Thursday, 13 June 2019

Bayani Akan Cutar Sarke Hakora

Bayani A Kan Ciwon Sarke Hakora (Tetanus) 

Ciwon sarke hakora ko tatanas kamar yadda wasu suka fi sanin sa da shi, shi ma nau’in ciwo ne da kan iya kama kowa, manya da yara, kuma kwayoyin cuta na bacteria da ake kira Clostridium tetani ke haddasa shi, kuma suna nan a kowane yanki na duniya.

Su wadannan kwayoyin cuta a cikin kasa suka fi rayuwa, amma iska kan kwashe su su bazu, wasu su hau fatar jiki. Idan suka samu suka shiga jiki sai su rika samar da wata guba da kan kama jijiyoyin jiki, su hana wurin motsi.

An yi kiyasin cewa duk shekara wannan ciwo na halaka mutane kusan dubu dari uku, yawancinsu jarirai, musamman a kasashe irin namu.

Yadda ake kamuwa da ciwon sarke hakora:
kwayoyin za su iya shiga jiki ne yayin da mutum ya ji rauni komi kan kantarsa (ko yanka ko kujewa ko gyambo ko kuna ko cizon wata dabba), idan  ba a dauki matakin kariya ba.

Jariri kan iya dauka a jikin abin da aka yanke cibi da shi, in ba mai tsabtaba ne. Bayan kamar kwanaki hudu zuwa mako biyu da yankan cibi ko yin rauni, gubar da kwayoyin cutar ke saki ta fara barna, za a ga jariri yana ta amai da zazzabi da yawan kuka da kin karbar mama. Wadannan su ne alamu na farko, in ba a dau matakin kai wa asibiti ba, za a ga wani bangare na jikin jariri ko kuma duk jikin gaba daya yana jijjiga, ko yana sandarewa.

A manya kuwa za a fara jin mukamukai sun cije, hakora sun sarke, sai wuya ya sandare, a kasa hadiyar ruwa ko abinci, sanadiyar wannan guba ta kwayoyin cutar. In ba a dauki mataki ba, haka za a ga duk jiki ya sandare daga sama zuwa kasa, wato daga kai har zuwa kafa, mara lafiya na bankarewa.

Kashi 40 zuwa 80 cikin dari na masu wannan karkarwa da sandarewa ba sa kai labari ko an je asibiti.

Hanyoyin kariya daga wannan ciwo: Allurar riga-kafin kamuwa da ciwon sarke hakora ita ce hanyar da aka tabbatar za ta kare kamuwa daga wannan ciwo.
Saboda haka:

1. Kowa da kowa ya samu a yi masa allurar riga-kafin sarke hakora akalla sau daya a cikin shekaru goma.

2. Mata masu ciki su rika zuwa awo domin a wurin ne ake ba da allurar riga-kafin wannan ciwo. Jaririn da ke ciki kan samu nasa rabon ta mahaifa.

3. A kai yara daga wata biyu ga cibiyoyin riga-kafi, a basu wannan allura, a sake komawa in sun kai wata hudu da wata shida, sannan duk yara daga shekaru 3-7 domin su suka fi yin rauni a yau da kullum ba tare da iyaye sun sani ba.

4. Idan yaro ko wani babba ya yi rauni, bayan zuwa asibiti an wanke ciwon, an ba da magunguna, to a tabbata an karbi allurar tatanas don yin riga-kafi.

5. A tabbatar ungozoma mai karbar haihuwa a gida tana amfani da sabuwar reza ko aska wajen yanke cibi, ba tsohuwar reza ko aska ba, domin ko tafasa reza da askar baya kashe kwayar cutar tatanas.

6. Manoma su yawaita zuwa karbar wannan allura, su kuma rika amfani da takalmin ruwa irin na roba domin wani zubin sukan yi rauni da lauje ko fartanya ba tare da ma sun sani ba.

7. A yi hanzarin kai jariri mai yin jijjiga ko mai nuna alamomin da aka zayyana a sama asibiti mafi kusa, ko da mai gida ba ya kusa, musamman in a gida aka haifi jaririn.

8. A yi hanzarin kai duk wani babba da hakoransa ko mukamukansa suka cije, ya kasa magana ko cin abinci asibiti mafi kusa.

Allah ya kara mana lafiya.

Bincike Da Yadawa:

Gidauniyar Musulunci Ta Al'azmiyya 

(Al'azmiyya Islamic Foundation Kano) 

Bayani Game Da Cutar Sankarar Mama

Bayani Game Da Cutar Sankarar Mama

Menene sankaran mama?

Sankaran mama na afkuwa ne a yayin da kwayoyin halittar jikin mama suka fara girma a kan kansu ba tare da jiki ya umarce su ko ya bukace su da su yi haka ba.

Me yake jawo sankaran mama?
Mutane da dama sukan so su san abinda yake jawo wannan cuta ta sankaran mama.  Har ma sukan tambayi kansu, me yasa na gamu da wannan cuta?  Ko me ya sa matata ko kanwata ko ya ta ko kawata ta gamu da wannan cuta?  Ko akwai wani abu da na yi ko suka yi, da ya kamata su yi, ko na yi, da banyi ba, ko basu yi ba domin kare kai na ko kansu daga wannan cuta?.

Babu wani sanannen dalili da za a iya kawowa kai tsaye wanda za a ce shi yake kawo wannan cuta.  Sai dai akwai wasu dalilai da sukan sanya wannan cuta ta fi saurin kama wasu matan a maimakon wasu.  Waɗannan dalilai su ne:

Shekaru – karfin zaton kamuwar mace da sankaran mama, yana karuwa ne da yawan shekarun mace.

Sinadarin iyistirogin – Yawan Sinadarin iyistirogin da yake jikin mace. Shi wannan sinadari na iyistirogin yana ɗaya daga cikin sinadaran da jikin mace ya kunsa kuma yana da kyau a ce jikin mace yana  da wannan sinadari isashshe. Sai dai kuma bai kamata a ce jiki yana fitar da shi ba tare da hutu ba.

Wannan hutun yana zuwa ne a lokacin da mace take da ciki ko take shayarwa. Don haka  dalilan da suke haifar da kasancewar sinadarin iyistirojin a jiki suna jefa jiki cikin haɗarin kamuwa da cutar sankaran mama.  

Daga ciki akwai fara jinin al’ada da wuri (kafin a kai shekara goma sha biyu), yin al’ada har a wuce shekara hamsin da biyar, rashin haihuwa, da kuma jinkirin haihuwa da wuri har a wuce shekara talatin.  Waɗannan abubuwa ba yin kanmu ba ne, kuma za a iya saisaita yawan wannan sinadari a jiki ta hanyar shan magungunan hana ɗaukar ciki da na sa haihuwa da sauransu.

Girman Jiki da sura- Mace mai tsaho da mace mai kiba ta fi faɗawa hadarin kamuwa da wannan cuta.  Matan da sukayi kiba kuma basu rame ba har bayan sun daina jinin al’ada haɗarin kamuwarsu da sankaran mama yafi yawa. Haka kuma komai shekarun mace, wanda suke da tarin kitse a tumbin su ko kuma a kugun su suma hadarin kamuwarsu da sankaran mama yafi yawa

Tarihin cuta a cikin ‘yan uwa – Macen da a cikin yan uwanta an taɓa samun wata kamar mahaifiyarta, ko yarta, ko ‘yarta ta tana da wannan cuta, ta fi fadawa haɗarin kamuwa da wannan cuta.

Tarihin Kamuwa da cutar Sankaran mama: Macen da cutar  sankara ta taɓa kama ta a mamanta guda ɗaya, cutar za ta iya kama ɗaya maman ma

Wasu cututtukan mama da ba sankara ba: Wasu matan da aka taɓa cire musu tsiro a mamansu wanda likita ya ce musu ba sankara bane.  Dole sai suna zuwa a na duba wannan mama akai-akai domin irin wannan tsiro  zai iya juyawa ya koma cutar sankara daga baya

Akwai tabbacin cewa kamuwa da cutar sankaran mama ba laifin mutum ba ne. Bata da alaka wacce take kai tsaye da abincin da muke ci, kuma ba cuta bace mai kwayoyi da za’a iya kamuwa dasu ba.  Haka kuma ba a daukar ta ta hanyar jima’i, ko ta hanyar hulda da wanda yake da wannan cuta.

Ta ya ya ake gane sankaran mama?

Abu na farko da za a fara lura a tabbatar da cewa jiki ya kamu da cutar sankaran mama shine samuwar wani dan tsiro a cikin nonon maras ciwo.
Shi wannan tsiro za a ji shi kamar kurjin maruru sai dai ba ya  ciwo.  Duk macen da ta ji irin wannan a jikin mamanta sai ta garzaya wajen likitanta nan take. Dole ne a cire duk ilahirin irin wannan tsiron sannan a gwada a asibiti.
Maman da cutar sankara ta fara kamashi in an kalle shi a ido ba za a ga wani canji ba, haka kuma a jiki ma ba za a ji komai ba.  Ba ya kawo ciwo, baya sa zazzabi, amai, gudawa ko rashin cin abinci kuma ba ya hana ayyukan yau da kullum.  Ba lallai ba ne a ce kin taɓa ganin ko jin labarin cutar ba, domin mai yiwuwa ne a ce bata taɓa kama wata yar uwarki ba ko wadda kika sani.  A wannan mataki na farkon shigar wannan cutar akwai fatan cewa in dai aka yi maganin wannan cutar za a iya warkar da ita.

Sankaran mama kuma tana iya farawa  ta hanyar fitowar ciwo a kan mama ko fatar da ta zagaye kan maman.

A wasu matan kuma, kan nonon ne zai fara shigewa ciki. Za’a ga mazaunin sa ba daya yake dana ɗaya ɓangaran ba.

Idan aka kyale tsiron, ci gaba zai yi tayi da girma. Zai iya girma daga cikin maman har ya ratso fatar maman ya zamo gyambo (ciwo) wanda yake fitar da ruwa  da jinni mai wari, kuma ba zai warke ba sai anyi maganin wannan cuta.

A sa’ar da wannan cuta ta cigaba da bunkasa, ta kan bazu zuwa wasu sassa na jiki kamar kwakwalwa, hunhu, kasussuwa da hanta ta wata hanya da ake kira (Metastasis) da turanci.  Ita wannan bazuwar zuwa ga wadannan gabobin ne ke cutarwa, kuma da zarar hakan ta faru, duk da cewa bayar da magani ya zama dole, samun waraka abu ne mai wahala. 

Za  a iya gane irin wannan buzuwar cutar ta hanyar samuwar tari, haki, kumburin ciki, ciwo a kasussuwa musamman ma baya, rashin karfin kafafu da rashin iya motsa su.

Shin za a iya gane cutar sankaran mama da wuri?

Za’a iya gane wannan cuta da wuri ta hanyar lura da halin da maman ke ciki.  Wannan wadansu matakai ne da mace zata rika bi sau daya a wata domin ta duba mamanta ko akwai wani tsiro, kumburi, ko wata cuta a jikin maman.  Ya kamata ki bukaci likitarki ta koya miki yadda zaki rika duba mamanki ita ma kuma ta duba miki mamanki a kalla sau daya a shekara.  Daukan hoton mamman a asibiti don binciken cutar, na iya taimakwa wajen gano ta da wuri.

Matakan Sankaran Mama

Ana iya fahimtar tsanin bazuwar da wannan cuta tayi a jikin marar lafiya ta hanyar matakin da cutar take a wannan lokacin. Waɗannan matakai su ne:

Mataki na I: Tsiron cikin maman da bai  kai sentimita biyu ba, ko kuma yana daidai da sentimita biyu.  Kuma idan aka gwada kaluluwar hammata za’a ga babu wannan cuta.

Mataki na II: Faɗin tsiron cikin maman yana tsakanin sentimeta biyu zuwa biyar tare da kaluluwar hammata wacce ta nuna akawai cuta ko kuma wacce ta nuna babu cutar. Zai kuma iya kasancewa faɗin tsiron cikin maman ya wuce sentimeta biyar tare da kaluluwar hammata wacce ta nuna cewa akwai cutar.

Mataki na III: Wannan matakin an kasa shi zuwa gida biyu A da B.

A: A nan faɗin tsiron cikin maman ya fi sentimita biyar, kuma akwai kaluluwar hammata masu motsi waɗanda suke dauke da wannan cuta.  Ko kuma girman kumburin zai iya zama ko ma ya ya da kuma kaluluwar wacce kaluluwar hammata waɗanda suka maƙalewa juna kokuma suna maƙale da wata tsoka dake wannan gurbin.

B: A nan faɗin tsiron cikin maman zai zama ko yaya amma ya bazu zuwa fata, bangon kirji, ko kaluluwa da suke can kasan nono kuma a can cikin kirji.

Mataki IV: A nan faɗin tsiron cikin maman ko ma ya girmansa yake anan ya bazu zuwa wurare masu nisa kamar ƙasussuwa, hunhu, ko kaluluwar jiki da suke nesa da mama.

Mataki na I da na II su ne farkon kamuwa da wannan cuta amma mataki na III da IV cutar ta riga ta bunkasa.

Yaya ake maganin cutar sankaran mama?

Ana maganin sankaran mama sabuwar kamu ta wadannan hanyoyi:

Surgery (Fiɗa): Wannan shine a cire maman gaba daya ko wani ɓangarensa ta hanyar fida.  Amma yin wannan fiɗa ya danganta da abubuwa da dama wanda zaki tattauna da likitanki.

Chemotherapy - Shine yin amfani da magani domin a kashe kwayoyin da suka gina wannan cuta, wadda ta riga ta bazu zuwa wasu ɓangarori na jiki ko a kankantar da wannan kumburi na mama.  Duk da dai waɗannan magunguna su na da illoli, amma akwai hanyoyin da likitoci sukan bi domin taimakawa mai wannan cuta wajen samun saukin waɗannan illoli.

Hormone Treatment - yin amfani da wannan sinadari na homon domin su hana kwayoyin wannan cuta girma.  Za a iya yin wannan ta hanyar fiɗa, radiotherapy, ko shan da magunguna.

Radiotherapy - yin amfani da kwayoyi na wuta wajen kashe kwayoyin wannan cuta.

Akwai hanyoyi da dama da ake bi a warkar da wannan cuta, sai dai ya danganta da bazuwarta a jiki,  zabin mai ɗauke da wannan cuta, kuɗin da za’a iya kashewa, da yadda za a iya daurewa bin ka’idojion shan magani, da kuma kayan aiki da ake da su.

Yin maganin wannan cuta ya kan ɗau lokaci mai tsaho kuma ana bukatar yawan zuwa asibiti.  Yana da tsada kuma yakan dau lokaci.  Duk wadannan abubuwa ne da suka zama dole a tattauna su da likita.

Haka kuma yana da kyau mai ɗauke da cutar sankaran mama ta tattauna da ‘yan uwanta domin su gane yadda cutar take domin su ba ta goyon baya da kwarin gwiwa, kuma su taimaka wajen faɗakarwa game da lura da mama.

Sakamakon magani

Karbar magani ga jiki ya bambanta daga mutum zuwa mutum kuma ya danganta da:-

·  Matakin cutar a lokacin da aka gano ta: Cutar da aka gano ta tunda wuri tafi saukin warkarwa.

· Yanayin cutar sankara: Saukin  warkewar ya danganta da irin cutar sankarar da ta kama mutum.  Ana gane irin cutar ne bayan an yi gwaje-gwaje akan tsiron da aka ciro daga jikin mai ɗauke da cutar.

· Bin ka’idojin magani ba tare da kuskerawa ba.

Idan babu kumburi a hammata kuma girman sankaran bai wuce girman sentimita uku ba ko kasa da haka, kashi casa’in da tara cikin dari na waɗannan majinyatan sukan rayu har tsahon shekara biyar.  Haka kuma kashi sittin  cikin dari na  majinyatan da suke da kaluluwar hammata guda biyu zuwa hudu za su iya rabuwa da cutar a cikin shekara biyar in aka haɗa da kashi arba’in cikin dari na masu ɗauke da kaluluwa shida zuwa goma.

Idan kuma cutar ta riga ta bunkasa fa? A na nufin kenan ba za ta warke ba? To in da rai da robo.  Domin kididdigar da aka bayar a sama, ta samu ne ta hanyar hada sakamakon mutane da yawa da aka yi.  Babu likitan da zai ce lallai yadda aka samu din nan, haka ne zai faru a kanki, koda a ce an yi ta maganin amma cutar ta ki warkewa, likita zai iya bakin kokarinsa wajen bada magunguna waɗanda za su rage zafin cutar.

To magungunan gargajiya fa? Abun sani anan shine, duk wanda yake jinyar mai ɗauke da cutar sankara, fatansa ne a samu sauki da wuri saboda mai cutar ta daina shan wahala. Abin takaici shine, cigaban da aka samu akan  shawo kan cutar a kimiyyance bai taka kara ya karya ba. Amma duk da haka, yafi amfani nesa ba kusa ba, yafi rashin cutarwa, kuma yafi tabbaci fiye da kowane irin hanyar magani da wani ko wata zai zo miki dashi a yanzu. A karshe, mutum zai iya taimakawaa ckin  binciken samo maginin da yafu na yanzu aiki ta hanyar ba da gudunmawa da haɗin kai ga masu bincike a asibiti.

Yana da mutukar amfani mutum ya je asibiti da wuri da zarar ya lura da waɗansu canje-canje don neman magani.

Bincike Da Yadawa:
Gidauniyar Musulunci Ta Al'azmiyya (Al'azmiyyah Islamic Foundation Kano)

Friday, 17 May 2019

TASIRIN AZIMI GA LAFIYAR JIKI

TASIRIN AZIMI GA LAFIYAR JIKI

Mai Gabatarwa: Auwal Zakari Ayagi
Chairman Al'azmiyyah Islamic Foundation

Da sunan Allah Mai yawan Rahama Mai yawan Jikai. Tsira da Aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad Salallahu Alaihi wasallam.

A yau da yarda Allah cikin wannan Zure zan dan kawo bayani mai taken: TASIRIN AZIMI GA LAFIYAR JIKI.

Dafatan zamu amfana da abin da zamu ji kamar yadda na tattaroshi.

Shi dai Azumi ya na wajaba ne a kan mutum mai cikakkiyar lafiya, lafiya ta hankali da lafiya ta jiki, ba ya halatta ga mara Cikakkaiyar lafiya ko kuma  yaro karami.

Wannan shi ya sa a addinance da kuma a likitance ba kowa ne aka yarda ya yi azumi ba. Duk da haka kuma, akwai marasa lafiyar da azumi kan yi wa amfani sosai wadanda su ma za a yi dan bayanin amfanin azumi a gare su.

Ilimin likitanci ya tabbatar da cewa yin Azimi yana daga mafi muhimmancin hanyar da mutum zai samu lafiya, kuma abu ne na tilas a rayuwar mutum ga wanda yake son lafiyarsa ta inganta.

Hikimar Allah madaukaki ta tabbatar da cewa hatta dabbobi suna barin cin abinci na wasu kwanaki a shekara don samun daidaito a rayuwarsu da lafiyar jikinsu, masu dabbobin sukan dauke shi wani lokaci a matsayin rashin lafiya alhalin lafiyar dabbobin lau.

Bincike ya nuna cewa kowace dabba tana da wata marhala da dole ne ta takaita cin abinci a cikinta don samun daidaito a lafiyar jikinta.

Littattafan Hindu, Buda, da Barahima suna dauke da bayanai cike da hikimar yin azumi irin nasu, gwargwadon koyarwar da addinansu suka nuna.

Abu Karat da ya zo kafin haihuwar Annabi Isa (A.S) da shekara 500, yana daga cikin mutanen da suka shahara da yin maganin cututtukan mutane ta hanyar sanya su yin azumi.

Don haka ne yin azumi ya zama wani lamari ne na fidirar halittar dukkan halittu masu jiki don samun cikakkiyar lafiyarsu, kuma duk wata halitta mai jiki tana samun wani lokaci da jikin zai tilasta mata dakatar da cin abinci ko da kuwa ta hanyar rashin lafiya ne don samun hutu da annashuwa da sabuwar rayuwa ga kwayoyin halittar jikin.

Karanta cin abinci yana sanya hutun hanji da yake takura ciki da sanya yawan maiko da kiba su taso su kange kirji ta yadda huhu zai kasa numfasawa cikin annashuwa, don haka ne ma mutane da yawa sukan samu dama a lokacin azumi don su dawo da kansu daidai da tsara cikinsu da rage kibarsu don samun sa'ida da walwalar jiki.

Akwai bayanai masu yawa na likitanci da suke nuna karantuwar gubar da take a cikin abinci da fitar ta daga jikin mutum sakamakon yin Azumi, sai dai da yake ni ba likita ba ne, yana da kyau mu koma wajen likitoci mu samu gamsassun bayanai masu yawa.

Na tattara bayanai masu yawa kan wannan lamarin, sai dai ba ni da lokacin da zan iya kawo su cikin wannan gajeriyar Mukala ga mai bibiyar Shafin ZAMANTAKEWA, amma ina fatan  kadan din ma zai wadatar matukar za a iya yin aiki da shi.

Azumi yana taimakawa wurin kona sukari, da man da ke cikin hanta da jini da fata, don samun lafiyar zuciya. Akwai bayanai masu yawa da likitoci irin su; Mark Pardon, Cases Karyl, Micheal Angilo, Dakta Muhammad Sa'id Suyuti, Dakta Muhammad Arrawi, da sauran manyan likitocin duniya suka yi kan wannan lamarin da yake nuna matukar mahimmanci da wajabcin Azumi ga rayuwar mutum.

Mutumin da yake jahiltar sirrin jikinsa sai ya dauka yunwa zata illa ta shi ne sakamakon yin Azumi, alhalin yana da ajiyayyen sukari da yake samun amfanin jiki a matsayin gulokojin da aka ajiye a hantarsa wanda zai iya amfana daga gare shi tsawon lokaci, sannan sai ya karkata ga ajiyayyun mai da yake jikinsa, wannan shi ne sirrin da ya sanya zamu ga mutum yana iya amfani da ruwa har kwanaki 40. Sai kuma jiki ya koma tara wasu sinadirai sakamakon hakan ya sake amfani da su don gina gabobinsa da daidaita tsarin rayuwarsu a lokacin Azumi.

Sai dai duk da muhimmancin Azumi ba a yarda kuma a wuce gona da iri wurin yunwata kai ba, don haka daidaito shi ne abin nema. Dreanik (a 1964) da masu taimaka masa sun kawo bayanai masu hadari ga jiki idan ya ci gaba da yunwatuwa tsawon lokaci da ya wuce kwanki 30 – 40.

A nan ne zamu ga hikimar shari'ar musulunci da ta yarda mutum ya yi azumi 30 ne kawai. Lallai tafarkin Addinin Manzon Allah (SAW) ne kawai ya yi daidai da ilimi a wannan fagen kamar yadda zamu iya gani.

A nan ne zamu ga kimar fadin jagoran halittu Annabin rahama (SAW) yayin da yake cewa: "Ku yi Azumi kwa yi lafiya". Lallai fa'idar yin azumi ga lafiyar jiki ba ta kirguwa, kuma ni'ima ce da Allah ya yi wa dan adam da bai san iyakarta ba, don haka ne littafin Allah yake nuni da cewa: "Don ku gode wa Allah kan abin da ya shiryar da ku…'. Domin ba don ya shiryar da mu ga wannan hanyar ta samun lafiya ba, da babu wani wanda zai iya shiryar da mu gare ta.

Bahasosin Holbrook, Dewey, Wilcod, Shelton, H. Lutzner, Morgulis, da tattaunawar Ecosse, da  makamantansu duk sun tabbatar da cewa; Azumi yana da muhimman abubuwa da babu wai magani da yake da su da suka hada da:

1.      Hutun jiki da dawowar asalin kwayoyin halittarsa.

2.     Dakatar da tsotsar sinadirai da suke ragewa a hanji da zubar da ita domin dadewarta a jiki zai iya mayar da ita guba.

3.     Dawo da ayyukan gabobi da nishadin su da daidaita ayyukansu.

4.     Narkar da sinadaran da suke kari ne a jiki da kona su.

5.     Dawowa da rayuwar kwayoyin jiki da samartaka.

6.     Kiyaye daidaiton karfin jiki.

7.     Gyara gabobin narkar da abinci a jiki.

8.     Bude kwakwalwa da kara hazaka.

9.     Tsaftace da tsarkake fata.

10.   Daidaita bugawar jini da narkar da kitse.

Da sauran abubuwa da ba a kawo su ba.

Don haka ne tun da har zuwa yau, kwararrun likitoci suka yi maganin manyan cututtuka ta hanyar yin Azumi. Wannan yana kara mana imani da dokokin da Manzon Allah mai daraja da gaskiya ya zo mana da su yayin da yake cewa: "Uwar hanji ita ce gidan dukkan cuta, kariya (riga kafi) ita ce babban magani".

Mutumin da yake son zaman lafiyarsa daram shi ne wanda zai lura da me yake ci, yaushe zai ci, yaya zai ci, nawa zai ci, da sauran mas'aloli irin wannan.

Don haka Annabin rahama (SAW) ya karbi kyautar Mariya daga Mukaukis na Masar, amma ya mayar da likitoci, yana mai ba shi amsa da cewar; Mu mutane ne da ba ma ci sai mun ji yunwa, kuma idan muka ci ba ma cika ciki. Sai wannan ya zama wata fomula mai daraja da likitocin Masar suka yi riko da ita a wancan lokaci suna mamakin wannan hikimar da suka yi amfani da ita wurin warkar da cututtukan da suka addabi al'ummarsu.

Haka nan likitoci sukan tilastawa wanda za a yi wa wata babbar tiyatar aiki ko ba ta hanji ba, a ce ya yi azumi kafin tiyatar saboda a lokacin jiki ya samu ya huta daga duk wata hayaniyar yau da kullum ta stress da sauransu. Sai an dora mutum a teburin tiyata ne kawai ake sa masa ruwan sukari.

Ita kuma hanta kan fito da abincin da ta tara (irinsu sinadaran glycogen da fatty acid na kitse) don jiki ya sarrafa su zuwa sukari wanda yake ba da kuzari na dan wani lokaci don amfanin jiki, domin ita hantar ta fara shirin ajiye sabo.

Haka nan ban da wadannan sinadarai akwai gubar da ke cikin hantar da ake fitarwa tare da su wadannan sinadarai. Wannan ma kadai kan kara lafiyar hanta.

Hakanan masu cutar hawan jinni, hawan jini kan kara sassaituwa a wasu mutanen yayin azumi, kamar yadda binciken masana da dama yakan nuna. Misali, wani likita dan kasar Amurka mai suna Dr. Goldhamer da ya kware a bincike kan azumi, ya yi nazarin amfanin azumi ga masu hawan jini. A cikin mutane masu hawan jini da ya gwada yayin da suke yin azumi, kashi 98 cikin 100 ba su bukaci magungunansu ba a tsawon ranakun da suka dauka suna azumi na wasu awoyi, wato azumi kawai ya sassaita hawan jinin nasu. Amma dai hakan ba ya nufin mutum ya ajiye maganin ya daina sha gaba daya, sai likita ya auna ya ce a huta.

Sai kuma masu ciwon suga, su ma azumi kan sassaita yawan sugan jikinsu, sai dai akan shawarce su da su rika yin amfani da na’urar auna suga a kullum saboda sugar zai iya yin kasa sosai su galabaita. Sai dai ana so mai ciwon suga mai amfani da allurar insulin ya shawarci likitan da ke ganinsa ko zai iya azumi, kuma ta yaya zai sassaita allurar saboda bambancin lokacin cin abinci.

Ga masu shan miyagun kwayoyi da taba sigari, azumi na daya daga cikin hanyar horar da kwakwalwa barin sabo da su. Ga mai so ya daina wannan dabi’a, azumi zai iya taimakonsa kwarai da gaske.

Amma kuma akwai wadansu larurori wadanda a addinance ba a dora wa masu su azumi ba, a likitance ma haka. Wadannan sun hada da marasa lafiyar da sai an kwantar an tayar wadanda basu san halin da suke ba, da wadanda suke kwance ake yi wa karin ruwa, tun da ruwan da abinci a ciki, da masu cututtukan da magungunansu dole a sha duk bayan ’yan awoyi da masu gyambon ciki da dai sauran ire-irensu.

Masu juna biyun ko masu shayarwa su ma sukan galabaita ko su ba abin da suke dauke da shi wahala, idan suka yi azumi. Akwai dai masu irin wadannan larurori da ke bukatar fatawa ta malamai makusanta da su don a tabbatar za su iya azumi ko akasin haka.
Wannan shine kadan daga dan abin da na binciko, dafatan zamu amfana da wannan dan takaitaccen bayani.

Wassalamu Alaikum Warahamatullah

Dafatan za mu sha Ruwa Lafiya.

11 ga Ramadan 1440
16/5/2019

Auwal Zakari Ayagi
07038775781
auwalzakari@gmail.com
http://sautulazmiyyah.blogspot.com/?m=1