HUKUNCE-HUKUNCEN SALLAR IDI BABBA DA LAYYA
Daga Auwal Zakari Ayagi Chairman Al’Azmiyyah Islamic
Foundation Kano State
GSM: 08090987314 www.sautulazmiyyah.blogspot.com Email:auwalzakari@gmail.com
SALLAR IDI BABBA
Sallar Idil Dhuha (Sallar Idi Bbba)
Sunnace mai karfi. Ubangiji Mai Girma da daukaka shi ya yi umarni da ayita
cikin Littafinsa Mai Girma in da ya ke cewa: “Hakika mun baka Alkausara, kayi
Sallah ga Ubangijinka, ka soke abin yankanka” (Suratul Kausar aya ta
1-2). Manzon Allah Alaihissalam ya yi ta kuma yayi umarni
da yinta, yana fita don yin Sallar tare da Mata da kananan yara, Sallar tana
kara Imani da tsoron Allah. Ana yin tane a ranar goma ga Zulhijja.
Lokacin Sallatarta:
Lokacin da ake Sallatar Idin shine daga lokacin da Rana ya
dago, ana so asaurari huduba yayin da aka kamala Sallar.
Ladaban
Sallar Idi: Ladubban Sallar idi sune kamar haka:
1.
Wanka da
sanya sababbin tufafi ko mafiya kyau, tare da fesa turare, saboda hadisin da ke
cewa: Manzon Allah ya umarcemu a ranakun
idi biyu da musanya tufafi kyawawa, mu fesa turare mafi kamshi….,(Hakim)
2.
Yana daga
Ladabanta canja hanyar da aka tafi yayin dawowa, Saboda Shugaba
Alaihissalam ya kasance yana canja hanya
a ranar idi (Buhari)
3.
Yin Sallah
a sarari ma’ana ba a cikin masallaci ba, sai dai idan da lalurar ruwa ko
makamancin haka, to sai ayi a cikin masallaci.
4.
Taya juna
farin ciki tare da fadin musulmi ga dan’uwansa, Allah ya karba agareni ya karba
a gareka. Kamar yadda aka rawaito Sahabban Manzo sun kasance idan sun hadu da
yan’uwansu suna fadin Allah ya karba garemu da gareka (TAKABBALALLAHU MINNA WA MINKA).
YANDA AKE YIN SALLAR IDI
Yadda
ake yin Sallar Idi shine, mutane su fito izuwa masallaci yayin da rana tafito,
sai liman ya tsaya don Salla batare da kiran Salla ko ikama ba, zaiyi Raka’o’i
biyu, a raka’ar farko zai yi kabarbari guda bakwai, tare da kabbarar harama,
mutanen da suke bayansa za su rika yin kabbara a duk yayin da yayi kabbararsa,
sai ya karanta Fatiha da Suratul A’ala, a bayyane. A raka’a ta biyu, zai yi
kabarbari guda shida tare da kabbarar tsayuwa, zai karanta Fatiha da suratul
Jashiyati ko suratul Shamsi, idan yayi sallama sai ya tashi don yiwa mutane
huduba. Bayan ya budeta da yabo da Allah, da godiya a gareshi, sai ya kwadaitar
da mutane akan falalar yin Layya da bayyana musu hukumce-hukumcenta da yanda a
ke yenta da kuma lokacin da ake yita, yayin daya kamala huduba sai mutane su
taya junansu murna, sannan su koma zuwa gidajensu, ba za ayi sallar nafila ba
bayan sallar Idi ko kafinta, sai dai in wanda sallar Idin ta kubuce masa ne,
sai ya sallaceta raka’a hudu, saboda fadin Ibn Mas’ud Allah ya kara yarda a
gareshi: “Wanda Sallar Idi ta kubuce masa
ya sallaci raka’a hudu, amma wanda ya riski wani abu tare da Liman koda zaman
tahiya ne to sai ya tashi bayan liman yayi sallama ya sallaci raka’a biyu.
HUKUNCE-HUKUNCEN LAYYA
MA’ANAR LAYYA: Al’udhhiyyati wato
Layya a shari’ance tana nufin wata dabba da ake yankawa ranar Sallar Idi Babba
don neman kusanci ga Allah madaukakin sarki.
HUKUNCIN LAYYA: Layya Sunna ce wajiba
akan dukkan musulmin da Allah ya horewa, Allah ta’ala Yana cewa: Kayi Sallah
ga Ubangijinka kuma kayi yanka. (Kausar:2) Akwai Hadisai masu yawa da sukayi
bayani a kan layya, daga cik akwai fadinSa Annabi Alaihissalam wanda ya yi
layya kafin sallar idi ya sake (Layyar) (Turmizi ya rawaito ya inganta shi).
FALALAR DA KE CIKIN LAYYA: Layya tana da falala
maigirma, sabo da fadin Annabi Alaihissalam cewa: “Babu wani aiki dad an Adam
zaiyi a ranar Idi da Allah yafiso fiye day a kwararar da Jini, (Layya) har zuwa
karshen hadisin ibn majah. Da kuma fadinsa yayin da aka tambayeshi game da
Layya Sai yace: Sunnar Baban ku Annabi Ibrahim ce, sai suka ce: mai ya ke
garemu da ita, Sai Manzo Yace: ga dukkan gashin ta akwai (Hasna) Lada, sai sukace
Ga buzun ta (Fata) sai yace ga dukkan gashin fatan akwai Lada.
HIKIMAR YIN LAYYA
ü
Neman kusanci ga Allah, domin fadin
Allah maigirma da daukaka “Kayi Salla ka soke abin yankanka” (Suratul Kausar,
Aya ta 2) da fadin sa cikin Suratul An’am Aya ta 162-163. Cewa: “Kace hakika
Sallah tad a yankana da Rayuwata da mutuwata ga Allah suke ubangijin talikai,
bashi da abokin tayayya.
ü
Raya Sunnar shugaban
masu kadaita Allah Annabi Ibrahim Alaihis Salam, yayin da Allah yayi wahayi
gareshi daya yanka dansa Annabi Isma’il, sai aka fansheshi da Rago, ya yankashi
don sauyi daga dan nasa, Ubangiji yace: “Sai muka fansheshi da abin yanka mai
girma” (Suratul Saafaat, Aya ta 107)
ü
Yalwatawa iyali ranar Idi, ta ciyar da
talakawa da mabukata.
ü
Godewa Allah madaukakin sarki bisa
horewar dabbobin Ni’ima garesu.
Layya tana wajaba kan wanda
ya cika sharudda masu zuwa:
ü
Ya kasance da ba bawa ba,
(namiji ko mace).
ü
Tana zama sunna kan mutum
a kansa da iyayensa, idan talakawa ne, da Yayansa Maza idan ba su balaga ba, da yayan sa mata idan ba su yi aure
ba.
ü
Kada ya kasance mahajjaci,
domin shi mahajjaci, hadaya ce a kansa ba Layya ba.
ü
Ya zamaba matalauci ne
ba. Ma'ana kada ya zama yana bukatar kudin yin layyar domin biyan wasu bukatu nasa.
Amma idan zai iya cin bashi ya yi layyar, to ya yi, idan ya san zai iya biya, ba
tare da takuruwa ba. Wasu malaman suka ce kada mutum ya ci ba shi domin yin layya.
DABBOBIN DA AKE YIN
LAYYA DA SU
Dabbobin da akeyin layya
da su akwai Rakumi, Sa, Rago da Taure, dakuma matansu. Rago sai wanda ya shekara, Taure kuwa sai ya shiga
shekara ta biyu. Sa kuma sai wanda ya kai shekaru uku. Shi kuwa rakumi sai ya kai
shekara biyar.
A wajen layya, Rago ya fi falala (sai tunkiya), sai Taure (sai
akuya), Sai kuma Sa (sai Saniya), bayan Sa sai kuma saniya, Sannan Rakumi (sai taguwa).
A cikin kuma dukkan dabbobin
da aka ambata anfifita mazansu a kan matansu, lafiyayyun su akan marasa Lafiya,
wadanda suke iya yin barbara a kan fidiyayyun su, Sai dai idan fidiyayyun sun fi
kitse ne sai a yi da su.
Sharuddan ingancin
layya
1.
Dole ne a yi yankan da rana, bai inganta ba a yi Layya da
daddare ba. Rana tana farawa ne daga ketowar alfijir, Amma game da layyar sai liman (shugaba) ya yanka nasa abin layyar sannan sauran jama’ar
gari su yanka nasu, ba kawai da an wayi gari ba sai kowa ya yanka na sa ba, idan
mutum yayi yanka kafin liman ya yanka nasa, layyarsa ba ta yi ba.
2.
Mai yin yankan dole ne ya zama Musulmi, yankan
kafiri bai halatta ba, koda kuwa ma'abocin liittafi ne (Ahlul-kitabi)
3.
Ya halatta a yi gamayya a cikin layya idan
dabbar layyar ta zama Rakumi ko Saniya. Sannan kuma kada adadin masu gamayyar ya wuce bakwai.
Idan suka wuce bakwai, bai halatta su yi gamayya a dabba daya ba. Dalili a nan shi ne
Hadisin Jabir (RA) da yake cewa: Mun yi layya tare Manzon Allah SAW) a shekarar
Hudaibiyya, kowace taguwa mutane bakwai,saniya ma mutane bakwai (Muslim ya ruwaito).
4.
Dole dabbar layyar ta kasanceta
kubuta daga cututtuka ko aibubbuka da sukea fili karara. Saboda Hadisin da Bara
(RA) ya ruwaito dagaManzon Allah (SAW) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya mike tsaye cikinmuyace: Dabbobi hudu bai
halatta a yi layya da su ba. Mai ido daya wadda rashin idon ya fito fili. Marar
lafiya, waddarashinlafiyarta ya fito fili, ko Gurguwa, waddan gurguntakarta fito
fili, wadda ta karye kafa da kuma wadda bata da bargo (Abu Dauda ya ruwaito), da
kuma Hadisin da aka ruwaito daga Aliyu (RA) cewa: Annabi (SAW) ya hanayin layya
da dabba mai gutsurarren kunne da gutsurarren kaho (Abu Dauda ya ruwaito).
Haka nan ba za a yi da
mai gutsurarriyar kafar gaba ko ta baya ba, ko marar ji ko mai warin baki,ko wadda
ba ta yin kuka, ko marar bargo,komai gutsurarren bindi ko marar lafiyar da
rashin lafiyarta yafito filiko mahaukaciya, ko madauwamin hauka, kogurguwa ko ramammiyar
da ramarta tafito fili. Dukkan abubuwanda aka ambata a baya, idan masu sauki ne,
babu laifi,
saia yi layya da ita. Haka nan bai halatta yi layya da dabbar da kahonta ya karye yake yin jini ba. Ko wadda kashi daya daga cikin uku na bindinta ya gutsure. Amma idan wanda ya gutsure bai kai kashi daya cikin uku ba, babu laifi.
Haka nan kuma wadda ta rasa hakora biyuko
fiyeba domin yarinta ko tsufa ba. Amma idan hakori daya ta rasa, babu laifi.
Haka nanidan fiye da kashi daya cikin uku na kunnenta ya tsage, ba a layya da
ita.
Wadanan sune kadan daga cikin bayanan hukumce
hukumce game da Sallar idi Babba da layya, abin da akaji na daidai daga Allah
ne, na kuskure kuwa daga gareni ne.
Allah
ya kara tsira da aminci ga shugaban halitta cikamakin Annabawa da ahalin
gidansa, da sahabbansa da dukkan wadanda suka bishi da kyautatawa, A kulu kauli
haza wa astagfirullaha li wa lakum, wassalamu alaikum warahamatullahi ta’ala wa
barakatuhu.