Friday, 20 June 2014

HUKUMCIN AZUMIN YA MACE A SHARIA

BAYANI AKAN HUKUMCIN AZUMIN MACE A SHARI’A

Daga www.sautulazimiyyah.blogspot.com

Da sunan Allah mai yawan Rahama,  Mai yawan jin kai, tsira da Aminci su kara tabbata ga fiyayyan halitta Annabin rahama, tare da saabbansa da iyalan gidansa, da duk masu binsa da kyautatawa har zuwa ranar Alkiyama.

Bayan haka Azumin watan Ramadan wajibi ne akan kowanne musulmi Namiji da musulma mace, kuma yana daya daga cikin manya manyan ginshikan musulunci, kuma daya ne daga cikin rukunansa, kamar fadin Allah (SWT) cikin littafinSa Mai tsarki cewa: "Yaku wadanda kuka yi imani, an wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi ga wadanda suka gabace ku, don kuji tsoron Allah" (Bakara aya ta 283).

Kamar yadda shari'a ta dora yin azumi akan namiji, haka ta dorawa ya mace yinsa, na Ramadanne ko na nafila, amma kuma shari'a ta rwangwantawa mace game da yin azumin a wasu wurare ko kuma ace awasu lokuta, wannan saboda kasancewar mace mai rauni ta fanin shari'a da hankali,

Idan watan ramadan ya tsaya to ya wajaba akan ko wanne musulmi da musulma, baligai, kuma masu lafiya, mazauna gida su yi azumi, ma'ana su kame bakinsu daga ci ko sha ko saduwar aure daga fudowar alfijir har zuwa faduwar rana, wanda kuma ya kasance mara lafiya ko yazamo matafiyi acikin kwanakin azumin ramadan, to ya halata agare shi da ya sha azumin sa'annnan ya rama adadin kwanakin da ya sha acikin kwanakin da bana ramadanba.

Allah (SWT) yace: "Wanda ya riski wata dag a cikin ku, to sai ya azumce shi, wanda kuma ya zamo maras lafiya ko matafiyi, to sai ya rama a kwanaki na gaba..." (bakara aya ta 185).

Don haka duk wanda watan Ramadan ya riske shi amma ya tsufa tukuf, ko kuma mara lafiya dake a kwance, da ba'a sa ran zai warke daga rashin lafiyar, mace ko namiji, to ko wanne daga cikin wadannan zai sha azumin, amma sai ya ciyar da miskini daya rabin sa'i, ma'ana mudu biyu na galibin abincin kasar, amaimakon ko wace rana, wacce ya sha azumi acikin ta. kamar yadda Allah maigirma da daukaka ya bayyana cikin suratul bakara aya ta 184.

To anan mace ma shari'a ta bata damar shan azumi saboda wadansu uzururuka wadanda ke faruwa agareta wadanda basa faruwa ga da namiji, wadannan uzururruka sune kamar haka:-

1. JININ HAILA DA JINI BIKI:- 
Ya haramta ga mace mai jinin biki ko na haila tayi azumi, amma kuma wajibi ne ta rama azumin awasu kwanaki da ba na ramadana ba, sabanin salloli su baza ta rama su ba.
Saboda Nana A'isha (RA) tace:- "Mun kasan ce ana umurtar mu da rama azumi amma ba'a umurtar mu da mu rama salla. Awata ruwayar ta imam muslim yace, "Mu'azatu tace na tambayi Nana A'isha nace saboda me mai haila zata rama azumi amma bazata rama sallah ba, sai tace:- ke 'yar (khawarijawa ce) sai nace ni ba ita ba ce nadai tambaya ne kawai, sai tace dani hakan na samun mu, sai aka umurce mu da mu rama azumi, amma ba'a umurce mu da mu rama salla ba, kuma ta kara da cewar wadannan al'amura ne da mutum yake tsayawa inda aka tsai da shi, ba ra'ayi ake bi ba a’a nassi ake bi. idan kuma mace taga farar kassa, wato wani ruwa da mahaifa take fitarwa bayan karewar jinin haila, wacce mace ke gane samun tsarkinta idan ta gan ta, to sai ta daura  niyya don daukan azumi. idan kuwa bata da wata takamaimiyar hanyar samun tsarki sai tayi kunzugu da Auduga ta gargajiya ko 'yar kanti, ko dai wani abu makamancinta kamar tolet paper, idan ta cirota da ganta tsaf babu jini ta tsarkaka kenan, to sai ta dauki azumi, amma kuma idan bayan ta dauki azumi sai jinin ya dawo mata a wannan ranar, to sai ta sha azumin, amma idan bata sha ba sai jinin ya dauke kafin magariba, to azuminta ya ingan ta. sa'annan matar da taji alamar fitowar jinin haila amma sai bai fito ba, sai bayan magariba to ita ma azumin ta yayi.
Matar da take haila sai jinin ta ya dauke tun dare sai tayi niyar yin azumi, kuma ta kasance bata yi wanka ba har alfijir ya keto to azumin ta ya ingan ta, bisa mazhabar daukacin malamai.
matar da tasan cewar gobe ne jini zai zo mata, amma sai ta tashi da azumi to ba zata ci abinci ba har sai idan jinin ya zo mata, sannan sai ta sha azumin, idan kuma bai zo mataba sai taci gaba da azuminta.
Mai biki idan ta samu tsarki kafin kwanaki Arba'in da haihuwar ta, to sai tayi wanka tayi niyyar azumi, amma idan jinin ya haura kwana Arba'in bai dauke ba to sai ta dauki jinin a matsyin jinin istihada (wato jinin cuta) sai dai kuma idan jinin ya yi dai dai da lokacin al'adarta wadda take yi duk wata, to wannan kam sai ta dauke shi amatsayin jinin haila.

2. Mace mai ciki da mai shayarwa:- Itama mace mai ciki ko mai shayarwa idan har yin azumi gareta zai cuce ta, ko ya cuce jaririn ta, ko kuma duka su biyun zasu cutu, to ita ma anyi mata rangwame akan ta sha azumi a cikin halin cikin ko shayarwar.
Amma kuma idan yin azumin zai cutar da jaririn ta ne kawai ban da ita, to zata rama azumin kuma ta ciyar da miskini daya maimakon azumin da duk ta sha aduk lokacin da tazo ramawa, amma idan yin azumin zai cutar da ita ne ita kadai to zata rama azumin kawai banda ciyarwa.Top of Form Domin Ayar da ke yin bayani akan wanda ke iya yin azumi amma da kyar to lallai akwai mace mai ciki da mai shayarwa idan suka jiwa kansu ko jaririn su tsoron cutuwa.
Don haka zance mafi rinjaye anan shine anyiwa mace mai ciki da mai shayarwa kiyasin marar lafiya don haka ya halatta da su sha azumin kuma ba su da kaffara sai dai ramuwa, ya Alla suna jiwa kan su tsoro ko suna jiwa 'ya'yan su tsoro, hujjar wannan itace ruwayar Imamu Tirmizi yace: Annabi (SAW) yace: Allah madaukakin sarki ya daukewa matafiyi wani yanki na azumi (wanda ya sha alokacin tafiyar sa) da wani yanki na sallah (yana nufin yin kasaru) kuma ya daukawa mace mai ciki, da mai shayarwa yin azumi.

3. Jini rashin lafiya:- ko kuma jinin ISTIHADHA macen da jini yake zuwar mata bana haila ba, azumi wajibi ne akan ta, bai halatta ta sha azumi saboda wannan jinin domin shi jinin rashin lafiya ne kamar zuwan kumallo ne ko fitar jini saboda rauni, ko fitar ruwan kurji, duk wadannan abubuwa ne wadanda basu da lokaci kayadadde na zuwan su, balantana ace mace tabar azumi domin su, ma'ana zuwan su ba zai hana mata yin azumi ba. 4. Matar aure:- Bai Halata ga Macar aure tayi Azumin Nafila ba, alhali mijin ta na gida sai da izinin sa ko idan baya gari ya yi tafiya, amma kuma ban da na ramadan, macen da azumi ya wajaba akan ta idan ta dauki azumin ramadan sai mijinta ya tara da ita da rana alhali tana dauke da azumin ramadan, kuma bisa yardarta, to dukkan su zasu yi ramuwa da kaffara, amma idan tilasta mata ya yi, to tayi iyakar kokarin ta na hana shi, amma bata yi nasarar hana shi ba, to ita babu kaffara a kanta sai dai ta rama azumi. Amma idan mace tana barci acikin watan ramadan sai mijinta ya tara da ita, to malamai sunce ita ma babu kafara akan ta sai dai ta rama azumi.

Anaso ga mace budurwa ko wacce mijinta ya yi mata izinin yin Azumin da ta rika yawan yin azumin nafila, ko yin Azumin mustahabbi (wato abin da aka so) da kuma yin azumin a ranakun litinin da Alhamis, da kwanaki shida na watan shawal, (wato Sittu Shawwal) da kwanaki goman farko na zulhijja, (Wato Ashara Zulhijja) da azumtar ranar Arafat da ranar Tasu'a da Ashura, sai dai kuma bai kamata ba gareta da tayi azumin nafila ba, alhali ana binta ramuwar wani azumin, har sai ta rama azumin da ake bin ta. kuma ya kamata ga duk matar da ta san cewa mijin ta baya iya danne sha'war sa a duk lokacin da dama ta samu, to ta nisanci mijin ta acikin azumi, kuma ta daina yin ado ko kwalliya a cikin watan azumi.

Akarshe malamai sun ce wajibe ne akan mace ta ramuwa azumin da ake binta kafin kamawar wani azumin, sai dai idan da wani uzuri mai girma, amma idan bata rama ba har wani azumin ya kama, ba tare da wani uzuri ba, to duk yayin da tazo rama wa, bayan ta rama sai ta ciyar da miskini daya. Kamamalawa Abin da akeso agare ki ya ke 'yar'uwa Musulma, idan kina Jinin haila to ki zauna bisa al'adarki tayin jini a duk wata, ki yarda da abinda Allah (SWT) ya hukunta agareki, kada kiyi kokarin shan wani abu da zai hana jinin fitowa, ki karbi abin da Allah ya yarje miki, na shan azumin akwanakin haila da yin ramuwar su bayan salla, domin kuwa haka matan Annabi (SAW) iyayen muminnai, da matan salihan bayin Allah, suka hakura.Amma idan kika ki, kika sha wani magani domin hana fitar jinin haila a watan azumi, jinin kuwa ya dauke kika samu tsarki kika cika azumin ki cif cif, batare da kin sha ko daya ba, to babu kommai amma baki yi koyi da iyayen muminai ba, kuma baki samu ladan yin koyi da salihan bayi ba.

Wannan shine dan abi da ya sawwaka game da hukumcin da shari'a ta dorawa mace game da azumi, da fatan zamu amfana, abin da akji na daidai daga Allah ne na kuskure kuma daga gareni ne, ina sauraron gyara,

Akulu kauli hadha wa astagfilullaha li wa lakum Wassalamu alaikum warahamatullah.

No comments:

Post a Comment