Tarihin Sahabi Salman Farisi (RTA)
Daga Auwal Zakari Muhammad Ayagi
Shugaban kungiyar Alazmiyyah Islamic Foundation
Takaitaccen tarihin sahabin Manzon Allah (SAW) mai girma wato Salman Farisi, to wasu ruwayoyi na tarihi sun bayyana cewar an haifi Salman al-Farisi ne a shekara ta 568 miladiyya ko kuma kusa da haka a wani gari na kasar Farisa da ake kira Jiyye da a halin yanzu yake kusa da garin Isfahan (a Iran). Asalin sunansa shi ne Rozeba, sai dai daga baya, bayan musuluntarsa Manzon Allah (s.a.w.a) ya sauya masa suna zuwa Salman, an ce a wasu lokuta a kan kira shi da Abu Abdullah. Mahaifin Salman dai attajiri ne sanann kuma mai fadi a ji a garin nasu da kewayensa. To sai dai duk da arzikin da yake da shi, Salman shi ne dansa kawai, don haka yake tsananin kaunarsa.A wancan lokacin mafi yawan al'ummar Farisa suna bin addinin bautan wuta ne, don haka cikin wannan addini ne Salman ma ya taso, inda mahaifinsa ya ware wasu malamai don koyar da shi akidu da koyarwar wannan addini, ta amma sakamakon irin hazakar da yake da ita ya zamanto ya sami ilmi mai yawan gaske sama da malaman da suke koyar da shi. A wancan lokacin babban abin alfahari ne ace mutum ya zamanto daya daga cikin malaman addini kuma mai hidima wa daya daga cikin dakunan bautan wutan a kasar Farisan, hakan na kawo wa mutum daukaka da girmamawa. Don haka ne mahaifin Salman yayi kokarin ganin dansa ya zamanto daya daga cikin irin wadannan mutane tun yana dan shekara sha shida a duniya.Salman yayi shekaru uku yana aiki a dakin bautan wuta na Jiyye, to sai dai ba a jima ba sai ya fara kosawa da wannan aiki da malaman dake karantar da shi saboda kasantuwansu mutane masu karancin tunani da ilimi. A mafi yawan lokuta ba sa iya amsa tambayoyin da yake musu ko kuma su ba shi amsa maras gamsarwa. Don haka tun daga lokacin ya fara tunanin yadda zai sami wata mafita. Salman ya fara samun damar ficewa daga wannan addini ne lokacin da mahaifinsa ya tura shi wani gari don ya wakilce shi a wajen. A hanyarsa ta zuwa wannan gari ne ya ci karo da wasu ma'abota addinin kirista da suka fito daga kasar Siriya, inda suka yi masa bayanin akidun addininsu, daga karshe dai Salman ya zama Kirista.Bayan da ya dawo gida, Salman ya shaida wa mahaifinsa ganawarsa da wadannan kiristocin da kuma karbar addinin kiristancin da ya yi. Hankalin mahaifin Salman ya kara tashi kwarai, nan take ya bukaci ya yi da wannan sabon addini amma Salman yaki, don haka sai ya sa aka ta dukansa aka kuma tsare shi kwana da kwanaki ba tare da abinci ko ruwan sha ba.Bayan zama a gidan yari na wani lokaci, Salman ya samu nasarar tserewa daga inda ake tsare da shi ta hanyar taimakon daya daga cikin bayin babansa mai suna Mehran wanda yake tsananin kaunar Salman saboda shi yake kula da shi tun yana yaro. Bayan da ya gudu Salman ya koma wajen wadannan kiristocin inda su kuma suka tura shi kasar Siriya tare da wani ayari.A lokacin da ya isa kasar Siriyan a nan ma ya ci gaba da karatu da neman ilimi ta haka ne ya tara dimbin ilimi mai yawa. To sai dai a wannan karon ma ya sake shiga wata damuwar, yana jin cewa lalle abin da yake kai ba shi ne hakikanin gaskiya ba, akwai gaskiya ta hakika da har yanzu bai same ta ba. Lokacin da wannan tunani ya dame shi sosai sai ya mika komai ga Allah Madaukakin Sarki Yana mai addu'ar cewa Allah Ya nuna masa hakikanin gaskiya. Allah Mai karban, Salman bai san cewa ya kusa kai wa ga gaskiyar da yake bukata ba..Bayan da ya bar garinsu Salman ya zauna a kimanin garuruwa guda hudu, gari na karshe da ya zauna shi ne Ammuriya dake karkashin daular Rumawa. A nan ne a karon farko ya sami labarin bayyanar wani Annabi a garin Makka da yazo da sakon bautan Allah Shi kadai da yin watsi da bautan gumaka. Nan take Salman ya fara tunanin cewa watakila wannan haske da ya bayyana a Makka shi ne shiriyar da yake bukata. Don haka ya fara shirye-shiryen tafiya Makka don ganawa da wannan sabon Annabi don jin ta bakinsa.To sai dai a hanyarsa ta tafiya Madina nan ya fuskanci matsala inda ayarin 'yan kasuwan da yake tare da su suka ha'ince suka sayar da shi ga wasu yahudawa. Su ma wadannan yahudawan sai suka sayar da shi ga wani attajiri mutumin Madina wanda yake zuwa wajen don kasuwanci. Duk da irin wahalhalun da ya fuskanta a matsayin bawa a Madina amma hakan bai hana shi ci gaba da binciken yadda zai sadu da Manzon Allah (s.a.w.a), duk da cewa a lokacin Manzo bai riga da ya yi hijira zuwa Madina ba. Wata rana Salman yana cikin aiki sai ya ji mai gidansa yana tattaunawa da wani mutum wanda yake bayyana masa cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi hijira zuwa garin Yathrib (Madina), nan take Salman ya fara tunanin yadda zai sami damar ganawa da wannan Annabin.Wata rana kuwa sai mai gidan nasa ya yi tafiya don haka sai ya nufi gidan Abu Ayyub al-Ansari (r.a) wanda Manzon Allah (s.a.w.a) yake zaune a gidansa a lokacin. Ko da suka yi ido biyu da Manzon Allah (s.a.w.a) nan take sai ya ji zuciyarsa ta cika da kaunar wannan Annabi yana gaya wa kansa cewa lalle wannan mutumi ba makaryaci ba ne.Bayan wani lokaci na tattaunawa a tsakaninsu, Salman ya karbi Musulunci, yayi imani da cewa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu bawansa ne kuma ManzonSa. A nan ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya sake masa suna zuwa Salman, wanda da hakan ne aka sanshi tsawon tarihi. Tun daga wannan lokaci Salman ya ci gaba da zuwa wajen Ma'aiki (s.a.w.a) a kai a kai.Da haka ne Salman ya cimma burinsa, wato ya samu tafarkin da zai amsa masa tambayoyin da yake da su da magance masa matsalolin da yake fama da su, baya ga samun darajar kasancewa daya daga cikin sahabban Ma'aikin Allah (s.a.w.a).Matsala guda da Salman yake fama da ita, ita ce bautan da ya ke yi don shi bawa ne. Don haka wata rana Manzon Allah (s.a.w.a) ya bukaci mai gidan Salman ya sayar masa da shi don ya 'yantar da shi daga bauta. Mai gidan Salman ya kafa sharadin cewa wajibi ne Salman ya shuka masa bishiyar dabino 300 sannan kuma ya biya oza arba'in na zinare a matsayin kudin fansarsa. Lokacin da Salman ya gabatar wa Manzon Allah (s.a.w.a) da wannan bukata ta mai gidansa, sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya juya ga sahabbansa ya ce musu: "ku taimaki dan'uwanku".Nan take Sahabbai suka mike suka hada wadannan bishiyoyi da bayahuden yake bukata, sannan Annabi (s.a.w.a) ya bukace su da su tona ramukan da za a shuka su, bayan da aka gama tona ramin sai Manzo (s) ya zo da kansa ya shuka bishiyar farko sannan sauran sahabbai suka biyo sahu. To an gama shuka bishiyoyi amma abu guda ya rage shi ne zinare, don haka har ya zuwa yanzu Salman yana a matsayin bawa. Bayan wani lokacin kuma Manzon Allah (s.a.w.a) ya tara wadanann zinare da ake bukata inda ya ba wa Salman don ya kai wa mai gidansa don cika wannan sharadi na 'yantar da shi.Ta haka ne Musulunci ya ‘yantar da Salman Al-Farisi.Daya daga cikin gagarumar hidimar da Salman yayi wa Musulunci shi ne lokacin da kafiran Makka suka shirya makircin kawo hari birnin Madina da mamaye shi gaba daya. A wannan lokaci ne Salman ya ba wa Ma'aiki (s.a.w.a) shawarar a tona rami mai zurfin gaske a kewaye garin Madina da shi don hana makiyan shigowa. Bayan gama tonun ramin sahabbai sun yi farin ciki da jinjina wa Salman kowani bangare naso ya janyo shi zuwa ga bangarensa, hakan ne ma ya sanya wani daga cikin Muhajirai (mutanen Makka da suka yi hijira zuwa Madina) ya ce: "Salman daya ne daga cikinmu mu Muhajirai", nan take sai wani Ba'ansare (mutumin Madina) ya yi caraf yace: ‘A'a Salmanu daya ne daga cikinmu, mu Ansarawa". Haka dai aka ci gaba da kace nace tsakanin bangarorin biyu.Bayan wani lokaci sai ga Manzon Allah (s.a.w.a) ya iso, yayin da yaji su suna wannan musu, sai yayi murmushi ya kawo karshen musun da cewa: "Salmanu ba Muhajiri ba ne ba kuma Ba'ansare ba ne, Salman yana daga cikin(mu) Ahlulbaiti".Wannan babban matsayi ne da Manzon Allah (s.a.w.a) bai taba ba wa wani mutum in ba Salman ba, wato Salmanu ya zamanto daga cikin Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a), zababbiyar zuriya daga wajen Allah Madaukakin Sarki. A tarihin Musulunci babu wani mutum da ya taba samun irin wannan gagarumin matsayi in ba Salman al-Farisi ba.Salman al-Farisi ya bar duniya ne yana da shekaru 88 a duniya.Salman al-Farisi ya rasu ne a lokacin halifancin Sayyadina Ali (RTA) a garin Mada'in, wajen da Sayyadina Ali ya nada shi a matsayin gwamnan wajen.
No comments:
Post a Comment