Saturday, 8 October 2022

HASKEN RAYUWATA: TARIHIN MANZON ALLAH SALALLAHU ALAIHI WASALLAM



HASKEN RAYUWATA

Tarihin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam

Rayuwa, Darussa Da Qyawawan Halaye

 

Wallafar

COMRADE AUWAL ZAKARI AYAGI

(Barden Ayagi)

Haqqin Mallaka (M)

Auwal Zakari Ayagi (Barden Ayagi)

Lambar Waya:         07038775781

Bugu Na Xaya         2026/1447

 

TSARAWA DA BUGAWA

Al-Azmiyya Islamic Foundation: No. 313 Al’Mustapha House Kadawa Western Bypass AL’EEMAAN Medicine Store Building, Adjacent to Gwarzo Road Kano.

E-mail: auwalzakari@gmail.com

www.sautulazimiyya.blogspot.co.uk/

GSM:  07038775781, 08023615685


SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan Littafi ga Mahaifana Marigayi Alhaji Zakari Muhammad Usman Ayagi (Allah ya gafarta masa) da Mahaifiyata Hajiya Rakiya Usaini Lawan (Inna) Allah ya qara mata Lafiya, Amin.

 GODIYA

Da sunan Allah mai yawan Rahama Mai Jin qai, Tsira da Aminci su qara tabbata ga shugaban halitta Annabi Muhammad Tsira da Aminci su qara tabbata a gareshi.

Da farko, ina miƙa godiya ta musamman ga Allah Maɗaukakin Sarki, wanda Ya bani ikon kammala wannan littafi cikin salama da nutsuwa. Shi ne Mai bai wa bawa ƙarfin tunani, hikima da nutsuwar zuciya, Ya kuma bayyana masa abin da zai amfane shi da alumma.

Godiya ta musamman ga abokai, dalibai da dangi, waɗanda a lokuta daban-daban suka ba ni shawara, goyon baya da addu’a. Hakan ya taimaka matuƙa wajen sauƙaƙa wannan rubutu, da bincike da kuma tsara littafin yadda ya kamata.

Ina kuma godewa masu karatu, waɗanda su ne ginshikin dalilin rubuta wannan littafi. Idan aka sami kura-kurai a ciki, ina roƙon a sanar da ni domin gyara. Idan kuwa aka samu daidai, ina roƙon Allah Ya sanya wannan aiki cikin abin da ake rubutawa a mizani na ranar sakamako.

Allah Ya sanya wannan littafi ya amfanar da kowa, ya kuma zamo hanya ta ƙarin ilimi da tsaftace Imani.

Auwal Zakari Muhammad Ayagi

 (Barden Ayagi)

22 ga Jumada Akhir 1447= 14/12/2025


 ABUBUWAN DA KE CIKI

– Sadaukarwa………………………………………..
– Godiya……………………………………………..
– Ta’aliqi…………………………………………….
– Abubuwan da ke ciki………………………………
– Dalilin rubuta littafin………………………………

– Gabatarwa………………………………………….
BABI NA 1: Nasabar Manzon Allah (SAW)

Nasabar Manzon Allah Ta vangaren Mahaifinsa……...
Nasabar Manzon Allah Ta vangaren Mahaifiyarsa……...

BABI NA 2: Alkunyar Manzon Allah Da Sunayensa

Alkunyar Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam……...
Sunayen Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam……...

BABI NA 3: Haihuwar Manzon Allah (SAW)

Tarihin Haihuwarsa Salallahu Alaihi Wasallam……...
Abubuwan da suka faru yayin Haihuwarsa ……...

Haihuwarsa da Alamomin da suka Bayyana…...
Alamomin Haihuwar Manzon Allah ……...

BABI NA 4: Rayuwar Annabi (SAW) Daga lokacin Shayarwa Zuwa Aikoshi

Shayar da Annabi a Gidan Mahaifiyarsa……...
Zuwansa Gidan Halimatus-Sa’adiyya……...

Tsaga Qirjinsa Salallahu Alaihi Wasallam………………

Rasuwar Mahaifiyarsa……...
Tarbiyya a Hannub Kakansa Abdulmutallib……..

Rayuwarsa a Gidan Abi Talib……………

Aurensa Dan Nana Khadija……...

 Aikoshi da Saqo Salallahu Alaihi Wasallam……………

BABI NA 5: Koyarwar Annabi Salallahu Alaihi Wssallam

Koyarwa akan Ilimi da Tauhidi……...
Bin Koyarwar Annabi (SAW)……...

Koyarwar Annabi a kan Sallah………………

Koyarwar Annabi a kan Azumi……...
Koyarwar Annabi a kan Zakka da kyautatawa……..

Halayen Annabi (Ahlaq)……………

Shugabanci da Tsarin Siyasar Annabi (SAW)………..

BABI NA 6: Mu’ujuzojin Manzon Allah (SAW)

Ma’amnar Mu’ujiza……...
Babbar Mu’ujiza Alqur;ani Mai Girma……...

Mu’ujizojin da Suka Faru tin Yana Qarami………………

Mu’ujizojin Annabi a lokacin Annabta……...
Mu’ujizojin Taimakon Allah……..

Isra’I da Mi’iraji……………

Mu’ujizojin Waraka………..

BABI NA 7: Kiran Annabi Zuwa Tauhudi a Makka

Shekaru Uku a voye, Goma a Bayyane……...
Farkon wadanda suka amsa kira……...

Ayyukan Annabi (SAW) a shekaru Goma………………

BABI NA 8: Hijirar Manzon Allah (SAW)

Ma’amnar Hijira……...
Dalilan yin Hijira……...

Zamansa a kogon Thawr………………

Tafiyarsa Daga Makka zuwa Madina……...
Shigar Manzon Allah Madina…….

Mahimman Abubawan da suka faru Bayan Hijira…..

Mahummancin Hijira a Musulunci………………….

BABI NA 9: Yaqoqin Manzon Allah (SAW)

Adadin Yaqe-yaqen Manzon Allah……...
Jerin Yaqe-Yaqen Manzon Allah……...

Hikimar Yaqe-Yaqen Manzon Allah………………

BABI NA 10: Matayen Manzon Allah (SAW)

Matayen Annabi da Matsayin su…………………….
Jerin Matayensa da Falalarsu……...

BABI NA 11: ‘Ya’yayen Manzon Allah (SAW)

‘Ya’yayen Manzon Allah Maza……...
‘Ya’yayen Manzon Allah Mata……...

Fadimatuz-Zahara da Aurenta da Sayyadi Aliyu………

BABI NA 12: Ammomin Manzon Allah (SAW)

Ammomin Manzon Allah Maza……...
Ammomin Manzon Allah Mata……...

BABI NA 13: Masu Hidima Manzon Allah (SAW)

Hadiman Manzon Allah Maza……...
Mawaqan Manzon Allah Mata……...

Masu Kiran Sallar Manzon Allah………

BABI NA 14: Siffofi da halayen Manzon Allah (SAW)

‘Ya’yayen Manzon Allah Maza……...
BABI NA 15: Wafatin Manzon Allah (SAW)

Farkon Rashin Lafiyar Manzon Allah Maza……...
Wafatin Manzon Allah Mata……...

Darussa daga Wafatinsa (SAW)………

Kammalawa……………………………………………

 

 DALILAN RUBUTA LITTAFI

Rubuta wannan littafi na tarihin Manzon Allah Annabi Muhammadu ya samo asali ne daga tsantsar so da ƙauna ga shugaba, jagora, da abin koyi a rayuwata. Tsananin soyayyar da biyayyar da nake yi ga Manzon Allah ya sanya ni ƙudur ci niyar da na rubuta wani abu akan rayuwarsa, da kyawawan dabi’unsa, da darussan da al’umma zasu koya a tarihin sa shugaba Alaihissalam.

Wannan littafi ba kawai tarihi bane, a’a akwai darussan da za’a koya cikin tarihin shugaban mu Annabi . Haka zalika wannan rubutu babban abin alfahari ne a gare ni da cewa na rubuta wani abu kan masoyina Manzon Allah , wanda soyayyar sa da koyarwarsa ta mamaye zuciyata.

Dalilin rubuta littafin ya haɗa da:

Yaxa sunan Manzon Allah da koyarwarsa ga matasa da dukkan al’umma.

Koyar da darussa da kyawawan halayensa domin koyi da shi a rayuwar yau da kullum.

Gina soyayya da biyayya ga Annabi ta hanyar kalmomi da labarin rayuwarsa ga Matasanmu dama dukkan Al’umma..

Rubutun wannan littafi ƙoƙari ne na musamman don nuna soyayya, girmamawa, da alfahari da kasancewa cikin masu bada gudummawa wajen isar da rayuwar Annabi ga masu karatu.

Wassalamu Alaikum.

GABATARWA

Alhamdulillah, wannan littafi na rubuta shi ne domin bayyana rayuwa, siffofi, kyawawan dabi’u, da koyarwar Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam shugaba, jagora, masoyin zukatanmu. Tsananin soyayya da girmamawa da nake yi ga shugaba Alaihissalam shi ya sanya ni ƙuduri na rubuta wannan littafi, domin na yaxa rayuwarsa da darussan dake ciki, na shiriya, domin ilmantar da al’umma musamman matasa da Mata.

Rubutun wannan littafi na tarihin rayuwar Ma’aiki Alaihissalam, baban abin alfahari ne kasancewa ta marubucin da ya rubuta wani abu akan masoyi kuma xan gatan Allah. Wannan littafi yana ɗauke da tarihi daga haihuwarsa, rayuwar Annabta, hijira, zaman Madina, yaƙe-yaƙe, zuwa wafatinsa, har ma da kyawawan dabi’u da siffofin da suka zama abin koyi ga dukkan Musulmi.

Ina fatan duk mai karatu zai sami shiriya da farin ciki, da karfafa imani daga wannan littafi, kuma ya koyi yadda zai bi koyarwar Annabi a rayuwar yau da kullum.

“Lallai haƙiƙa Manzon Allah abin koyi ne mafi kyau ga ku.” (Suratul Ahzab: 21)

Wassalamu Alaikum.

Auwal Zakari Ayagi

(Barden Ayagi)

BABI NA XAYA

NASABAR MANZON ALLAH SALLAHU ALAIHI WASALLAM

Nasabarsa Ta Vangaren Mahaifinsa

Shine: Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muṭṭalib (ana kiransa da Shaybatul Hamd) ɗan Hāshim (ʿAmr) ɗan Abdu Manāf (Al-Mughīra) ɗan Qusayy (Zayd) ɗan Kilāb ɗan Murrah ɗan Kaʿb ɗan Lu’ayy ɗan Ghālib ɗan Fihr (wanda ya zamo shugaban Quraysh, shi ake kira Quraysh) ɗan Mālik ɗan An-Nadr ɗan Kinānah ɗan Khuzaymah ɗan Mudrikah (ʿĀmir) ɗan Ilyās ɗan Muar ɗan Nizār ɗan Maʿadd ɗan ʿAdnān.

Nasabarsa Alaihissalam da ta haɗa har zuwa ga Annabi Ibrahim (AS)):

Adnān ɗan Udd ɗan Muqawwam ɗan Nāḥūr ɗan Tayra ɗan Yaʿrub ɗan Yashjub ɗan Nābit ɗan Is’hāq ɗan Ibrāhīm (Khalīlullāh) ɗan Āzar (Tāri) ɗan Nāḥūr ɗan Sārūgh ɗan Arghū ɗan Fāliq ɗan ʿĀbir (Hud AS ko Eber) ɗan Sālih ɗan Arfakhshad ɗan Sam ɗan Nūḥ ɗan Lamk ɗan Matushailah ɗan Idrees (Hannūkh AS) ɗan Yard ɗan Mahlāīl ɗan Qainan ɗan Anūsh ɗan Shīth ɗan Ādam (AS).

 

 

1.   Maxauka a zuriyar Banu Hāshim

  Muhammad (SAW)

  Abdullāh

  Abdul-Muṭṭalib

  Hāshim

  Abdu Manāf

  Quayy

2. Asalin Quraysh:         Fihr shi ne Shugaban Quraysh gaba ɗaya.

3. Asalin Larabawa Adnāniyya: Daga Maʿadd zuwa ʿAdnān shi ne uban Larabawan Arewa.

4. Nasaba zuwa Annabi Isma’il (AS): Adnān daga zuriyar Ismāīl ɗan Ibrāhīm (AS).

Malamai sun ce: “Abin da ya tabbatar sahihi daga Manzon Allah shi ne nasabarshi ta kai daga Muhammad zuwa Adnān. Bayan Adnān ana dogaro ne da ruwayoyi na tarihi, ba duka suka kai matsayin sahihanci ba.”

NASABAR MANZON ALLAH (SAW) TA BANGAREN MAHAIFIYARSA – ĀMINAH

Muhammad (SAW) ɗan Āminah bint Wahb, ya ga Wahb bn ʿAbd Manāf, ɗan Zuhrah bn Kilāb, ɗan Murrah bn Kaʿb, ɗan Lu’ayy bn Ghālib, ɗan Fihr bn Mālik, ɗan An-Nadr bn Kinānah, ɗan Khuzaymah bn Mudrikah, ɗan Ilyās bn Muar, ɗan Nizār bn Maʿadd, ɗan Adnān

Daga nan zuwa sama:

Adnān ɗan Udd ɗan Muqawwam ɗan Nāḥūr ɗan Tayra ɗan Yaʿrub ɗan Yashjub ɗan Nābit ɗan Ismāīl (AS) ɗan Ibrāhīm (AS) ɗan Āzar (Tāri) ɗan Nāḥūr ɗan Sārūgh ɗan Arghū ɗan Fāliq ɗan ʿĀbir ɗan Sālih ɗan Arfakhshad ɗan Sam ɗan Nūḥ (AS) ɗan Lamak ɗan Matushailah ɗan Idrees (Hannūkh) ɗan Yard ɗan Mahlāīl ɗan Qainan ɗan Anūsh ɗan Shīth ɗan Ādam (AS).

MUHIMMAN BAYANAI GAME DA DANGIN MAHAIFIYARSA ĀMINAH (RA):

1. Ƙabilarsu ta Zuhrah

  Āminah tana daga ƙabilar Banū Zuhrah, ɗaya daga cikin manyan rassan Quraysh.

  Shi ma Kilāb bn Murrah uban su ne, wanda ya haɗa nasaba da na Manzon Allah ta wajen mahaifinsa.

2. Kyakkyawan asalinta

Malamai sun yi ittifaqi cewa dangin Banū Zuhrah suna cikin mafiya daraja da ƙima a Quraysh tun kafin Musulunci.

3. Dangantakar ta da Manzon Allah (SAW)

  Nasabar mahaifiyar sa da ta mahaifin sa sun haɗu ne da:

Kilāb bn Murrah

Wannan yana nufin Annabi Muhammad (SAW) da mahaifiyarsa suna da nasaba mai kusanci a cikin Quraysh.

 

BABI NA BIYU

ALKUNYAR MANZON ALLAH SALALLAHU ALAIHI WASALLAM DA SUNAYEN SA TSARKAKA

ALKUNYAR MANZON ALLAH (SAW)

Manzon Allah (SAW) yana da alkuniya guda biyu mafiya shahara:

1. Abul-Qāsim (أبو القاسم)

Uban Qāsim saboda ɗansa Qāsim wanda ya rasu tun yana ƙarami.

2. Abū Ibrāhīm (أبو إبراهيم)

Saboda yana da ɗa mai suna Ibrāhīm daga ƙwarqwararsa Mariya tul-Qibiyya.

Sauran alkunyoyi da malamai suka ambata:

Abū ʿAbdillāh saboda sunansa Muhammad ɗan Abdullāh

Abū Ṭāhir daga ɗa mai suna Ṭāhir/ayyib

Abū ayyib – wannan ma daga laƙaban ɗansa

Amma mafi inganci kuma mafi shahara a hadisi shi ne: Abul-Qāsim.

Akwai hadisi da Annabi (SAW) ya ce:

“Ku sanya sunana amma kada ku sanya alkunyata.”

Domin Abul-Qāsim na musamman ne a gare shi.

SUNAYEN MANZON ALLAH (SAW)

An ambaci sunayensa da dama a Qur’ani da Sunnah. Mafi shahara su ne:

 1. Muhammad محمد)

Wanda ake yawaita yabonsa.

An ambace shi a Qur'ani: “Muhammadun rasūlullāh.

2. Ahmad (أحمد

Wanda ya fi kowa godiya ga Allah.

Annabi Isa (AS) ya yi busharar zuwansa da sunan Ahmad.

3. Al-Māhi (الماحي)

Mai gogewa — wanda Allah ya share kafirci da shi.

4. Al-Hāshir (الحاشر)

Mai tara mutane — domin mutane za a tattaro a kan tafkonsa a ranar kiyama.

5. Al-ʿĀqib (العاقب)

Wanda ya zo a ƙarshe, babu wani annabi bayansa.

6. Al-Muqaffā (المقفى)

Mai biyo bayan annabawa.

7. Nabiyyur-Rahmah (نبي الرحمة)

Annabin rahama.

8. Nabiyyut-Tawbah (نبي التوبة)

Annabin tuba da gafara.

9. Nabiyyu al-Malhamah (نبي الملحمة)

Annabin yakin kare adalci (ba zalunci ba).

10. Rasūlullāh, Nabiyyullāh

– Manzon Allah, Annabin Allah.

11. Al-Mustafa (المصطفى)

Wanda aka zaɓa.

12. As-Sādiq Al-Amīn (الصادق الأمين)

Mai gaskiya, amintacce.

(Wannan ya kasance lakabinsa tun kafin aiko shi da Manzanci).

 

BABI NA UKU

TARIHIN HAIHUWAR MANZON ALLAH (SAW)

Lokacin da aka haife shi: An haifi Manzon Allah Muhammad (SAW) a Ranar Litinin, cikin Watan Rabi’ul Awwal, Shekarar da ake kira “Shekarar Giwaye” (‘Āmul-Fīl), a cikin birnin Makka.

Shekarar Giwaye: Ita ce shekarar da Abrahah ya kawo giwaye domin ya rusa Ka’abah, amma Allah ya halaka su da tsuntsaye kamar yadda Allah ya ambata cikin Suratul Fīl.

Shekarar Haihuwar sa ta Miladiyya: Mafi yawan malamai sun ce: a shekara ta 570 Miladiyya, wasu kuma suna cewa 571 CE.

Malamai sun yi sabani, An kawo ra’ayoyi da dama, amma babu wani hadisi sahihi da ya tabbatar da takamaiman kwanan watan haihuwarsa. Amma akwai shahararrun ruwayoyi guda huɗu:

(1) Ruwayar da ta fi shahara: 12 ga Rabi’ul Awwal

Wannan shi ne abin da yawancin malamai na fiƙhu da tarihin Musulunci suka ɗauka, musamman a al’ummomin musulmi.

Amma ya samo asali ne daga ruwayar Ibn Ishaq wadda ba ta kai matsayin sahihi ba.

Saboda haka 12 ga Rabi’ul Awwal ruwaya ce ta tarihi, ba tabbataccen dalili na hadisi ba ne.

(2) Ra'ayin da ya fi ƙarfi a wurin masana: 8 ga Rabi’ul Awwal

Wannan ya fi kusanci da inganci, daga Ibn Kathir da Ibn Hajar da Ibn Abdil Barr, wadanda su na daga cikin malaman da suka ƙarfafa wannan kwanan.

 (3) Wasu malamai sun ce: 10 ga Rabi’ul Awwal

 (4) Ra'ayi mafi rauni: 2 ga Rabi’ul Awwal

Me yasa aka samu sabani?

Dalilai uku:

1.       A lokacin Jahiliyya ba a daidaita tsarin kalandar wata ba.

2.       Babu sahihin hadisi da ya ce ranar kaza aka haife shi.

3.       Ibn Ishaq (marubucin Seerah) bai tabbatar da kwanan rana da isnad mai ƙarfi ba.

Lokacin da aka haife shi cikin yini

Ruwayoyi sun nuna: An haifeshi Alaihissalam da sassafe wato da (asubah). Ko kuma attsakar dare zuwa asuba.

KARIN BAYANI:

Hadisin da ya fi ƙarfi:

Abu Qatada ya ruwaito cewa Manzon Allah (SAW) ya ce:

"Ana tambayarshi game da azumin Litinin, sai ya ce:

'Wannan rana ce da aka haife ni, kuma rana ce da aka sauke mani wahayi.'"

(Sahih Muslim)

Wannan shi ne hujjar gaskiyar ranar Litinin, amma kwanan wata ba a fayyace ba.

Haihuwarsa Alaihissalam

Mahaifiyarsa Aminah bint Wahb ta haife shi a gidanta na Banū Hāshim a Makka.

ABUBUWAN DA SUKA FARU YAYIN HAIHUWAR MANZON ALLAH (SAW)

1. An haife shi a ranar Litinin: Wannan shi ne ingantacce sahihi, kamar yadda ya fada:

An haife ni a ranar Litinin.”

(Sahih Muslim)

2. Haske ya futo daga mahaifiyarsa (Aminah): Aminah (RA) ta ruwaito cewa: “Na ga wani haske ya fito daga gare ni, ya haskaka mini gidajen Shaam.”

(Ibn Sa’d, Ibn Ishaq – ruwaya mai karfi a tarihi)

Ma’ana: Wannan alama ce ta cewa zai zama Annabi ga duniya, hasken da zai watsu ya zarce Arabia har Sham.

3. Wutar masarautar Fāris ta mutu bayan shekaru 1,000 tana ci: A masarautar Persia, akwai wuta mai suna Ātash Bahram da take ci ba tare da ta an kasha ta ba na tsawon shekaru, amma A daren haihuwar sa ta mutu gaba ɗaya.

Wannan ruwaya ce ta tarihi, malamai suka karɓa domin ba ta yi karo da hankali ba.

4. Karyewar manyan tagogi 14 na fadar Kisra (Sarkin Persia): Wani babban gini mai tagogi 14 ya kakkarye ba tare da wani abu ya buge shi ba.

Malamai sun ce waɗannan tagogi 14 suna nuni da sarakunan Persia 14, waɗanda mulkinsu zai shuɗe kafin Musulunci ya rinjaye.

5. Kogin Samawah da ya bushe, sai ga ruwa ya cika shi: Wani kogi ne a ƙasar Persia wanda ya shekara yana bushe, sai gashi ya cika da ruwa a daren haihuwar sa.

Wannan Ruwaya ce ta tarihi mai karɓuwa.

6. Gumakan Quraysh sun fadi ko sun rushe: A cewar ɗan Abbas da wasu daga cikin Tabi’ai, gumakan da Quraysh suke bautawa sun faɗi kasa a fadar sa. Wannan alamar bacewar bautar gumaka ne , da bayyanar tauhidi.

 7. An haife shi yana wankakke kuma cikin tsabta

An ruwaito cewa: An haife shi cikin tsarki, babu datti a jikinsa, kuma yana da alamar hatimin annabci a bayansa.

Ruwaya mai kyau (Ibn Hajar ya karɓa).

8. An haife shi ba tare da jini da kazanta ba

Malamai sun ce: “An haife shi ba tare da al’adar haihuwa da jini ko kazanta ba.”

Wannan alama ce ta tsarkin Annabci.

9. An hanguo haske zuwa sama yayin hauhawar sa

Wasu suka ce: Haske ya yi sama zuwa sararin samaniya a daren haihuwarsa.

Ruwayar tarihi ce.

10. Sheɗan ya yi ƙara, kuma an katse satar ji a sama da ƙasa, A lokacin haihuwarsa: Aljannu ba su sake satar ji daga sama ba. Haske ya rufe sama, kuma ƙasashen gabas suka ga wani haske mai ban mamaki.

11. An kira shi da sunan “Muhammad” tun kafin a zuwan shi. Kakan sa Abdu-lMuttalib ya yi mafarki yana ganin cewa: Za a haifi yaro wanda zai shahara a duniya da sama.

Don haka ya sa masa suna Muhammad – “Abin yabawa.”

 

HAIHUWAR MANZON ALLAH DA ALAMOMIN DA SUKA BAYYANA A CIKINSA

A ranar da Allah Madaukakin Sarki ya kawo fitilar halitta, Sayyidina Muhammad ɗan Abdullah ɗan Abdul-Muṭṭalib, duniya ta karɓi jariri wanda babu kamarsa cikin halitta da kamala. Tun kafin a haife shi, alamomin Nnubuwa da tsarkinsa sun bayyana a cikin Mahaifiyarsa, Sayyida Āmina bint Wahb.

An Haife Shi a Tsarki da Kyau Mai Wuce Misali

Malamai da dama sun kawo riwayoyi game da yanayin haihuwarsa, wasu sahihai ne, wasu raunana, amma duk suna nuni da cewa haihuwar Annabi ba ta yi kama da ta kowa ba.

1. Game da an haife shi da Kaciya (Shayi)

Wasu malamai sun rawaito cewa:

An haifi Manzon Allah yana makutu — wato cikin yanayin da al'aurarsa ta riga ta yanke kamar wanda aka yi masa kaciya.”

Wannan ra’ayi an kawo shi a cikin wasu littattafan tarihin Annabi kamar:

Dalāil al-Nubuwwa na al-Bayhaqī

Khaṣāis al-Kubrā na Suyūṭī

Amma masana sun bambanta:

Wasu sun ce wannan ba hujja sahihiya ba ce, saboda a sahihan hadisai babu wannan tabbatacciyar magana.

Wasu kuma sun ce koda kuwa bai kasance an haife shi ne da kaciya ba, an yi masa kaciya ne a ranar bakwai kamar sauran ’ya’yan Larabawa.

Saboda haka, a salon littafi, ana bayyana haka:

Daga cikin alamu masu girma da aka nakalto a littattafan tarihin Annabi, akwai cewa an haife shi a tsarkake, babu datti, babu ƙazanta, har ma wasu sun rawaito an haife shi da kaciya, kamar wanda malaiku suka yi masa tun daga sama.

2. Ya zo Da Kwalli a Idanunsa

Da yawa daga wasu malamai sun nuna cewa idanun Annabi tun haihuwarsa suna da kyalli na musamman, kamar wanda aka shafa masa kwalli, saboda tsarkin halittarsa da annuri da ke fizgarwa daga idanunsa.”

A hakikanin ilimi, abin da ya tabbata shi ne:

Idanun Annabi sun kasance masu sheƙi, baki masu kyau, suna burgewa ga mai kallo kamar yadda sahihi ya zo a Shamāil Muhammadiyya.

 

3. Yazo Shafe Da Mai Da Kyalli a Jikinsa

Wannan kuwa tabbatacce ne cikin sifofinsa (Shamāil). An ce: Jikinsa yana fitar da ƙamshi mai dadi. Gashin kansa yana kyalli. Fuskar sa tana walwali kamar wata xan daren sha huxu. Bakin sa da jikinsa suna fitar da qamshi mai daxi fiye da turaren miski.

“Jikinsa ya kasance tamkar an shafe shi da mai mai tsarki; yana sheƙi, yana ƙamshi, yana kyalli. Duk wanda ya zauna kusa da shi, sai kamshin Annabi ya lullube shi.

ALAMOMIN HAIHUWAR MANZON ALLAH

A lokacin da Aminah ta ji haihuwa ta gabato, ba ta wahalta ba kamar yadda mata ke yi.

A ruwayar Aminah:

Da na haife shi, haske ya fito daga cikina ya haskaka min gidajen Busra a Sham.”

Nan take jaririn ya fito, tsaf, tsare, cike da annuri. Babu ƙazanta a jikinsa, babu jinin da ake gani a sauran jarirai. An karɓe shi cikin tsarki da natsuwa.

Wasu riwayoyi sun ce:

An haife shi yana kwance da ƙafafunsa suna katse, kamar wanda aka yi masa kaciya. Idanunsa suna kyalli kamar an shafa masu kwalli.  Jikinsa yana sheƙi kuma yana fitar da ƙamshi. Mala’iku suka sauko suna murna da haihuwarsa.

Fāṭimah bint Asad (uwargidan Abu Ṭālib) ta kasance daga cikin matan da suka taimaka Aminatau a lokacin haihuwar Shugaba Alaihissalam.

An haife shi a cikin riga (wato al'amarin da ba a saba gani ba), alamar kariya daga Allah.

Kakan sa Abdul-Muṭṭalib ya sa masa suna Muhammad, wanda bai saba da shi a cikin Quraysh ba a wancan lokaci.

Bayan kwanaki bakwai, Abdul-Muttalib ya yanka abin yanka har guda bakwai, ya kira mutane suka yi murna da haihuwarsa.

 

 

 

 

 

 

 

 

BABI NA HUXU

RAYUWAR MANZON ALLAH A LOKACIN SHAYARWA ZUWA AIKO SHI

Shayar da Annabi a Gidan Mahaifiyarsa

Bayan haihuwar Manzon Allah a Ranar Litinin, an bada shi ga matar da ta fara shayar da shi, wato Swaybah, baiwar Abu Lahab kamar yadda yake a al’adar Larabawa.

Ita ce ta fara ba shi nono kafin a kai shi ga shahararriyar mai shayarwa wacce duniyar Larabawa ta sani, wato Halimah bint Abu Zuwaib as-Sa’diyyah daga ƙabilar Banū Sad.

Tsarinta mai hankali da nutsuwa ya bayyana tun a lokacin da ta rungume shi, inda ta ce:

Da na ɗauke shi, na ji jikinsa kamar wani haske ne mai sanyaya zuciya, kuma jinin nonona ya fara yawowa.”

Zuwansa Gidan Halimah Sa’diyya – Albarka Ta Farko

Kabilar Banū Sad ta yi suna a wajen shayarwa da tarbiyya, kuma Halimah ce ta yi wa Annabi shayarwa na tsawon shekaru biyu.

Tun daga cikin kwanaki na farko, Halimah da mijinta Harith suka lura cewa:

Rakumarsu ta fara zubar da madara fiye da da.             Awakinsu sun komo daga kiwo sun cika da kiba. Gidansu ya cika da albarka fiye da sauran gidajen makwabta.

Kamar yadda marubucin wannan littafi ta waqe wacce ta Shayar Da Manzon Allah (SAW) wato Halimatussa'adiyya, a wata qasida mai taken:

Halimatus-Sa'adiyya Ta Shayar Da Nura

                     Haltmatus-Sa Adiyya Ta Rabauta A Duniya.

 

1. Farko Nasa Gwani Rabbana Mai Duniya

    Wanda Yai Malaika Can Cikin Samaniya

    Yayi Ruwan Korama Yai Babbarsu Maliya.

 

2. Bayan Nai Basmala Ga Khailikin Auliya,

    Na Daxa Yin Hamdala Ga Rabbana Shi Xaya,

    Wanda Ya Turo Mursalai Don Ceton Duniya.

 

3. Ya Rabbi qara Tsira Ga Khatimul Anbiya,

    Wanda Yake Shugaba ne Ga Dukkann Duniya,

    Don Ya Zamo Zuwansa Duniya Ta Shiriya.

 

4. A Yayin Haihuwarsa Shugaban Duka Anbiya,

    Haske Sai Ya Fece Ya Haske Duk Duniya

    Ya Haska Mana Nan Qasa Ya Haska Samaniya.

 

5. Bayan ‘Yan Kwanaki Da Haihuwar Nabiya,

    Kamar Yadda Can Ga Jamaár Makiyya,

    In An Haifa Musu Xa Sai Su baiwa Balarabiya.

 

6. Taje Da Shi Ta Shayar Tai Tayi Masa Tarbiya,

    To Haka Ma Ya Faru Ga Shugaban Anbiya,

    Sai Aka Nemo Xaya Taje Da Shi Ta Goya.

 

7. Ai Matan Bani Sa’ad Su Suka Zo Makiyya,

    Don Neman Shayarwa Su Samu Kuma Dukiya,

    Sun Hawo Kan Jakuna Sun Taho Gaba Xaya.

 

8. Sunzo Gun Amina Xayarsu Bayan Xaya,

    Suna Yi Mata Tambaya Xa Ne Ko Ko Xiya,

    Mijinki Yana Da Rai Ko Mun Samu Dukiya.

 

9. Sai Ta Furta Da Bakin Ta Tace Da Su Ku Tsaya,

    Shi Wannan Xa Na Wa Ya Zamo fa Maraya,

    Kar Kusa Ran Za Ku Samu Kuxi Da Yawan Tsiya.

 

10. Sai Nan Take Matannan Dukkanninsu Gaba Xaya,

      Sai Suka Sa Takalma Sunka Juya Da Baya,

      Don Sun San Ga Maraya Ba A Samun Dukiya.

 

11. Sai Wata Mata Tazo Kan Jaka Ramammiya,

      Sam Jakar Bata Gudu Duk Itace A Baya,

      Matar Ramammiya Jakar Ramammiya.

 

12. Kai Tafiyar Matannan Sai Kace Hawainiya,

     Don Tsananin Kasala Kana Ga Gajjiya,

     Taje Gurin Aminaa Ta na yi mata Tambaya.

 

13. Ko Kunsan Wacece Jakarta Ramammiya?

      Ta Je Wajen Amina Tana Tayin Tambaya?

      To Wannan Ai Itace Halimas-Sa’adiyya.

 

14. Gata Fara Kyakyyawa A Tsawo Tsakatsakiya,

      Me Fuska Doguwa Kana Shiryayyiya,

      Ga Hakorin Fari Tas Yana Haske Walkiya.

 

15. In Har Tai Muku Murmushi Sai Kuga ‘Yar Walkiya,

      Me Idanu Fari Tas Halimatus-Sa’adiya,

      Baqin Idon Wulik Ne Na Halimatus-Sadiya.

 

16. Amina Tace Mata Da Gani Kin Sha Wuya,

      Kina Bidar Shyarwa Anan Garin Makiya,

      Wallahi Ni A Guna Sai Wannan Maraya.

 

17. Ga Shi Kuma Kin Sani In an xau Maraya,

      In Har Kun Gama Shayarwa Kun Dawo Makiyya,

      Babu Kuxi Masu Yawa Balle Kuma Dukiya.

 

18. Sai Nan Take Tace Mata Halimatus-Sa'adiya,

      Zan Xaukeshi Don Kauna Bawai Don Dukiya,

      Ke Dai Fadan Sunansa In Xauka In Goya.

 

19. Lokacin datan Nufo Shugaban Duka Anbiya,

      Domin Nufin Ta Dauka Ta’azashi Ga Baya,

      Tana Miqo Hannunta Sai Taga Yai Dariya.

 

20. Me Sauraro Saurara Don Yanzu Zaka Jiya,

      Abubuwan Mamaki Nan A Gunta Sa'adiya,

      A Lokacin Da Ta Dau Shugaban Duka Duniya.

 

21. A Nan Take Tai Qiba Halimatus-Sadiya,

       Kamanninta ya Canja Halimatus-Sadiya,

       Sai Kyawunta Ya Qaru Haltmatus-Sadiya

 

22. Suna Zuwa Ga Jakarta Domin Fara Taffiya,

      Sai Jakar Tai Qiba Tana Ta Haniniya,

      Tana Tsalle Da Qara Tana Tayin Dariya.

 

23. A Sannan Bani Sa'ad Sun Wuce Ta Sa'adiya,

      Tintini Sunyi Nisa Sun Wuce Ta Sa’adiya,

      Tana Hawa Jakarta Sai Ta Fara Gudun Tsiya.

 

24. A Nan Take Tai ta Gudu Sai Kace Wata Walkiya,

      Tana tayin Sassarfa Tana Harbi Ta Baya,

      Tana Ta Qarin Sauri Kamar Tana Ninkaya.

 

25. Bani Sa’ad Sun Kace Ga Wata Nan Daga Baya,

      Tazo Ta Wucemu Sai Kace Wata Walkiya,

      Sai Sukace Wallahi Ba Wata Sai Sa’adiya.

 

26. Dabbobinta Sun Yi Qiba Sunyi Nono Sa’adiya,

      Arzikinta Ya Karu Ya Zarce Duk Na Baya,

      A Duniya Da Lahira Ta Rabauta Gaba Xaya.

 

27. Sai Gashi A Bani Sa’ad Ba Kamarta Sa’adiya,

      Wai Don Mene Ta Samu Xaukakar Nan Sadiya,

      Ta Samu Don Ta Shayar Da Shugaban Anbiya.

 

28. Kana Ta Kaunace Kauna ta Gaba Xaya,

      Ta Kaunace shi Don Allah Ba Wai Don Dukiya,

      Ya Zama Lallai Mu Koyi HalimatuSa’adiyya.

 

29. Duk Mai Son Mustafa Da Zuciyarsa Daya,

      Na Rantse Rabbana Zai yaye masa Duk Tsiya,

      Ya Sa Shi A Aljanna Bashi Ba Shan Wuya.

 

30. Na Yi Roko Ya Allah Don Darajar Sa’adiya,

      Ka Arztrta Dukkanin Yan Kungiyar Azmiyya,

      Da Hakikanin Soyayya Ga Shugaban Anbiya.

 

31. Ya Allah Don Darajar Shugaban Duka Anbiya,

      Ka Arzurta Dukkanin Yan Kungiyar Azmiyya,

      Da Arziki Mai Yawa Wanda Babu Hisabiya.

 

32. A Nanne Zan Dakatar Da Begen Kuma In Tsaya,

      Ni Auwal Na Shirya Shugaban Al-Azmiyya

      Wannan Bege Gurinta Halimatus-Sadiya.

 

33. Allah Ka Karbi Wannan Bege Da Na Shirya,

      Ka Mikashi Gareta a Lahira Sa’adiya,

      Har Ta Kaimu A Ranar Ga Shugaban Anbiya.

 

Zaman Annabi a Tsakanin Banū Sad

Ma’aiki Alaihissalam ya shahara da hankali tun yana ƙarami, ba ya yawan kuka, gashi mai yawan shiru ga nutsuwa da hankali.

Tsaga Kirjinsa  (Shaqqu adr)

A lokacin da yake ƙauyen Banū Sad, inda ake shayar da shi cikin albarka, wata rana yana wasa tare da yan uwansa a wajen kiwon dabbobi, sai wani al’amari ya faru wanda ya girgiza zukatan qauyen, ya kuma ƙara tabbatar da tsarkin Manzon Allah tun kafin zuwan wahayi.

Yanda al’amin ya faru

Lokacin yana kusan shekaru huɗu, Halimah Sa’diyya da mijinta sun barshi yana wasa a bayan gida tare da ɗan’uwansa ’Abdullāh. A cikin kwanciyar hankali, sai wani abu ya bayyana cikin sauri kamar ɗigon haske daga sararin sama.

Abdullāh ɗan Halimah ya dawo da gudu yana kuka yana cewa:

"Wallahi wasu mutanen farare sun kama ɗan ƙanenmu Muhammad! Sun kwantar da shi, sun buɗe kirjinsa!"

Halimah da mijinta suka firgita. Suka fita da gudu kamar zuciyarsu za ta faso kirjin su, don zuwa suga wannan al’amari.

A ruwaya sahihiya, cikin Sahih Muslim, an tabbatar da cewa: Mala’iku biyu ne suka zo, Suka kwantar da shi a ƙasa cikin tausayi, ba da azabtarwa ba. Suka buɗe kirjinsa cikin tsabta. Suka fitar da wati ƙaramar tsoka daga zuciyarsa.

Suka ce:Wannan shi ne rabon shaidan da ke cikin zuciyarka.Suka zubar da shi.

Suka ciro zuciyarsa suka wanke ta da ruwan Zamzam a cikin kwano na zinariya.

Aka cika kirjinsa da: Haske da Hikima da Imani da Tsarki da Albarka

Daga na sai suka mayar da qirjinsa nasa, suka xinke shi, ba tare da wasu raunuka ko jini ba.

Halin da Annabi Ya Shiga

A lokacin da Halimah ta iso, sai ta tarar da shi:            Zuciyarsa tana bugawa cikin natsuwa. Launin jikinsa ya ɗan canza saboda girman al’amarin, Amma ba shi da wani ciwo ko rauni, fuskar sa cike da annuri. Ya gaya mata abin da ya faru cikin kalma kaɗan da nutsuwa.

Halimah sai ta fara kuka, saboda abin ya tsorata, sai ta fara tunanin cewa ta mayar da shi ga mahaifiyarsa don tsoron kada wani abu ya same shi.

Dalilin da yasa aka tsaga kirjin sa

Malamai sun yi bayani cewa: an tsaga kirjin sa ne sabo da tsarkake zuciyarsa tun kafin zuwan wahayi, Allah ya shirya zuciyar Annabi tun yana yaro, ya cire duk wani abu na rabon shaidan daga zuciyar.

Jawabin Malaman Tarihi kan tsaga qirjinsa

Ibn Hajar al-Asqalani ya ce:

Wannan al’amari gaskiya ne kuma ya tabbata a sahihan ruwayoyi, ba abin al’ajabi ba ne ga darajar Manzon Allah .”

Imam Nawawi ya ce:

An tsaga kirjinsa ne domin qara albarka a zuciyar, da karfafa Zuciyar, domin nauyin risala da zuciyar zara xauka.”

Tasirin Al’amarin ga Halimah

Bayan wannan al’amari, Halimah ta tabbatar cewa wannan yaro ba kamar sauran yara ba ne.

Ta ce a wata ruwaya:

Daga wannan rana, na san cewa Muhammad bawan Allah ne, Allah ne yake kiyaye shi da kansa.”

Sai ta yanke shawarar mayar da shi ga mahaifiyarsa Sayyada Aminah saboda tsoron kada wani abin almara ya sake faruwa da shi a karkarar.

Wannan al’amari shi ne shaqu-adri na farko; akwai wasu da suka faru a lokacin aiko shi da kuma lokacin Isra’i da Mi’raj

Rasuwar Mahaifiyarsa

RASUWAR MAHAIFIYAR MANZON ALLAH

Sayyida Aminah bint Wahb, mahaifiyar Manzon Allah , mace ce mai kamala, tsarki da natsuwa. Ta haifi Annabi Muhammad ne a Makkah, sannan ta yi masa tarbiyya cikin ƙauna da kulawa bayan rasuwar mijinta Abdullah, wanda ya rasu tun kafin haihuwar Annabi.

Lokacin da Annabi ya kai kimanin shekaru 6, Aminah ta ɗauke shi zuwa Madina don ziyarar dangin kakarsa ta ɓangaren uba (Banū Najjār), Kuma su ziyarta dangin mahaifinsa. Sun zauna Madina kusan wata guda.

A hanyarsu ta dawowa, lokacin da suka iso Abwā (wani wuri ne tsakanin Makkah da Madina), Aminah sai rashin lafiya ya kamata, da ciwon da ya yi tsanani sai ta gajiya ta kamata sosai, inda anan Allah yayi mata rasuwa.

Manzon Allah yana da shekaru 6 kacal ya rasa mahaifiyarsa, ya zama maraya na hakika babu uwa ba uba.

Wanda ya dawo da shi Makkah

Bayan rasuwarta Ummu Ayman (Barakah), baiwar Aminah, ce ta dawo da shi Makkah, Sannan Kakansa Abdul-Muṭṭalib ya rungume shi cikin tsananin ƙauna yacigaba da rainon sa.

Tarbiyya a Hannun Kakansa Abdul-Muṭṭalib

Kakan sa ya rungume shi cikin ƙauna, ya riqa zaunar dashi a kan shimfixarsa wadda ba a barin kowa ya zauna a kai.

Abdul-Muṭṭalib ya ci gaba da rainon Annabi cikin girma da kulawa don ganin Annabi a matsayi na mai albarka.

Ya ce: Wannan ɗan zai kai ga sabon matsayi mai girma.”

Sai dai bayan shekaru 2 shi ma Abdul-Muṭṭalib ya rasu.

Rayuwarsa a Gidan Abu Ṭālib

Daganan a sai ya koma rayuwa a gidan kawunsa Abu Ṭālib, wanda shi ma ya ba shi mahimmanci fiye da yayansa cikin kulawa da qauna.

Annabi ya tashi cikin halaye maisu kyau na Mutuntawa, yawan sadaka da girmama manya, ya zamo mai gaskiya.

Duk wanda ya haxu da shi yana cewa:

Muhammad yaro ne mai kamala, nutsuwa, da gaskiya.”

A gidan Abu Ṭālib ne ya fara aikin kiwon dabbobi, sannan ya tashi cikin halaye masu tsabta na Larabawa.

Lokacin Samartakarsa da Sana’a

Aikin kiwo

Annabi Alaihissalam ya yi kiwon dabbobi a Makka kamar yadda Annabawa da dama suka yi.

Kasuwanci

Annabi Alaihissalam ya bi Abu Ṭālib zuwa Sham, don ya koyi lasuwanci, ya zama nagari, mai gaskiya da ruqon amana.

Duniya ta kira shi: As-Ṣādiq al-Amīn wato Mai Gaskiya Mai Amanah.

Auren Manzon Allah Da Sayyida Khadija

Sayyida Khadīja bint Khuwaylid ta kasance mace mai daraja a garin Makkah, macece mai Girma, da tsarki, da arziki, da mutunci. Duk wani dan kasuwa mai gaskiya yana tare da ita, kuma duk wani mai neman amana yana girmamata.

Malamai suka kira ta:

Sayyidat Quraish” – Mace mafi daraja a cikin Quraysh.

A lokacin da Manzon Allah Muhammad ɗan Abdullah yana shekaru 25, kafin ya zama Annabi ya shahara da:

Gaskiya da Aminci da Kyawawan halaye ga Tausayi ga Adalci ga Natsuwa, dukkan mutune suna kira shi da "As-Sādiq al-Amīn".

Farkon Kasuwancinsa Da Khadija

Khadija ta ji labarin mutuncinsa, da gaskiya da Amanarsa sa ta gayyace shi ya yi mata tafiyar kasuwanci zuwa Sham, tare da bawanta Maysarah.

A wannan tafiya, Maysarah ya lura da abubuwa waɗanda suka bambanta shi da sauran mutane: domin ya sameshi Alaihissalam bashi da yaudara, baya yawan Magana, bai san ha’inci ko cuta ba.

Maisarah ya ga abubuwar mamaki tare da shi, kamar rana da tana masa inuwa, da sauran abubuwan mamaki tare da shu.

Lokacin da suka dawo daga Sham, sun dawo da ribar mai yawa, da ta wuce kowane lokaci da aka taɓa samu.

Maysarah ya faɗa mata kywawan halayensa da suka saka ta ta nutsu da shi.

Khadija Ta Nuna Sha’awar Aurensa

Bayan ta tantance gaskiyar halayensa, ta ga cewa wannan matshi ba kamar kowa ba ne.

Ta ambata wa aminiyarta Nafisa bint Munabbih cewa tana sha’awar auren shi, amma cikin kunya da ladabi.

Nafisa ta je ta ambatawa Annabi Muhammad (SAW) ta ce:

 “Idan aka kawo maka mace mai daraja, mai arziki, mai tsafta fa zaka aureta?”

Ya tambaya: “Wacece?”

Ta ce: “Khadija bint Khuwaylid.”

Sai ya ce da mamaki:

Ita take so na?”

Nafisa ta tabbatar masa — zuciyar sa ta amince.

Abu Talib ne ya jagoranci nemna auren, kuma aka yi auren bisa ka’idar Larabawa, manyan Quraysh ne suka halarta. An yi taro mai annashuwa da mutunci. A ranar da aka yi auren, Abu Talib ya yi jawabi a inda ya ce:

"Idan akwai wanda ya cancanci Khadija, to shi ne Muhammad. Haka kuma idan akwai wanda ya cancanci Muhammadu, to ita ce Khadija."

Khadija ta kasance mace: Mai kwantar masa da hankali, mai tallafa masa, mai bayar da dukiyarta don alheri.

Sun haifi 'ya'ya shida kamar haka:

1.       Qasim

2.       Zainab

3.       Ruqayyah

4.       Ummu Kulthum

5.       Fāṭimah

6.       Abdullah (Tayyib/Tahir)

Duk ’ya’yan Annabi, in banda Ibrahim, daga Khadija ne.

AIKO SHI DA SAƘO

A shekara ta 40 ne, a cikin watan Ramaan, a wata dakiƙa mafi daraja a tarihin duniya, Malaika Jibrilu ya zo wa ma’aiki Alaisalam a kogon Hira, ya ce:

Iqra’ —Yi karatu.”

Daga nan Annabci ya fara.

Zuciyarsa ta yi nauyi, jikinsa ya xauki rawar sanyi yana kar-karwa, ya dawo gare ta Sayyida Khadijah yana cewa:

"Zammilūnī, zammilūnī"

Ku lullube ni! Ku lullube ni!”

A take Khadija ta kwantar masa da hankali tana mai cewa:

Kada ka ji tsoro. Wallahi babu wani abu mara kyau da zai taɓa samun ka. Domin kai mutum ne mai yawan zumunci, mai taimakon marasa ƙarfi, mai ciyar da talakawa, mai girmama baƙi.

Khadija ta kasance mace ta farko da ta yi shahada. Allah Ya zaɓe ta, Ya ɗaukaka ta, Ya girmama, ta har Mala'ika Jibrilu ya gaisheta tare da yi mata bushara da gida Aljanna.

Kamar yadda Hadisi ya tabbata cewa:

                                                        ، قَالَ عنه الله رضي هُرَيْرَةَ أَبِي عَنْ:
جَاءَ جِبْرِيلُ إِلَى النَّبِيِّ ﷺ فَقَالَ: "يَا رَسُولَ اللَّهِ، هَذِهِ خَدِيجَةُ قَدْ أَتَتْ، مَعَهَا إِنَاءٌ فِيهِ إِدَامٌ أَوْ طَعَامٌ أَوْ شَرَابٌ، فَإِذَا هِيَ أَتَتْكَ فَاقْرَأْ عَلَيْهَا السَّلَامَ مِنْ رَبِّهَا وَمِنِّي، وَبَشِّرْهَا بِبَيْتٍ فِي الْجَنَّةِ مِنْ قَصَبٍ لَا صَخَبَ فِيهِ وَلَا نَصَبَ".

Ma’ana:

Jibrilu ya zo wurin Annabi ya ce:

"Ya Manzon Allah! Ga Khadija ta zo, tana ɗauke da abin ci ko abin sha. Idan ta iso gare ka, ka gaishe ta da sallamar Ubangiji, kuma ka gaishe ta da sallamarka. Ka kuma yi mata bushara da cewa Allah Ya tanadar mata gida a Aljanna na lu’u-lu’u, ba hayaniya a cikinsa kuma babu gajiya."

Sahih al-Bukhari – Hadisi mai lamba (3820)

Sahih Muslim – Hadisi mai lamba (2432)

 

Ta rasu a shekarar ‘Āmul uzn — Shekarar Baƙin Ciki, saboda irin matsayinta a rayuwar Annabi .

 

BABI NA 5

Koyarwar Annabi

Kan Imani (Aqida)

1. Tauhidi

Manzon Allah ya zo da sakon tabbatar da Tauhidi, wato kadaita Allah a cikin:

·         Rububiyya: Yarda da cewa Allah shi ne kaxai mahalicci, mai rayawa kuma da kashewa.

·         Uluhiyya: Bauta ga Allah shi kaɗai ba tare da haxa komai da Shi ba.

·         Sifofi: Yarda da dukkan sifofin kamalar Allah kamar yadda suka zo a cikin Alƙurani da Hadisai.

Allah ya yi hani ga shirka, (wato haxa wani da shi) domin shirka ita ce babbar kafa da ta jawo halakar al’umman baya, haka nan itace babbar kofar da ke fitar da bawa daga musulunci a take.

2. Yarda Da Annabci Da Bin Koyarwar Manzon Allah

Ma’anar Yarda da Annabci (Imanun bi an-Nubuwwah)

Yarda da annabci na nufin:

·         Gaskata cewa Annabi Muhammad bawan Allah ne kuma ManzonSa.

·         Allah ne ya aiko shi da sakon shiriya ga dukkan al’umma.

·         Ya zo da gaskiya, ba ya magana da son rai.

Allah Madaukakin Sarki Ya ce:

:﴿ وَمَا آتَاكُمُ ٱلرَّسُولُ فَخُذُوهُۥ ۖ وَمَا نَهَىٰكُمْ عَنْهُ فَٱنتَهُوا۟

Ma’ana

“Abin da Annabi ya baku ku karɓa, abin da ya hana ku ku guje shi.” (Al-Hashr: 7)

Abubuwan da ke cikin yarda da Annabci:

1.      Gaskata shi cikin zuciya.

2.      Furta shahada da harshe.

3.      Bin koyarwarsa a zahiri da ɓoye.

4.      Kaunar sa sama da kaunar duk abin da mutum yake so.

5.      Karrama shi ba tare da wuce gona da iri ba.

6.      Yarda da hukuncinsa a dukkan lamura.

 

Inda Yarda da Annabci take kai mutum

Yin imani da Annabi yana inganta zuciya, yana kawar da shakku.
Shi ne abin gwajin imanin kowanne bawa.

Allah Ya ce:
“Ba su yi imani ba har su yarda da hukuncinka.” (An-Nisa'i: 65)

Duk wanda ya bi Annabi ba zai ɓata ba, domin Annaba ne jagoran kaiwa ga gafara da dukkan alheran duniya.

Wanda ya gaskata Annabi kuma ya bi shi, to wannan Aljanna ce makomarsa.

Bin Koyarwar Annabi (Ittiba’u Sunnah)

Bin koyarwar Annabi na nufin:

·         Yin ibada kamar yadda ya koyar.

·         Guje wa abin da ya hana.

·         Yin mu'amala da halaye kamar yadda ya koayar kuma ya yi.

·         Karɓar rayuwarsa da koyarwarsa a matsayin jagora.

Siffofin bin koyarwar Annabi

1.      Bin koyarwarsa da niyya ta samun yardar Allah, ba don duniya ba.

2.      Bin koyarwarsa a zahiri da ɓoye.

3.      Bin koyarwarsa cikin sauƙi ba tare da tsanantawa ba.

4.      Bin koyarwarsa cikin ilimi, ba cikin son rai ba.

 

Wuraren Da Ya Kamata Musulmi Ya Fara Biyayya da Bin Sunnah

A cikin ibada

·         Yin sallah kamar yadda Annabi ya yi.

·         Yin azumi da hajj  ko umrah bisa koyarwarsa.

·         Koyon alwala da tsarki yadda ya yi.

A cikin mu’amala

·         Aikata Gaskiya a dukkan mu’amala.

·         Yin Adalci a dukkan ayyuka.

·         Rashin cin amana.

·         Kyautata mu'amala ga abokan hulɗa.

A cikin halaye

·         Zamantowa mai tausayi da ladabi, da natsuwa a kowanne yanayi.

·         Rashin kamun harshe wajen aikata zagi, ko cutar da mutane.

·         Kulawa da marasa ƙarfi da tallafamusu.

A cikin zamantakewa

·         Kyautata wa iyaye.

·         Kyautata wa mata da yara.

·         Kula da makwabci da jama’a.


5. Dalilan da yasa dole a bi Annabi

Annabi shine mafi kusanci da wahayi, shi ne mafi sani ga Addini, kuma mafi daraja a dukkan bayin Allah.

Allah ya umurce mu da biyayya gare shi

Biyayya ga Annabi ita ce biyayya ga Allah. Kaurace wa koyarwarsa na kaiwa ga ɓacewa.

Shi ne mafi kyawawan halaye da kyautatawa

Allah Ya ce:
“Hakika kana da
ɗabi’a mafi girma.” (Al-Qalam: 4)

Rayuwarsa ita ce mafi dacewa ga ɗan Adam

Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam ya yi jagoranci, ya yi aure, ya yi kasuwanci, ya yi yaƙi, ya yi zaman lafiya.
Dukkan fannonin rayuwasa akwai abin koyi a cikinsu.

Alamar Wanda Ya Yarda Da Annabi Kuma Yake Bin Koyarwarsa

1.      Tsoron Allah a voye da bayyane.

2.      Yin sallar dare ko lokutan da ake barci.

3.      Gaskiya da amana a kowane hali.

4.      Tausayi da mutunci ga kowa.

5.      Rashin aibata mutane ko yawan faɗa.

6.      Neman halal da guje wa abin da ya haramta.

7.      Yawaita yin salati a gareshi.

Yarda da annabci da bin koyarwar Annabi shine ginshiƙin Musulunci. Duk wanda ya zamo mai yarda da bi koyarwarsa zai zamo:

·         Zuciyarsa za ta tsarkaka.

·         Halayensa za su gyaru.

·         Al’amuransa za su zamo masu albarka.

·         Makomarsa ita ce Aljanna.

3. Imani da Mala’iku, Littattafai da Kaddara

Manzon Allah ya karfafa imani da wanzuwar Mala’iku da yin Imani da su, da Imani da Littattafan Allah kuma su zamo su ne jagora ga dukkan rayuwa mu. Sannan mu yarda da qaddara mai kyau da mara kyau duk mu amince daga Allah suke.

Koyarwar Annabi Kan Sallah

1. Muhimmancinta

Sallah ita ce ginshiƙin Musulunci. Manzon Allah ya nuna cewa sallah ita ce farkon abin da za a tambayi bawan a ranar alqiyama, in tayi kyau za a karvi sauran ayyukan sa, in kuma batayi kyau ba, to baza a duba dukkan sauran ayyukan da ya aikata ba.

2. Tsarin Sallar Annabi

Annabi ya koya mana:

·         Tsarki da yin alwala cikin ladabi.

·         Tsayuwa da nutsuwa a cikin sallah.

·         Karatun Fatiha da surori.

Musamman ya umurci mutane da cewa:


"Ku yi sallah kamar yadda kuka ga ni ina yi."

3. Tarbiyyar Sallah

– Sallah tana hana alfasha da mummunan aiki.
– Tana qara tsoron Allah da natsuwa.
– Tana magance damuwa da munanan halaye.

Koyarwa Kan Azumi

– Azumi yana tsarkake ruhu da zuciya.
– Yana koyar da ha
ƙuri, juriya da jinkan raunana wato talakawa.

Kyawawan Halaye a Lokacin Azumi

Annabi ya ce:

·         Wanda yake azumi ya kiyaye harshensa da gabobinsa.

·         Ya guji zagi, tsinuwa, da yawan jayayya.

·         Ya zama mai ƙoƙarin samun lada wajen yawaita addu'a da sadaqa.

Bukatar Ciyarwa da Tausayi

– Annabi ya kasance mafi karamci a Ramadan.
– Ya koyar da buda baki cikin sau
ƙi da rashin wahala.

Zakka, Sadaka da Kyautatawa

1. Ma’anar Zakka

Zakka tana tsarkake dukiya, tana kuma kawo albarka.
Annabi
ya yi hani ga qin bada zakka a dukiya, in har ta kai yawan da za a fitar da zakkar.

Kyautatawa ga Talakawa

Annabi Ya nuna cewa akwai lada mai yawa wajen taimakon marayu, da marasa lafiya, da miskinai da mabuqata.
– Ya ce: “Ku ceci kanku daga wuta ko da da kashi daya na dabino.”

Sadakatu Jariya

– Gina masallatai
– Koyar da ilimi
– Samar da ruwan sha
Wadannan duk suna ci gaba da zama lada bayan mutuwa.

Halayen Annabi (Akhlaq)

1. Haƙuri

– Annabi ya jure wahalhalu da cin zarafi.
– Idan aka zubar masa jini a Ta’if, bai yi addu'ar halaka ba.

2. Gaskiya da Amana

– Kafin aiko shi, an san shi da “Al-Amin”.
– Bai ta
ɓa karya ba ko cuwa-cuɗi.

3. Tausayi

– Ya tausaya wa matasa, tsofaffi, marayu, talakawa da mata.
– Ya nuna kyakyawan fuska da dariya mai annashuwa.

Iyali, Zumunci da Auren Annabi

1. Darajar Iyaye

Ya ce:
“Aljanna na
ƙarƙashin ƙafafun uwa.
– Ya jaddada kula da uba, uwa, kakanni da ‘yan uwa.

2. Auren Annabi

Dukkanin Auren da Ma’aiki Alaihissalam ya yi, yana nuna zumunci, da kunya, da tausayi yana yawan kyautatawa ga matansa. Ya kasance yana taimakawa matan sa a aikace-aikacen gida.

3. Tarbiyyar Yara

Ma’aiki Alaihissalam yana wasa da yara, yana musu addu’a, ya koya musu gaskiya, da tsoron Allah da nutsuwa.

Shugabanci da Tsarin Siyasar Annabi

1. Shura

Ma’aiki Alaihissalam ya gina gwamnatin Madina bisa tattaunawa da sahabbansa tare da neman shawara daga garesu. A tsarin shugabancin sa bai yarda da zalunci ba, balle cin zarafin juna.

2. Adalci

Ma’aiki Alaihissalam ya haramta cin hanci da rashawa, yana hukunci ga kowa bisa gaskiya da adalci.

3. Kula da Talakawa

Annabi ya ce:
“Duk wanda ba shi da tausayi, Allah ba zai tausaya masa ba.”

Koyarwa Kan Kasuwanci da Hulɗar Zamani

Bincike da Gaskiya a Ciniki

Ma’aiki Alaihissalam ya haramta cin riba a dukkan kasuwanci, ya haramta zamba, da boye aibu a cikin cinikayya, yana bayyana cewa yin gaskiya a kasuwanci ytana kawo albarka.

Mu’amala da Mutane

Ma’aiki Alaihissalam ya kasance yana kare harshen mutum, yana kula da haƙƙin makwabta, sannan bai yarda da a cutar da kowa ba.

3. Sana’a da Neman Halal

Annabi ya koyar da cewa neman halal ibada ne, domin shi ma ya taba yin kiwon dabbobi da cinikayya.

Darajar Ilimi da Malamai

Wajibcin Neman Ilimi

Annabi ya wajabta ga kowane Musulmi da ya nemi ilimin da zai gyara addininsa, domin shi Ilimi haske ne da ke yaye duhun jahilci.

Girman Mai Ilimi

Annabi ya bayyana cewa su Malamai magada Annabawa ne, kuma Allah yana ɗaukaka darajar masu ilimi.

Aiki da Ilimi

Annabi ya ce:
“Ilimi ba ya amfani sai idan an yi aiki da shi.”

Koyarwa Kan Tsarkake Zuciya da Ibadu

Tawakkali

Annabi ya kouar da dogaro ga Allah tare da miqa dukkan lamara gareshi.

2. Zikri da Istigfari

Annabi ya sanar da mu cewa zikiri yana magance damuwa, sannan yana kawo nutsuwa. Sannan ya kasance yana yawan neman gafara fiye da sau 70 a rana, domin zikiri yana qankare zunubai, yana qara arziki.

Tuba da Tsoron Allah

Annabi ya karfafemu da yawan tuba saboda yawan tuba yana qarawa ɗan Adam daraja, tareda da koyar da cewa, tsoron Allah shi ne ginshiƙin dukkan alheran duniya da lahira.

Koyarwar Annabi ta shafi kowane fanni: imani, ibada, mu’amala, halaye, siyasa, zamantakewa, da tarbiyya. Wanda ya bi koyarwarsa zai rayu cikin nutsuwa da haske a duniya da lahira.

 

BABI NA 6

MU'UJIZOJIN MANZON ALLAH (SAW)

1. Ma’anar Mu’ujiza

Mu’ujiza ita ce wani abin al’ajabi wanda ya sava wa tsarin dabi’a, Allah Yana bayar da ita ga Annabawa domin tabbatar da gaskiyar saƙon da suka zo da shi.
Allah Madaukakin Sarki ya ce:

“Manzanni ba su da wani abin da ya rataye a kansu face isar da saƙo bayyananne. (Surah An-Nahl: 35)

2. MU’UJIZAR DA TA FI GIRMA: ALƘURANI

2.1. Dalilin da yasa Alƙurani Muujiza ce

Alƙurani shi ne mafi girman muujiza ce saboda:

·         KalamanSa sun gagari malaman Larabawa a lokacin Jahiliyya.

·         Ya taho da ilimin da ya zarce duk tunanin ɗan Adam.

·         Ya kasance hujja mai xorewa har ƙarshen duniya.

Allah Ya ce:

“Idan mutane da aljannu sun haɗu don su kawo makamancin wannan Alƙurani, ba za su iya ba…”
(Surah Al-Isra: 88)

2.2. Hadisin da ya tabbatar da mu’ujizar Alƙurani

Annabi (SAW) ya ce:

“Babu wani Annabi da Allah ya ba shi mu’ujizojin da mutane suka gaskata shi da su. Amma abin da aka ba ni shi ne Wahayi (Alƙurani). Ina fatan in kasance mafi yawan mabiya a ranar ƙiyama.
(Bukhari da Muslim)

3. MU’UJIZOJIN DA SUKA FARU TUN YANA QARAMI

3.1. Tsaga Kirjin Annabi (SAW)

Lokacin yana ƙarami a gidan Halima Saadiyya, Malaika Jibrilu ya zo, ya tsaga kirjinsa, ya cire wani ɓangare “hazzun-shaidan” wato wani abu da ka iya zama rabo na Shaixan Allah ya cireshi da ga zuciyarsa, ya tsarkaketa.

Hadisin Anas (RA) ya ce:

“Jibrilu ya zo ya tsaga kirjinsa, ya fitar da wani baƙin abu ya ce: wannan ne ɓangaren shaidan da yake nak.”
(Muslim)

4. MU’UJIZOJIN A LOKACIN AIKIN ANNABCI

4.1. Ƙaruwar Abinci

A lokuta da dama abinci ya nininku fiye da yadda ake tsammani.

Misali – Abincin Jabir

Jabir (RA) ya ce:

“Annabi ya sanya hannunsa cikin gurasar, sai ta yi yawa har ta wadaci mutane dubu.”
(Bukhari)

4.2. Fitar Ruwa daga Hannunsa

An tabbatar da cewa ruwa ya fito daga yatsun Annabi (SAW) har Sahabbai suka sha.

Jabir (RA) ya ruwaito:

“Na ga ruwa yana zuba daga yatsun Annabi kamar zubar ruwa daga rijiya.”
(Bukhari 3572)

4.3. Kukan Rakumi

Annabi (SAW) ya share hawayen wani rakumi da aka zalunta, raqumin ya gane Annabi kuma ya kai kuka tare da neman taimakoSa Salallahu Alihi wasallam.

“Rakuninsa ya zo wurin Annabi ya yi kuka, sai Annabi ya ce: ku ji tsoron Allah a kan waɗannan dabban.”
(Abu Dawud)

4.4. Bishiya tayi tafiya ta je zuwa ga Annabi

An ga bishiya ta taso daga inda take zuwa wajen Annabi, sannan ta koma.

“Bishiya ta zo gabansa ta tsaya, sannan ya mayar da ita inda take.”
(Tirmidhi)

5. MU’UJIZOJIN TAIMAKON ALLAH

5.1. Saukar Mala’iku a Yaƙin Badar

Allah ya saukar da mala’iku domin tallafa wa musulmai a lokacin da ake tsaka da yaqin Badar.

“(Allah) Ya saukar da mala’iku domin su taimaka muku.”
(Surah Al-Anfal: 9–12)

5.2. Tsira a lokacin Hijira

A likacin da Ma’aiki Alaihissalam zai yi hijra, makiyansa sun kewaye gidansa, domin du cutar da shi kuma su hanashi yin hijira, amma sai Allah Ya lullube idanunsu da barci. Kamar yadda ya faqa cikin littafinsa maitsarki:

“Mun sanya wani shinge a gabansu da bayan su, sai suka zama makafi.”
(Surah Yasin: 9)

Hadisi:

“Suka zuba masa ido amma ba su gan shi ba.”
(Ibn Hibban)

6. ANNABCI: BAYANIN ABUBUWAN DAZA SU FARU

Annabi (SAW) ya annabcin abubuwa da dama kuma suka faru kamar yadda ya faɗesu:

6.1. Faxuwar Farisa da Rum

Manzon Allah (SAW) ya bayyana cewa lallai kisra da rum zasu faxi, kuma abin ya faru kamar yadda ya faxa:

Ya ce: “Za a warware kujerar Kisra (sarkin Farisa).” Kuma haka ya faru.
(Bukhari)

6.2. Warwatsuwar Musulunci

Manzon Allah (SAW) ya bayyana cewa Addinin Musulunci zai watsu a ko ina gabas da yamma kudu da aewa, kamar yadda ya faxa a Hadisi:

“Addinina zai kai har inda rana ta faɗa da inda take fitowa.”
(Ahmad)

7. ISRA’I DA MI’IRAJI

Tafiyar da akyi da Annabi Alaihissalam daga Masallacin Harami zuwa Masallacin Al-Aqsa, sannan aka tafi da shi zuwa sama wato Mi’iraaji, inda ya gana da Allah ya karvo Sallah, kamar yadda Allah ya faxa cewa:.

“Tsarki ga Wanda Ya tafiyar bawansa daga Masallacin Harami zuwa Masallacin Al-Aqsa…”
(Surah Al-Isra: 1)

Hadisi:

Ya sadu da Annabawa, sannan aka wajabta masa sallolin farilla.
(Bukhari da Muslim)

8. MU’UJIZOJIN WARKARWA

8.1. Warkar da Sahabbai

Lokaci da Sayyadi Aliyu (RA) yana ciwon Ido, ya shafi idon nasa da hannayensa, a take sai idon ya warke nan take.

Kamar yadda Hadisi ya fada:

“Sai Annabi ya shafe idanunsa da hannunsa, ya warke kamar bai taba ciwo ba.”
(Muslim)

9. MU’UJIZAR DA TA DAWWAMA: SUNNARSA

Duk sauran mu’ujizojin Annabawa suna wuce wa ne bayan Annabwan sun faku, Amma shi Manzon Allah (SAW) abubuwan da ya bari suna nan har zuwa ranar Alqiyama zasu tabbata, wato Alƙurani da Sunnarsa (Hadisai) da sauran kq’idodin rayuwa da zamantakewa da ya bar mana.

Hadisi:

“Na bar muku abu biyu, ba za ku bata ba matuqar kun riƙe su: Littafin Allah da Sunnata.
(Malik a Muwatta')

Mu’ujizojin Manzon Allah (SAW) hujja ce ta gaskiyar saƙon sa da matsayin da Allah Ya girmama shi da shi.
Rayuwarsa ta tabbata a matsayin jagora, al
ƙibla, da misali na nagarta.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BABI NA 7

KIRAN ANNABI (SAW) ZUWA TAUHIDI A MAKKAH

Shekaru Uku a ɓoye, da Shekara Goma a bayyane

Da Allah Madaukakin Sarki Ya aiko Annabi Muhammadu (SAW) da saƙon Musulunci, farkon abin da ya fara kira shi ne Tauhidi, wato a bauta wa Allah shi kaɗai ba tare da haɗa wani da Shi ba. Wannan kira shi ne tushen dukkan hukunce-hukuncen Musulunci.

A lokacin da aka fara saukar da wahayi, daular Qur’aysh da mazaunanta cike suke da shirka, bautar gumaka, zalunci da ɗabi’u marasa kyau. Saboda haka, Manzon Allah (SAW) ya fara kira a hankali, a tsanake, domin a kare saƙon daga barazanar Quraysh tun farko.

2. Farkon Kira: Shekaru Uku a ɓoye

2.1. Dalilin da ya sa yin kira a ɓoye

Annabi (SAW) ya yi kira a ɓoye shekaru uku saboda: Matsin lambar Qur’aysh da azabtar da duk wanda ya ƙi bautar gumaka. Kuma domin shugaba ya kafa ƙananan tushe na muminai masu aminci daga makusantansa. Kuma duk wani yunkuri na bayyana kiran a wannan lokaci zai iya kawo hare-hare tun da wuri.

Allah Ya ce:

“Ka yi haƙuri da abin da suke faɗi.”
(Surah Ta-Ha: 130)

2.2. Suwaye na farko da suka amsa kira?

A wannan lokacin ne makusanta ga shugaba suka fara karɓar Musulunci, daga cikin na farko farkon amas kira sun hadar da:

·         Sayyida Khadija (RA)

·         Abu Bakr Siddiq (RA)

·         Aliyu bn Abi Dalib (RA)

·         Zaid bn Haritha (RA)

·         A wasu riwayoyi kamar Bilal, Ammar, Sumayya da Yasir.

2.3. Gidan Al-Arqam

Ina ne Gidan Arqam: shine gidan da Annabi (SAW) yake tara sahabbansa a ɓoye, yana koyar da su Tauhidi, karatun Alƙurani da ladubban Musulunci.

Hadisi:

 “Muminai na farko sun kasance ƙasimi-ƙasimi, ba su da yawa.
(Ibn Sa’d, a
abaqāt)

 

3. Kiran Bayyane: Na tsawon Shekara Goma

Bayan an gina Imani a zukatan ƙananan muminai a ɓoye, sai Allah ta;ala Ya yi umarni da ya fito yayi kira a bayyane, kamar yadda ya bayyana a cikin littafin sa maitsarki:

أَنْذِرْ عَشِيرَتَكَ الْأَقْرَبِينَ

“Ka yi wa danginka mafi kusa gargaɗi.”
(Surah Ash-Shu’ar
ā: 214)

Wannan shi ne matakin da ya canza yanayin kira daga ɓoye zuwa fili.

3.1. Kiran farko a kan Dutsen afa

Annabi (SAW) ya hau dutsen afa ya ce:

“Da zan faɗa muku cewa akwai mayaƙa suna zuwa daga bayan wannan dutse, shin za ku gaskata ni?
Suka ce:
“Mun san ba ka ta
ɓa yin ƙarya ba.
Sannan ya ce:
“Ni Manzon Allah ne gare ku, ina gargadin ku daga azabar da ta gabato.”
(Bukhari)

3.2. Turjiya daga Qur’aysh

Tun daga wannan rana Qur’aysh suka fara yaƙi da saƙon Tauhidi, suna fara sukar sa da yunƙurin kashe shi, da tozarci ga muminai tare da fatattakar dukkannin waxanda  suka karɓi Addinin Musulunci

3.3. Ayyukan Annabi (SAW) a Shekaru Goma

A cikin wannan lokaci wato shekaru Goma, Ma’aiki Alaihissalam ya yi abubuwa masu muhimmanci kamar:

1. Kiran jama’a daga kowane matsayi

Ya yi kira ga talakawa da matasa da bayi da attajirai har da shugabanni.

2. Jarabawar Musulmai

Muminai da suka amshi wannan kira daga shugaban halitta sun sha tsananin azaba, waxanda suka sha azabar sun haxar da:

·         Sayyadina Bilal (RA) da azabarsa a rana, domin ana kwantar da shi ne a tsakiyar rana mai zafi cikin sahara a xora dutse a cikin sa akan lallai sai ya bar addinin Musulunci

·         Yasir da Sumayya (RA) sune na farko da sukayi  shahada, don sun ki barin Addinin Musulunci aka kasha su

·         Hijira ta farko zuwa Habasha: sabo da tsanani azabar da muminai ke ciki yasaka wasu daga cikin su yin kaura zuwa kasar Habasa.

3. Da’awah cikin hikima

Allah Ya ce:


“Ka kira zuwa hanyar Ubangijinka da hikima da nasiha mai kyau.”
(Surah An-Na
l: 125)

Annabi Salallahu Alaiji wasallam ya yi amfani da hikima wajen isar da saƙon Tauhidi, yana kauce wa tashin hankali.

4. Shiga Tsakanin Qabilu

Annabi (SAW) yana ziyartar ƙabilu a lokacin hajji yana cewa:

“Ku ce: ba wani abin bautawa sai Allah, za ku ci nasara.”
(Ahmad)

4. Muhimman Abubuwan da kira a Makkah ya kunsa

1. Tauhidi

Kira zuwa ga bautawa Allah shi kaɗai ba tare da haɗa wani da Shi ba.

2. Kiyaye da zalunci

Annabi Alaihissalam ya faɗakar da quraysh da su daina azabtar da talakawa da mata da bayi.

3. Girmama hakkin ’yan uwa

Annabi Alaihissalam ya kira su zuwa adalci da kaucewa cin amanar jama’a.

4. Kiyaye alfarmar iyaye

Annabi Alaihissalam yayi kira da a kare alfarmar iyaye a girmamasu, a kula da dangantaka waro yan’uwantaka, ya qarfafa sada zumunci da girmama maqota.

5. Sakamakon Kiran Shekaru Goma

1.      An sami ƙaramin al’umma ta muminai masu aminci.

2.      An shimfiɗa tushe da ba za a gusar da shi ba.

3.      An samu mummunan turjiya daga Qur’aysh wadda ta haifar da hijira zuwa Madina.

4.      Saƙon Tauhidi ya watsu a hankali har zuwa lokacin da Allah Ya buɗe Madina ga Musulunci.

Kiran Annabi (SAW) zuwa Tauhidi a Makkah na ɓoye da na bayyane ya kafa ginshikin Musulunci.
Shekaru uku na farko sun gina
ƙananan muminai, shekaru goma na bayyane kuwa sun tabbatar da haƙurinsa, jajurcewa da tsantsar daawah.

Daga wannan, Musulunci ya samu direba, tushe, da al’umma da suka zama madogara bayan hijira.

BABI NA 8

HIJIRAR MANZON ALLAH

MA’ANAR HIJIRA

Hijira na nufin barin ƙasa ko wuri zuwa wani wuri domin kare addini da imani, da kuma samun damar bauta wa Allah cikin ’yanci.

Hijirar Manzon Allah ita ce barinsa Makkah zuwa Madinah a shekarar 622 Miladiyya, wacce ta zama tushen tarihin Musulunci (Hijira Calendar).

DALILAN HIJIRAR MANZON ALLAH

1. Tsananin takura daga kafiran Makkah

Kafirai sun tsananta wa Musulmin da suka bar bautar Gumaka da tsananin azba ga irin su Bilal bn Rabah, sannan suka kashe Sumayyah (wacce ta zamo farkon shahidai), haka zalika sun lillace Banu Hashim daga dukkan wata mu’amala.

2. Makirci na kashe Annabi

Kafirai sun yanke shawarar kashe Annabi gaba ɗaya, a cikin wata tattaunawa da sukayi suka amince da su tura matasa daga mabanbantan qabilu din su kasha shi.

Dalili daga Al-Qur’ani:

 (Suratul Anfal: 30)

Fassara:
“Ka tuna lokacin da kafirai suka shirya makirci a kanka, ko su tsare ka, ko su kashe ka, ko su fitar da kai. Suna shirya makirci, Allah kuma yana shirya, kuma Allah Shi ne mafi kyawun masu shirya makirci.”

SHIRIN HIJIRA

1. Izinin Allah

Annabi bai bar Makkah ba sai da Allah Ya ba shi izini.

2. Zabar Abu Bakr (RA) a matsayin abokin tafiya

Abu Bakr (RA) ya kasance shine Annabi (SAW) ya zava domin suyi tafiyar tare.

3. Shigarsu Kogon Thawr

Ma’aiki Alaihissalam da Abubakar (AS) Sun ɓuya a Kogon Thawr na tsawon kwanaki uku a hanyarsu ta tafiya Madina.

ABIN DA YA FARU A KOGON THAWR

Kafirai sun zo har bakin kogon. Abu Bakr (RA) ya ji tsoro.

Hadisi (Bukhari da Muslim):

مَعَنَا  اللَّهَ إِنَّ تَحْزَنْ لَا

Fassara:
“Kada ka damu, lallai Allah Yana tare da mu.”

Hujjar Qur’ani:

Fassara:
“Idan ba ku taimake shi ba, to lallai Allah Ya taimake shi, lokacin da kafirai suka fitar da shi, su biyu ne kawai, suna cikin kogo...”

(Suratut Taubah: 40)

TAFIYA DAGA MAKKAH ZUWA MADINAH

Wanda ya Jagoranci tafiyar shi ne: Abdullahi bn Uraiqit (duk da bai Musulunta ba)

Sun bi hanyar da ba hanyar da ake bi kai tsaye ba, don bavadda sawu da nuna hikima a cikin tafiyar

Abubuwa masu ban mamaki sun faru, ciki har da:

Labarin Suraqa bn Malik wanda ya so kama Annabi amma Allah Ya kare shi

A lokacin Hijirar Annabi Muhammad daga Makkah zuwa Madina, mushrikan Quraysh suka sanya lada mai yawa ga duk wanda ya kama Annabi ko Sahabinsa Abubakr  (RA). Saboda wannan lada da aka sanya, Suraqa bn Mālik bn Jushum ya fito da niyyar sai ya nemo su a duk inda suke.

Da ya hango su ya kusanta zuwa wajen su a cikin hamada, sai dokin Suraqa ya fara nutsewa a cikin ƙasa, in ya jiya sai dikin yaci gaba da tafi, in ya sake bin su sai ya cigaba da nutsewa, haka yayi tayi sau da dama, har sai ya gane cewa wannan kariya ce daga Allah ga Annabinsa . Sai tsoro ya kama shi, ya roƙi Annabi da ya yi masa addu’a, ya kuma yi alƙawarin ba zai cutar da su ba.

Sai Annabi ya yi masa addu’a, dokinsa ya kuɓuta, sannan Annabi ya ba shi bishara mai girma, yana cewa:

“Yaya za ka ji, ya Suraqa, idan ka sa munduƙan Kisra (Sarkin Farisa) a hannunka?”

Daga baya, bayan Musulunci ya yi ƙarfi a zamanin Sayyidina Umar bn Khattab (RA), bayan ancinye Kisra da yaqi da aka kawo dukiyar Kisra, sai aka bawa Suraqa ya sa munduƙan Kisra, kamar yadda Annabi ya faɗa tun farko.

Wannan labari yana nuna:

·         Kariyar Allah ga Manzonsa

·         Cikar annabcin Annabi

·         Ikon Allah kan dukkan al’amura

·         Kuma yadda Allah ke juya maƙiyi ya zama mai imani

Daga baya Suraqa ya karɓi Musulunci, ya kuma zama Sahabi mai daraja.

SHIGOWAR MANZON ALLAH MADINAH

1. Tarba mai girma

Bayan kammala Hijira daga Makkah, Annabi Muhammad ya iso yankin Yathrib (Madina) a cikin watan Rabi‘ul Awwal, shekara ta 13 bayan fara wahayi. Shigowarsa Madina ya zama babban sauyi a tarihin Musulunci.

1. Tsayuwarsa a Qubā

Da Annabi ya iso kusa da Madina, ya fara sauka a Qubā, inda ya kwana na wasu kwanaki (kimanin huɗu). A can ne ya gina Masallacin Qubā, masallaci na farko a Musulunci, inda ya hadu da Sahabbai, yana jagoranci sallah tare da su.

Allah ya faxa a Qur’ani:

 (Suratut Taubah: 108)

2. Shigowarsa cikin Madina

A ranar Juma’a, Annabi ya nufi Madina daga Qubā. A hanya ya yi sallar Juma’a ta farko a wuri da ake kira Banu Salim bn ‘Awf. Daga nan ya ci gaba da tafiya har ya shiga cikin birnin Madina.

3. Yadda aka tarbe shi

Mutanen Madina – Ansar (Aus da Khazraj) maza da mata, yara da manya – sun fito suna murna, suna tarbarsa da girmamawa. Sun riƙa Raira waƙar maraba:
ala‘al-badru ‘alaynā…”

Sun nuna farin ciki da albarka saboda shigowar Manzon Allah . Kowanne gida yana fatan Annabi ya sauka a wajensa.

4. Zabin inda zai sauka

Annabi ya ce:

“Ku bar rakumina, domin an umarce ta.”

Rakumar tasa Al-Qaswā ta tsaya a wani fili na marayu biyu daga Banu Najjar. A nan ne: Annabi ya sauka a gidan Abu Ayyub al-Ansari (RA). Daga baya aka gina Masallacin Annabi a wannan fili.

5. Ma’anar wannan tarba

Tarbar Annabi a Madina ta nuna:

·         Soyayya da biyayya ga Manzon Allah .

·         Haɗin kan Musulmi (Muhajirai da Ansar).

·         Farkon kafuwar ƙasar Musulunci mai cikakken tsari.

Shigowar Annabi Madina ya zama tushen nasarar Musulunci, kuma daga nan ne aka fara sabon babi na tarihi mai cike da shiriya da adalci.

MUHIMMAN ABUBUWAN DA SUKA BIYO BAYAN HIJIRA

1.      Gina Masallacin Annabi

2.      Ƙulla ‘yan uwantaka tsakanin Muhajirai da Ansar

3.      Kafa tsarin mulki (Sahifatul Madinah)

4.      Musulunci ya samu ƙarfi da yanci

5.      Hijira ta zama rabo tsakanin gaskiya da ƙarya

MUHIMMANCIN HIJIRA A MUSULUNCI

1. Hijira ibada ce

Annabi ya ce:

 (Bukhari da Muslim)

Fassara:
“Ayyuka suna tare da niyya… Duk wanda hijirarsa ta kasance zuwa ga Allah da Manzonsa, to hijirarsa ta tabbata zuwa ga Allah da Manzonsa.”

BABI NA TARA

Yakokin Annabi Muhammad

Rayuwar Annabi Muhammad ba ta taƙaita ga kira zuwa ga tauhidi da koyarwa kawai ba, har ta haɗa da jagoranci a fagen tsaro da kare Musulunci. Yake-yaken da Annabi ya shiga ba don zalunci ko mamaya ba ne, sai dai don kare addini, rayuka da ’yancin bauta wa Allah. Dukkan yaƙe-yaƙen sun gudana ne bisa ƙaidojin adalci da rahama.

Adadin Yake-yaken Annabi

Malamai na tarihi sun yi bayani cewa:

·         Yake-yaken da Annabi ya fita da kansa (Ghazawāt): 27

·         Yaƙe-yaƙen da bai fita da kansa ba, ya aika sahabbai (Sarāyā): sama da 50

Wannan babi zai mayar da hankali ne kan Ghazawāt – wato yaƙe-yaƙen da Annabi ya halarta da kansa.

Ma’anar Ghazwah da Sariyya

·         Ghazwah: Yaƙin da Annabi Muhammad ya jagoranta da kansa.

·         Sariyya: Rundunar yaƙi da Annabi ya aike ta ƙarƙashin jagorancin sahabi, shi kuma bai fita ba.

Jerin Yake-yaken (Ghazawāt) na Annabi

1. Ghazwatul Abwā (Waddān) – Shekara ta 2 bayan Hijira

·         Yaƙi na farko da Annabi ya fita

·         Ba a yi artabu ba

2. Ghazwatul Buwāṭ

3. Ghazwatul ‘Ushayrah

4. Ghazwatul Badr al-Kubrā – 17 Ramadan, 2H

·         Babban nasara ga Musulmi

“Hakika Allah Ya taimake ku a Badar alhali kuna kaɗan.”
(Suratul Al-Imran: 123)

5. Ghazwatul Banī Qaynuqā

6. Ghazwatul Uhud – Shekara ta 3H

·         Jarrabawa ga Musulmi

7. Ghazwatul Hamrāul Asad

8. Ghazwatul Banī Naḍīr

9. Ghazwatul Khandaq (Ahzāb) – Shekara ta 5H

·         An haƙa rami domin kare Madina

“Kuma Allah Ya wadatar da muminai daga yaƙi.
(Suratul Ahzab: 25)

10. Ghazwatul Banī Qurayah

11. Ghazwatul Banī Liyān

12. Ghazwatul Dhātur-Riqā

13. Ghazwatul Banī Muṣṭaliq (Muraysī)

14. Ghazwatul Khaybar – Shekara ta 7H

·         Nasara babba ga Musulmi

15. Ghazwatul ‘Umratul Qaḍā

16. Ghazwatul Fatu Makkah – Shekara ta 8H

·         Nasara ba tare da jini ba

“Idan taimakon Allah da nasara suka zo.”
(Suratun Na
r: 1)

17. Ghazwatul unayn

18. Ghazwatul Ṭāif

19. Ghazwatut Tabūk – Shekara ta 9H

·         Yaƙi mafi nisa

Hikimar Yake-yaken Annabi

·         Kare Musulmi daga zalunci

·         Kare ’yancin addini

·         Kafuwar adalci da tsaro

·         Nuna cewa Musulunci addinin zaman lafiya ne, amma ba na rauni ba

Ƙa’idojin Yaƙi a Musulunci Daga Annabi

·         Haramcin kashe fararen hula

·         Haramcin kashe mata, yara da tsofaffi

·         Haramcin lalata amfanin gona

·         Umurnin kyautata wa fursunoni

Yake-yaken Annabi Muhammad darussa ne na jagoranci, haƙuri da adalci. Duk da yaƙe-yaƙe sun faru, rahama da tausayi su ne ginshiƙan tafiyarsa.

Allah Ya sanya mu cikin masu fahimtar hikimar rayuwar Annabinsa , Ya kuma ba mu ikon koyi da kyawawan dabi’unsa. Ameen.

 

 

 

Babi Na 10

MATAYEN ANNABI ALAIHISSALAM

Matan Annabi Muhammad suna da matsayi na musamman a Musulunci. Allah Ya kira su "Ummuhātul Muminīn" (Uwayen Muminai), domin girmama su da nuna matsayin da suke da shi a rayuwar Musulmi. Tarihinsu cike yake da darussa na tarbiyya, haƙuri, ilimi, sadaukarwa da biyayya ga Allah.

Matayen Annabi da Matsayinsu

Matan Annabi su ne matan da Annabi ya aura bisa halaccin aure. Allah Ya haramta wa muminai su aura su bayan rasuwarsa, yana cewa:

“Annabi ya fi kusa da muminai fiye da kansu, kuma matansa uwayensu ne.”
(Suratul Ahzab: 6)

Haka kuma Allah Ya ce:

“Ba ya halatta a gare ku ku cutar da Manzon Allah, kuma ba ya halatta ku auri matansa bayan sa har abada.”
(Suratul Ahzab: 53)

Yawan Matan Annabi

Annabi Muhammad ya aura mata 11, ya rasu yana tare da 9 daga cikinsu.

1. Sayyidatina Khadija bint Khuwaylid (RA)

Nasaba da Tarihi

·         ‘Yar Khuwaylid bn Asad

·         Mace mai daraja da kasuwanci a Makka

Auren ta da Annabi

·         Annabi ya aure ta yana da shekara 25, ita kuma tana kusan 40

·         Ita ce mace ta farko da Annabi ya aura

Falalarta

·         Ita ce ta farko da ta yi imani da Annabi

·         Ta tallafa masa da dukiyarta da zuciyarta

Annabi ya ce:

“Ta yi imani da ni lokacin da mutane suka kafirta, ta gaskata ni lokacin da mutane suka ƙaryata ni.

2. Sayyidatina Sawda bint Zam‘ah (RA)

·         Mace mai haƙuri da sauƙin kai

·         Annabi ya aure ta bayan rasuwar Khadija (RA)

·         Ta sadaukar da kwanakinta ga A’isha (RA) domin faranta wa Annabi rai

3. Sayyidatina A’isha bint Abi Bakr (RA)

Matsayinta

·         ‘Yar Khalifa Abu Bakr As-Siddiq (RA)

·         Mafi ilimi daga cikin mata

Falalarta

·         Ta rawaito fiye da hadisai 2,000

·         Annabi ya ce:

“Falalar A’isha akan sauran mata kamar falalar Tharid akan sauran abinci.”

4. Sayyidatina Hafsa bint Umar (RA)

·         ‘Yar Umar bn Khattab (RA)

·         Ita ce ta ajiye mushafin Alƙurani a zamanin Abu Bakr (RA)

·         Mace mai yawan azumi da sallah

5. Sayyidatina Zaynab bint Khuzayma (RA)

·         Ana kiranta Ummul Masakinai

·         Ta rasu bayan ‘yan watanni da aurenta

6. Sayyidatina Ummu Salama (RA)

·         Mace mai hikima da basira

·         Ta ba Annabi shawara a yarjejeniyar Hudaybiyya

·         Daya daga cikin manyan malaman mata

7. Sayyidatina Zaynab bint Jahsh (RA)

·         ‘Yar ammin Annabi

·         Allah Ya aura ta da Annabi daga sama

“Sa’annan muka aurar da kai da ita.”
(Suratul Ahzab: 37)

8. Sayyidatina Juwayriya bint Al-Harith (RA)

·         Aurenta ya zama sanadiyyar ‘yantar da bayin kabilarta

9. Sayyidatina Ummu Habiba Ramlah bint Abi Sufyan (RA)

·         Ta yi hijira zuwa Habasha

·         Najashi ne ya aurar da ita da Annabi

10. Sayyidatina Safiyya bint Huyayy (RA)

·         Daga zuriyar Annabi Haruna (AS)

·         Annabi ya ‘yantar da ita sannan ya aure ta

11. Sayyidatina Maymuna bint Al-Harith (RA)

·         Ita ce ta ƙarshe da Annabi ya aura

·         Aurenta ya ƙarfafa zumunci tsakanin Musulmi

Hikimar Yawan Auren Annabi

·         Koyar da mata hukunce-hukuncen addini

·         Ƙarfafa zumunci tsakanin kabilu

·         Kula da zawarawa da marayu

·         Watsa Sunnah ta hanyar yakokinsa

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BABI NA SHA XAYA

‘YA’YAYEN MANZON ALLAH

’Ya’yan Manzon Allah Muhammad suna da matsayi mai girma a Musulunci. Rayuwarsu ta ƙunshi manyan darussa na haƙuri, jarabawa, tausayi da yarda da ƙaddarar Allah. Duk da cewa Annabi shi ne mafi daraja a cikin halitta, Allah Ya jarabce shi da rasuwar yawancin ’ya’yansa tun suna ƙanana, domin ya zama abin koyi ga alumma wajen haƙuri da tawakkali.

Annabi ya haifi ’ya’ya guda bakwai (7): maza uku (3) da mata huɗu (4). Dukkansu daga Sayyidatina Khadija bint Khuwaylid (RA) ne, sai Ibrahim wanda aka haife shi daga Māriyah Al‑Qibtiyya (RA).

’Ya’ya Maza na Manzon Allah

1. Al‑Qāsim bn Muhammad

Shi ne babban ɗan Annabi . Da sunansa ne aka yi wa Annabi kunya da Abul‑Qāsim. Mahaifiyarsa ita ce Sayyidatina Khadija (RA). Ya rasu yana ƙarami a Makka.

Darasi: Rasuwar Al‑Qāsim ta nuna haƙurin Annabi da cikakkiyar yarda da hukuncin Allah tun farkon rayuwarsa.

2. Abdullahi bn Muhammad

Ana kiransa da ayyib da Ṭāhir. Mahaifiyarsa ita ce Sayyidatina Khadija (RA). Ya rasu yana jariri. A lokacin rasuwarsa, mushrikai suka ce Annabi ya zama abtar (wanda zuriyarsa ta yanke), sai Allah Ya saukar da Suratul Kawthar a matsayin ta’aziyya da girmamawa.

“Lalle Mun ba ka Al‑Kawthar.”
(Suratul Kawthar: 1)

3. Ibrahim bn Muhammad

Mahaifiyarsa ita ce Māriyah Al‑Qibtiyya (RA). An haife shi a Madina, ya rasu yana da kusan watanni goma sha shida zuwa goma sha takwas. Annabi ya yi kuka a rasuwarsa, amma ya nuna cikakkiyar yarda da ƙaddarar Allah.

Annabi ya ce:

“Ido na zubar da hawaye, zuciya na baƙin ciki, amma ba za mu faɗi sai abin da Ubangijinmu Ya yarda ba.”

Darasi: Halaccin kuka da nuna tausayi, tare da haƙuri da tawakkali.

’Ya’ya Mata na Manzon Allah

4. Zaynab bint Muhammad

Ita ce babbar ’yar Annabi . Ta auri Abul‑‘Āṣ bn Rabī. Ta rasu a Madina a shekara ta 8 bayan Hijira.

Darasi: Darajar aure da kiyaye amana ko da a lokacin sabani.

5. Ruqayya bint Muhammad

Ta auri Uthman bn Affan (RA). Ta yi hijira zuwa Habasha tare da mijinta. Ta rasu a Madina a lokacin da Musulmi suke Yaƙin Badar.

6. Ummu Kulthum bint Muhammad

Bayan rasuwar Ruqayya (RA), Annabi ya aurar da ita ga Uthman bn Affan (RA). Saboda auren ’ya’yan Annabi biyu da yayi, aka kira Uthman da Dhun‑Nurayn (Mai haske biyu). Ta rasu a shekara ta 9H.

7. Fāṭima Az‑Zahrā bint Muhammad

Ita ce ƙaramar yar Annabi kuma mafi soyuwa a gare shi. Ta auri Ali bn Abi Talib (RA). Daga gare ta ne zuriyar Annabi ta ci gaba ta hanyar Hasan da Husain (RA).

Annabi ya ce:

“Fāṭima yanki ce daga jikina; duk wanda ya cutar da ita ya cutar da ni.”

Ta rasu watanni kaɗan bayan rasuwar Manzon Allah .

’Ya’yan Manzon Allah sun kasance ginshiƙai na darasi ga alumma wajen haƙuri, tarbiyya, tausayi da yarda da ƙaddarar Allah. Rayuwarsu ta nuna cewa daraja a wurin Allah ba ta hana jarabawa ba, amma tana ƙara lada da ɗaukaka ga masu haƙuri.

Auren Nana Fāṭima

Auren Nana Fāṭima (RA) ‘yar Manzon Allah da Sayyidina Aliyu bn Abi Ṭālib (RA) na ɗaya daga cikin auren da suka fi albarka a tarihin Musulunci. Wannan aure ya haɗa gidan Annabci da gidan Jarumta da Ilimi, kuma daga cikinsu Allah Ya azurta Musulunci da jikokin Annabi (SAW)

Nana Fāṭima (RA) Ta kasance: mai tsananin kunya da tsarki, Mai ibada da haquri, Mai ƙaunar mahaifinta matuƙa

Sayyidina Aliyu bn Abi Ṭālib (RA)

Sayyidina Aliyu shi ne:

·        Ɗan ammin Annabi

·        Ɗaya daga cikin farkon masu karɓar Musulunci

·        Jarumi, masani, kuma mai tsananin ƙauna ga Manzon Allah

Annabi ya ce game da shi:

“Aliyu yana tare da gaskiya, gaskiya kuma tana tare da Aliyu.”

Yadda Aka Yi Auren Fatima da Ali (RA)

Neman Auren

Sayyidina Aliyu (RA) ya nemi auren Nana Fāṭima (RA), amma saboda kunya da talaucinsa bai da kayan duniya. Da ya zo wajen Annabi , sai Annabi ya tambaye shi:

“Me kake da shi na sadaki?”

Aliyu ya ce ba shi da komai sai garkuwarsa. Annabi ya ce ya ba da ita a matsayin sadaki, ya aurar masa da Fāṭima.

Sauƙin Aure

Babu almubazzaranci

Babu girman kai

Aure ne bisa tsoron Allah da albarka

Annabi ya yi musu addu’a, ya ce:

 “Ya Allah, ka albarkaci aurensu, ka albarkaci zuriyarsu.”

4. Rayuwar Aurensu

Rayuwar Fāṭima da Ali (RA):

·         Ta kasance mai sauƙi da haquri

·         Sun yi rayuwa bisa ibada, aiki da juna

·         Sun sha wahala amma ba su koka ba

Nana Fāṭima tana niƙa hatsi da hannu har hannuwanta suka kumbura, Aliyu kuma yana aiki tukuru. Duk da haka, Annabi ya koya musu tasbihi maimakon bawa.

5. ‘Ya’yan Fatima da Ali (RA) – Jikokin Annabi

(a) Hasan bn Ali (RA) Shi ne Jikan Annabi na farko ga Annabi, har Annabi ya ce: “Hasan da Husain shugabannin matasan Aljanna ne.”
(Tirmidhi)

Sayyadina Hassan ya kasance mai haquri da son zaman lafiya. Ya kasance mai sadaukar da mulki domin zubar da jini ya tsaya

(b) Husain bn Ali (RA): shi ne jikan Annabi (SAW) na biyu, shi ma ya zamo Jarumi, mai gaskiya, ya yi shahada a Karbala

Annabi ya ce: “Husain daga gare ni ne, ni kuma daga gare shi nake.”
(Tirmidhi)

(c) Zaynab (RA): Zainab ita ma ‘ya ce ga Fāṭima da Ali, ta kasance itama Jaruma mai yawan haquri.

(d) Ummu Kulthum (RA): Ita ma ‘ya ce ga Fāṭima da Ali, ta shahara da tsoron Allah da ladabi

 Darussa daga Auren Fatima da Ali (RA)

1.      Sauƙaƙa aure shi ne albarka

2.      Darajar tsoron Allah fiye da dukiya

3.      Gina gida bisa imani da haquri

4.      Darajar zuriyar Annabi da girmamawarsu

Auren Nana Fāṭima da Sayyidina Ali (رضي الله عنهما) misali ne na aure na Musulunci mai tsarki da albarka. ‘Ya’yansu – Hasan, Husain, Zaynab da Ummu Kulthum – sun zama haske a tarihin Musulunci, kuma su ne jikokin Manzon Allah da Musulmi ke girmamawa da ƙauna.

Allah Ya yarda da su baki ɗaya, Ya haɗa mu da Annabi da iyalansa a Aljanna.

 

 

 

 

 

BABI NA SHA BIYU

AMMOMIN MANZON ALLAH

Ammomi Maza:

Malamai sun ruwaito cewa Abdul-Muṭṭalib yana da ’ya’ya maza da dama, daga cikinsu shahararru su ne:

1.      Al-Ḥārith – Shi ne babba daga cikinsu

2.      Abu Ṭālib – Shi ne wanda ya raini Annabi

3.      Abdullahi – Shi ne mahaifin Annabi

4.      amza bn Abdul-MuṭṭalibSayyidus-Shuhadā, shahidi a Uhud

5.      Al-‘Abbās – Daga zuriyarsa ne aka samu Banu Abbas

6.      Abu Lahab – Ya zamo makiyi Annabi (ya mutu a kan kafirci)

Ammomi Mata:

Daga cikin ’yan Abdul-Muṭṭalib mata, shahararru sun haɗa da:

1.      afiyya bint Abdul-Muṭṭalib (RA) – Ta zamo Musulma, kuma itace mahaifiya ga Zubair bn Awwam (RA)

2.      Ātikah bint Abdul-Muṭṭalib

3.      Arwā bint Abdul-Muṭṭalib

4.      Ummayma bint Abdul-Muṭṭalib

5.      Barrah bint Abdul-Muṭṭalib

Wasu daga cikinsu sun musulunta, wasu kuma sun rasu kafin Musulunci ya bayyana sosai.

Ammominsa sun taka rawa daban-daban a rayuwarsa, wasu suka kare shi (kamar Abu Talib da Hamza), wasu kuma sun yi gaba da shi (kamar Abu Lahab)

Wannan ya nuna cewa gaskiya ba ta la’akari da zumunci, sai bin umarnin Allah.

 

 

 

 

 

 

 

 

BABI NA SHA UKU

MASU HIDIMA GA MANZON ALLAH

Manzon Allah Muhammad ya kasance yana da manyan Sahabbai masu hidima a fannoni daban‑daban: masu tsaro, masu kiran salla, mawaƙa, da masu hidimar gida. Waxannan Sahabbai sun taka muhimmiyar rawa wajen kare shi, isar da saƙonsa, da tallafa masa a rayuwa da jihadi.

Ga wasu daga cikin su:

1. Anas ɗan Mālik (RA) – Ya kasance mai hidimar ga Annabi (SAW)

Asalinsa da zamansa mai hidima

Anas bn Mālik Al‑Ansari daga Banu Najjar ne. Mahaifiyarsa Ummu Sulaym (RA) ce ta kai shi wajen Annabi yana ƙarami, tana cewa:

“Ya Rasulallah, ga ɗana Anas, ka ɗauke shi ya yi maka hidima.”

Annabi ya karɓe shi, Anas ya yi hidima tsawon shekaru goma a Madina.

Halayensa a hidima

·         Ya kasance mai biyayya, ladabi da gaskiya.

·         Annabi bai taba tsawata masa ba, bai ce masa “me ya sa ka yi haka?” ko “me ya sa ba ka yi ba?”.

·         Ya shaida cikakken halin Annabi a gida da wajen gida.

Darajarsa

·         Ya ruwaito dubban hadisai.

·         Ya rayu tsawon lokaci, ya yada ilimi a Basra.

·         Annabi ya yi masa addu’ar yawaitar arziki da zuriya.

Mawaƙan Manzon Allah (Masu kare Musulunci da harshe)

1- Hassan ɗan Thābit (RA) Hassan shi ne babban mawaƙin Annabi . Ya yi amfani da waƙa wajen kare Annabi da Musulunci daga zagin mushrikai.

Annabi ya ce masa:

“Ka yi musu martani, Ruhu’l‑Qudus (Jibril) yana tare da kai.”

2-Abdullahi ɗan Rawāḥa (RA) Shi ma Sahabi ne, kuma mawaƙi gashi kuma jarumi a fagen jihadi. Waƙoƙinsa suna ƙarfafa Musulmi a filin yaƙi, ya yi shahada a Yaƙin Muuta.

3-Ka‘abu ɗan Mālik (RA) shi ma ya zamo mawaƙi mai yawan hikima, ya shahara da labarin tuba bayan Yaƙin Tabuk. Waƙoqinsa suna tattare da gaskiya, nasiha da tsoron Allah.

4-Ka‘ab bn Zuhayr (RA) – shi ma mawaqi ne shi ne marubucin “Banat Su‘ad”, shi ne wanda Annabi ya lullube shi da bargonsa.

3. Masu kiran Sallar Annabi (Mu’azzinai)

(a) Bilāl Al‑Habashi (RA): Bilal ya zamo shi ne mai kiran Sallah (mu’azzini) na farko a Musulunci. Annabi ya zaɓe shi saboda kyakkyawar murya da tsarkin imani. Bilal ya sha wahala a wajen mushurikan Makkah saboda Musulunci. Har Annabi ya ce ya ji takunsa a Aljanna.

(b) Abdullahi ɗan Ummu Maktūm (RA): shi ma Sahabi ne kuma makaho, ya kasance mai kiran Sallah (mu’azzini) tare da Bilal. Annabi yana barinsa a matsayin wakili a Madina idan ya fita jihadi.

An saukar da aya game da shi a Suratul ‘Abasa.

(c) Abu Mahdhura (RA): shi ma ya zamo maikiran Sallah  a garin Makkah bayan fatahu Makkata. Annabi ya koyar da shi lafazin kiran salla kai tsaye.

4. Sauran Muhimman Masu Hidima ga Annabi

(a) Abu Ayyub Al‑Ansari (RA): Shi ne wanda Annabi ya sauka a gidansa bayan hijira.

(b) Zayd ɗan Hāritha (RA): Shi ya zamo Bawan Annabi da ya ‘yanta shi. Ya kasance kamar ɗa a gare shi (SAW).

(c) Usāma ɗan Zayd (RA): Shi Ɗa ne ga Zayd bn Haritha. Annabi ya naɗa shi shugaban runduna tin yana saurayi.

(d) Asmāu bint Abi Bakr (RAا):  Ita ma ta yi hidima ga Annabi (SAW) a lokacin hijira, ana kiranta “Dhatun‑Nitaqayn”.

Masu hidimar Manzon Allah sun kasance ginshiƙai wajen nasarar da’awar Musulunci. Kowa ya bayar da gudummawa bisa baiwar da Allah Ya ba shi: hidima, waƙa, kira zuwa salla, tsaro, ko ilimi. Tarihinsu darasi ne na biyayya, sadaukarwa da ƙauna ga Annabi .

 

 

 

 

 

 

 

BABI NA SHA HUXU

SIFFOFI DA HALAYEN MANZON ALLAH

Siffofin Annabi Muhammad suna daga cikin manyan hujjojin annabtcinsa. Allah Ya haɗa masa kyawawan siffofi na halayya (akhlaƙ) da kamala ta ɗabi’a, har ya zama abin koyi ga dukkan halittu.

Kyawawan dabi’u na Manzon Allah Muhammad su ne tushen shiriya da tarbiyya ga al’umma. Allah Ya haɗa masa kamala ta ɗabi’a, tausayi, adalci da hikima, har ya zama abin koyi mafi kyau ga duk wanda yake neman kusanci da Allah.

Wannan babi zai tattauna siffofinsa tare da Kyawawan dabi’unsa tare da hujjoji daga Al-Kur’ani da Hadisai sahihai.

1)   Gaskiya (A-idq)

Annabi ya shahara da gaskiya tun kafin a ba shi wahayi, har mushrikai suke kiransa Al-Amīn (Amintacce).

Allah ta’ala yana cewa:

“Wanda ya zo da gaskiya, kuma aka gaskata shi, su ne masu taƙawa.
(Suratu Az-Zumar: 33)

Malamai suka ce: wanda ya zo da gaskiyar nan shi ne Annabi Muhammad .

Yazo a Hadisi Abu Sufyan ya shaida wa Heraclius cewa:

“Ba mu taɓa gwada shi da ƙarya ba.
(Sahih Bukhari)

2)   Amana (Al-Amāna)

Annabi ya kasance abin dogaro wajen ajiya da al’amuran jama’a, har ma abokan gābansa suna ajiye masa dukiyarsu.

Allah Ta’ala yana cewa:

“Lallai Allah yana umartar ku da ku mayar da amana ga ma’abotanta.”
(Suratu An-Nisa’i: 58)

Annabi ya fi kowa cika wannan umarni.

3)   Cikar Kyawawan Dabi’u (Husnul-Khuluq):

Dukkan halayensa Alaihissalam cikin maganganunsa, aikisa, mu’amalarsa duk sun kasance bisa daidaito da adalci.

Allah ta’ala yana cewa:

“Kuma lallai kai kana kan kyakkyawan ɗabi’a mai girma.”
(Suratu Al-Qalam: 4)

Yazo a Hadisi: Annabi ya ce:

“An aiko ni ne domin cika kyawawan ɗabi’u.”
(Muwatta’ Malik)

4)     Tausayi da Rahama:

Manzon Allah (SAW) ya zamo mai tausaya wa yara, da mata, da talakawa, har ma da dabbobi.

Allah ta’ala yana cewa:

“Ba Mu aiko ka ba face rahama ga talikai.”
(Suratu Al-Anbiya’: 107)

Yazo a Hadisi: Annabi ya ce:

“Masu rahama, Mai Rahama zai yi musu rahama.”
(Tirmidhi)

5)     Haƙuri da Juriya:

Annabi ya fuskanci tsangwama, duka da ƙauracewa, amma bai rama da zalunci ba.

Allah ta’ala yana cewa:

“Ka yi haƙuri, haƙurinka kuwa ba zai kasance ba sai da taimakon Allah.”
(Suratu An-Nahl: 127)

“Ka yi haƙuri, lallai Allah yana tare da masu haƙuri.
(Suratu Al-Baqara: 153)

Yazo a Hadisi: Yayin da aka jikkata shi Alaihissalam a yaqin Uhudu, sai manzon Alah (SAW) ya ce:

“Ya Allah! Ka gafarta wa mutanena, domin ba su sani ba.”
(Bukhari)

6)     Tawali’u (Ƙanƙantar kai):

Duk da matsayinsa na Annabi da shugaban al’umma, Annabi ya kasance mai sauƙi da tawaliu, yana zama da talakawa, yana gyara kayansa da hannunsa.

Yazo a Hadisi: Annabi ya ce:

“Ni bawa ne, ina ci kamar yadda bawa yake ci, ina zama kamar yadda bawa yake zama.”
(Ahmad)

7)     Adalci da Gaskiya a Hukunci:

Ma’aiki Alaihissalam ya zamo mai adalci da gaskiya a dukkan hukunce hukuncen sa.

Allah Ta’ala yana cewa:

“Lallai Allah yana umartar da adalci.”
(Suratu An-Nahl: 90)

Yazo a Hadisi: Annabi ya ce:

“Da Fatima ‘yata ta yi sata, da zan yanke hannunta.”
(Bukhari da Muslim)

8)     Afuwa da Yafe Laifi:

Ma’aiki Alaihissalam ya zamo mai yawan afuwa da yafiya a dukkan laifukan da aka yi masa, har a ranar Fatahun Makkah, duk da abin da kafirai suka yiwa Musulunci da Musulmai, amma da aka cisu da yaqi saya ce: “Ku tafi, ku ‘yantu.”

Allah Ta’ala yana cewa:

“Ka yi afuwa, ka umarci alheri.”
(Suratu Al-A’raf: 199)

9)   Kunya da Tsarkin Zuciya:

Manzon Allah (SAW) ya kasance mai yawan kunya da tsarkin zuciya.

Yazo a Hadisi: An ce: “Annabi ya fi budurwa kunya a cikin ɗakinta.”
(Bukhari da Muslim)

10)   Ƙauna ga Alumma

Allah Ta’ala yana cewa:

“Lallai Manzo ya zo muku daga cikinku; yana jin nauyin abin da ya same ku, yana matuƙar son alherinku.
(Suratu At-Tawba: 128)

11)   Tausayi da Rahama

Rahamar Annabi ta shafi Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba.

Allah Ta’ala ya faxa a cikin Al-Kur’ani

“Ba Mu aiko ka ba face rahama ga talikai.”
(Suratu Al-Anbiya’: 107)

Yazo a Hadisi Annabi ya ce:

“Masu rahama, Mai Rahama zai yi musu rahama.”
(Tirmidhi)

Kyawawan dabi’u da kyawun halayen Manzon Allah su ne haske ga rayuwar Musulmi. Yin koyi da shi hanya ce ta samun yardar Allah da zaman lafiya a duniya.

“Lallai haƙiƙa Manzon Allah abin koyi ne mafi kyau a gare ku.
(Suratu Al-Ahzab: 21)

 

 

 

 

 

 

BABI NA SHA BYAR

WAFATIN MANZON ALLAH

Wafatin Manzon Allah Muhammad shi ne lamari mafi girman abin da ya taɓa girgiza zukatan Sahabbai da al’ummar Musulmi gaba ɗaya. Duk da kasancewarsa mafi soyuwa ga Allah, rayuwar duniya ba madawwama ba ce, domin Allah Ya ƙaddara mutuwa ga kowane rai.

“Kuma lallai kai ma za ka mutu, kuma lallai su ma za su mutu.”
(Suratu Az-Zumar: 30)

1. Farkon Rashin Lafiyarsa

Rashin lafiyar Annabi ya fara ne kwanaki kaɗan bayan dawowarsa daga Baqi’a‘. Ya fara jin: - Zazzabi mai tsanani da Ciwon kai da Rauni a jiki

Yana cewa: “Ina jin zafin gubar da na sha a Khaybar har yanzu.”
(Sahih Bukhari)

Wannan na nuna cewa wafatinsa ya kasance cikin jarabawa da ladan shahada.

2. Kwanaki na Ƙarshe a Rayuwarsa

(a) Jagorantar Sallah: Duk da tsananin ciwon da yake fama da shi, Annabi yana daurewa ya fita zuwa masallaci don jagorantar Sallah. Sai da ciwon ya tsananta sosai, sai ya ce:  “Ku umurci Abubakr ya jagoranci mutane a sallah.”
(Bukhari da Muslim)

Wannan alama ce ta darajar Abubakr (RA).

 (b) Ziyarar Xakunan Matansa: Annabi ya nemi izinin matansa a bar shi ya zauna a ɗakin Nana A’isha (RA) domin samun sauƙin jinya. A nan ne ya shafe kwanaki na ƙarshe.

3. Shawarwarin Ƙarshe na Annabi

Daga cikin maganganunsa na ƙarshe akwai: - “Ku kiyaye sallah, ku kiyaye sallah.” - “Ku ji tsoron Allah game da mata.” - “Ku kula da bayinku.”

Wannan na nuna muhimmancin ibada, adalci da tausayi a Musulunci.

4. Wafatinsa

Annabi yayi wafati a Ranar Litinin ta cikin Watan Rabi‘ul Awwal Shekararsa: 63.

Annabi ya jingina kansa a kan kirjin Nana A’isha (RA). A hannunsa akwai aswaki, ta taimaka masa ya yi amfani da shi.

Ya kan yi addu’a, sai ransa mai tsarki ya fita cikin nutsuwa.

 

5. Girgizar da Ta Kama Sahabbai

Da labarin wafatinsa ya bazu: - Umar bn Khattab (RA) ya ƙi yarda, yana cewa bai rasu ba. Abubakr (RA) ya shigo, ya tabbatar da wafatinsa, ya sumbaci goshinsa.

Sai Abubakr (RA) ya yi jawabi mai ratsa jiki yace: “Duk wanda yake bauta wa Muhammad, to Muhammad ya rasu; duk wanda yake bauta wa Allah, to Allah Rayayye ne, ba Ya mutuwa.”

Sannan ya karanta fadin Allah ta’ala: “Muhammad ba wani abu ba ne face Manzo; manzanni sun shude a gabansa.”
(Suratu Al-Imran: 144)

6. Wankan, Jana’iza da Binnewa

An yiwa Ma’aiki Alaihissalam wanka da tufafinsa a jikinsa, Sahabbai suka yi sallah a kansa rukuni-rukuni, ba tare da limami ba, aka binne shi a ɗakin Nana A’isha (RA), inda ya rasu.

7. Darussa daga Wafatinsa

Wafatin Shugaba Alaihissalam na nuna cea mutuwa gaskiya ce ga kowa kuma shu Annabi bawa ne na Allah, ba wai abin bautawa ba ne. Sannan an tabbatar da Addinin Musulunci ya cika kafin wafatinsa, sai dai yin ruqo da Al-Kur’ani da Hadisai (Sunnah), kamar yadda yake cewa:

“Na bar muku abubuwa biyu; ba za ku ɓata ba matuƙar kun riƙe su: Littafin Allah da Sunnata.

Wafatin Manzon Allah babban rashi ne, amma saƙonsa ya wanzu har abada. Soyayyarsa ta gaskiya ita ce bin Sunnarsa da kiyaye umarnin Allah.

Allah Ya ƙara tsira da amincinsa ga Annabin rahama, da iyalansa, da Sahabbansa baki ɗaya.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

KAMMALAWA

Wannan Littafin ya yi cikakken bayani kan rayuwa da koyarwar Manzon Allah Muhammad , daga haihuwarsa, zamanin Annabci, hijira, rayuwarsa a Madina, zuwa wafatinsa. Hakanan ya bayyana siffofi, kyawawan dabi’u, masu hidimarsa, da abubuwan da suka faru a lokacin rayuwarsa.

Abubuwan da muka tattauna sun haɗa da: ’Ya’yansa da ammominsa, da yadda ya yi hulɗa da su. Yakokin da yayi

Sahabbai masu hidima, kamar Anas bn Mālik, Bilal Al-Habashi, Hassan bn Thabit, da sauran mawaƙa da muazzinai.

Kyawawan dabi’u da siffofi da suka sa ya zama abin koyi ga Musulmi.

Shigarsa Madina da tarbar Ansar, da kuma kafa ƙaidojin alumma da addini.

Wafati da janarwarsa, da darussan da Musulmi za su koya daga rayuwarsa.

Wannan littafi ya nuna cewa Manzon Allah ya zo ne domin cika kyawawan ɗabi’u, isar da gaskiya, da shiryar da al’umma. Duk wanda ya karanta wannan littafi da zuciya ɗaya, zai fahimci cewa bin koyarwar Annabi shi ne ginshiƙin nasara a duniya da lahira.

A ƙarshe, wannan littafi yana ƙarfafa Musulmi da matasa musamman su riƙa koyi da Manzon Allah , su kiyaye addini, su girmama Sahabbai, su yi kyawawan ayyuka, kuma su yi tunani akan mutuwa da rayuwa ta lahira.

“Lallai haƙiƙa Manzon Allah abin koyi ne mafi kyau ga ku.” (Suratul Ahzab: 21)

 

Comrade Auwal Zakari Ayagi

(Barden Ayagi)

14/12/2025

24/Jumada Thani 1447


No comments:

Post a Comment