Thursday, 19 September 2013

HUKUNCE-HUKUNCEN SALLAR IDI BABBA DA LAYYA


HUKUNCE-HUKUNCEN SALLAR IDI BABBA DA LAYYA
Daga Auwal Zakari Ayagi Chairman Al’Azmiyyah Islamic Foundation Kano State
GSM: 08090987314 www.sautulazmiyyah.blogspot.com Email:auwalzakari@gmail.com

SALLAR IDI BABBA
Sallar Idil Dhuha (Sallar Idi Bbba) Sunnace mai karfi. Ubangiji Mai Girma da daukaka shi ya yi umarni da ayita cikin Littafinsa Mai Girma in da ya ke cewa: “Hakika mun baka Alkausara, kayi Sallah ga Ubangijinka, ka soke abin yankanka” (Suratul Kausar aya ta 1-2). Manzon Allah Alaihissalam ya yi ta kuma yayi umarni da yinta, yana fita don yin Sallar tare da Mata da kananan yara, Sallar tana kara Imani da tsoron Allah. Ana yin tane a ranar goma ga Zulhijja.
          Lokacin Sallatarta: Lokacin da ake Sallatar Idin  shine daga lokacin da Rana ya dago, ana so asaurari huduba yayin da aka kamala Sallar.
          Ladaban Sallar Idi: Ladubban Sallar idi sune kamar haka:
1.              Wanka da sanya sababbin tufafi ko mafiya kyau, tare da fesa turare, saboda hadisin da ke cewa: Manzon Allah ya umarcemu a ranakun idi biyu da musanya tufafi kyawawa, mu fesa turare mafi kamshi….,(Hakim)
2.              Yana daga Ladabanta canja hanyar da aka tafi yayin dawowa, Saboda Shugaba Alaihissalam  ya kasance yana canja hanya a ranar idi (Buhari)
3.              Yin Sallah a sarari ma’ana ba a cikin masallaci ba, sai dai idan da lalurar ruwa ko makamancin haka, to sai ayi a cikin masallaci.
4.              Taya juna farin ciki tare da fadin musulmi ga dan’uwansa, Allah ya karba agareni ya karba a gareka. Kamar yadda aka rawaito Sahabban Manzo sun kasance idan sun hadu da yan’uwansu suna fadin Allah ya karba garemu da gareka (TAKABBALALLAHU MINNA WA MINKA).
YANDA AKE YIN SALLAR IDI
Yadda ake yin Sallar Idi shine, mutane su fito izuwa masallaci yayin da rana tafito, sai liman ya tsaya don Salla batare da kiran Salla ko ikama ba, zaiyi Raka’o’i biyu, a raka’ar farko zai yi kabarbari guda bakwai, tare da kabbarar harama, mutanen da suke bayansa za su rika yin kabbara a duk yayin da yayi kabbararsa, sai ya karanta Fatiha da Suratul A’ala, a bayyane. A raka’a ta biyu, zai yi kabarbari guda shida tare da kabbarar tsayuwa, zai karanta Fatiha da suratul Jashiyati ko suratul Shamsi, idan yayi sallama sai ya tashi don yiwa mutane huduba. Bayan ya budeta da yabo da Allah, da godiya a gareshi, sai ya kwadaitar da mutane akan falalar yin Layya da bayyana musu hukumce-hukumcenta da yanda a ke yenta da kuma lokacin da ake yita, yayin daya kamala huduba sai mutane su taya junansu murna, sannan su koma zuwa gidajensu, ba za ayi sallar nafila ba bayan sallar Idi ko kafinta, sai dai in wanda sallar Idin ta kubuce masa ne, sai ya sallaceta raka’a hudu, saboda fadin Ibn Mas’ud Allah ya kara yarda a gareshi: “Wanda Sallar Idi ta kubuce masa ya sallaci raka’a hudu, amma wanda ya riski wani abu tare da Liman koda zaman tahiya ne to sai ya tashi bayan liman yayi sallama ya sallaci raka’a biyu.
HUKUNCE-HUKUNCEN LAYYA
MA’ANAR LAYYA: Al’udhhiyyati wato Layya a shari’ance tana nufin wata dabba da ake yankawa ranar Sallar Idi Babba don neman kusanci ga Allah madaukakin sarki.
HUKUNCIN LAYYA: Layya Sunna ce wajiba akan dukkan musulmin da Allah ya horewa, Allah ta’ala Yana cewa: Kayi Sallah ga Ubangijinka kuma kayi yanka. (Kausar:2) Akwai Hadisai masu yawa da sukayi bayani a kan layya, daga cik akwai fadinSa Annabi Alaihissalam wanda ya yi layya kafin sallar idi ya sake (Layyar) (Turmizi ya rawaito ya inganta shi).
FALALAR DA KE CIKIN LAYYA: Layya tana da falala maigirma, sabo da fadin Annabi Alaihissalam cewa: “Babu wani aiki dad an Adam zaiyi a ranar Idi da Allah yafiso fiye day a kwararar da Jini, (Layya) har zuwa karshen hadisin ibn majah. Da kuma fadinsa yayin da aka tambayeshi game da Layya Sai yace: Sunnar Baban ku Annabi Ibrahim ce, sai suka ce: mai ya ke garemu da ita, Sai Manzo Yace: ga dukkan gashin ta akwai (Hasna) Lada, sai sukace Ga buzun ta (Fata) sai yace ga dukkan gashin fatan akwai Lada.
HIKIMAR YIN LAYYA
ü  Neman kusanci ga Allah, domin fadin Allah maigirma da daukaka “Kayi Salla ka soke abin yankanka” (Suratul Kausar, Aya ta 2) da fadin sa cikin Suratul An’am Aya ta 162-163. Cewa: “Kace hakika Sallah tad a yankana da Rayuwata da mutuwata ga Allah suke ubangijin talikai, bashi da abokin tayayya.
ü    Raya Sunnar shugaban masu kadaita Allah Annabi Ibrahim Alaihis Salam, yayin da Allah yayi wahayi gareshi daya yanka dansa Annabi Isma’il, sai aka fansheshi da Rago, ya yankashi don sauyi daga dan nasa, Ubangiji yace: “Sai muka fansheshi da abin yanka mai girma” (Suratul Saafaat, Aya ta 107)
ü  Yalwatawa iyali ranar Idi, ta ciyar da talakawa da mabukata.
ü  Godewa Allah madaukakin sarki bisa horewar dabbobin Ni’ima garesu.
Layya tana wajaba kan wanda ya cika sharudda masu zuwa:
ü  Ya kasance da ba bawa ba, (namiji ko mace).
ü  Tana zama sunna kan mutum a kansa da iyayensa, idan talakawa ne, da Yayansa Maza idan ba su balaga ba, da yayan sa mata idan ba su yi aure ba.
ü  Kada ya kasance mahajjaci, domin shi mahajjaci, hadaya ce a kansa ba Layya ba.
ü  Ya zamaba matalauci ne ba. Ma'ana kada ya zama yana bukatar kudin yin layyar domin biyan wasu bukatu nasa. Amma idan zai iya cin bashi ya yi layyar, to ya yi, idan ya san zai iya biya, ba tare da takuruwa ba. Wasu malaman suka ce kada mutum ya ci ba shi domin yin layya.

DABBOBIN DA AKE YIN LAYYA DA SU
Dabbobin da akeyin layya da su akwai Rakumi, Sa, Rago da Taure, dakuma  matansu. Rago sai wanda ya shekara, Taure kuwa sai ya shiga shekara ta biyu. Sa kuma sai wanda ya kai shekaru uku. Shi kuwa rakumi sai ya kai shekara biyar.
A wajen layya,  Rago ya fi falala (sai tunkiya), sai Taure (sai akuya), Sai kuma Sa (sai Saniya), bayan Sa sai kuma saniya, Sannan Rakumi (sai taguwa).
A cikin kuma dukkan dabbobin da aka ambata anfifita mazansu a kan matansu, lafiyayyun su akan marasa Lafiya, wadanda suke iya yin barbara a kan fidiyayyun su, Sai dai idan fidiyayyun sun fi kitse ne sai a yi da su.
Sharuddan ingancin layya
1.     Dole ne a yi yankan da rana, bai inganta ba a yi Layya da daddare ba. Rana tana farawa ne daga ketowar alfijir, Amma  game da layyar sai liman (shugaba) ya  yanka nasa abin layyar sannan sauran jama’ar gari su yanka nasu, ba kawai da an wayi gari ba sai kowa ya yanka na sa ba, idan mutum yayi yanka kafin liman ya yanka nasa, layyarsa ba ta yi ba.
2.     Mai yin yankan dole ne ya zama Musulmi, yankan kafiri bai halatta ba, koda kuwa ma'abocin liittafi ne (Ahlul-kitabi)
3.     Ya halatta a yi gamayya a cikin layya idan dabbar layyar ta zama Rakumi ko Saniya. Sannan kuma kada adadin masu gamayyar ya wuce bakwai. Idan suka wuce bakwai, bai halatta su yi gamayya a dabba daya ba. Dalili a nan shi ne Hadisin Jabir (RA) da yake cewa: Mun yi layya tare Manzon Allah SAW) a shekarar Hudaibiyya, kowace taguwa mutane bakwai,saniya ma mutane bakwai (Muslim ya ruwaito).
4.    Dole dabbar layyar ta kasanceta kubuta daga cututtuka ko aibubbuka da sukea fili karara. Saboda Hadisin da Bara (RA) ya ruwaito dagaManzon Allah (SAW) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya mike tsaye cikinmuyace: Dabbobi hudu bai halatta a yi layya da su ba. Mai ido daya wadda rashin idon ya fito fili. Marar lafiya, waddarashinlafiyarta ya fito fili, ko Gurguwa, waddan gurguntakarta fito fili, wadda ta karye kafa da kuma wadda bata da bargo (Abu Dauda ya ruwaito), da kuma Hadisin da aka ruwaito daga Aliyu (RA) cewa: Annabi (SAW) ya hanayin layya da dabba mai gutsurarren kunne da gutsurarren kaho (Abu Dauda ya ruwaito).
Haka nan ba za a yi da mai gutsurarriyar kafar gaba ko ta baya ba, ko marar ji ko mai warin baki,ko wadda ba ta yin kuka, ko marar bargo,komai gutsurarren bindi ko marar lafiyar da rashin lafiyarta yafito filiko mahaukaciya, ko madauwamin hauka, kogurguwa ko ramammiyar da ramarta tafito fili. Dukkan abubuwanda aka ambata a baya, idan masu sauki ne, babu laifi,

saia yi layya da ita. Haka nan bai halatta yi layya da dabbar da kahonta ya karye yake yin jini ba. Ko wadda kashi daya daga cikin uku na bindinta ya gutsure. Amma idan wanda ya gutsure bai kai kashi daya cikin uku ba, babu laifi.
Haka nan  kuma wadda ta rasa hakora biyuko fiyeba domin yarinta ko tsufa ba. Amma idan hakori daya ta rasa, babu laifi. Haka nanidan fiye da kashi daya cikin uku na kunnenta ya tsage, ba a layya da ita.
Wadanan sune kadan daga cikin bayanan hukumce hukumce game da Sallar idi Babba da layya, abin da akaji na daidai daga Allah ne, na kuskure kuwa daga gareni ne.
Allah ya kara tsira da aminci ga shugaban halitta cikamakin Annabawa da ahalin gidansa, da sahabbansa da dukkan wadanda suka bishi da kyautatawa, A kulu kauli haza wa astagfirullaha li wa lakum, wassalamu alaikum warahamatullahi ta’ala wa barakatuhu.

No comments:

Post a Comment