Memene sankaran mama?
Sankaran mama na afkuwa ne a yayin da kwayoyin halittar jikin mama suka fara girma a kan kansu ba tare da jiki ya umarce su ko ya bukace su da su yi haka ba.
Me yake jawo sankaran mama?
Mutane da dama sukan so su san abinda yake jawo wannan cuta ta sankaran mama. Har ma sukan tambayi kansu, me yasa na gamu da wannan cuta? Ko me ya sa matata ko kanwata ko ya ta ko kawata ta gamu da wannan cuta? Ko akwai wani abu da na yi ko suka yi, da ya kamata su yi, ko na yi, da banyi ba, ko basu yi ba domin kare kai na ko kansu daga wannan cuta?.
Babu wani sanannen dalili da za a iya kawowa kai tsaye wanda za a ce shi yake kawo wannan cuta. Sai dai akwai wasu dalilai da sukan sanya wannan cuta ta fi saurin kama wasu matan a maimakon wasu. Waɗannan dalilai su ne:
Shekaru – karfin zaton kamuwar mace da sankaran mama, yana karuwa ne da yawan shekarun mace.
Sinadarin iyistirogin – Yawan Sinadarin iyistirogin da yake jikin mace. Shi wannan sinadari na iyistirogin yana ɗaya daga cikin sinadaran da jikin mace ya kunsa kuma yana da kyau a ce jikin mace yana da wannan sinadari isashshe. Sai dai kuma bai kamata a ce jiki yana fitar da shi ba tare da hutu ba.
Wannan hutun yana zuwa ne a lokacin da mace take da ciki ko take shayarwa. Don haka dalilan da suke haifar da kasancewar sinadarin iyistirojin a jiki suna jefa jiki cikin haɗarin kamuwa da cutar sankaran mama.
Daga ciki akwai fara jinin al’ada da wuri (kafin a kai shekara goma sha biyu), yin al’ada har a wuce shekara hamsin da biyar, rashin haihuwa, da kuma jinkirin haihuwa da wuri har a wuce shekara talatin. Waɗannan abubuwa ba yin kanmu ba ne, kuma za a iya saisaita yawan wannan sinadari a jiki ta hanyar shan magungunan hana ɗaukar ciki da na sa haihuwa da sauransu.
Girman Jiki da sura- Mace mai tsaho da mace mai kiba ta fi faɗawa hadarin kamuwa da wannan cuta. Matan da sukayi kiba kuma basu rame ba har bayan sun daina jinin al’ada haɗarin kamuwarsu da sankaran mama yafi yawa. Haka kuma komai shekarun mace, wanda suke da tarin kitse a tumbin su ko kuma a kugun su suma hadarin kamuwarsu da sankaran mama yafi yawa
Tarihin cuta a cikin ‘yan uwa – Macen da a cikin yan uwanta an taɓa samun wata kamar mahaifiyarta, ko yarta, ko ‘yarta ta tana da wannan cuta, ta fi fadawa haɗarin kamuwa da wannan cuta.
Tarihin Kamuwa da cutar Sankaran mama: Macen da cutar sankara ta taɓa kama ta a mamanta guda ɗaya, cutar za ta iya kama ɗaya maman ma
Wasu cututtukan mama da ba sankara ba: Wasu matan da aka taɓa cire musu tsiro a mamansu wanda likita ya ce musu ba sankara bane. Dole sai suna zuwa a na duba wannan mama akai-akai domin irin wannan tsiro zai iya juyawa ya koma cutar sankara daga baya
Akwai tabbacin cewa kamuwa da cutar sankaran mama ba laifin mutum ba ne. Bata da alaka wacce take kai tsaye da abincin da muke ci, kuma ba cuta bace mai kwayoyi da za’a iya kamuwa dasu ba. Haka kuma ba a daukar ta ta hanyar jima’i, ko ta hanyar hulda da wanda yake da wannan cuta.
Ta ya ya ake gane sankaran mama?
Abu na farko da za a fara lura a tabbatar da cewa jiki ya kamu da cutar sankaran mama shine samuwar wani dan tsiro a cikin nonon maras ciwo.
Shi wannan tsiro za a ji shi kamar kurjin maruru sai dai ba ya ciwo. Duk macen da ta ji irin wannan a jikin mamanta sai ta garzaya wajen likitanta nan take. Dole ne a cire duk ilahirin irin wannan tsiron sannan a gwada a asibiti.
Maman da cutar sankara ta fara kamashi in an kalle shi a ido ba za a ga wani canji ba, haka kuma a jiki ma ba za a ji komai ba. Ba ya kawo ciwo, baya sa zazzabi, amai, gudawa ko rashin cin abinci kuma ba ya hana ayyukan yau da kullum. Ba lallai ba ne a ce kin taɓa ganin ko jin labarin cutar ba, domin mai yiwuwa ne a ce bata taɓa kama wata yar uwarki ba ko wadda kika sani. A wannan mataki na farkon shigar wannan cutar akwai fatan cewa in dai aka yi maganin wannan cutar za a iya warkar da ita.
Sankaran mama kuma tana iya farawa ta hanyar fitowar ciwo a kan mama ko fatar da ta zagaye kan maman.
A wasu matan kuma, kan nonon ne zai fara shigewa ciki. Za’a ga mazaunin sa ba daya yake dana ɗaya ɓangaran ba.
Idan aka kyale tsiron, ci gaba zai yi tayi da girma. Zai iya girma daga cikin maman har ya ratso fatar maman ya zamo gyambo (ciwo) wanda yake fitar da ruwa da jinni mai wari, kuma ba zai warke ba sai anyi maganin wannan cuta.
A sa’ar da wannan cuta ta cigaba da bunkasa, ta kan bazu zuwa wasu sassa na jiki kamar kwakwalwa, hunhu, kasussuwa da hanta ta wata hanya da ake kira (Metastasis) da turanci. Ita wannan bazuwar zuwa ga wadannan gabobin ne ke cutarwa, kuma da zarar hakan ta faru, duk da cewa bayar da magani ya zama dole, samun waraka abu ne mai wahala.
Za a iya gane irin wannan buzuwar cutar ta hanyar samuwar tari, haki, kumburin ciki, ciwo a kasussuwa musamman ma baya, rashin karfin kafafu da rashin iya motsa su.
Shin za a iya gane cutar sankaran mama da wuri?
Za’a iya gane wannan cuta da wuri ta hanyar lura da halin da maman ke ciki. Wannan wadansu matakai ne da mace zata rika bi sau daya a wata domin ta duba mamanta ko akwai wani tsiro, kumburi, ko wata cuta a jikin maman. Ya kamata ki bukaci likitarki ta koya miki yadda zaki rika duba mamanki ita ma kuma ta duba miki mamanki a kalla sau daya a shekara. Daukan hoton mamman a asibiti don binciken cutar, na iya taimakwa wajen gano ta da wuri.
Matakan Sankaran Mama
Ana iya fahimtar tsanin bazuwar da wannan cuta tayi a jikin marar lafiya ta hanyar matakin da cutar take a wannan lokacin. Waɗannan matakai su ne:
Mataki na I: Tsiron cikin maman da bai kai sentimita biyu ba, ko kuma yana daidai da sentimita biyu. Kuma idan aka gwada kaluluwar hammata za’a ga babu wannan cuta.
Mataki na II: Faɗin tsiron cikin maman yana tsakanin sentimeta biyu zuwa biyar tare da kaluluwar hammata wacce ta nuna akawai cuta ko kuma wacce ta nuna babu cutar. Zai kuma iya kasancewa faɗin tsiron cikin maman ya wuce sentimeta biyar tare da kaluluwar hammata wacce ta nuna cewa akwai cutar.
Mataki na III: Wannan matakin an kasa shi zuwa gida biyu A da B.
A: A nan faɗin tsiron cikin maman ya fi sentimita biyar, kuma akwai kaluluwar hammata masu motsi waɗanda suke dauke da wannan cuta. Ko kuma girman kumburin zai iya zama ko ma ya ya da kuma kaluluwar wacce kaluluwar hammata waɗanda suka maƙalewa juna kokuma suna maƙale da wata tsoka dake wannan gurbin.
B: A nan faɗin tsiron cikin maman zai zama ko yaya amma ya bazu zuwa fata, bangon kirji, ko kaluluwa da suke can kasan nono kuma a can cikin kirji.
Mataki IV: A nan faɗin tsiron cikin maman ko ma ya girmansa yake anan ya bazu zuwa wurare masu nisa kamar ƙasussuwa, hunhu, ko kaluluwar jiki da suke nesa da mama.
Mataki na I da na II su ne farkon kamuwa da wannan cuta amma mataki na III da IV cutar ta riga ta bunkasa.
Yaya ake maganin cutar sankaran mama?
Ana maganin sankaran mama sabuwar kamu ta wadannan hanyoyi:
Surgery (Fiɗa): Wannan shine a cire maman gaba daya ko wani ɓangarensa ta hanyar fida. Amma yin wannan fiɗa ya danganta da abubuwa da dama wanda zaki tattauna da likitanki.
Chemotherapy - Shine yin amfani da magani domin a kashe kwayoyin da suka gina wannan cuta, wadda ta riga ta bazu zuwa wasu ɓangarori na jiki ko a kankantar da wannan kumburi na mama. Duk da dai waɗannan magunguna su na da illoli, amma akwai hanyoyin da likitoci sukan bi domin taimakawa mai wannan cuta wajen samun saukin waɗannan illoli.
Hormone Treatment - yin amfani da wannan sinadari na homon domin su hana kwayoyin wannan cuta girma. Za a iya yin wannan ta hanyar fiɗa, radiotherapy, ko shan da magunguna.
Radiotherapy - yin amfani da kwayoyi na wuta wajen kashe kwayoyin wannan cuta.
Akwai hanyoyi da dama da ake bi a warkar da wannan cuta, sai dai ya danganta da bazuwarta a jiki, zabin mai ɗauke da wannan cuta, kuɗin da za’a iya kashewa, da yadda za a iya daurewa bin ka’idojion shan magani, da kuma kayan aiki da ake da su.
Yin maganin wannan cuta ya kan ɗau lokaci mai tsaho kuma ana bukatar yawan zuwa asibiti. Yana da tsada kuma yakan dau lokaci. Duk wadannan abubuwa ne da suka zama dole a tattauna su da likita.
Haka kuma yana da kyau mai ɗauke da cutar sankaran mama ta tattauna da ‘yan uwanta domin su gane yadda cutar take domin su ba ta goyon baya da kwarin gwiwa, kuma su taimaka wajen faɗakarwa game da lura da mama.
Sakamakon magani
Karbar magani ga jiki ya bambanta daga mutum zuwa mutum kuma ya danganta da:-
· Matakin cutar a lokacin da aka gano ta: Cutar da aka gano ta tunda wuri tafi saukin warkarwa.
· Yanayin cutar sankara: Saukin warkewar ya danganta da irin cutar sankarar da ta kama mutum. Ana gane irin cutar ne bayan an yi gwaje-gwaje akan tsiron da aka ciro daga jikin mai ɗauke da cutar.
· Bin ka’idojin magani ba tare da kuskerawa ba.
Idan babu kumburi a hammata kuma girman sankaran bai wuce girman sentimita uku ba ko kasa da haka, kashi casa’in da tara cikin dari na waɗannan majinyatan sukan rayu har tsahon shekara biyar. Haka kuma kashi sittin cikin dari na majinyatan da suke da kaluluwar hammata guda biyu zuwa hudu za su iya rabuwa da cutar a cikin shekara biyar in aka haɗa da kashi arba’in cikin dari na masu ɗauke da kaluluwa shida zuwa goma.
Idan kuma cutar ta riga ta bunkasa fa? A na nufin kenan ba za ta warke ba? To in da rai da robo. Domin kididdigar da aka bayar a sama, ta samu ne ta hanyar hada sakamakon mutane da yawa da aka yi. Babu likitan da zai ce lallai yadda aka samu din nan, haka ne zai faru a kanki, koda a ce an yi ta maganin amma cutar ta ki warkewa, likita zai iya bakin kokarinsa wajen bada magunguna waɗanda za su rage zafin cutar.
To magungunan gargajiya fa? Abun sani anan shine, duk wanda yake jinyar mai ɗauke da cutar sankara, fatansa ne a samu sauki da wuri saboda mai cutar ta daina shan wahala. Abin takaici shine, cigaban da aka samu akan shawo kan cutar a kimiyyance bai taka kara ya karya ba. Amma duk da haka, yafi amfani nesa ba kusa ba, yafi rashin cutarwa, kuma yafi tabbaci fiye da kowane irin hanyar magani da wani ko wata zai zo miki dashi a yanzu. A karshe, mutum zai iya taimakawaa ckin binciken samo maginin da yafu na yanzu aiki ta hanyar ba da gudunmawa da haɗin kai ga masu bincike a asibiti.
Yana da mutukar amfani mutum ya je asibiti da wuri da zarar ya lura da waɗansu canje-canje don neman magani.