Tuesday, 17 June 2014

Bayani akan Aikin Hajji a takaice

Takaitaccen bayani kan aikin Hajji
Daga: www.sautulazimiyyah.blogspot.com

Da sunan Allah mai yawan Rahama mai yawan jinkai, tsira da aminci sukara tabbata ga Shuhaban Halitta da dukkanin sabansa baki daya.

Bayan haka Shi dai aikin Hajji ya kasu kashi uku ne:
1. Hajjin Tamattu’i.
2. Hajjin Kirani.
3. Hajjin Ifradi.

1. Hajjin tamattu'i: Shi ne wajibin wanda yake zaune a nesa da garin Makkah, nisan da ya kai mil 48, yayin da Hajjin Kirani da Ifradi sune wajibin wanda yake zaune a garin Makkah da kewayenta, wato nesansu da garin Makkah bai kai mil 48 ba. To amma a aikin Hajjin bakance, ko na mustahabbi, ya halatta ga mazaunin Makkah da wanda ke nesa da Makka ya zabi duk aikin Hajjin da ya ga dama tsakanin raben-raben da aka ambata a sama.
To bisa la’akari da cewa aikin Hajjin Tamattu’i shi ne wajibin mafiya yawa mutane, musamman mutanenmu, don haka za mu yi bayani ne kan wannan nau’i na aikin Hajji.

Ga yadda ake yin Umurar Tamattu’i: Da farko mutumin da ya yi niyyar yin aikin Hajjin Tamattu’i zai fara ne da daura harami a daya daga cikin wararen da ake daura haramin guda biyar, ko kuma abin da ake ce wa ‘mikati,’ wato: 

(1) Zul Hulaifa 

(2) Akik 

(3) Juhfa 

(4) Yalamlam 

(5) Karnil Manazil.


1. Harami: Shi ne sanya kyallen tufafin nan guda biyu da Alhaji zai sa yayin aikin Hajjin. 

Yadda ake daura harami shi ne: Mutum zai yi niyyar yin harami da Umurar Tamattu’i na Hajjin wajibi, sannan ya sanya tufafin haraminsa guda biyu, zai daura guda, ya kuma yafa guda, wato ya yi mayafi da shi. Daga nan sai ya fara ‘talbiyya’ wato fadin: Labbaikallahumma labbaik, labbaika la sharika laka labbaik, innal hamda, wan ni’amata laka wal mulk, la sharika laka. To idan mutum ya yi haka ya zamanto muhrimi (wanda ya daura harami) kenan da aikata wasu abubuwa suka haramta masa kamar su kusantar mace, shafa turare, sanya kewayayyen tufafi ga namiji, farauta da makamantansu. Akwai kuma wasu ayyuka na mustahabi da ake so mutum ya aikata, misalin yin wanka kafin daura harami da makamantan hakan. 

2. Dawafi: Abu na biyu cikin aikin Umrar Tamattu’i shi ne Dawafi, wato kewaya Dakin Ka’aba. Yadda kuma ake yin sa shi ne: Mutum zai fara da yom niyyar Dawafin Umurar Tamattu’i ne,sai ya fara zagaya Dakin Ka’aba har sau bakwai, zai fara ne daga inda Hajrul Aswad yake, wato Dakin Ka’aba na hannunsa na hagun. Idan ya fara daga wajen Hajrul Aswad ya zagayo ya zo wajen da ya fara, to ya yi guda kenan, haka-haka har sau bakwai.

3. Sallar Dawafi: Idan mutum ya gama dawafi wato ya kewaye Dakin sau bakwai, sai ya yi sallar Dawafin raka’a biyu a Makama Ibrahim. Wannan shi ne wajibin Umura ta Tamattu’i.

4. Sa’ayi: Wajibi na hudu shi ne Sa'ayi, wato tafiya tsakanin Safa da Marwa, yadda ake yin ta kuwa shi ne: Mutum ya yi niyyar yin Sa'ayi na Umrar Tamattu’i na Hajjin wajibi, sai ya fara tafiya daga Safa ya zo Marwa, daya kenan, sannan daga Marwa ya zo Safa, biyu kenan har sau bakwai. Wato tafiya daga Safa zuwa Marwa sau hudu, daga Marwa kuma zuwa Safa sau uku, wanda karshen tafiyar za ta kare ne a Marwa.

5. Aski: Wajibi na biyar kuma na karshe a Umurar Tamattu’i shi ne: Aski, ko kuma saisaye, mutum ya aske wani abu daga cikin gashin kansa ko gemunsa, ko gashin bakinsa, ko kuma ya yanke farcensa. Da hakan ne ake kare aikin Umurar Hajjin Tamattu’i, wanda hakan na nufin kenan dukkan abubuwan da aka haramta masa saboda harami a halin yanzu ya halatta a gare shi, misali kusantar mace, sanya turare da sauransu. Daga nan sai mutum ya jira lokacin daura haramin Hajjin Tamattu’i.

HAJJIN TAMATTU'I: 

Ayyukan Hajjin Tamattu'i Su ne: 

1. Saka harami a Makka.

2. Tsayuwa a Arafa.

3. Tsayuwa a Mash'arul Haram.

4. Jifan Jamratul-Akaba (jifan shaidan).

5. Yin hadaya.

6. Aske gashin kai ko rage shi.

7. Kwana a Mina a dare na sha daya.

8. Jifan jamrori(shedanu) uku a rana ta sha daya.

9. Kwana a Mina a dare na sha biyu.

10. Jifan jamrori (shedanu) uku a rana ta sha biyu.

11. Dawafin hajji.

12. Sallar dawafi.

13. Sa'ayi (Safa da Marwa).

14. Dawafin mata.

15. Sallar dawafi.

HUKUNCE - HUKUNCEN HAJJIN TAMATTU'I

An shardanta wa hajjin tamattu'i abubuwa kamar haka:

Na daya: Niya, ita ce nufin aikata irin wannan nau'in hajjin yayin daura ihramin umarar. Idan ba haka ba, bai inganta ba.

Na biyu: Ya zama umrar da hajjin ya yi su a watannin aikin hajji.

Na uku: Tilas ya yi hajji da umrar a cikin shekara guda.

Na hudu: Ya zama mai yin hajjin da umrar mutum guda ne.

Da zai dauki hayar mutum biyu su yi wa mamaci hajjin tamattu'i, watau daya ya yi umra dayan kuma ya yi masa hajjin, bai isar masa ba.

No comments:

Post a Comment