
Ø Rage (bad cholesterol) kolastila maras
kyau (LDL) da qara (good
cholesterol) kolastila mai kyau (HDL).
Ø Yana rage yiwuwar hawan jini da ciwon
zuciya.
d. Zuciya (Heart)
Ø Azumi yana rage inflammation (quna da kumburi a jiki) wanda ke haifar
da cututtuka kamar cutar toshewar hanyoyin jinni da kitse (atherosclerosis).
Ø Yana inganta zagayen jini a jiki (circulation)
da qarfafa zuciya.
Ø Yana taimakawa rage haɗarin kamuwa da ciwon zuciya.
6. Tasirin Azumi ga Kwakwalwa da Tunani
a. Inganta aikin kwakwalwa
• Azumi yana qara sinadarin BDNF (Brain-Derived
Neurotrophic Factor), wanda ke taimakawa wajen:
Ø Qara kaifin tunani
Ø Qara lafiyar qwaqwalwa
Ø Rage alamun damuwa (depression)
b. Rage damuwa da gajiya
Ø Azumi yana taimaka wa kwakwalwa wajen
daidaita hormone na stress (cortisol).
Ø Mutum yana samun nutsuwa da qarin juriya ga damuwa.
c. Kare kwakwalwa daga cututtuka
§ Binciken kimiyya ya nuna cewa azumi na
rage haɗarin cukuttukan qwaqwalwa (Alzheimer, da
Parkinson) da sauran cututtuka masu alaka da tsufa.
§ Yana rage kumburi (inflammation) a
kwakwalwa, wanda ke kare qwayoyin kwakwalwa.
§ Yana qara nutsuwa da fahimta
§ Yayin azumi, mutum yana qara mayar da hankali ga addini da tunani
mai kyau.
§ Wannan yana taimakawa wajen tsarkake
zuciya da hankali, da kuma inganta rayuwa ta ruhi.
BABI NA SHIDA
AMFANIN AZUMI GA CUTUTTUKA
1. Ciwon Suga
Azumi yana rage (insuling resistance), wato jiki ya
daina karvan sinadarin insulin, sannan yana kawar da {prediabetes), wato matakin farko na kamuwa da sutar sukari, hakanam azumi
ya shahara a duniya a matsayin magani.
Masu ciwon suga, su ma azumi kan sassaita yawan
sugan jikinsu, sai dai akan shawarce su da su riqa yin amfani da na’urar auna suga
a kullum saboda sugar zai iya yin qasa sosai su galabaita. Sai dai ana so mai
ciwon suga mai amfani da allurar insulin ya shawarci likitan da ya ke ganinsa
ko zai iya yin azumin, kuma ta yaya zai sassaita allurar saboda bambancin
lokacin cin abinci.
Wani Kwararren Likita yace: Yin azumi a kai a kai
yana xaya daga cikin sahihan hanyoyin magance ciwon suga nau’in type-2. (kamar
yadda muka kawo a baya)
2. Ciwon Zuciya da Hawan Jini
Yin
azumi akai akai
–
Yana Rage cholesterol (kitse mara kyau)
– Yana Rage hawan jini
– Yana Karfafa zuciya
Hakanan masu cutar hawan jini, hawan jinin nasu ya kan
qara sassaituwa ga wasu mutanen a yayin da suke azumi, kamar yadda binciken
masana da dama nuna. Misali, wani likita dan kasar Amurka mai suna Dr.
Goldhamer da ya qware a bincike kan azumi, ya yi nazarin amfanin azumi
ga masu hawan jini. A cikin mutane masu hawan jini da ya gwada ya yin da suke
yin azumi, kashi 98 cikin 100 ba su bukaci magungunansu ba a tsawon ranakun da
suka dauka suna azumi na wasu awoyi, wato azumi kawai ya sassaita hawan jinin
nasu. Amma dai hakan ba ya nufin mutum ya ajiye maganin ya daina sha gaba xaya
ba, sai likita ya auna shi ya ce ya huta.
3. Ciwon Qiba
Azumi yana maganin rage qiba mafi inganci, qibar da
bata komawa (no rebound weight). Azumi
na taimaka wa masu fama da cutar qiba domin yana rage mummunar qiba da kuma
sauran sinadaran da jiki ba ya bukata.
4. Cutar Alzheimer da Mantuwa
Menene Alzheimer?
Cutar Alzheimer cuta ce mai shafar kwakwalwa ɗan
adam. Tana faruwa ne musamman ga tsofaffi, tana iya shafar wasu matasa, amma
idan akwai wasu abubuwan haɗari da zasu haddasata.
Alamomin cutar sun haɗa
da:
· Mantuwa
mai yawa
· Rashin
iya tsara abubuwa
· Qarancin fahimta da hankali
· Sauyin
hali da halaye
b. Menene Mantuwa (Memory
Loss)? Mantuwa yanayi ne da mutum ke rasa ko qara matsala wajen tuna abubuwa. Yana iya
faruwa a kowane lokaci na rayuwa, amma yana qaruwa
da yawan shekaru.
Mantuwa na iya zama na ɗan
lokaci ko na dindindin (kamar a Alzheimer).
c. Dalilan da ke haddasa
Alzheimer: Tsufa da shekaru: kwayoyin kwakwalwa suna raguwa.
§ Inflammation
a kwakwalwa: kumburi da yawaitar guba.
§ Rashin
motsa jiki da cin abinci mara kyau.
§ Kwayoyin
cuta da guba in suka taru a qwaqwalwa.
§ Rashin
natsuwa da damuwa mai yawa.
d. Yadda Azumi ke taimakawa
wajen rigakafi
Azumi na qara autophagy, wato ya na tsaftace kwayoyin
kwakwalwa daga guba, ya na rage inflammation, wanda ke rage haɗarin
kamuwa da cutar kumburi. Yana qara
sinadarin BDNF, wanda ya ke taimakawa qwaqwalwa wajen sabunta qwayoyin tunani ga
qwaqwalwar.
Rage kiba da daidaita
insulin da kitse mara amfani (cholesterol), wanda kimiyya ta tabbatar yana rage
haɗarin kamuwa da cutar Alzheimer.
e. Kula da kwakwalwa
• Yin
azumi lokaci-lokaci
• Cin
abinci mai kyau
Da
ya kunshi (Omega-3) wato wasu mai ne masu amfani ga jiki (healthy fats) da jiki
ba zai ya qirqirarwa ba, sai dai a samu daga abinci, ana samu ne a gyaxa, man
zaitun, kifi sadin, da sauransu. Sai kayan lambu, da ‘ya’yan itatuwa.
• Motsa
jiki da motsa kwakwalwa, wajen yin karatu, da wasanni na tunani.
• Rage
damuwa da samun isasshen barci
A takaice: Alzheimer cuta ce
mai shafar kwakwalwa da tunani, amma azumi da salon rayuwa mai kyau na
taimakawa wajen rage haɗarinta da kuma kare qwaqwalwa.
5. Cutar
Borin Jiki Da Daji
Yawan Azumi
kariya ne daga cututtuka da sukan faru dalilin borin jiki (inflammation) irin
su sanyin kashi da sauransu. Masana suka kara da cewa ban da irin waxannan cututtuka
Azumi har kiyaye cututtukan daji zai iya yi, saboda shi ma daji sanadinsa shi
ne borin jiki. Haka nan sun kara da cewa yawan azumi a kuruciya yana iya rage
kaifin tsufa da alamominsa wato irin tamojin xinan da tattarewar fata da tsufa.
6. Lafiyar
Jiki Da Tinani Da Qwaqwalwa
Da farko dai Azumi na xaya daga cikin hanyoyin gyara
lafiyar jiki da ta tunani wato lafiyar kwakwalwa, domin binciken kimiyya ya
tabbatar a wasu lokuta ciki da hanji sukan bukaci hutu daga kowane irin abinci
na wani xan lokaci. Hakan kan sa kitsen jiki ya narke, sinadarai da guba da
hanta ta tara kuma su qone. Jiki kan narka kitse ne ta hanyar amfani da shi a
matsayin abinci. Wannan kan sa mutum ya dan save.
Ban da tacewa da qona guba, har ila yau hanta kan
fito da abincin da ta tara (irin su sinadaran glycogen da fatty acid na kitse)
don jiki ya sarrafa su zuwa sukari wanda yake ba da kuzari na dan wani lokaci
don amfanin jiki, domin ita hantar ta fara shirin ajiye sabo. Wannan ma kaxai
kan qara lafiyar hanta.
7. Hutawatar
Hanji
Bayan hanta shi ma hanji yakan samu ya dan huta na
wani lokaci ya daina kumburi ko cushewar da yake yawan yi a wasu mutanen,
musamman irin masu cututtukan hanji daban-daban.
8. Cutar
Shaye Shaye
Ga masu shan miyagun kwayoyi da taba sigari, Azumi
na xaya daga cikin hanyar horar da kwakwalwa barin sabo da su, wato barin nacin
begen abin shan (addiction). Wato Azumi zai iya maganin addiction tunda Azumi
na tarbiyyantar da jiki da kwakwalwa a kan kore begen ko ma mene ne mutum ke ta’ammali
da shi. Ga mai so ya daina wannan dabi’a, Azumi zai iya taimakonsa kwarai da
gaske.
9. Ciwon
Damuwa
Masu yin Azumi suna cike da tunani na annashuwa
domin hasashen lada na aikin ibada, wanda wannan annashuwa kaxai wani qarin
lafiya ne ga tunani da aikin kwakwalwa. Wannan ne ya sa masana ke ganin Azumi
zai iya tasiri akan ciwon damuwa na (depression), da ciwon gajiyar yau da
kullum wato (stress).
Waxansu za su ce ai duk jiki zai iya samun waxannan
ba tare da Azumi ba, sai masana kimiyya suka ce, eh haka ne amma me yasa ko a
wurin gwaje-gwaje na Asibiti wurin auna sukari da maikon jini da wasu sinadaran
jiki akan ce mutum sai ya yi Azumin akalla awa takwas kafin a auna su? Domin a
lokacin ne jiki ke nuna sinadarai na hakika ba na zukale ba.
10. Qone
Sinadaran Da Jiki Baya Buqata
Azumin na taimaka wa jiki wajen qone dukkan
sinadaran da ba ya buqata, ta yadda garkuwar jikin xan Adam za ta samu daidaito
da qarin kuzari cikin ’yan sa’o’i da fara azumin.
Manyan likitocin
duniya da cibiyoyin bincike na kimiyya sun bayyana cewa azumi (fasting) yana da
muhimman fa'idodi ga lafiyar jiki da kwakwalwa, ba kawai a matsayin ibada ba,
har ma a matsayin hanya ta lafiya (medical therapy) kamar yadda mukaji a baya.
Azumi ya na rage
matsalolin ciki kamar ciwon ulcer, gyambon ciki, da kumburin ciki da basir.
Annabi Salallah Alaihi
Wasallam ya yi gaskiya, sabo da faxinsa: "Azumi shine tsayayyen shinge
(protection) daga wuta da kuma cututtuka." [24]
Matsalolin
Da Za Su Iya Samun Mai Azumi
Ø
Qarancin ruwa a Jiki
Ø
Yawan Gajiya
Ø
Yawan Ciwon kai
Ø
Ga masu shan magani, akwai bukatar shawarar likita
Ø
Mata masu juna biyu da masu shayarwa masu rauni su nemi shawara ga
Likitoci
Qarancin
Ruwa a Jiki (Dehydration) a Lokacin Azumi
Lokacin
azumi, musamman a watan Ramadan ko lokacin da rana take da tsawo, jiki na iya
rashin isasshen ruwa, wanda ke haifar da matsaloli da dama.
Yawan
Gajiya: Rashin
abinci da ruwa a jiki yana sa qarfin jiki ya ragu, mutum ya fi gajiya ne a lokacin da
babu isashshen abinci ko ruwa a jikin sa, hakanan yana rage kuzari da qarfi.
Yawan Ciwon
Kai: Rashin
abinci da ruwa ya na iya haifar da ciwon kai mai tsanani. Inda mutum zai iya
samun matsaloli wajen rashin samun natsuwa da yin wasu ayyuka.
Ga Masu Shan Magani: Idan mutum ya na shan magani, yana da
muhimmanci ya tuntuɓi
likita kafin azumi. Domin wasu magungunan na iya sa jiki ya raunana, wanda hakan
zai iya kawo haɗari ga lafiya.
Shawarwari Don Kare Rashin
Ruwa a jiki (Dehydration)
§
Shan ruwa mai yawa a lokacin buxe baki da sahur.
§
Cin ’ya’yan itatuwa da kayan lambu masu ruwa.
§
Gujewa abinci masu yawan gishiri sosai waxanda su ke kawo qarancin ruwa.
§
Yawan
zama wuri mai inuwa, musamman idan ana rana mai zafi a qauracwa shiga cikin
rana.
BABI NA BAKWAI
CUTUTTUKAN DA BA SA BARI A YI AZUMI
Akwai wasu larurori na rashin lafiya wadanda a
Addinance ba a xorawa masu su yin Azumi ba. Domin Allah ya yi da rangwame ga
waxanda suke ke da uzuri na irin waxannan cututtuka masu tsanani. Ga wasu
cututtuka da ba sa bari mutum ya yi azumi:
1. Ciwon
Suga da yake da Tsanani (Diabetes – Type 1 & Type 2): Domin ana buqatar shan magani akai-akai ko cin abinci
a lokaci na musamman. Azumi na iya sa hypoglycemia (raguwar suga) ko
hyperglycemia (yawaitar sugar), wanda zai iya kai mutum ga suma ko mutuwa. Masu
amfani da insulin galibi ba su da ikon yin azumi sai da izinin likita.
2. Ciwon Qoda (Kidney Disease); Musamman tunda mai ciwon yana buqatar shan ruwa da yawa, domin rashin ruwa
na tsawon sa’o’i yana iya qara lalata qoda,
ko da buqatar yi masa (dialysis). Wata hanya ce ta tsabtace jini ga mutanen da
kodar su ba ta aiki yadda ya kamata.
3. Ciwon Qwaqwalwa mai tsanani; Idan ana amfani da magungunan ciwin qwaqwalwa a lokaci
na musamman, barin maganin saboda azumi na iya haddasa qaruwar ciwon, don haka
wannan ciwon shima baya bari ayi azumi.
4. Ciwon Gyambon Ciki
(Ulcer mai tsanani)
Rashin cin abinci ga mai wannan ciwon, na iya sa
acid ya qaru a ciki, hakan
na iya haddasa zafi, ko zubar jini ko hargitsin ciki, wanda za a iya galabaita
sosai.
5. Tarin Fuka (TB) ko
Ciwon Numfashi (Asthma)
Suma waxannan cututtuka ana buqatar amfani da maganin shaqawa (inhaler)
ko shan magani a kai akai. Azumi zai iya haddasa wahalar numfashi ko taqaita shi.
6. Ciwon Hanta; Ga masu xauke da ciwon hanta, su na buqatar tsarin cin abinci na musamman da shan
magani. Azumi zai iya janyo gajiya, amai ko qarancin jini.
7. Mutane da ke cikin
Jinya ko Rauni mai Tsanani
• Misali: Masu jiyar rauni da aka yiwa aikin
tiyata (surgery), ko waxanda ake yiwa (chemotherapy) wani magani ne da ake
amfani da shi wajen kashewa ko dakile ciwon daji (cancer) a jiki.
8. Masu Ciwon Zuciya
Mai Tsanani (Heart Disease)
Domin suma suna amfani da magunguna akai-akai da buqatar cin abinci nau’i na musamman. Idan suka tsallake magani
ko ruwa, suna iya haxuwa da haxari.
9. Masu Juna
Biyu Da Masu Shayarwa
Su ma akan yi musu sauki, saboda irin waxannan
larurori suna bukatar fatawoyin malamai, da shawarwarin likitoci, don a
tabbatar musu za su iya azumi ko akasin haka da kuma hanyoyin ramuwa ko
kaffara. Domin kada su galabaita ko su saka abin da suke xauke da shi wahala.
(zamu kawo cikakken bayani a darisi nag aba)
Akwai wasu da dama masu irin waxannan larurori da su
ma ke buqatar fatawa dag malamai makusanta da su don a tabbatar za su iya azumi
ko akasin haka.
Me ya kamata Masu Waɗannan
cututtuka Suyi?
Masu waxannan cututtuka da muka ambata, ya kamata su
tuntubi likita nagari (Musulmi idan zai yiwu) kafin yanke shawara. Idan azumin
zai iya cutar da su ko qara musa ciwo, shari’a ta yarda su sha, sai a rama daga
baya, ko a ciyar idan ba za a iya rama yin azumin ba.
Alqur'ani mai
tsarki yana cewa:
وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَىٰ
سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ ۗ البقرة: 185
Ma’ana
"...Wanda
ya kamu da rashin lafiya ko yana halin tafiya, to ya rama daga wasu
kwanaki."
[25]
BABI NA TAKWAS
KAMANCECENIYA DA BAMBAMCIN AZUMIN MUSULUNCI DA
INTERMITTENT FASTING
·
Azumin Musulunci
Shi ne kaucewa abinci, da abin sha, da saduwa da iyali,
da duk abin da yake karya azumi, tin daga fitowar alfijir har zuwa faduwar
rana, saboda girmama Allah.”
Shi azimin Musulunci, ba a cin komai daga hudowar rana
har zuwa faxuwar rana (yamma)
Ana kiyaye salla da ibada a lokacin da ake yin sa, ana yin sahur a qarshen dare,
sannan a gaggauta buxe baki a farkon dare, kamar yadda yazo a hadisi,
عـن سَهل بِن
سعد رَضى اللهُ عنهُ أنَّ رسول اللهِ صلى اللهُ عليهِ وسلَّم قال: لاَ يزَّالُ
النّاس بخَيْرٍ مَا عَجْلو الفِطْر. متفق
عليه.
Daga Sahl xan Sa’ad- Allah
ya yarda da shi, Lalle Manzon Allah tsira da aminci su tattaba a gare Shi- ya
ce: Mutane ba zasu gushe ba a cikin alheri matuqar suna gaggauta buxa baki. (Sahih Bukhari 10198)
عن أَنس بن
مالك رضى الله عنه قال: ما رأيت رسول الله صلى الله عليه وسلم قطُ صلَّى صلاة
المغْرُبِ حتى يَفْطرولَوْ على شربَة من الماءِ. رواه ابن حبّان.
Daga Anab bn Malik (R.A) ya
ce: ban tava ganin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi yayi
Sallar Magriba ba, face ya yi buxa baki koda da kurbar Ruwa ne. Ibn Hibban ya
ruwaito.
Jinkirta
Sahur: Anso a jinkirta sahur, saboda hadisin Anas da Zaidu
xan Sabit Allah ya yarda dasu suka ce: munyi Sahur tare da Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tattabata a gareShi, sannan sai ya taShi zuwa salla, aka ce
tsakanin gama sahur dinku da tayar da sallarKu zai kai ya ya? Sai suka ce: zai
kai kimanin a karanta ayoyi hamsim (50) na alqur’ani.
Anas bn Mali ya ruwaito
Hadisi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare Shi. Cewa
Annabi (S.A.W) ya ce: Kuyi sahur acikinsa akwai albarka.
· Intermittent
Fasting? (Azumin likitanci)
Shi kuma Intermittent Fasting (IF) na nufin tsarin
cin abinci da mutum ke rage lokacin da yake ci a kullum, yana barin lokaci mai
tsawo ba tare da ya ci komai ba, sai ruwa kawai ko wasu abubuwan da ban.
Wato ba wai irin azumin Ramadan ba ne, amma azumi ne
na lafiya da tsarin rayuwa wanda ake amfani da shi don: Rage kiba, Inganta
lafiyar jiki da kwakwalwa, da kuma tsarkake jiki daga cututtuka
· Yadda
Intermittent Fasting Ke Aiki
Intermittent fasting yana aiki ne ta barin jiki ya huta
daga sarrafa abinci, domin Jiki ya qone
mai, kuma yana sa sauqin narkewar abinci, yana saukar da sinadarin insulin,
yana taimakawa gyaran sel (autophagy)
Nau’ukan
Intermittent Fasting
|
Nau’i
|
Bayani
|
|
16/8
|
Cin abinci cikin
awanni 8, Azumi awanni 16. Misali: ka ci daga 12:00pm – 8:00pm, sauran
lokutan azumi.
|
|
5:2 Diet
|
Cin abinci na yau da
kullum tsawon kwanaki 5, sai rage kalori sosai (500–600) a kwanaki 2.
|
|
Eat-Stop-Eat
|
Kafa azumi na awanni
24, sau 1 ko 2 a mako.
|
|
Alternate Day Fasting
|
Cin abinci ranar yau,
azumi gobe, haka a jere.
|
|
One Meal A Day (OMAD)
|
Cin abinci sau 1 a
rana kawai – misali da yamma ko dare.
|
·
Amfanin Intermittent Fasting Ga Lafiya
1)
Rage
qiba: yana taimakawa rage nauyi da mai.
2)
Rage
sugar (glucose) da insulin: yana da amfani ga masu ciwon suga (Type 2
diabetes).
3)
Inganta
lafiyar qwaqwalwa: ya na qarfafa
fahimta da rage damuwa.
4)
Gyaran
jiki (Autophagy): ya na tsabtace sassan jiki daga gurvatattun sel.
5)
Inganta
zuciya: yana rage cholesterol da matsin jini (blood pressure).
6)
Kare
daga cututtuka kamar kansa, da dai sauransu.
Waxanda basu kamata da yin shi ba har sai sun
tuntubi likita sune:
•
Mata
masu ciki ko masu shayarwa
•
Masu
ciwon suga mai tsanani
•
Masu
matsananciyar yunwa ko ciwon gyambon ciki (ulcer)
•
Masu
fama da rashin lafiya ko kumburi mai tsanani.
Intermittent Fasting ba wani abinci bane, amma tsari
ne na cin abinci cikin lokacin da aka ware, domin gyaran jiki da lafiyar zuciya
da qwaqwalwa. Yana kama da azumin Musulunci, amma ba ibada ba ne, ana yi ne da
niyyar lafiya.
BABI NA TARA
HANYAR CIN ABINCI MAI LAFIYA
YAYIN BUXE BAKI (IFTAR)
Abincin Da Ya Fi Dacewa
Wajen buxe baki (Iftar)
Buxe
baki na da matukar muhimmanci domin dawo da kuzarin da jiki ya rasa, shi yasa
ake son cin abici cikin tsari, kuma lafiyayye waxanda baza su wahalar da jiki ko
kawo matsala ga lafiya ba.
Ruwa da abubuwan sha
§
Ana so a fara da dabino (in ya samu), sai ruwa mai kyau domin mayar da
ruwan da jiki ya rasa.
§
Za a iya shan zobo, ko kunu ko koko ko haxaxxen kayan itace masu ɗanɗano, da suke xauke da
sinadarai masu amfani ga jiki.
§
A guji shan abun sha mai xauke sukari mai yawa, domin hakan ba zai
taimaka wa jiki ya dawo da kuzarin da ya rasa da wuri ba.
‘Ya’yan itatuwa
‘Ya’yan
itatuwa kamar markaxaxxun ayaba, kankana, lemun zaqi, suma suna qarawa jiki qarfi,
kuma suna qara ruwan da jiki ya rasa,
Hakanan
suna taimakawa wajen saka kuzari cikin sauri ba tare da cutarwa ga jiki ko ciki
ba.
Abinci mai
sauqin narkewa: Za a iya cin abinci mai saurin narkewa kaxan, kamar shinkafa,
talitya da makamantansu domin jiki ya samu qarfi.
Abincin mai
Xauke da Sinadarin Furotin: cin abinci mai xauke da sinadarin Furotin shi ma ya na
taimakawa wajen gyara tsokoki da qwayoyin jiki, kamar kifi, naman
kaza, wake, kwai, madara da makamantan su.
Ammafa kada a ci da yawa a lokaci xaya, domin su a
hankali jiki yake sarrafasu.
Gujewa
abinci masu kitse ko Mai: Ana son a guji cin abinci mai kitse ko mai da yawa, domin ya na jawo
nauyin jiki da matsaloli a cikin ciki da rashin narkewar abinci da wuri, (idan
jiki yai nauyi zai sa akasa yin Sallar Tarawih (Sallar Asham).
Rage cin
Abinci ko abin Sha mai Sukari da yawa: ana son a rage ci ko shan abinci mai xauke da Sukari
mai yawa, domin ya na gajiyar da jik sosai.
Yin Addu’ar buxe baki kamar yadda addini ya koyar a
na yi ne lokacin buxe baki (in an kai azumi), don
neman albarka da gafara daga Allah.
Allahumma
inni laka sumtu wa bika aamantu wa ‘alayka tawakkaltu wa ‘ala rizq-ika-aftartu
Ma’ana:
“Ya Allah,
na yi azumi ne domin Ka, na yi imani da Kai, na dogara ga Kai, kuma da rizqinka
nake bude azumina.”
Ana karanta wannan idan aka bude azumi (Iftar). Hakanan
za a iya kuma yin addu’o’in musamman na iftar, kamar neman gafara, lafiya, da
albarka.
Sannan bayan minti 15–30, sai a ci abinci mai sauqin narkewa, hakannan ana son
shan ruwa mai yawa tsakanin buxe baki da sahur.
Jadawalin Cin Abinci Mai Gina
Jiki a Lokacin Azumi
|
Lokaci
|
Abinci & Sha
|
Bayani / Fa'ida
|
|
Iftar (Buxe Baki)
|
Ruwa,
'ya'yan itatuwa (dates, ayaba, kankana, lemun tsami)
|
Mayar
da ruwa da kuzari na halitta, sinadarin antioxidants, da fiber
|
|
Bayan minti 15–30
|
Abinci
mai sauqin
narkewa: shinkafa, gero, masara, dankalin turawa, miya mai kayan lambu
|
Inganta
narkewar abinci, samar da kuzari cikin sauri
|
|
Furotin
|
Kifi,
kaza, wake, kwai, madara
|
Gina
tsokoki, qwayoyin
jiki, da qarfafa
garkuwar jiki
|
|
Kayan lambu
|
Karas,
kabewa, latas, tumatir, wake mai ganye
|
Fiber,
sinadaran vitamins da minerals, taimakawa narkewar abinci
|
|
Abin Sha
|
Ruwa
mai yawa, kamar zobo, lemun zaki, ruwan kayan itatuwa
|
Mayar
da ruwa da sinadarai masu amfani, rage gajiya
|
|
Guji
|
Fried
foods, abinci mai kitse sosai, sugar mai yawa
|
Hana
jin nauyi, ciwon ciki, da rage kuzari
|
|
Sahur
|
Ruwa,
koko maiqarancin sukari, kwai, wake, 'ya'yan itatuwa
|
Bayar
da kuzari mai ɗorewa
har zuwa iftar, rage yunwa, kiyaye ruwa a jiki
|
Abincin Da
Ya Fi Dacewa a Sahur
A yayin Sahur ana son cin abinci mai fiber da furotin
waxanda su ke bayar da kuzarin da zai ɗore har zuwa shan ruwa (iftar).
• Misali: koko
mara sukari sosai, kwai, wake, 'ya’yan itatuwa, ko hatsi kamar shinkafa, ko
tuwon masara ko na gero. Amma a guji mai maiqo da yawa domin zai iya kawo yawan
jin qishirwa,
Wasanni da
Motsa Jiki
Ana son a motsa jiki ba da yawa ba, bayan shan ruwa, kamar
tafiyar a qasa.
Yin Sallar Tarawihi (Asham) itama tana taimakawa wajen
jiki ya motsa, sannan abinci yayi saurin narkewa,
Ana so a gujewa motsa jiki da yawa kafin shan ruwa,
domin a lokacin jiki bashi da kuzari da yawa.
BABI NA GOMA
AZUMIN NAFILA DA BA NA RAMADAN BA
Kamar yadda muka
ji mahimmancin da azumi ke da ga lafiyar mu, don haka bai kamata mu tsaya kaxai
wajen azumtar Ramadan ba, sabo da haka ga qarin wasu azumin na Nafila
(nafilfili) da ba na watan Ramadan ba, da ya kamata mu lazimce su a tsawon
rayuwar mu, don qara inganta lafiyar mu.
Su wadannan azumi
na Nafilfili sune; waɗanda Manzon Allah ﷺ ya yi ko ya qarfafa sahabbai da musulmai su riqa yin su. Ana samun lada mai girma da
ximbin yawa in muna yin su, sannan kuma zamu samu qarin lafiya, kunga riba biyu
kenan, ga Lada ga samun qarin Lafiya, azumin Nafila (Nifilfili) a Musulunci
sune kamar haka:
1.
Azumin Litinin da Alhamis
Shi ne azumtar
dukkan ranakun Litinin da Alhamis.
Dalilin yinsa: Anas bn Malik ya ruwaito daga Manzon Allah Alaihissalam
cewa: “An kasance ana gabatar da ayyuka ga Allah a ranakun Litinin da Alhamis,
kuma ina son a gabatar da aikina ina azumi.” [26]
2. Azumin
Ayyaamul Bidh (Ranakun Haske)
Shi ne azumtar ranakun haske na kowanne watan
Hijriyya, sune ranakun da 12 da 14 da 15, wato in wata ya raba kenan.
Dalilin yinsa: Abu Hurairah ya ce: Manzon Allah ﷺ ya umarce ni da na yi azumi uku a kowane wata, da
sallar duha biyu, da nafila raka’a biyu kafin na kwanta.” [27]
3. Azumin
Ashura da Tasu’a
Wato azumtar ranaku 10 da kuma 9 ko 11 na watan
Muharram na kowacce shekara.
Dalilin yinsa: “Azumin ranar Ashura yana kaffarar
zunubai na shekara guda.”
[28]
Manzon Allah ﷺ ya ce: “Idan na rayu shekara mai zuwa, zan azumci
ranar tara (Tasu’a) da goma (Ashura).”
[29]
4. Azumin Arafah (9 ga Zul-Hijjah)
Shi ne Azumtar ranar Arfa wato ranar 9 ga Zul-hijja
na ko wacce shekara, amma wanda ya ke cikin aikin Hajji, ba zai yi azumi a
ranar Arafah ba.
.
Dalilin yin sa: “Azumin ranar Arafah yana kaffarar zunubai na
shekarar da ta gabata da ta gaba.” [30]
Saboda faxin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareShi
cewa:
صيامُ يوْمُ عرفَة أحْتَسبُ على اللهِ أنْ يُكفر
السَنة التِى قَبْلهُ، والسّنة التى بَعْدَهُ.
Annabi tsira da amincin su tabbata a gareShi ya ce: Azumin Ranar Arfa ina
sa ran Allah zai gafarta zunubin da ya gabata da kuma wacce ta ke tafe. Muslim (1162)
5. Azumin Watan Sha’aban
Manzon Allah ﷺ yana azumta da yawa daga watan Sha'aban.
“Yana azumtar (kusan) duk watan, sai in ce ba zai
bar shi ba.” [31]
6. Azumin Annabi Dawud (Azumi Mafi alheri)
Azumin Annabi Dawud:
shi ne a Azumci rana ɗaya, sai a huta a rana ta gaba.
Manzon Allah Alaihissalam
yace: “Mafi alherin azumi a wurin Allah shi ne azumin Annabi Dawud...” [32]
7- Azumin Sitta Shawwal
Wato azumtar
kwana shida a watan Shawwal.
Dalilin yin sa:
Manzon Allah Alaihissalam yace: “wanda ya azumci Ramadan ya bishi da shida a
watan shawwal, kamar ya azumci zamani ne”
8- Azumin Gwagwaye
Ana son
waxanda basu da aure wato (Gwagware) su yawaita yin azumi
Dalili: Annabi Alaihissalam yace: “Wanda bai samu
damar aureba na horeshi da yin azumi domin kariya ce a gare shi”[33]
9. Azumin
Watan Rajab
Ana son yawaita azumi a cikin watan rajab’
Domin Manzon Allah Alaihissalam yace da Mujibaul
bahily: “Ka azumci watanni masu alfarma (4) ya isa. Watan rajab yana cikin
watanni 4 masu alfarma.
Kamar yadda muka ji qarin ranakun da ake son
a azumumta tare da Hadisan Manzo Alaihissalam da suka yi nuni da yin su, zamu
fahimci yadda addinin Musulunci yak e qarfafar musulmi da yin azimi, domin
lafiyarsu ta qara ingantuwa.
BABI NA GOMA SHA XAYA
Hukumcin Azumin ‘Ya Mace
Kamar yadda shari'a ta xora yin azumi akan namiji,
haka ta xorawa ‘ya mace yin sa, na Ramadanu ne ko na nafilfilu kamar yadda muka
kawo su a babin da ya gabata, amma kuma shari'a ta rawangwantawa mace game da
yin azumin a wasu wurare ko kuma ace awasu lokuta, wannan saboda kasancewar
mace mai rauni ta fanin shari'a.
Don haka duk wanda watan Ramadan ya riske shi amma
ya tsufa tukuf, ko kuma mara lafiya dake a kwance, da ba'a sa ran zai warke
daga rashin lafiyar, mace ko namiji, to ko wanne daga cikin waxannan zai sha
azumin, amma zai ciyar da miskini xaya rabin sa'i, ma'ana mudu biyu na galibin
abincin qasar, amaimakon ko wace rana, wacce ya sha azumi acikin ta. kamar
yadda Allah maigirma da daukaka ya bayyana cikin suratul bakara aya ta 184.
To anan ma mace shari'a ta bata damar shan azumi
saboda waxansu uzururuka waxanda ke faruwa agareta waxanda basa faruwa ga da
namiji, wadannan uzururruka sune kamar haka:-
1. Jinin
Haila Da Jini Biqi:-
Ya haramta ga mace mai jinin biqi ko na haila tayi
azumi, amma kuma wajibi ne ta rama azumin a wasu kwanaki da ba na ramadana ba,
savanin Salloli su baza ta rama su ba.
Saboda Nana A'isha (Radhiyallahu Anha) tace:-
"Mun kasance ana umurtar mu da rama azumi amma ba'a umurtar mu da mu rama
salla. Awata ruwayar ta imam muslim yace, "Mu'azatu tace na tambayi Nana
A'isha nace saboda me mai haila zata rama azumi amma bazata rama sallah ba, sai
tace:- ke 'yar (khawarijawa ce) sai nace ni ba ita ba ce, nadai tambaya nai
kawai, sai ta ce dani hakan na samun mu, sai aka umurce mu da mu rama azumi,
amma ba'a umurce mu da mu rama salla ba, kuma ta kara da cewar waxannan
al'amura ne da mutum yake tsayawa inda aka tsai da shi, ba ra'ayi ake bi ba,
a’a nassi ake bi.
Idan kuma mace taga farar kassa, wato wani ruwa da
mahaifa take fitarwa bayan karewar jinin haila, wacce mace ke gane samun tsarkinta
idan ta gan ta, to sai ta xaura niyya don xaukan azumi. idan kuwa bata da wata
takamaimiyar hanyar samun tsarki sai tayi kunzugu da Auduga ta gargajiya ko
'yar kanti, ko dai wani abu makamancinta kamar tolet paper, idan ta cirota da
ganta tsaf babu jinni, to ta tsarkaka kenan, to sai ta xauki azumi, amma kuma
idan bayan ta dauki azumi sai jinin ya dawo mata a wannan ranar, to sai ta sha
azumin, amma idan bata sha ba sai jinin ya dauke kafin magariba, to azuminta ya
ingan ta. Sa'annan matar da taji alamar fitowar jinin haila amma sai bai fito
ba, sai bayan magariba to ita ma azumin ta yayi.
Matar da take haila sai jinin ta ya dauke tun dare,
to sai tayi niyar yin azumi, in kuma ta kasance bata yi wanka ba har alfijir ya
keto to azumin ta ya ingan ta, bisa mazhabar daukacin malamai.
Matar da tasan cewar gobe ne jini zai zo mata, amma
sai ta tashi da azumi to ba zata ci abinci ba har sai idan jinin ya zo mata,
sannan sai ta sha azumin, idan kuma bai zo mata ba sai taci gaba da azuminta.
Mai biqi (wacce ta haihu) idan ta samu tsarki kafin
kwanaki Arba'in da haihuwar ta, to sai tayi wanka tayi niyyar azumi, hakanan
idan jinin ya haura kwanaki Arba'in bai dauke ba, to sai ta dauki jinin a
matsyin jinin istihada (wato jinin cuta), sai dai kuma idan jinin ya yi dai dai
da lokacin al'adarta wadda take yi duk wata, to wannan kam sai ta xauke shi
amatsayin jinin haila.
2. Mace mai
ciki da mai shayarwa:- Ita ma mace mai ciki ko mai shayarwa idan har yin
azumi gareta zai cuce ta, ko ya cuce jaririn ta, ko kuma duka su biyun zasu
cutu, to ita ma anyi mata rangwame akan ta sha azumi a cikin halin cikin ko
shayarwar.
Amma kuma idan yin azumin zai cutar da jaririn ta ne
kawai ban da ita, to zata rama azumin kuma ta ciyar da miskini xaya maimakon
azumin da duk ta sha a duk lokacin da tazo ramawa, amma idan yin azumin zai
cutar da ita ne ita kadai to zata rama azumin kawai banda ciyarwa.
Domin Ayar da ke yin bayani akan wanda ke iya yin
azumi amma da kyar to lallai akwai mace mai ciki da mai shayarwa idan suka jiwa
kansu ko jaririn su tsoron cutuwa.
Don haka zance mafi rinjaye anan shine, an yiwa mace
mai ciki da mai shayarwa kiyasin marar lafiya, don haka ya halatta da su sha
azumin kuma ba su da kaffara, sai dai ramuwa, ya Alla suna jiwa kan su tsoro ko
suna jiwa 'ya'yan su tsoro.
Hujjar wannan itace ruwayar Imamu Tirmizi yace:
Annabi Alaihissalam yace: Allah madaukakin sarki ya xaukewa matafiyi wani yanki
na azumi (wanda ya sha alokacin tafiyar sa) da wani yanki na sallah (yana nufin
yin qasaru) kuma ya daukawa mace mai ciki, da mai shayarwa yin azumi. [34]
Amma sai ta nemi shawara daga sahihin likita, kamar
yadda muka kawo abaya.
3. Jini
Rashin Lafiya:- ko kuma jinin ISTIHADHA macen da jini yake zuwar mata bana haila ba, azumi
wajibi ne akan ta, bai halatta ta sha azumi saboda wannan jinin ba, domin shi
jinin rashin lafiya ne kamar zuwan kumallo ne, ko fitar jini saboda rauni, ko
fitar ruwan kurji, duk waxannan abubuwa ne waxanda basu da lokaci kayyadadde na
zuwan su, ballantana ace mace tabar azumi domin su, ma'ana zuwan su ba zai hana
mata yin azumi ba.
4. Matar Aure:-
Bai Halata ga matar aure tayi azumin Nafila ba, alhali mijin ta na gida sai da
izinin sa, ko idan baya gari ya yi tafiya, amma kuma ban da na ramadan, macen
da azumi ya wajaba akan ta, idan ta dauki azumin ramadan sai mijinta ya tara da
ita da rana alhali tana xauke da azumin ramadan, kuma bisa yardarta, to dukkan
su zasu yi ramuwa da kaffara, amma idan tilasta mata ya yi, tayi iyakar kokarin
ta na hana shi, amma bata yi nasarar hana shi ba, to ita babu kaffara a kanta
sai dai ta rama azumi.
Amma idan mace tana barci acikin watan ramadan sai
mijinta ya tara da ita, to malamai sunce ita ma babu kafara akan ta sai dai ta
rama azumi.
Ana so ga mace budurwa ko wacce mijinta ya yi mata
izinin yin azumin da ta riqa yawan yin azumin nafila, ko yin azumin mustahabbi
(wato abin da aka so) da kuma yin azumin a ranakun litinin da Alhamis, da
(kamar yadda muka kawo su a baya), sai dai kuma bai kamata a gareta da tayi
azumin nafila ba, alhali ana binta ramuwar wani azumin, har sai ta rama azumin
da ake bin ta.
Haka kuma ya kamata ga duk matar da ta san cewa mijin
ta baya iya danne sha'warsa a duk lokacin da dama ta samu, to ta nisanci mijin
ta acikin azumi, kuma ta daina yin ado ko kwalliya a cikin watan azumi.
Abin da a ke so agare ki ya ke 'yar'uwa Musulma,
idan kina jinin haila to ki zauna bisa al'adarki tayin jini a duk wata, ki
yarda da abin da Allah ta’ala ya hukunta agareki, kada kiyi qokarin shan wani
abu da zai hana jinin fitowa, ki karvi abin da Allah ya yarje miki, na shan
azumin akwanakin haila da yin ramuwar su bayan salla, domin kuwa haka matan
Annabi Alaihissalam iyayen muminnai, da matan salihan bayin Allah, suka
hakura.Amma idan kika qi, kika sha wani magani domin hana fitar jinin haila a
watan azumi, jinin kuwa ya xauke kika samu tsarki kika cika azumin ki cif-cif,
batare da kin sha ko xaya ba, to babu kommai amma baki yi koyi da iyayen
muminai ba, kuma baki samu ladan yin koyi da salihan bayi ba.
TSOKACI GA MAI KARATU
Mai karatu mai daraja, wannan littafi an rubuta shi
ne domin ya zamar maka jagora wajen fahimtar tasirin azumi ga lafiyar jiki da
ta ruhu. A cikin wannan zamani da ake fama da cututtuka daban-daban, rashin
nutsuwa da takurawar rayuwa, azumi ya kasance ɗaya
daga cikin manyan hanyoyin da Musulunci ya tanadarwa mutum domin gyaran jiki,
kwakwalwa da zuciya.
A yayin da kake karanta wannan littafi, ina roqon ka ka buɗe
ranka da zuciyarka domin karɓar ilimi cikin natsuwa. Wannan rubutu ba
wai kawai ya ta'allaka kan hujjojin addini ba, har ila yau ya tattaro bayanan
masana kimiyya na zamani, waɗanda suka tabbatar da hikimar da ke
cikin ibadar azumi tun kafin kimiyya ta gano su.
Za ka tarar da wasu abubuwa sun kasance sabbin
bayanai gare ka, yayin da wasu kuma ka taɓa
jinsu. Amma ba a taɓa yi maka cikakken bayani irin wannan
ba. Manufar wannan littafi ita ce ya ɗora ka a kan hanya madaidaiciya ta fahimtar
amfanin azumi ga lafiyarka, da yadda zaka iya cin moriyarsa a rayuwarka ta yau
da kullum.
Ina qarfafar
ka da ka yi amfani da abin da ka koya a nan. domin ilimi ba ya amfanar da mutum
sai idan ya yi aiki da shi. Ka yi qoqari ka isar da wannan faɗakarwa ga sauran jama’a, musamman ma ’yan uwanka, da
abokanka, da yara da Matasa maza da mata, domin ilimi yana yawaita ne idan aka
yaxa shi.
Idan kuma ka samu wani abu da kake ganin ya kamata a
qara, ko a gyara
ko a qara fayyace shi, ka hanzarta ka sanar da ni. Littafi tamkar gonar noma
ne: ana gyarawa, ana qawatawa,
ana qara inganta shi
lokaci zuwa lokaci.
Allah Ya sanya wannan littafi ya zama haske a gareni
da gare ka, Ya kuma biya ka da ladan neman ilimi da aikata abin da ya dace da
shi.
Dafatan Allah Ta’ala zai datar damu, ya shiryar damu
ya qaramana tsoronsa da biyayya agareshi, ya qara mana Lafiya da zaman Lafiya
da kwanciyar hankali a garunmu Kano da sauran garuruwan musulmi. Allah ka qara
tsira da aminci ga shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, da
ahalin gidansa da dukkan sahabbansa, da wadanda suka bishi da kyautatawa har
zuwa ranar karshe.
Alhamdulillah.
Kammalawa
Azumi ibada ce mai fa’idodi masu yawa ga ruhi, da jiki,
da kwakwalwa. Wannan littafi ya tattara bayanan malamai, masana kimiyya, da
shawarwarin kan abinci (dieticians) domin ilimantar da mai karatu yadda zai yi
azumi lafiya da amfani.
A karshe, manufa ita ce:
§ qara sanin hikimar azumi
§ Kula da lafiyar jiki da kwakwalwa
§ Inganta ruhi da halaye na addini
§ Samar da shawarwari masu amfani ga masu
azumi da duk mai sha’awar rayuwa lafiya
Ina fatan wannan littafi ya zama tushen qarin ilimi
ga al’umma da inganta lafiyar su, kuma Allah ya saka wa dukkan waxanda suka
bada gudunmawa wajen kammaluwar wannan littafi da alheri.
Godiya mai tarin yawa ga Mal. Kabiru Zubairu (Kabu)
bisa ga qoqarin da yake wajen ganin wannan littafi yakammala, Allah ya
saka masa da mafificin alhairi amin
Wassalamu
Alaikum
Auwal Zakari Muhammad Ayagi
(Barden Ayagi)
10 ga Rajab 1447 = 30/12/2025
TAQAITACCEN
TARIHIN MARUBUCI
An haifi Auwal Zakari Ayagi, (Barden
Ayagi) a Unguwar Ayagi, kuma marubuci ne qwararre
daga Kano Najeriya wanda ya himmatu wajen rubututtukan Addini, Tarihi, Nishadi
da kuma rubututtukan da suke saukaka ilimin fasahar zamani ga al'umma, a harshen
Hausa. Yana ɗaya
daga cikin marubutan farko-farko da suka rubuta littafi da hausa kan yanda za’a
koyi aiki da na’ura mai qwaqwalawa mai taken: “Koyon Kwamfuta a Saukake” Littafin
da ke koyar da kwamfuta daga tushe har zuwa matakin amfani da software da
Intanet, a cikin harshen Hausa.
• Manufarsa: “Ilimantarwa da
Nishaxantarwa da kuma fatan kowa ya iya kwamfuta, ko da ba ya jin Turanci
sosai.”
Fitattun
Ayyuka
1. Koyon Kwamfuta a
Saukake – Littafi mai koyar da kwamfuta daga
tushe har zuwa amfani da software da intanet.
2. Al-Usmaniyya I & II
– Tarihi da zuriyar Mal. Usman Hussaini Ayagi, mai dauke da Hotuna da dukkan
sunayen Zuriyar
3. Tasirin Azimi Ga
Lafiyar Xan Adam – Wanda Ya Tattara
Bayanan Manyan Malamai Da Likitocin Duniya.
4. Ruba da Illolinta –
Littafi mai ilimantarwa kan haɗarin
mu’amala da ruba a Musulunci.
5. Tarihin Unguwar Ayagi – Littafi
mai xauke da cikakke tarihin Unguwar Ayagi ta karamar hukumar Dala.
6. Hasken Rayuwata –
Littafi mai xauke da tarihin Manzon Allah (SAW); Rayuwa, Darussa, da Kyawawan
halaye
7. Aminchi a Zamanin Rashhin Aminci:
Littafin Nishaxi da faxakarwa
8. Sallah da
Hukunce-Hukuncenta a Musulunci: Littafin dake
bayani akan Sallah da Hukunce-hukuncenta.
9. Haquri Ginshikin Rayuwar Musulmi –
Littafi mai xauke da cikakke bayani akan Haquri da mahimmancin sag a dukkan
musulmi.
Manufofi
• Auwal
Zakari Ayagi na da burin ganin dukkan matasa a Arewa da Nijeriya baki ɗaya
sun ilimantu da koyarwar Addinin Islama, tare da nishxantuwa sannan su iya
amfani da na’urorin zamani kamar: kwamfuta, wayar zamani, da intanet, cikin
koyarwa addini
Hanyoyin Sadarwa da Tuntuɓa
§ E-mel:
auwalzakari@gmail.com/
§ Facebook:
www.facebook.com/auwal.ayagi
§ X (Twitter):
@auwalzakari
§ Website/Blog: www.sautulazmiyyah.blogspot.co.uk/
§ TikTok:
www.tiktok.com/auwalzakariayagi
§ Instagram: @auwalzakari.ayagi
·
GSM:
07038775781, 08023615685
Manazarta (Reference)
1.
Alqur’anil Kareem
2.
Sahih Buhari/Sahih Muslim da sauran
sahihan Litattafan Hadisi
3.
Al-talqeenu fil fiqhil Maliky: na Abu
Muhammad Abdulwahab Albagadady (Shafi na 171 -185)
4.
Al-Mulakhkhas Al-Fiqhy: na Shaik Salih
bn Fauzan Alfauzzan (Shafi 211- 222)
5.
Fatahul Jawad fi Sharhil Irshad: na Alh.
Yahuza bn Sa’id bn Muhammad (Shafi na 131-137)
6.
Fung, J. (2016). The Obesity Code:
Unlocking the Secrets of Weight Loss. Greystone Books.
7.
Longo, V. D., & Panda, S. (2016). Fasting,
circadian rhythms, and time-restricted feeding in healthy lifespan. Cell
Metabolism, 23(6), 1048–1059.
8.
https://doi.org/10.1016/j.cmet.2016.06.001
9.
Horne, B. D., et al. (2008). Usefulness
of routine periodic fasting to lower risk of coronary artery disease in
patients undergoing coronary angiography. American Journal of Cardiology,
102(7), 814–819.
10.
https://doi.org/10.1016/j.amjcard.2008.05.021
11.
Mattson, M. P., Longo, V. D., & Harvie, M. (2017). Impact of intermittent
fasting on health and disease processes. Ageing Research Reviews, 39, 46–58.
12.
https://doi.org/10.1016/j.arr.2016.10.005
13.
Mattson, M. P. (2012). Energy intake
and exercise as
determinants of brain health and vulnerability
to injury and disease. Cell Metabolism, 16(6), 706–722.
14.
https://doi.org/10.1016/j.cmet.2012.11.008
15.
Panda, S. (2016). Circadian physiology
of metabolism. Science, 354(6315), 1008–1015.
16.
https://doi.org/10.1126/science.aah4967
17.
Longo, V. D., & Mattson, M. P. (2014).
Fasting: Molecular mechanisms and clinical applications. Cell Metabolism,
19(2), 181–192.
18.
Fontana, L., & Neel, B. A. (2015).
Effect of low-calorie and intermittent fasting on aging and longevity. Current
Opinion in Clinical Nutrition & Metabolic Care, 18(4), 401–406.
19.
https://doi.org/10.1097/MCO.0000000000000183
20.
Varady,
K. A. (2011). Intermittent versus
daily calorie restriction: Which diet regimen is more effective for weight
loss? Obesity Reviews, 12(7), e593–e601.
21.
https://doi.org/10.1111/j.1467-789X.2011.00873.x
22.
https://www.health.harvard.edu/blog/intermittent-fasting-surprising-update-2018062914156
23.
https://www.mayoclinic.org/healthy-lifestyle/nutrition-and-healthy-eating/expert-answers/intermittent-fasting.
24.
https://chatgpt.com/c/6978ea2e-460c-8332-8bd0-d6944431d177
[1] - Suratul Baqata ayata 183
[3] -
Dr. Yoshinori Ohsumi:
Kwararren Likita ne dan kasar Jamus,
wanda ya lashe kyautar Nobel Prize sabo da binciken da yayi game da azumi.
[4] -
Dr. Valter
Longo: shi
ma masanin kimiyya ne akan kwayoyin halitta da kimiyyar tsufa, yana da asali
daga Italita, kuma kwararren masani a Amurka
[5] -
Cleveland
Clinic: Wata qungiyace da aka kafa a 1921, domin bayar da kulawa ga lafiya, da
bincike da kuma horar da ma’aikatan lafiya
[7] - Suratul Baqata ayata 183
[8] -
Bukhari (1894)– Muslim (1151)
[9] -
Bukhari (1896)- Muslim (1152)
[10] -
Bukhari (2840)- Muslim (1153) – Daga Abu Sa’id al-Khudri
[11] -Ibn
Majah (1638) – Tirmidhi (1624, ya ce Hasan Sahih) – Daga Abu Umamah al-Bahili
[12] – Bukhari (38)–
Muslim (760)
[13] – Bukhari (1904) –
Muslim (1151)
[14] – Bukhari (1904) –
Muslim (1151)
[15] – Tirmidhi (3598) —
Hasan
[16] –– Bukhari (1904) –
Muslim (1151)
[17] - Suratul Baqata ayata 185
[18] - Suratul Baqata ayata 185
[19] Suratul Nahl, aya ta
12 ko kuma Suratul Ibrahim, aya ta 7
[20] Mashahurin Masanin
kimiyyar Kwakwalwa ne(Neuroscience) yayi aiki a NIH, ya shahara sosai wajen
bincike kan azumi, qwaqwalwa da tsufa.
[21] Likita ce kuma
masaniyar kimiyar lafiya, ta shahara a vanbaren abinci da rayuwa (Metabolic
health)
[22] Likita ne masanin
tiyata ( surgeon)
[23] Shine masani kimiyya
da ya rubuta littafin (Fasting and Undernutrition) a 1925 littafin yayi bincike
sosai akan azumi da yunwa.
[24] (Sahih Bukhari, Sahih Muslim
[25] - Suratul Baqata ayata 184
[27] -
Buhari da
Muslim suka rawaito
[28] -
Sahih
Muslim, 1162