Friday, 29 August 2014

TARIHIN SHAIK AHMADU TIJJANI (RTA)

An haifi Shaihu Ahmad Tijjani, wanda ya kafa darikar Tijjaniyya, a garin Ainu Mali a shekara ta 1150 BH. Mahaifinsa ya rasu a lokacin yana da shekaru goma sha shida a duniya.Shaihu Tijjani ya haddace Alkur’ani yana dan shekara bakwai a hannun wani malami da ake kira Abu Abdullahi Muhamamd binu Hamu.

Sa’an nan ya ci gaba da neman ilmi inda ya karanta fannoni dabam-daban a hannun malamai masu yawa. Daga nan kuma sai ya karkata zuwa ga tafarkin Sufanci,ya shagala da yakar kai da hore dare da gudun duniya da sauran abubuwan dake hawa wuyan wanda ya bi tafarkin Sufanci.

A lokacin da Shaihu Tijjani ya yi nufin shiga sha’annin Sufanci tsundum, sai ya rabu da matarsa ta aure don ya zama ya samu damar tattara hankalinsa a kan abinda ya sa a gaba. Kuma a bayan da ya gamsu da cewa ya samu abinda ya samu a cikin wannan sha’ani, watau ya kai wani mukami babba a Sufanci, sai ya sayi kuyangi guda biyu, ya ‘yanta su, kana ya daura aure da su. Ya sanya wa dayarsu suna Mabruka dayar kuma Mubaraka.

Allah ya arzuta Shaihu Tijjani da ‘ya’ya maza guda biyu da kuma mata masu yawa. Babban dansa shi ne Muhammad Kabir, dan wajen matarsa Mabruka, na biyun kuwa shi ne Muhammad Sagir wanda aka yi wa lakabi da Habib. Shi wannan matarsa Mubaraka ce ta haifa masa shi, kuma shi ne ya zama halifar Shaihin na farko a bayan rasuwarsa.

Shaihu Ahmad Tijjani ya yi tafiye-tafiyeda dama wajen neman ilmin Sufanci, kuma ya shiga dariku masu yawa kafin daga bisani ya zauna a wuri guda ya kafa tasa darikar ta kansa. A lokacin dayake zaune a Moroko, Shaihin ya shigadarikun Qadiriyya da Nasiriyya da kuma darikar Shaihu Abul Abbas Ahmad Habib wanda aka fi sani da lakabin Algimari. Bayan ya bar wadan nan dariku duka, ya tashi daga Moroko ya nufi cikin hamadar Sahara inda ya ya da zango a zawiyar Shaihu Abdulkadir binu Muhammad Al’abayal.

Daga nan Shaihu Tijjani ya fita zuwa Hajji. A kan hanyarsa ta zuwa Makka, ya wuce ta kasashen Tilmisan da Tunis da Masar. Ya isa Makka a shekara ta 1187 BH, inda ya sauke farali kuma ya sadu da malamai masu yawa. Bayan kammala aikin hajji, ya komo ta kan hanyarsa ta Masar da Tunis, sa’an nan Tilmisan wurin da ya ya da zango kadan kafin ya wuce zuwa birnin Fas, inda ya ziyarci kabarin Maula Idris kakan Sharifan Moroko a shekara ta 1191 BH. A wannan tafiya ne har ila yau, a wani kauye da ake kira Wajda, Shaihu Tijjani ya gamu da babban alamajirinsa, Shaihu Ali Harazimi.

A shekara ta 1196 BH, Shaihu Tijjani yakafa darikar Tijjaniyya a wani gari da ake kira Abu Samgun wanda a yanzu yake cikin kasar Aljeriya. Sa’an nan ya yi kaura daga wannan garin ya koma birnin Fas, a cikin kasar Moroko, inda Sarkin Moroko na wannan lokaci, Sarki Sulaiman, ya ba shi gida wanda ya zauna a cikinsa har zuwa karshen rayuwarsa. A nan ne kuma ya kafa zawiyarsa, ya tattaro alamajiransa, kuma ya ci gaba da aikin yada darikarsa. Shaihu Tijjani ya rasu a shekara ta 1213 BH. Ya bar matan aurebiyu, ‘ya’ya maza biyu da mata masu yawa.Sabanin Sidi Abdulkadir, Shaihu Tijjani ya mutu bai bar wani littafi da ya tattare lamuran darikarsa ba.

Amma mutane uku daga cikin manyan almajiransa sun rubuta littafai wadanda suka kunshi tarihin Shaihin da ka’idojin darikarsa da kuma ra’ayoyinsa dangane da tafarkin Sufanci. Wadan nan alamajirai su ne, Shaihu Ali Harazimi wanda ya rubuta littafin Jawahirul Ma’ani, Shaihu Muhammad binu Mushri wanda ya wallafa Aljami’u fil Ulumil Fa’ila da Shaihu Muhammad Dayyib Assufyani, wanda ya rubuta Al’ifadatul Ahmadiya. Daga wadan nan littafai ne mai bincike zai iya samun kusan duk abinda yake bukata dangane da darikar Tijjaniyya da tarihin Shaihinta.

Darikar Tijjaniyya tana da sharadai guda bakwai wadanda su ne harsashen da aka gina ta a kansa. Sharadan su ne kamar haka:

1. Wanda ya shiga darikar Tijjaniyya, yakarbi wurdinta, to ba ya fita har abada.

2. Kar ya gama ta da wata darikar dabam, watau kada ya zama yana Tijjaniyya kuma yana yin wata darikar alokaci guda.

3. Kada ya ziyarci wasu waliyyai, na raye ko mamata, sai dai Sahabban Annabi (SAW) kawai, da Shaihu Tijjani da sauran Shaihinnan Tijjaniyya.

4. Ya lazimci tsoron Allah a ko wane hali.

5. Ya lazimci kaunar Shaihu Tijjani da zuri’arsa da almajiransa.

6. Ya debe kauna daga abinda yake hannun mutane na samu, sai dai abinda suka kawo suka ba shi ba tare da ya roka ba.

7. Har abada ya rika sada zumunci da sasanta tsakanin ‘yan uwa.

Wurdin Tijjaniyya kuwa ya kasu gida uku:•

Na Farko: Wurdi Lazimi, watau wurdin farilla.
Wannan ya kunshi istigfari kafa dari, salatin Annabi dari, da hailala dari.
Ana yin wannan wurdi safe da yammaci.
Lokacin wurdin safe shi ne tun daga bullowar alfijir har ya zuwa lokacin walaha.
Lokacin wurdin yammakuma, daga bayan La’asar zuwa sallar Isha. Wanda lokacin safe ya wuce shi bai yi wurdin a cikinsa ba, to wannan zai iya ramawa a sauran wuni duka.
Wanda lokacin yamma ya wuce shi kuwa, yana iya ramawa a sauran dare duka. Haka nan, wanda wurdin rana guda (watau safe da yamma gaba daya) ya wuce shi, to dole ya biya wannan wurdi har abada.
Watau ana bin sa bashin wannan wurdi har tsawon rayuwarsa. Wannan shi ne wurdin farilla, ko kuma Lazimi.•

Na Biyu: Wurdin Wazifa.
Wannan ya hada da istigfari kafa dari, Salatul Fatihidari ko hamsin, Hailala dari ko dari biyu, da kuma wata addu’a da ake kira Jauharatul Kamal kafa goma sha daya.
Ba’a karanta Jauhara sai da cikakkiyar alwala, kuma taimama ba ta isarwa wajen karatun ta.
Wazifa ba farilla ba ce, saboda haka ana iya yin ta a safe da yamma ko kuma a lokaci daya kawai.•

Na Uku: Zikirin Jumma’a.
Wannan anayin sa ne ranar Jumma’a kawai, kuma ba ya inganta sai a cikin jama’a.
Lokacinsa shi ne daga bayan sallar La’asar har zuwa faduwar rana. Baya inganta mutum daya ya yi zikirin jumma’a sai fa in ya zama a garin babu‘yan Tijjaniya. Zikirin Jumma’a ya kunshi Hailala ne kawai, kuma bai da wani adadi kayyadajje.

Darikar Tijjaniyya ta watsu a sassa da dama na duniyar Musulmi. Daga cikin kasashen da ake samun mabiyan darikar akwai Masar, Turkiya, Muritaniya, Sudan, Senegal, Nijeriya, Gini, Gambiya da sauransu.

No comments:

Post a Comment