Tuesday, 17 June 2014

Riba Da Illolinta A Musulunci

Riba Da Illolinta A Musulunci

Littafin Da yake Tsoratarwa Game da Masu mu’amala da Riba, da Hatsarin dake cikinta

 

 

 

 

 

 

Wallafar

 

Comrade Auwal Zakari Ayagi

(Barden Ayagi)

2025

Haqqin Mallaka (M): Auwal Zakari Ayagi (Barden Ayagi)

Lambar Waya:      07038775781

Bugu Na Xaya      2025/1446

 

 

 

 

 

 

 

 

TSARAWA DA BUGAWA

Al-Azmiyya Islamic Foundation: No. 313 Al’Mustapha House Kadawa Western Bypass AL’EEMAAN Medicine Store Building, Adjacent to Gwarzo Road Kano.

E-mail: auwalzakari@gmail.com

www.sautulazimiyya.blogspot.co.uk/

GSM:  07038775781, 08023615685


Sadaukarwa

Na sadaukar da wannan Littafi ga Mahaifana Marigayi Alhaji Zakari Muhammad Usman Ayagi (Allah ya gafarta masa) da Mahaifiyata Hajiya Rakiya Usaini Lawan (Inna) Allah ya qara mata Lafiya, Amin.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Godiya

Da sunan Allah mai yawan Rahama Mai Jin qai, Tsira da Aminci su qara tabbata ga shugaban halitta Annabi Muhammad Tsira da Aminci su qara tabbata a gareshi.

Bayan haka ina godiya ga Allah Subhanahu wata’ala da ya bani ikon rubuta wannan qaramin littafi mai Suna: RUBA DA ILLOLINTA A MUSULUNCI.

Godiya mai tarin yawa ga Malamaina, da Abokaina Almajirai bisa ga yanda suka bani kwarin gwiwa wajen ganin na wallafala wannan littafi.

Daga qarshe nake mai qara Addu’a ga dukkan ‘Yan’uwa da suka bada gudunmawa wajen kammaluwar wannan littafi, Allah ya sakawa kowa da Alhairi Ameen.

Auwal Zakari Muhammad Ayagi

 (Barden Ayagi)

5 ga Zulhijja 1445= 1/6/2025


 

Ta’aliqi

Da sunan Allah mai rahama da jinqai. Salati da taslimi ga fiyayyen halitta salallahu alaihi wasallam.

Batan haka, na ke tofa ‘yan kalmomi game da wannan littafi, wanda na nazarce shi tun daga gabatarwa izuwa kammalawa, inda ya qunshi babuka guda uku, da nuquxoxi ashirin da biyu cikin ayoyi da Hadisai da maganganun malamai masana duk cikin bayanin ita riba da kuma illolinta, wanda xan uwa Com. Malam Auwal Zakariyya Ayagi/Kabuga ya wallafa, Allah ya saka masa da alkhairi. Kalmomi na suna ne:

·        Babu shakka mawallafin ya fito mana da illolin riba fai-da-fai tarwai abun da ya rage mana shi ne mu karanta wannan littafi kuma mu yi aiki da abin da ke ciki gwargwadon iko.

·        Wannan littafi ne da zai yi mutuqar amfani kuma littafi ne da ya zo a lokacin sa, wato wannan zamanin da mu ke ciki na yaki halal yaki haram, lokaci na a yi kuxi dare xaya, inda da yawan mu ke mance faxin Allah (يا أيها الذين آمنوا عليهكم أنفسكم).

·        Littafi ne da ya kamaci a ce kowane xan kasuwa ya mallake shi don ya samu madubin da zai dinga dubawa yana kaucewa abin da ake kira Riba.

·        Duk mai neman albarka cikin kasuwanci ko wata sana’a kuma yake fatan samun dacewar Allah duniya da lahira to ga mafita nan a fanni gujewa riba.

Allah ya saka da alkhairi ya yawaita mana ire-iren wannan mawallafi, albarka Shugaba (S.A.W).

 

Wassalamu Alaikum

Mallam Muhammad Shafi’u Almaliky

Qofar Kabuga

25/06/2025

 

 

 


 

ABUBUWAN DA KE CIKI

Sadaukarwa…………………..…………………. 3

Godoiya…………………………………………. 4

Ta’aliqi………………………………………….. 5

Abubuwan da ke ciki……………………………..7

Gabatarwa …………………………………........ 8

Babi Na Farko:

Cin Riba tanadin yaki ne da Allah da Manzosa….9

Menene Riba? ………………………………..... 10

Rabe Rabeb Riba ……………………………… 11

Hukumcin Riba ……………………………….. 12

Uqubar Masu cin Riba ………………………… 14

Hikimar Haramta Riba ………………………… 21

Babi Na Biyu:

Hukuncin Imam Mālik Game da Riba …………25

Babi Na Uku:

Fatawowin Malaman Musulunci Game da Riba..31

Fatawowin wasu daga Malaman Nigeria ……... 33

Riba A Bankuna……………………………….. 40

Babi Na Huxu:

Wasu daga Nau’o’in kasuwanci Halatttatu……….42

Kammalawa……………………………………. 47

Taqaitawa……………………………………….48

Shawarwari……………………….................................................... …………… 49

Gabatarwa

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin-qai, tsira da Aminci su qara tabbata ga shugaban halitta Annabin Rahama Salallahu Alihi Wasallam.

Bayan haka duba ga yanayin da muke a ciki a halin yanzu na kasancewa tsindum cikin Riba, a kasuwanci, a mu’amalar yau da kullum kamar a wajen bada Bashi, da Bankuna da makamantansu.

Don haka naga dacewar in rubuta wannan littafi dana tattaro daga litattafan Malamai, da Fatawoyin su, da karatuttukansu don daxa fadakarwa, da wayar da kan Al’umma game da Riba, domin wasu da dama suna ma’amala da ita bisa rashin sani ne.

Dafatan Allah yasa wannan littafi ya zamo sila na sanin Menene Riba, da qoqarin ganin an kauce mata, abin da aka gani kuma na kurakurai a ciki dafatan Allah ya yafe mana, wanda kuma akayi daidai Allah ya karva mana yasa a mizani.

Wassalamu Alaikum

Auwal Zakari Muhammad Ayagi

 (Barden Ayagi)

5 ga Zulhijja 1445= 1/6/2025

Kashi Na Farko

(1)

Cin Ruba Tanadin Yaqi Ne Da Allah Da Manzosa

Ubangiji mai girma da daukaka yana fada cikin Alkur’ani mai girma:

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَذَرُوا۟ مَا بَقِىَ مِنَ ٱلرِّبَوٰٓا۟ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِين (278)َ

فَإِن لَّمْ تَفْعَلُوا۟ فَأْذَنُوا۟ بِحَرْبٍ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَإِن تُبْتُمْ فَلَكُمْ رُءُوسُ أَمْوَٰلِكُمْ لَا تَظْلِمُونَ وَلَا تُظْلَمُون (279)

Ma’ana

 “Yaku Waxanda Kukayi Imani Kuji Tsoron Allah ku bar Abin da yayi saura daga Riba In kun kasance Mumunai[1].

In har baku Aikata ba (Barin cin Ribar) Ina muku Izini da Yaki da Allah da ManzonSa, In kuka Tuba asalin Dukiyarku na gareka baku yi Zalunci ba ba’a Zalince kuba”[2].  

Wannan aya tana tsoratar damu game da Mu’amala da Riba, inda Allah da kansa yake cewa; duk wanda bai bar cin Riba ba, ya na masa izinin yin yaqi dashi da AnnabinSa , kamar yadda yazo a labari cewa: Ranar Alqiyama Ubangiji zai bawa mai cin Riba makami, ya umarce shi da ya yi yaqi da shi, Allah ya kiyaye mu, Allah yace; amma in kuka tuba to sai ku xebi asalin Dukiyarku (Jarinku) ragowar kuxin sai ku rabar, in kukai haka bakuyi zalunci ba kuma ba’a zalunce ku ba.

Menene Riba a Musulunci?

Riba: a larabci na nufin "ƙari" ko "yawaita abu fiye da yadda ya dace", amma a cikin shari’ar Musulunci, Riba tana nufin: "Kowane irin ƙari da aka samu a cikin wata mu'amala, wanda ba a halatta ba, musamman a cikin bashin kudi ko cinikin kayayyaki masu nauin Riba."

Rabe-Raben Riba

Riba ta rabu gida biyu a Musulunci

1.     Riba al-Nasīah

2.     Riba al-Fal

1.     Ribal-Nasīah: Tana nufin: "Ƙarin da ake karɓa a kan bashi saboda jinkirin biya." Wato, mutum ya ba wani bashi (misali: kuɗi ko kaya), amma ya sa ƙarin adadi a cikin bashin idan har lokacin biyan ya wuce.

 Ma’anar Riba al-Nasīah daga Larabci:

•        "Nasīah" na nufin "jinkiri" ko "xage lokaci".

•        Don haka, Riba al-Nasīah ita ce ribar da ke aukuwa, sakamakon xage lokacin biyan bashi tare da ƙarin adadi na abin da aka bayar.

Misali: Ka ba wani bashin (N10,000) zai biya cikin wata ɗaya, amma sai ka ce: "Idan ka jinkirta wato in lokaci yayi baka biya ba, to za ka ƙara (N1,000)." Wannan shi ne mafi shahara kuma mafi tsanani daga cikin Riba. Shi ne Allah da Manzonsa suka ayyana yaƙi da duk wanda ya ke aikata shi a cikin Suratul Baqarah 2: Aya ta 279.

Rabe-Raben Ribal-Nasīah

Ribal-Nasīah: Ribar jinkiri ta rabu kashi biyu Kamar haka:

i)      Riba Mai Ninkawa

ii)   Riba Mai daxuwa don dogon lokaci.

i.                Riba mai ninkawa: Ita ce ake cewa Rubar Jahiliyyah, wannan ita ce ubangiji ya haramtata da nassin Alkur’ani mai girma, inda yake cewa:

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَأْكُلُوا۟ ٱلرِّبَوٰٓا۟ أَضْعَٰفًا مُّضَٰعَفَةً وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُون  (130)

Ma’ana:

Yaku Wadanda Kukayi Imani Kada Kuci Riba Ninkin-Baninkin, Kuji Tsoron Allah ko kwa Rabauta[3].

Yanda wannan Riba take, Shi ne a baiwa mutum bashi zuwa wani lokaci abin ayyanawa, idan lokacin ya yi bai samu damar biya ba, sai ace dashi ko dai ya biya ko kuma a qara masa kuxin, sannan kuma a qara masa lokacin biyan, haka za’a riqa qara masa kuxin, ana kuma qara masa lokacin biyan, har kuxin su ninninka kansu.

Misali kan wannan shine, kamar bashin da qasashe suke ciyowa bisa yarje-jeniyar zasu biya zuwa Shekarun da aka ayyana, idan lokacin yayi basu biya ba, sai kuxin suyi ta karuwa gwargwadon tsawon lokacin da qasar tayi bata biya ba, sai aga kuxin sun ninka kansu ninkin-ba-ninkin, to wannan itace Ribar da wannan aya take Magana akai.

ii.             Ruba Mai Daxuwa Don Dogon Lokaci; Wannan ita ce Rubar da ake bada bashi da qari don bashin zai xauki dogon lokaci, misali: abada bashin Naira Dubu Goma (N10,000) amma za’a biya Naira dubu Goma sha xaya (N11,000) a tsawon kwanaki ishirin ko makamancin haka.

Ko sayen wani abu da qari kan asalin kuxin sa don xaukan dogon lokaci, misali sayen Sha’ir ko Dabino ko wake, ko masara, ko gero da makamantansu, amma da qarin kuxi in zai kai wani lokaci, misali: ana sayar da Masara Naira Dubu xaya da xari biyar (N1,500) a ko wacce kasuwa, sai abada ita bashi akan Naira dubu xaya da xari shida (N1,600) a watanni biyu, ko biya biyu ga ma’aikata, da makamantansu, to wannan qarin Riba ne.

2.     Ribal-Fal: Wannan shi ne cinikin abubuwa masu kama (irin su Zinariya da Zinariya, Alkama da Alkama, Naira da Naira), amma ɗaya yafi ɗaya nauyi ko ƙima ko yawa.

Misali: A musanya mudu xaya na Alkama da mudu biyu na Alkama, wannan Riba ce a cewar hadisin Manzon Allah .

Zinariya da zinariya, Azurfa da Azurfa, Alkama da Alkama, sha'ir da sha'ir, Tamar da Tamar, Gishiri da Gishiri, sai dai dai-dai da dai-dai, kuma hannu-da-hannu. Duk wanda ya ƙara ko aka ƙara masa, to ya ci riba. [4]

Wato ita Ribal-Fadl tana nufin cinikin Jinsi xaya kamar (Gero da Gero, Dawa da Dawa, Naira da Naira da dai sauransu) amma tare da daxi akan cinikin, kamar asayi Gero kwano xaya, amma sai ace sai an daxa rabin kwano akan kwano dayan, ko sayan sababbin kuxi misali na Naira Dubu biyar amma ace sai ka daxa Naira Dubu xaya akai, da sauransu.

Har ila yau Ribal-Fal na nufin: Ƙarin da ake samu yayin musayar kaya guda biyu iri ɗaya, amma ba daidai suke ba, ko a nauyi ko a ƙima."

Fassarar Ma’anarta:

•       “Fal” a larabci na nufin Qari ko Fifiko.

•       Don haka, Ribal-Fal tana nufin ƙari ko fifiko a cikin musayar kayayyaki waxanda suke iri xaya da juna.

 Misali cikin Sauƙi shine:

§  Idan mutum ya musanya mudu xaya na Alkama da mudu biyu na Alkama, wannan Ribal-Fal ce. (Kamar yanda muka kawao a baya)

§  Ko ya musanya Zinariya mai nauyin Gram 10 da Zinariysa irinta mai nauyin Gram 12, wannan ma Ribal-Fal ce.

Koda kuwa suma kayayyaki iri ɗaya ne, idan ƙimar su ko nauyin su bai daidaita ba, kuma musayar bata yi kai-da-kai ba, to haramun ne.

 Hadisin Manzon Allah :

Zinariya da zinariya, Azurfa da Azurfa, Alkama da Alkama, sha'ir da sha'ir, Tamar da Tamar, Gishiri da Gishiri, sai dai dai-dai da dai-dai, kuma hannu-da-hannu. Duk wanda ya ƙara ko aka ƙara masa, to ya ci riba [5].

Sharuɗɗan Gujewa Riba al-Fal:

1.     Kaya iri ɗaya?

Dole suyi daidai a ƙima (a nauyi ko a yawa).

Dole musayar ta zama kai-da-kai.

 

2.     Kaya iri daban?

Za a iya musanya da ƙari, amma dole ta zama kai-da-kai.

Muhimmancin Saninta:

Riba al-Fal tana faruwa a cikin cinikayya, ba bashin kuɗi kawai ba. Don haka ya ke da matuƙar muhimmanci ga dukkan yan kasuwa da masu canjin kuxaxe ko dillalai da su kula su hankalta da wannan Riba, don su guje mata.

Dalilin Haramcinta:

      Kare mutane daga cuta da zalunci.

      Hana makircin ciniki da ya ke haifar da rashin daidaito.

      Koyar da adalci da gaskiya a mu'amala.

Hukuncin Riba

Ita dai Riba haramun ce, sabo da fadin Ubangiji maxaukakin sarki cikin suratul Bakara Ayata 275 cewa:

وَأَحَلَّ ٱللَّهُ ٱلْبَيْعَ وَحَرَّمَ ٱلرِّبَو

Ma’ana:

Allah Ya Halatta Ciniki Ya Haramta Ruba” [6]

Da fadinsa maxaukakin Sarki cikin Suratu Ali Imram Ayata ta 130:

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَأْكُلُوا۟ ٱلرِّبَوٰٓا۟ أَضْعَٰفًا مُّضَٰعَفَةً  (130)

 “Yaku Wadanda Kukayi Imani Kada Kuci Ruba Ninkin-Baninkin. [7]

Ga kuma fadin Annabi Alaihissalam cewa:

Allah ya tsinewa mai cin Riba, da wakili akan Riba, da masu shaida akan Riba, da marubucin Riba” [8] (As-habu Sinan)

Har ila yau da faxin sa Alaihissalam , cewa:

“Sisi na Riba da Mutum yake cin sa yana sani, shi yafi tsananin Azaba da Zina Talatin da mutum zaiyi. [9]

Da fadin Annabi Alaihissalam cewa:

“Riba kofa Saba’in da Uku ce mafi saukinsu shine mutum ya auri mahaifiyarsa. [10]

Da fadin Annabi Alaihissalam cewa:

Ku nisanci abubuwa bakwai mafiya Ukuba, sai aka ce; Ya Rasulullahi Menene? Sai ya ce: Yin Tarayya da Allah, da Sihiri, da Kashe Ran da Allah ya Haramta, da cin Riba, da cin dukiyar Marayu, da juya baya (Guduwa) Ranar yaki, da yin kazafi ga Mumina Katangaggiya” [11]

Ukubar Masu Cin Riba

Ubangiji madaukakin sarki yafaxa a cikin Suratul Bakara Ayata 275:

ٱلَّذِينَ يَأْكُلُونَ ٱلرِّبَوٰا۟ لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ ٱلَّذِى يَتَخَبَّطُهُ ٱلشَّيْطَٰنُ مِنَ ٱلْمَسِّ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوٓا۟ إِنَّمَا ٱلْبَيْعُ مِثْلُ ٱلرِّبَوٰا۟ ....

Wadannan da suke cin Riba basa tashi (yayin tashi daga Qaburbura) sai kamar misalin waxanda shaixanu suke bubbugewa (tashin su kamar na masu fyar-fyadiya) da shafa (ta Aljanu) waxannan don cewa su suna cewa shi ciniki kamar Riba ne”[12]

Idan Ubangiji ya tashi mutane a ranar Alqiyama zasu fita suna masu gaggawa, sai masu cin Riba su zasu tashi, suna faduwa kamar masu fyarfyadiya, kasan cewar su ya yin da suke cin Riba, Ubangiji ya na tara Ribar a cukkunansu har ta rinjaye su ranar Alqiyama, duk ya yin da suka tashi sai su faxi, suna son suyi gaggawa kamar sauran mutane amma baza su iya ba.

 

 

 

Hadisan Manzon Allah Da Suke Hani kan Riba

1. Hadisi daga Sahih Muslim

“Annabi ya ce: **Duk wanda ya ci riba, to shi ya yi yaƙi da Allah da Manzonsa.’” [13]

2. Hadisi daga Sahih Bukhari

“Manzon Allah ya ce: ’Riba tana da yawa kamar yadda na gani a cikin abincin.’ [14]

3. Hadisi daga Sahih Muslim

“Duk mai cin riba zai tashi a ranar Qiyama kamar wanda yake mahaukaci.” [15]

4. Hadisi daga Sahih Bukhari

“Annabi ya ce: **Wanda ya ci riba sau ɗaya, to Allah ba zai karɓi sadakarsa ba har sai ya daina riba.’”[16]

5. Hadisi daga Sahih Muslim

“Riba ta fi zina yawa.” [17]

6. Hadisi daga Sunan Abu Dawud

“Annabi ya ce: Riba tana yin laifi iri ɗaya a idanun Allah.’” [18]

7. Hadisi daga Sunan Tirmidhi

“Riba tana hallaka mai yawan ta kamar yadda wuta ke hallaka itace.” [19]

8. Hadisi daga Sahih Muslim

“Annabi ya haramta riba, kuma duk wanda ya ci shi, to shi ya yi yaƙi da Allah da Manzonsa. [20]

9. Hadisi daga Sahih Bukhari

“Wanda ya ci riba a lokacin da aka sani, to ya ci riba, kuma idan ya muta, yana ɗauke da zunubi har abada.[21]

10. Hadisi daga Sunan Abu Dawud

“Allah ya haramta riba, mai cin riba ba zai shiga Aljanna ba har sai ya daina.” [22]

11. "Ku guji riba, koda da ƙanƙantaccen kaso ne."[23]

12. An karvo Hadisi daga Jabir (RA): "Manzon Allah (SAW) ya la’anci mai cin riba, da wanda yake ba da ita, da wanda yake rubuta ta, da kuma shaidunta. Ya ce: dukkansu dai-da-dai suke.” [24]

13. "Riba tana da nau’i saba’in (70) ko fiye, mafi sauƙinta kamar namijin da ya yi zina da mahaifiyarsa." [25]

Waxannan Ayoyi da Hadisai suna nuna girman laifin Riba, da irin Azabar da zata riski masu mu’amala da ita, da kuma mahimmancin barinta.

Hikimar Haramta Riba

Haramcin mu’amala da Riba na xauke da hikima kamar sauran ibadu, an haramta ta ne sabo da jarraba imanin bawa ga biyayya a cikin aikatawar ko hani, sannan yana daga cikin haramcin Riba:

1.     Kiyaye wa a bisa dukiyar Musulmi, don kada yaci dukiya yana mai varna.

2.     Fiskantowar musulmi bisa yaxuwar dukiyar sa cikin hali maxaukaki ba tare da cutar da sauran musulmi ba, a cikin sana’arsa ta Moma ko Kasuwancin ko aikin Gwamnati da sauransu.

3.     Toshe duk wasu hamyoyi masu saka qiyayya ga musulmi, domin qiyayya tsakanin musulmi tana wahalshesu, kuma abar qi ce kuma abar hani ce.

4.     Tseratar da musulmi bisa ga abin da zai kaishi ga halaka, don cin Riba zalunci ne kuma halaka ne.

5.     Bude kofofin biyayya ga musulmi don suyi guzuri sabo da lahira.

Ataqaice: An Haramta Riba ne Domin:

1.  Tana cutar da talaka – Mai bashi ya na cin Riba daga mai buƙata.

2.  Tana haifar da rashin daidaito da zalunci.

3.  Tana hana alheri da albarka.

4.  Tana tayar da husuma tsakanin mutane.

 

 

 

 

 

 

Babi Na Biyu

(2)

Hukuncin Imamu Mālik (RA) Game da Riba

Imam Mālik bn Anas (Allah ya ji ƙansa), wanda shi ne shugaban Mazahabar Malikiyya, ɗaya daga cikin manyan mazahabobin Musulunci guda huɗu, ya rayu daga shekara ta 93 bayan Hijira zuwa 179H, Imamu Mālik yana ɗaya daga cikin manyan malaman hadisi da fikihu da suka yi tasiri a tarihi. An haife shi a Madinah a shekara ta 93 bayan Hijra, cikin gida mai bin addini da ilimi. Mahaifinsa Anas da kakanninsa sun kasance mutane masu tsantseni da kula da ilimi.

Tun yana ƙarami ya zauna cikin Masallacin Manzon Allah (SAW), inda ya koyi hadisi daga manyan malamai fiye da 900, ciki har da Nafi’u (bawan ɗan Umar), da Ibn Shihab az-Zuhri, da Yahyā ibn Saīd al-Ansari, da Rabiatu ar-Rayi.

A cikin ilimin Hadisi shi ne marubucin Al-Muwaṭṭa, ɗaya daga mafi inganci da tsofaffin littattafan hadisi, wanda ya shahara saboda tsantsar zaɓen hadisan da ya tattara.

Imamu Mālik ya yi rayuwa cikin gaskiya da tsoro ga Allah. Ba ya bayar da fatawa sai ya tabbatar da abin da ya fito daga Alƙur’ani, Sunnah, ko abin da Ahlul Madinah suka aikata. Ya shahara da cewa: “Na ce ban sani ba fiye da yadda na ce na sani.”

Ya rasu a shekara ta 179H a Madinah, aka binne shi a Jannatul Baqi’a.

Imam Malik yana daga cikin malamai masu tsauraran ra’ayi akan Riba, musamman Riba a cikin mu'amala da ciniki (Riba al-buyu'u), wanda aka fi samun sa a harkar kasuwanci da musayar kaya.

Hukuncinsa

1.     Riba Haramtacciya ce gaba ɗaya

Imam Mālik ya na ganin duk wani nau'in Riba wato Riba Al-Fadhl da Riba Al-Nasia, haramun ne kuma babban zunubi ne. Ya jingina da nassosin Qur’ani da Hadisi kamar yadda na kawo a baya.

2.     Musayar Kayayyaki Masu nau’in Riba

Imam Mālik ya karɓi cewa musayar abubuwan da suka yi kama (irin su zinari da zinari, ko Alkama da Alkama) dole ne ta kasance:

•   Kai-da-kai wato (Hannu-da-Hannu) wato (yadan –bi-yadan)

•   Adalci cikin nauyi da kuma ƙima

Idan aka savawa hakan, to an shiga Riba, kuma haramun ne.

3.     Duk wata hanya da aka bi don yaudarar tsarin Allah ta hanyar Riba, shi ma haramun ne

Imam Mālik ya yi gargadi daga duk wata hanya da mutane ke amfani da ita don su guje wa hukuncin Riba ta hanyar "makaranta" da "dabara" ya na cewa abin da aka yi da nufin Riba, to haramun ne, koda kuwa ta hanyar dabara ce.

4.     Fatwarsa akan mu’amalar da take ƙunshe da riba a ɓoye (Riba Al-Khafiyyah)

Imam Mālik ya na da tsaurin raayi kan muamaloli da a zahiri kamar ba Riba ba ne, amma a gaskiya Riba ce cikin dabara. Irin waɗannan mu'amaloli ya haramta su bisa ƙaidar:

“Saddan li-dh-dhara’i” – wato toshe hanyar da ke kai wa ga haram.

Misalai daga Al-Muwaxxa ta Imam Mālik:

A cikin "Al-Muwaxxa", Imam Mālik ya kawo ruwayoyi da fatawowi daga Sahabbai da Tabiai da suka haramta riba da tsananin nuni da illarta a cikin al'umma.

Misali:

“Duk wanda ya karɓi Riba ko ya ba da ita ko ya rubuta ta ko ya kasance shaida a kanta, ya shiga cikin haramun." [26]

Hukuncinsa a Taqaice:

•   Riba haramun ce ko da ƙarama ce.

•   Ba a halatta ciniki da ya ƙunshi riba ko ɓoyayyen riba.

•   Hanyoyin dabara don kaucewa riba haramun ne.

•   Zina da mahaifiya ya fi sauƙi fiye da riba, idan aka dubi hadisin da Imam Mālik ya karɓa.

Wasu Bayanai Daga Littafin Al-Muwaxxa ta Imam Mālik Da Suka Shafi Riba:

1. Riba a zamanin Jahiliyya

Imam Mālik ya ruwaito daga Zayd ibn Aslam cewa:

"Riba a zamanin Jahiliyya ita ce: mutum yana ba wani bashi na wani lokaci. Idan lokacin ya cika, sai ya ce masa: 'Za ka biya ko ka ƙara mini?' Idan ya biya, sai ya karɓa; idan kuma bai biya ba, sai ya ƙara masa a cikin bashin kuma ya tsawaita masa lokaci."[27] Al-Muwaṭṭaʼ, Kitāb al-Buyuʻ

Wannan ya na nuna cewa Riba Al-Nasīʼa (ƙarin kuɗi saboda Jinkirin biyan bashi) an haramta ta a Musulunci.

 

2. Musayar Zinariya da Azurfa

Imam Mālik ya ruwaito daga Al-Qāsim Ibn Muammad cewa:

"Umar Ibn Al-Khaṭṭāb ya ce: 'Dīnār da Dīnār, Dirham da Dirham, Sa'a da Sa'a. Abin da za a karɓa daga baya ba za a sayar da shi da abin da ke hannu ba.” [28] Al-Muwaṭṭaʼ, Kitāb al-Buyuʻu

Wannan ya na nuni da cewa musayar abubuwa masu nau'in Riba (kamar Zinariya da Azurfa) dole ne su kasance kai-da-kai kuma daidai gwargwado.

3. Riba a cikin Ciniki

Imam Mālik ya ce: "Abin da ba mu yarda da shi ba, kuma babu sabani a tsakaninmu, shi ne: mutum ya ba wani bashi na wani lokaci, sannan mai bashi ya rage masa adadin bashin, amma ya karɓi kuɗin kafin lokacin. A gare mu, wannan kamar wanda ya jinkirta biyan bashinsa ne, sannan mai ba da bashin ya ƙara masa bashin. Wannan ba komai ba ne face Riba, babu shakka a ciki."[29]

Wannan yana nuna cewa duk wata dabara da ake amfani da ita don samun Riba ta hanyar ciniki ko bashi, haramun ce.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Babi Na Uku

(3)

Fatawowin Malaman Musulunci Game da Riba

Ga wasu daga cikin fitattun malamai da fatawarsu game da riba:

1. Sheikh Ibn Baz (Rahimahullah) – Saudiya

Fatawa: Riba haramun ce, babbar zunubi ce, kuma duk wata fa'ida ko ƙari da ake samu daga bashin kuɗi to riba ce.

Ya ce: "Babu bambanci tsakanin karamin riba da babban riba. Dukkan su haramun ne[30]."

2. Sheikh Muhammad Salih Al-Uthaymeen (Rahimahullah)

Fatawa: Ya bayyana cewa duk wata mu’amala da ke da ƙarin kudi bisa wani jinkiri ko lokaci, to wannan Riba ce. Ya kuma jaddada da cewa: "Ko da mutumin yana da niyyar taimako ne, muddin ya ce za a dawo da bashin da ƙari – to wannan haramun ne." Malamin yanuna cewa in har za’a bada bashi da sunan taimako. In har da qari aciki to wannan Haramunne.[31]

3. Sheikh Dr. Yusuf Al-Qaradawi (Rahimahullah)

Fatawa: Ya bayyana Riba a matsayin babbar hanyar da ke halakar da tattalin arzikin al’umma, kuma ya ce: "Riba ba wai kawai haramun ce bane, amma tana da illoli da dama ga al'umma, ana ƙara talauci, hana taimako, da karya jinkai[32]."

4. Malaman Azhar – Masar

Malaman jami'ar Azhar da majalisar fatawa ta Masar sun haɗu kan cewa Riba haramun ce – komai ƙanƙantarta. Sun ce: "Riba tana daga cikin abin da Qur’ani ya bayyana a fili cewa haramun ne, kuma wanda ya ci gaba da cin Riba bayan ya samu bayani, Allah zai yi masa yaƙi. [33]" (Duba: Suratul Baqara: 278-279)

 

5. Sheikh Ibrahim Inyass (RA) – Senegal

Fitaccen jagoran Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Inyass, yana da rubuce-rubuce da kalamai kan haramcin riba:

Ya ce: "Riba tana haifar da rugujewar arziki da lalata zamantakewa, kuma Musulmi ya wajaba ya kauce mata gaba ɗaya."

Ya ƙarfafa mutane su dogara ga halal, su yi kasuwanci da gaskiya, su guji cin amana da riba[34].

Fatawowin Wasu Daga Malaman Najeriya

1.   Sheikh Ja'afar Mahmud Adam (Rahimahullah)

A cikin karatuttukansa, Sheikh Ja'afar ya bayyana cewa duk wata mu'amala da ke da fa'ida ko ƙari akan bashin kuɗi – ko da sun canza sunanta, Riba ce.

Ya ce: "Bari mu sani cewa Riba ba sai mutum ya je banki bane. Idan ka bai wa mutum kuxi ya ce zai dawo da shi da ƙari wannan Riba ce."

Ya bayyana kuma a cikin wasu darussan cewa:

"Duk wani bashi da ƙari, Riba ce. Ko da mutum ya ce 'na baka dubu, ka dawo da dubu da ɗari' – wannan Riba ce."

Ya ƙara da cewa: "Riba tana da matuƙar haɗari a addinin Musulunci. Allah da Manzonsa sun yi wa mai cin riba tayin yaƙi. [35]"

Dalili: Suratul Baqarah, aya ta 278–279.

2. Sheikh Dahiru Usman Bauchi (Rahimahullah)

A cikin wa’azinsa, ya bayyana cewa:

"Riba tana daga cikin babbar haramun da take haddasa fushin Allah. Idan mutum yana da Riba a asusun sa – ya fitar da ita ba da niyyar lada ba, domin haramun ce."

Ya kara da cewa: "Cin Riba ko mu’amala da ita ba abun barin Musulmi ba ne. [36]"

 

3. Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara (Kano) – Jagoran Qadiriyya

A wata fassara da ya yi, ya bayyana cewa:

"Wajibi ne Musulmi ya tsarkake kasuwancinsa daga duk wata hanyar haram. Riba tana hana albarka kuma tana jawo halakar arziki."

Ya kuma ce: "Ma’aikata a bankunan Riba su nemi halal domin kada su shiga cikin la’anar Manzon Allah. [37]"

4. Sheikh Muhammad Sanusi Kerau (Kaduna) – Malamin Darikar Tijjaniyya

"Riba yana da ruɗi, amma mai cin riba yana haddasa halakar kansa da al’ummarsa. Yin kasuwanci cikin gaskiya da tausayi shi ne hanya mafi dacewa da Musulunci. [38]"

5. Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Gumi (Kaduna)

Ya bayyana cewa: "Riba a bankuna haramun ce, domin suna ba da kudi da ƙari ba tare da wata halal muamala ba. Wannan shine abin da aka haramta a Qurani."

Amma ya yi bayani: a wasu lokuta na matsananci (necessity) ana iya buɗe asusu na banki ko karɓar albashi ta banki, amma ba da riba ko karɓar riba haramun ne[39].

6. Sheikh Kabiru Gombe

"Riba na daga cikin laifuffuka masu girma. Kowa yana neman karin kudi, amma idan ya wuce hanya – ya shiga cikin riba – ya shiga cikin haddi."

Ya fadi cewa ko da aka sauya sunan mu'amala, misali a kira ta “service charge” ko “interest,” idan da ƙari ne akan bashi riba ce[40].

7. Sheikh Sani Yahaya Jingir (Jos)

"Ko da gwamnati ce ko kamfani ne ya ce zai ba da bashin da ribar kashi 5%, hakan haramun ne. Domin bai banbanta da abin da aka hana ba."

Ya ce, “Wanda ke karbar riba da wanda ke bayarwa da wanda ke rubutawa da wanda ke shaida – duka Allah ya la’anta su kamar yadda Hadisi ya nuna. [41]

Manyan Malamai da dama suna jaddada cewa:

•        Bankin da ke bayar da riba yana haramta duk wata fa’ida da Musulmi zai samu ta hakan.

•        Wanda ke da kuɗi a irin wannan banki, ya nemi hanyar halal don cirewa, ba tare da karɓar ribar ba.

Duk malamai – ko na Darika ne ko na Izala ko Salafiyya – sun amince da cewa Riba babbar haramun ce, kuma tana da illoli masu yawa a rayuwar Musulmi da al’umma gaba ɗaya. Wannan ya dogara da nassoshin Qur’ani da Hadisi, da kuma ijma’in malamai.

Ka'idodin Gabaɗaya na Malamai:

1.       Riba haramun ce da ƙarfi ba kawai makruh ba ce.

2.       Fa'ida akan bashi na kuɗi ko kayayyaki riba ce – ko da da yardar mai karɓar bashi ne.

3.       Babu bambanci tsakanin riba ta banki da riba ta mutane kai-tsaye.

4.       Riba ba za ta halatta ba saboda bukata – sai dai in akwai matsanancin hali (ƙarancin abinci ko rayuwa).

Riba a Bankuna

Riba a Bankuna (Interest a Turance), na nufin ƙarin kuɗi da ake bayarwa ko karɓa bisa wani lokaci da aka amince da shi akan kuɗin da aka ajiye ko aro.

Ga cikakken bayani:

1. Interest a matsayin Riba da Banki ke bayarwa:

Idan ka ajiye kuɗinka a banki (misali a asusun ajiya), bankin zai iya ba ka ƙarin kuɗi a kowane wata ko shekara bisa adadin da ka ajiye. Wannan ƙarin ana kiransa interest. Misali:

•        Ka ajiye 100,000

•        Banki ya ce zai ba ka 5% interest a shekara

•        Bayan shekara ɗaya, za ka samu 105,000 (ƙarin 5,000 ribar da banki ya ba ka)

2. Interest a matsayin Riba da Banki ke karɓa:

Idan ka ciwo bashi daga banki, bankin zai ce dole ka biya da ƙari akan kuɗin da ka aro. Wannan ƙarin shi ake kira interest. Misali:

•        Ka aro 100,000

•        Banki ya ce interest ɗin bashin ya kai 10%

•        Bayan shekara, dole ka biya 110,000 (wato asalin bashin da ƙarin 10,000)

A Taƙaice:

Ka ajiye kuɗi        Banki ya ba ka riba (interest)

Ka ciwo bashi       Kai ne za ka biya riba (interest)

A Mahangar Musulunci:

A cikin Musulunci, riba (interest) ana kallonta a matsayin haramun, saboda tana da nasaba da cin hanci da zalunci a ciniki. Wannan ya fito a cikin Alkur’ani da Hadisai da dama.

 

Babi Na Hudu

(4)

Wasu daga Nau’o’in kasuwanci Halatttatu

1. Muḍāraba

Ma’ana:
Mu
ḍāraba ita ce yarjejeniyar kasuwanci da ake yi tsakanin mai jari (rabbul-māl) da mai aiki (muḍārib), inda mai jari ya ba da kuɗi, mai aiki kuma ya yi kasuwanci da su, riba su raba bisa yarjejeniya.

Yadda take aiki:

·         Mai jari shi ne yake samar da kuɗi gaba ɗaya.

·         Mai aiki shi ne yake bibiyar kasuwanci, saye-da-sayarwa, ko zuba jari.

·         Idan an sami riba: a raba bisa kaso da aka yi yarjejeniya tun farko (misali 60% ga mai jari, 40% ga mai aiki).

·         Idan asara ta samu: mai jari ne ke ɗaukar asarar, mai aiki asarar tasa ce wahalar da ya yi ba ya karɓar komai.

Sharudda:
A fayyace kaso na riba tun farko.
Mai aiki ba shi da garanti akan riba.
Ba a haɗa kasuwar halal da haram.
A amince akan nau’in kasuwanci.

Dalilin halaccin Muḍāraba:
An yi ta tun zamanin Annabi SAW, shi kansa ya yi wa Khadija ciniki cikin irin wannan tsarin.

2. Murābaa

Ma’ana:
Murabaha ita ce saye-da-sayarwa da bayyana tsadar jari da riba ta halal da mai siyarwa ya amince ya kar
ɓa.

A tsarin bankin Islama, murabaha ita ce lokacin da:

·         Abokin ciniki ya nemi kaya,

·         Banki ko mai jari ya saya da kansa,

·         Sai ya sayar masa da tsadar da ya saya da ƙarin riba da aka yi yarjejeniya, kuma mafi yawanci a biya a hankali.

Misali:
Kana son siyan mota.
Banki ya saya da
3,000,000
Sai ya sayar maka da ita da
3,500,000 a biyan wata-wata.
An bayyana jari da
ƙarin riba (margin profit), ba laifi idan an bi tsari na sharia.

Sharudda:
Banki ya mallaki kayan kafin ya sayar.
A bayyana jari da ƙarin riba ba tare da ɓoye komai ba.
Biyan bashin ya kasance na halal ba tare da tara tara ba (late payment interest haram ne).

3. Mushāraka

Ma’ana:
Musharaka ce ha
ɗin gwiwa tsakanin mutane biyu ko fiye wajen:

·         zuba jari

·         aiki

·         raba riba

·         raba asara

Kowa yana da kaso a jari, kuma riba a raba bisa yarjejeniya, amma asara a raba bisa kaso na jari.

Nau’o’i:

1. Musharaka al-Aqd

Haɗin gwiwa na yau da kullum, kowa ya kawo jari ko baiwa da aiki.

2. Musharaka Mutanaqisa (Diminishing Musharaka)

Ana amfani da ita a ginin gida ko manyan ayyuka:

·         Kungiya ko banki su yi gini tare da mutum.

·         Ɗan lokaci-lokaci mutum yana biyan wani ɓangare har sai ya mallaki sabon ginin kafaɗa ɗaya.

Misali:
Ka kawo 40%, banki 60%.
Riba a raba bisa yarjejeniyar ku.
Idan asara, kowa ya
ɗauki rabon da ya yi dai-dai da jarinsa.

4. Qarul-asana – Bashi na alheri

Ma’ana:
Wannan shi ne bashi da ake bayarwa a Musulunci ba tare da wani
ƙarin riba ba, ko da kuwa ƙanƙanin ƙari ne.

Manufarsa:

·         Taimako

·         Jinƙai

·         Gujewa matsalar kuɗi da wahala

Halaye:
Ba a ƙara komai akan kuɗin da aka bayar.
Ba a ɗora tara idan mai bashi ya yi jinkiri, sai dai idan lalaci ne.
An so a yi kyauta ko sassauci idan mai bashi ya tsinci kansa cikin wahala.
Musulmi yana da lada mai girma idan ya bayar da Qarzul-Hasana.

Dalili daga Alkur’ani:
“Wanda ya ba Allah bashi na alheri, to zai ninka masa.” – Surat Al-Baqarah 245

Kammalawa

A ƙarshe, wannan littafi ya yi ƙoƙarin fayyace maanar riba, nau’o’inta, da yadda malamai na fikihu suka yi ittifaqi a kan haramcinta bisa hujjojin Alƙurani da sahihan hadisan Manzon Allah (SAW). Riba tana daga cikin manyan laifuka da ke lalata tattalin arziki, rushe zumunci, da jefa alumma cikin talauci da rashin adalci. Wannan ya sa Shari’ar Musulunci ta yi tsaurin hani a kanta, domin kare rayuwar mutane, tsaron dukiya, da tabbatar da musayar amana a cikin al’umma.

Hujjojin da suka fito daga Alƙurani sun yi nuni kai tsaye da cewa riba tana kawo yaqi daga Allah da Manzonsa, tare da gargaɗi mai tsanani ga masu mu’amala da ita. Haka hadisai sahihai sun tabbatar da la’antar mai cin riba, mai bayarwa, wanda ya rubuta, da wanda ya shaida, dukkansu ana ɗaukar su a matsayin masu haɗaka a wannan laifi. Wannan ya nuna cewa Musulunci ba wai kawai ya haramta riba ba ne, har ma ya rufe duk wata ƙofa da za ta kai ga aikata ta.

Saboda haka, musulmi ya kamata ya nisanci duk wata mu’amala da ta ƙunshi riba, yana neman halal cikin sanaoi, kasuwanci, da musayar kuɗi. Samun halal ko da kaɗan ce tafi arzikin da aka samu ta hanyar riba wanda arzikin ya ƙunsa laana da fushin Ubangiji. Sharia ta buɗe hanyoyi masu tsabta irin su mudaraba, murabaha, musharaka, da qarzun hasana, domin tabbatar da cika bukatun al’umma ba tare da cin zarafi ba.

Allah Ya sa wannan aiki ya zama hujja mai kyau ga marubuci da mai karatu, Ya sa mu daga cikin waxanda ke bin halal su guji haram, Ya kuma kare mu daga jarabar riba a dukkan siffofinta. Ameen.

Takaitawa

Wannan littafi ya yi bayani dalla-dalla game da riba: ma’anarta, nau’o’inta, da yadda malamai suka yi ittifaqi a kan haramcinta. An kawo hujjoji daga Alƙurani da hadisai waɗanda suka yi tsaurin hani ga mai cin riba da mai bayarwa, tare da yin nuni da illolinta ga tattalin arziki da rayuwar al’umma. Littafin ya kuma nuna hanyoyin mu’amala na halal da Musulunci ya shar’anta domin kare al’umma daga zalunci, ya tabbatar da adalci da amana a cikin harkokin kuɗi.

 

Shawarwari

1. Nisantar Mu’amalar Riba: Musulmai su kauce wa duk wata hulɗa da ta ƙunshi riba, ko da tana ɓoye, saboda tsananin haramcinta a Shari’a.

2. Neman Halal a Harkokin Kasuwanci: Ya dace al’umma su mai da hankali kan hanyoyin da Shari’a ta halatta kamar mudaraba, musaraka, murabaha, da qarzun hasana.

3. Ƙarin Ilimi: Ana bada shawara ga masu kasuwanci, ɗalibai, da malamai su zurfafa karatu kan fikihun mu’amalah domin fahimtar bambanci tsakanin riba da halal mu’amala.

4. Tattaunawa da Malamai: Idan mutum ya shiga mu’amala mai rikitarwa, ya kamata ya tuntuɓi malaman Shari’a domin samun hukunci mai tsafta.

5. Ƙarfafa Bankunan Islama: Akwai buƙatar goyon bayan bankunan Islama domin samar da zaɓuɓɓuka na halal ga al’umma, su kauce wa tsarin ribace-ribace.

6. Gyaran Al’umma: Masu wa’azi da malamai su ci gaba da wayar da kai kan illolin riba, domin kare al’umma daga shiga hanyoyin da za su cutar da su a nan duniya da lahira.



[1] - Suratul-Al-Baqara aya ta 278

[2] - Suratul Baqata ayata 279

[3] - Suratu Ali Imran ayata 130

[4] - Sahih Muslim, Hadisi mai lamba 1587

[5] - Sahih Muslim, Hadisi mai lamba 1587

[6] - Suratul Bakara Ayata 275

[7] - Suratul Bakara Ayata 130

[8] - As-habu Sinan  

[9] - Ahmad da Hakim

[10] - Hakim

[11] - Buhari da Muslim

[12] - Suratul Baqara Ayata 275

[13] - •    Sahih Muslim, Hadisi 1598

[14] - •    Sahih Bukhari, Kitab al-Buyu, Hadisi 2084

[15] - •    Sahih Muslim, Hadisi 1599

[16] - •    Sahih Bukhari, Hadisi 2075

[17] - •    Sahih Muslim, Hadisi 1597

[18] - •    Abu Dawud, Hadisi 3584

[19] - •    Tirmidhi, Hadisi 1287, Hadisi Sahih

[20] - •    Sahih Muslim, Hadisi 1598

[21] - Sahih Bukhari, Hadisi 2085

[22] - Abu Dawud, Hadisi 3582

[23] - Sahih Muslim

[24] - Sahih Muslim

[25] - Tirmizi Ibn Mahja Sahihul Na’ani

[26] - Muwaxxa Al-Malik

[27] - Al-Muwaxxa Kitabul Biyu’u

[28] - Al-Muwaxxa Kitabul Biyu’u

[29] - Al-Muwaxxa Kitabul Biyu’u

[30] - Shaik Ibn Baz RA

[31] - Sheik Muhammad Salih Al-Uthaymin RA

[32] - Sheik Dr. Yusuf Al-Karadawi RA

[33] - Malaman Jami’ar Azhar dake Masar

[34] - Sheik Ibrahim Nyas RA

[35] - Mallam Ja’afar Mahmud Adam cikin Karatuttukan

[36] - Mallam Xahiru Uthman Bauchi cikin Karatuttukan

[37] - Mallam Qaribulla Sheik Nasiru Kabara cikin Karatuttukansa

[38] - Mallam Muhammad Sunusi Qerau cikin Karatuttukansa

[39] - Mallam Dr. Ahmad Gumi cikin Karatuttukansa

[40] - Mallam Kabiru Gombe cikin Karatuttukansa

[41] - Mallam Sani Yahaya Jingir cikin Karatuttukan

No comments:

Post a Comment