Saturday, 28 February 2026

TARIHIN MARIGAYI MALLAM BASHIR HALADU



TARIHIN

MARIGAYI MAL. BASHIR HALADU

(ALQAUMU)

 

 

DAGA XALIBAI

AISHA BADAMASI

SADIYYA MUSA SABI’U

HABIBA IDRIS UMAR

 

DAGA

MAKARANTAR ANWARUL-ISLAMA QOFAR KABUGA KANO

1439AH/2017

Sake Rubutawa

Comrade auwal Zakari ayagi (Barden Ayagi)

27/2/2026 

 

ABUBUWAN DA SU KE CIKIN LITTAFI:

1.     Shafi na farkoi ……................................. 

2.     Abubuwan da su ke ciki …...................... 

3.     Gabatarwa ................................................

4.     Dalilin Rubuta Littafi ...............................

5.     Godiya ......................................................

6.     Sadaukarwa ..............................................

7.     Babi na I ...................................................

8.     Babi na II ................................................. 

9.     Babi na III ...............................................

10.                        Kammalawa ............................................

                       Masamar Bayani .....................................

 

 GABATARWA

Bismillahir Rahmanir Raheem, Wasalallahu Alannabiyyl kareem

Bayan haka, na himmatu ne wajen sake kwafar wannan littafi da waxannan xalibai masu albarka sukayi ne shekaru tara da suka gabata akan abokin mu kuma amininmu, sakamakon ‘yar qanwata Sadiya da ta bani labarin cewa sun tava rubtua littafi akan rayuwar Mal. Bashir.

Sai mamaki ya kamani kasancewar yanda muke dashi ace an rubuta littafi bani da labara, sai nace ta bani in duba, ta kawomin littafinn , cikin ikon Allah na kasa karancece da na duba sai na jiyeshi, yakai kusan shekaru biyu a ajiye, a cikin wannan satin tayimin waya tanaso in dawo mata da shi, sai a jiya Juma’a 27/2/2026, na xaukoshi sai na xauki hoton littafin gaba xayan sa da wayata, nayi amfani da wata manhaja na mayar da hoton zuwa rubutu, na mayar dashi kan computer, tin da na dawo daga masallacin Juma’a har zuwa daf da shan ruwa ina aikin.

Sai na bari yau Asabar don nayi gyare gyare don in xora shi a yanar gizo-gizo, da safe in buxe wayata sai naga qanin Mal. Bashir ya saka a shafin san a facebook cewa, jiya juma’a Mal. Bashir yak e cika shekaru goma da rasuwa, sai nace wannan karama ce ta malamin domin duk shekara in ta kewayo insa yin posting don ayi masa addu’a, amma wannan shekara sai namanta, amma kuma sai nayi wani babban aikin akan littafin tarihin rayuwarsa.

Allah ya jiqan mal. Bashir, domin tare muke xaukan karatu a makarantar Mal. Auwlu Isa Yakasai, komai tare muke yi, duk wasu karatuttuka tare muke, da Mauludi da sauransu, don haka dukkan kyawawan halayen sa da akaji a wannan littafi, kaxan ne daga ciki, domin ko iya gudun duniyarsa kaxai aka xauka sai ayi littafi guda akansa, balle azo fagen haxuri, da kyautata abokan sa, balle uwa uba azo fagen qaunar shugaba Alaihissalam,

Allah ya jixansa Allah ya yafe masa Amin.

Comrade Auwal Zakari Ayagi

(Barden Ayagi

27/02/2026

  

GABATARWA

Da sunan Allah Mai Rahma Mai Jinqai, dukkan yabo da godiya da tsarkakewa da kirari sun tabbata ga Allah Maxaukakin Sarki, Mamallakin halittu mai kowa mai komai, wanda bai haifa ba ba a haife shi ba, sannan wani kini bai kasance a gare shi ba.

Tsira da amincin Allah su qara tabbata ga Shugabanmu Annabinmu Muhammadu, da Alayensa da Sahabbansa da duk waxanda su ka yi koyi da shi har zuwa ranar Al’qiyama.

Bayan haka, ya ‘yan’uwa Musulmi, muna farin cikin gabatar muku da wannan Littafi mai tarin al’barka.

Littafi ne da ya qunshi abubuwa masu anfani ga al’ummah cikin tarihin rayuwar marigayi Mal. Muhammad Bashir Haladu (Al’qaumu), tun daga haihuwarsa har zuwa rasuwarsa amma a takaice. Allah ya taimake mu bisa wannan aiki, shi kuma ya ji kan sa amin summa amin.

 

 DALILIN RUBUTA LITTAFI

Lallai akwai dalilai masu yawa game da rubutun wannan littafi mai al’barka su ne kamar haka:

  • Wanda bai san shi ba zai san shi.
  • Wanda ya san shi ya qara saninsa.
  • Wanda ya mance da shi ya tuna shi.
  • Wanda bai mance da shi ba ya xora a kan inda ya ke.
  • Kwaxaitarwa game da ayyukan al’khairi.

Allah ya taimake mu. Amin.

 GODIYA

Muna godewa Allah (SWT) mawadaci mai azurtawa, wanda ake nufa da duk wata buqata, mabuwayi mai hikima cikin dukkanin al’amuransa na fili da na boye.

Bayan haka zamu mika cikakkiyar godiyarmu ga malaminmu Mal. Abdullahi Baballe wanda shi ne ya doramu a hanya domin mu yi wannan rubutu akan wannan bawan Allah, muna fatan Allah ya saka masa da al’khairi, ya saka masa da sanya shi cikin al’jannarsa ta firdausi, ameen summa ameen.

 

 SADAUKARWA

Muna sadaukar da wannan Littafi mai Al’barka ga iyayenmu da malaman makarantarmu na islamiyya jumlatan, sannan malamai, wato Mal. Abdullahi Sabi’u Baballe a kevance. Allah ya sa duk abin da ya koyar damu ya zamo mafi al’khairi agaremu ameen.

 

BABI NA FARKO

Bayani Daga Gidan su Marigayi Mal. Bashir Haladu

An haifi Mal. Bashir a Unguwar Mandawari/Magashi wadda ke a nan birnin Kano, a ranar 11/10/1976, bayan an haife shi sai mahaifinsa ya dawo Qofar Kabuga.

Mal. Bashir ya halarci makarantu da dama, kama daga makarantun addini da ma na zamani, kaxan daga makarantunsa na addini sune:

  • Kusan Mal. Bashir Haladu ya fara da makarantar islamiyya wacce a keyi da daddare mai suna Najahul Islam Kabuga ta Mal. Rabi’u.
  • Sannan ya samu halartar makarantar Yaqinil Islam Qofar Kabuga ta Mal. Alhassan Xantsoho.
  • Makarantar Karatun zaure ta Mal. Auwal Isah Yakasai.
  • Makarantar Karatun zaure ta wajen Mal. Nasiru Khamis (Mai sunan malam).

Baya ga waxannan makarantu, Mal. Bashir ya halarci makarantu da dama gaban manyan Malamai a gurare da dama a wajen wannan unguwa, kamar haka:

  • Makarantar Shaikh Karibullahi Shaikh Nasir Kabara.
  • Makarantar Shaikh Sidi Musal-Kasiyuni Shaikh Nasir Kabara.
  • Makarantar Shaikh Abdul-Jabbar Shaikh Nasir Kabara.

Sannan a bangaren karatun zamani (boko) Mal. Bashir Haladu (Al’qaumu) ya halarci waxannan makarantu kamar haka:

  • Ya fara da halartar special primary school da ke Qofar Kabuga a shekarar 1983 zuwa 1988.
  • Ya tafi zuwa makarantar Secondary School wacce ta ke a Kofar famfo (GSS Gwauron Dutse, Kano) ya yi junior.
  • Sannan ya cigaba da senior secondary duk dai a GSS G/Dutse daga shekarar 1988 zuwa 1994.
  • Daga nan sai ya tafi kwalejin tarayya ta F.C.E, Kano inda ya yi PRE-NCE a shekarar 1995 zuwa 1996, ya gama F.C.E ya samu certificate na NCE, daga nan sai ya samu aikin koyarwa a secondary school wacce ta ke a unguwar Sheka. Sannan aka dawo dashi makarantar C.E.R.C cikin K.E.R.D wacce ta ke a gandun albasa ya yi wasu shekaru, sai aka sake dawo da shi zuwa secondary school ta W.T.C da ke Kofar famfo.
  • Ya samu halartar Semena ta National Mathematics Centre, a birnin tarayya Abuja Nigeria, a shekarar 2003 8/8 (December). Sannan a 2004.
  • Ya samu certificate na taron inuwar Jama’a Kano wanda ya samu certificate of forum a 24 July, 2004.
  • Ya samu admission a B.U.K Department of Mathematics (tsangayar koyar da lissafi) a shekarar karatu ta 2004/2005 zuwa 2010.
  • Ya kamala sai ya tafi bautar qasa shekara xaya a jihar Dalta (Delta State) a shekarar 2011.
  • Ya samu halattar yin rijista a haxaxxiyar qungiyar malaman ta qasa, ya samu certificate of teachers 26 June, 2007. Daga nan sai sakamakonsa ya fito na BUK a 9 April, 2008.
  • Daga nan sai ya samu certificate of Merit Award.
  • Daganann ya hallaci makarantar koyan computer a Gateway Computer Institute 2 Nubember, 2009 yagama kuma sun bashi certificate wanda ya samu Distiction (wato karshen daraja ta sakamako).

Waxannan su ne makarantun da ya samu halarta na zamani. Mal. Bashir kusan a iya cewa ya kammala shirye-shiryen da su ka kama ya quduri niyyar komawa cigaba da wannan karatu na zamani domin samun shaidar digiri na biyu a Jami’ar Amadu Bello da ke garin Zariya cikin jihar Kaduna (A.B.U Zaria), sai dai Allah Maxaukakin Sarki bai cika masa wannan buri ba, Allah ya karvi rayuwarsa kafin ya fara karatun.

Daga nan Mal. Bashir Haladu ya samu yin Aure, inda Allah ya qaddara masa auren Matarsa mai suna Aminatu Mukhtar Umar Kabuga (Ummi), har Allah ya azurtasu da samun zurriya, inda su ka haifi ’ya’ya guda uku, biyu mata, xaya namiji, wato Fadimatu Amatul-jabbar (Ummulkhairi), na biyu kuma Muhammadu Fatihu, sai ta uku ita ce Bushranatu, wanda aka haifa kenan bayan ya rasu.

Amma kafin ya rasu ya samu koyarwa a qarqashin kwalejin tarayya ta Kano Federal College of Education, Kano (F.C.E) 27 November, 2013 (Lecturer III Department of Science) inda ya ke koyar da mathematics (Ilimin lissafi).

Mal. Bashir ya ci gaba da mu'amalolinsa da al'umma daban-daban, da ma kungiyoyi na addini, kamar Kungiyar sharifan kano, da kuma kungiyoyi na yabon Annabi Salalllahu alaihi wasallam, da kuma jajircewa kan jawo hankalin matasa kan tsayuwa bisa yiwa addinin musulinci hidima da naci a kan neman ilimi.

Mal. Bashir baya ga jajurcewarsa a wannan lamari bai gushe ba har sai da shi ma ya assasa makarantu ko majlisai wadanda yake zama domin koyar da jama'a ilimin addini. Wasu daga cikin waxannan makarantu:-

·        Makarantar koyar da matasa a masallacin juma'a na Sharu Lawan.

·        A bangaren mata ma akwai makaranta wadda su ke zama da ba'arin 'yan'uwansa matan aure.

·        Sannan ya koyar da majalin marigayi Mal. Auwalu Isa Yakasai bayan rasuwar Malamin, sai dai bai xauki tsawon lokaciba, Allah ya yi masa rasuwa.

Mal. Bashir ya yi rayuwa mai kyau, inda ya zauna da kowa lafiya har izuwa 27 Febuary, 2016 wanda a ranar Allah ya yi masa rasuwa.

Mal. Muhammadu Bashir Haladu (Al'qaumu) ya rasu ya na xan kimanin shekaru Arba'in dai-dai, ya kuma rabu da iyayensa lafiya da dukkanin 'yan uwansa da maqotansa da kuma duk wanda Allah ya sa su ka yi mu'amala tare da shi. Mu na fatan Allah ya yi masa rahma saboda Manzon Allah Alaihis salam.

Wannan shi ne taqaitaccen bayani daga gurin mahaifiyarsa

Qarin bayani daga wajen Mahaifiyarsa:-

Mahaifinsa Alh. Haladu ya cigaba da cewa: Mal. Bashir ya yi Makarantar Allo ta Malam Hasan Muqaddami a Unguwar Mandawari cikin Birnin Kano (wato tun ya na karami kenan kafin su dawo wannan unguwa ta Kabuga).

Mal. Bashir mutum ne ba mai girman kai ba, ya na da kyakkyawar mu'amulla da mutane, ba shi da abokin gaba ko faxa, ya na da rikon amana da zuminci, domin kuwa a duk sati ya na ziyartar 'yan'uwansa mata a gidaddajin aurensu, gami da karantar da 'ya'yansu, har ita mahaifiyarsa su na zama da safe su yi karatu.

Haka nan Mal. Bashir ya na ziyartar Malamai da sauran bayin Allah a dukkanin sati ranakun Asabar ko Lahadi, sannan uwa uba Mal. Bashir ya na da yawan ziyartar Waliyyan Allah, rayayyu da wadanda su ka rasu.

Mal. Bashir mutum ne shi wanda bai damu da sanya kaya masu tsada ba, idan aka tambaye shi mai ya sa ba ya son sanya kaya masu tsada tunda dai ya na da hali?, sai ya ce: Gani ya ke yi kamar zai banbanta da sauran mutane.

Mal. Bashir ba ya zaman Majalisar hirarraki tun kafin ya yi aure har izuwa sanda yai aure da ma bayan ya yi aure, daga xaki sai masallaci. Ba ya banbance gidan qannansa da gidan yayyansa, duk zuwa ya ke yi tare da hidimta masu.

Akwai wani lokaci da ya je gidan 'yar'uwarsa ya tarar ta na naquda za ta haihu kuma ga shi gidan ba kowa, haka yai ta zurga-zurga a gidan kasancewar shi ba mace ba ne ballantana ya yi mata abin da mace kewa 'yar'uwarta mace a irin wannan yanayi, amma sakamakon haka sai kawai yai ta yin Addu'oi, haka kuwa cikin ikon Allah ya zamo shi ne wanda ya karbi wannan haihuwa tata.

Mal. Bashi ya kasance idan yana karatun Sirar Annabi Salalllahu alaihi wasallam yana yawan shiga hali!, har wasu lokutan ma matarsa za ta zo ta zauna a kusa da shi amma bai san ta zo ba, har sai bayan ya gama karatun sai ya ce da ita: Yaushe ki ka zo nan ban sani ba?.

Allah yai masa wata baiwa a tafin hannunsa <Allahu Muhammadu da kuma LA'ILAHA ILLALLAH». A yanda mu ka samu bayani Mahaifiyarsa ta ce mana ko ita kanta ba ta san da wannan baiwar ba, sannan a lokacin da ya zo rasuwa sai na tafin kafarsa su ma su ka bayya, wanda sai a lokacin ne a ka gani baki xaya.

An yi wani lokaci da a ke wahalar ruwa, rijiyar gidansu ta qafe, a nan sai ya yi wa rijiyar tofi, tun daga lokacin ba ta qara kafewa ba, kuma ba su kuma yin wahalar ruwa ba har izuwa yanzu.

Kafin rasuwar Mal. Bashir sai da Mal. Nasir Mai Sunan malam (shugaban halararsu ta ziyara) yai wani mafarki da Annabi Salalllahu alaihi wasallam cewa a cikin xalibansa akwai wanda Manzon Allah Salalllahu alaihi wasallam ya yi wa sa hannu (Sign), amma ba a gane ko wane ne ba sai da Mal. Bashir din ya rasu sannan tukun aka gane cewa shi ne. Allahu Akbar Allah ya ji qansa da Rahmah amin summa amin.

 

BABI NA BIYU

Bayani daga wajen Amina Mukhtar matar Marigayi Mal. Bashir Haladu. Ta fara da cewa:-

Assalamu alaikum wa Rahmatullahi Ta'ala wa barakatuhu. Bayan haka kun nemi da na yi muku xan taqaitaccen bayani game da tarihin marigayi Malam Bashir tun farkon haxuwarmu da shi har izuwa rasuwarsa:

To ni dai suna na Amina Mukhtar Umar 'Yar garin Kano Unguwar Q/Kabuga.

Na fara sanin Malam Bashir ta hanyar aiko min da saqon wasiqa da ya yi, a ciki ya ke mini bayanin yabawa da tarbiyyar gidanmu da soyayyarmu ga Annabi Salalllahu alaihi wasallam da makamancin haka, ya aiko min da wannan wasika ne a ranar 13/7/2009, amma a lokacin ni ma zan fara jarrabawa a Makarantar Ligal, na ba shi uzuri na da ya bari na kamala, sai kuwa ya ce ya amince.

To bayan mun gama jarrabawa sai kai tsaye aka bi ta bangaren Mahaifina Alh. Mukhtar ya kira ni yai min bayani cewa shi dai ya yaba da Halkalin Mal. Basher, ga shi kuma Mutum ne mai Ilimi da sanin ya kamata, ya ce na yarda da wannan buqata, nan take na ce na yarda. Tun da Mal. Bashir ya fara zuwa waje na gaba xaya halinsa sai dai a ce son barka! To abin sani dai shi zance a na zuwa ne don a yi hira, amma shi kuwa zuwa ya ke yai mini karatu da qasidu na yabon Annabi Salalllahu alaihi wasallam, to kun ga kenan idan har mun yi hira magana ce ta walimar aurenmu, da lokaci ya gabato, ya sanya min littattafai don na koya kamar haka:

الأحاديث المختار.

. المديح ة برد.

. الخيرات دلائل.

. برزنجي.

Ga kuma kasidu da ya ke yi min idan mun kammala karatu, sai mu rufe da kasidun kamar haka:

[1]الله نور يا بك وسهلا أهلا.

Da kuma:

قلبي ثتب الحبيب محاة في القلوب بلقم يا

Da kuma:

Kallonka Rahama ne Kallemu ya Masoyina [2]

Sannan da:

Ya Dan Baiwa Sannu Annabi Gatan kowa. [3]

To 'Yan uwa an xaura aurenmu da marigayi Mal. Bashir bisa Shari'ar Musulunci da bin Sunnar Ma'aikin Allah Salalllahu alaihi wasallam cikin yardarmu da qaunar junanmu a ranar Lahadi 19/12/2010 dai-dai da 13-01/1432AH da safe. [4]

Allahu Akbar Allah ya ba mu zaman lafiya ni da shi da fahimtar halayen juna, tun ana samun savanin fahimta har dai mu ka saba, sai shi dai Mal. Bashir Baqadire! ni kuma 'Yar Tijjaniyyah ce, amma bai ce na dawo tasa xarikar ba, kuma bai hana ni yin tawa ba, kai har ma idan ya ga ban yi zikirin safe na xarikar tawa ba zai yi min magana ya ce na daure na zauna na yi. [5]

Zama ya fara nisa na san abin da ya ke so da wanda ba ya so. Marigayi Mal. Bashir Mutum ne bawan Allah mai koyi da halayen Manzon Allah Salalllahu alaihi wasallam cikin yawaita Zikirai, Salati, Istigfari, Addu'oi da sauransu.

Mal. Bashir ya na da Ilimi kuma ya na qara nemansa, abin mamaki duk Addu'ar da za a ce masa ta Ilimi ce sai ya yita duk saukinta duk wahalarta, zai yi ko sau xaya ne a rana[6], ya na naci wajen neman Ilimi da aiki da shi, masamman Al'kur'ani Mai Girma da Hadisi da fiqhu da sauransu, na daga dukkanin abin da zai kai shi ga Halarar Ma'aikin Allah Salalllahu alaihi wasallam.

Mal. Bashir Mutum ne Mai qaunar Ahlin gidan Manzon Allah Salalllahu alaihi wasallam. duk wanda ya zauna da shi ba zai so su rabu ba, saboda hirarsa itace karatu da faxin a bi Allah a bi Manzon Allah Salalllahu alaihi wasallam.

Mal. Bashir ba ya iya tsawaita hirar duniya amma sai ya iya kwana ya na magana a kan bayin Allah.

Akwai wata Rana da na ke tambayarsa a kan tarin littattafan da ya fansa na ce: amma na ga koyarwar da ka ke yi ta makarantar Boko Lissafi ka ke koyarwa?. Sai ya ce: Ai Allah ne ya qaddara na koyar da Lissafin tun da a nan abinci na ya ke, amma na fi sha'awar Arabic Islamic. Ya ce bai tava zuwa Makaranta don ya koyi Ilimin Nahawu ba amma ga shi Allah ya ba shi. Mamakin ya isa. Allah ya karvi ayyukansa amin."

Mal. Bashir ya rasu da burin zai fansshi wasu manyan littattafai na Addini masu mujalladai da yawa, kasancewar da ma shi kusan duk wata idan ya xauki albashi to akwai kuxin fansar littafi ko aikin wasu takardu na amfanin Musulinci. kuma ina ma za a ce Ahlinsa su yi masa wani karin gata, su yi amfani da littattafan da ya bari wajen boxe masa wajen bincike (Laburare) da sunansa, a yi tsari, inda xaliban ilimi za su dinga zuwa su na bincike, hakan zai qara yawaita masa lada da haske. Sannan su duba akwai littattafai da ya rubuta, wasu ma bai kammalasu ba ya rasu, su fito da su a tace su a dinga koyarwa da su ga 'ya'yan al'ummah.

Har yau daga halayen Mal. Bashi akwai:

·        Kaudakai.

·        Juriya da yafiya.

·        Iya Mu'amullah da Mutane.

·        Barkwanci.

·        Haquri.

·        Zuminci.

·        Son ya ga waninsa ya qaru.

·        Amsa gayyata masamman ta mauludin Annabi Salalllahu alaihi wasallam, har ya na cewa: Ko xan jariri ne ya gayyace ni zan je ko don a qara ba su kwarin guywa.

·        Qokarin rikon Amana da cika Alkawari ko da kuwa zai takura wa kansa.

·        Ya na son danginsa sannan nima ya na son nawa dangin.

·        Yana da girmama malamansa a duk inda su ke.

·        Yana girmama duk wanda ya zo wajensa neman Ilimi ko suka haxu wajen neman Ilimi.

·        Sam ba shi da riqo, domin ko ni da na ke kasan shi a matsayin matarsa idan mun sami savani shi ne yake ba ni hakuri. Allah ya ba mu Albarkacinsa ya haskaka Kabarinsa, ya bamu Albarkar bayin Allah amin.

Allah Subhanahu wa Ta'ala ya azurta mu da 'Ya'ya uku ni da Mal. Bashir, biyu mata xaya na miji, su ne:

1) Muhammadu Fatihu Bashir.

2) Fadimatu Bashir (Amatul-Jabbar)

3) Bushira Bashir.

Biyu daga cikinsu sun fara rayuwa da mahaifinsu sun ganshi ya gansu, sun yi sabo da shi.

Mal. Bashir yana jin kunyar fita da 'ya'yansa waje, amma ya kan iya zama da su, ya shiga ransu sun shiga ransa su ne Amatul-Jabbar da Muhammadu Fatihu. Sai xayar wadda ita ce Bushira, Allah bai qaddara za su ga junansu ba, domin kuwa ya rasu da kwanaki talatin da tara aka haife ta, sai dai ta ji tarihinsa ta ga hotonsa. Allah ka raya su ka sanya haske a rayuwarsu Allah ya haxa mu duka a Al'jannar Fiddausi, Allah ka sanya Albarka ga duk wani maraya na musulmi amin.

 

RASHIN LAFIYARSA

Mal. Bashir ya kwanta rashin lafiya bayan dawowarsa daga wani xaurin auren da ya je a garin Gora, ranar Lahadi, ya tashi da amai, Ranar Litinin, tun daga ranar babu abin da ya qara shiga cikinsa, ko ya ci sai ya amayo shi, mu na zaune ya ki zuwa Asibiti har ranar laraba, to sai wani abokin aikinsa na FCE ya zo duba shi sai su ka tafi Asibiti tare, sai Mal. Bashir yai yo min waya cewa: An kwantar da shi a Asibitin, ya ce min na gaya wa Mahaifiyarsa, sai kuwa na gaya mata, mu ka tafi Asibitin tare da ita, a lokacin ni ma ina fama da rahin lafiya, shi ya sanya ya ce mata bai yarda ta dinga kwana a asibitin ba saboda ita ma ba ta da lafiya, sai ta roqe shi al'farmar ya barta ta dinga zuwa duba shi, sai ya ce mata ya yarda. To na koma asibitin ranar al'hamis, mu na zaune ni da Mahaifiyarsa kamar bayan sallar La'asar kawai sai mu ka ga ya tashi daga barci ya sauko daga kan gado ya na cewa: Ga ni nan!. sai mu ka rike shi ya na cewa mu cika shi, can sai ya fara fadin:

 

Ya na ta fada ya na cewa mu cika shi ya tafi kawai, sai mu ka fara Addu'oi har Allah ya sa yai barci, to tun wannan barcin bai farka ba har lokacin komawa ta gida ya yi, kimanin karfe sha xaya na dare11:00, na koma Asibiti Ranar Juma'a na iske cewa barcin dai ya ke yi bai farka ba, duk wanda ya je duba shi a ranar har zuwa dare ba zai gan shi ido biyu ba, sai na tambayi Mahaifiyarsa cewa: Tun barcin jiya ne har yanzu bai farka ba?. Sai t ace: ai ya tashi misalign karfe uku na dare3:00 ya ci gaba da fadin:

Da kuma:

To a nan ne sai Likita yai masa Allurar awa ishirin da hudu. Kusan zan dawo gida sai mu ka ji numfashinsa ya na fita kaxan-kaxan sai Likita ya zo ya ce ai allurer ce haka amma za ta sake shi, shi ya sa numfashin ya ke haka, wayyo a ranar dai na so na kwana amma da na tina maganar shi haka na xau shirin komawa gida, Likita yai min tambayoyi a kansa sosai, masamman da su ka ga ya na tashi da karfinsa ya na Addu'o’i da kyar a ke kwantar da shi na amsa masa abin da zan iya, su ka tabbatar min cewa idan na dawo gobe zan tarar da shi ya na cin abincinsa, na kwantar da hankalina sai na ce to, na taho gida na gaya wa babana.

Gari ya na wayewa ina shirin tafiya asibitin, na bar su fatihu a gida Amira qanwata ta shirya su su tafi gidanmu sai na ji daga nesa Masallacin Malam Anka a na sanarwa cewa an yi rasuwa amma ban ji wa a ka ce ya rasu ba, kawai na ce Allah ya jikan wanda ya rasu, kawai sai ga qanwata Nusaiba ta shigo ta ganni a tsaye ta ce min ina zan je?, na ce mata asibiti mana, sai ta ce min na jira wasu zasu zo mu tafi tare, ba ta san asibitin ba, sai na ce mata to, ta ce na je na zauna kafin su zo, ai zaman da na yi sai ko a Masallacin Marigayi Sharif Lawan akai sanarwa cewa Mal. Bashir Allah yai masa rasuwa.

Allah ya yi masa rasuwa a ranar Asabar 18/5/Hijira 1437 dai-dai da 27/2/ 2016.

Mal. Bashir Haladu ya sami kyakkyawar shaida da yabo, 'Yan Qofar Kabuga faxi su ke an yi rashi babba. Mal. Bashir ya sami waxanda su ka raka shi zuwa gidansa na gaskiya babu adadi, yanda ake faxar yawan Jama'ar sai dai godiya kawai, Allah ya sa 'ya'yansa da ni kaina Matarsa da 'yanuwansa mu yo kyakkyawan halayensa da duk masoyansa. Allah ya jikan Mal. Auwal Isa Yakasai Malamin Malam Bashir, Allah ya jikan dukkanin Malamanmu da dukkanin Musulmi Masoya Allah da Ma'aiki Salalllahu alaihi wasallam da Sahabbansa da Ahlisa Amin.

Mal. Bashir ya rubuta Littatafi mai suna: [7]

                                                                

Mal. Bashir ya rasu ya bar Mahaifinsa da Mahaifiyarsa da Matarsa da 'Ya'yansa uku da yayye da qanni maza da mata.

Mu na godiya ga dukkanin Masoyansa, Allah ya saka musu da al'khairi ya bar zuminci amin.

 BABI NA UKU

RAGOWAR BAYANAI

Bayani daga Gidan Marigayi Mal. Auwalu Isah Yakasai (Jigon kadiriyya a Qofar Kabuga):

Haduwarsu da Mal. Auwalu Isah da shi:

Da farko dai sun fara haxuwa da shi a makarantar Gwamnati ta GSS G/Dutse da kusa da kofar famfo a matsayin xalibinsa, tun daga nan ne sai Mal. Auwalu ya yaba da halayen Mal. Bashir da hazaqarsa da biyayyarsa ga Malamansa, sai Mal. Auwalu ya nemi da Mal. Bashir ya dinga zuwa wajensa xaukar karatu, kasancewar dukkan Malami ya na so ya samu mai irin halayen Mal. Bashir a cikin xalibansa, masamman wakilci da gudanarwa.

Mal. Bashir ya fara tun daga karatun littafin Ahalari har zuwa tafsirin Al'kur'ani mai girma, sannan ya karanta littattafai da dama a wajen Mal. Auwalu, daga cikin Litttattafan da ya karanta a wajen asa akwai:

·        Ishmawuy.

·        Kawa'idi.

·        Risalah.

·        Iziyyah.

·        Arba'una Hadis.

·        Bulugul-Maram.

·        Riyadus-salihina.

·        Muwadda Imam Malik

·        Sahihul-Bukhari.

·        Sahihul-Muslim.

Da sauransu [8]

Sakamakon haka ne ya zamo idan an gayyaci Mal. Auwalu zuwa Walima ko wani abu mai kama da haka, su na tafiya tare da Mal. Bashi da sauran xalibai irin su Auwal Zakari Ayagi domin shi ne babban alamjirin Malam, da su Mal. Kabiru Bello Iman a lokacin, har ta kai ta kawo ma idan an gayyaci Mal. Auwalu a wasu lokutan sai ya tura Mal. Bashir ya wakilce shi a wajen.

BIYAYYARSA GA MALAMANSA

Duk wata biyayya da ta kamata xalibi ya yi wa malaminsa to Mal. Bashir ya yi wa Malamansa, ta haka ne ma ya sa idan Mal. Bashir ya doso Malamansa tun daga nesa ya ke cire taaklminsa

Haka nan idan Mal. Bashir ya je xaukar Karatu gidan Mal. Auwalu har durkusawa ya ke ya gaida Matansa, ya na yin haka ne don girmamawa ga Mal. Auwalu, domin al'barkar Ilimi ba ta samuwa sai ta irin hakan.

Mal. Bashir ya kasance idan ya je karatu ya tarar Mal. Auwalu ya na yin barci to ba ya tashinsa!, zai jira shi har sai ya tashi koda kuwa zai kai karfe xaya ne na dare, har Matan Mal. xin su zo za su tashe shi sai Mal. Bashir ya ce a’a ka da a tashe shi, haka nan idan lokacin damuna ne zai taho ana yayyafi idan ya sami Mal. Ya na cikin xaki haka zai zauna a tsakar gidan ba zai shiga ba, har sai wata daga cikin Matan Malam ta gan shi sannan su yi magana ta ce ya shiga xakin.

Gaskiya Mal. Bashir Mutumin kirki ne ya na daraja 'ya'yan Malaminsa su ma kuma su na girmama shi, wallahi biyayyar Mal. Bashir ba za ta kwatantu ba, domin kuwa ba mu san ta inda za mu fara ba, har sai da ta kai ta kawo cewa Mal. Auwalu ya riki Mal. Bashir abokin sirrinsa, sirrin da ko Matansa da 'Yayansa ba su san abin da su ke tattaunawa ba, saboda gaskiya da riqon amanarsa, Ubangiji Allah ya jikansa da Rahma amin summa amin.

BAYANI DAGA MAKWABTANSA:

A cikin Al'umma samun irin Mal. Bashir sai an duba, wallahi da yaro da babba idan Mal. Bashir ya gan shi kafin ya durqusa ya gaishe shi, shi za ka ga ya na qoqarin durqusawa ya gaishe shi, a matsayinsa na Malami.

Haka nan a lamarin maqwabtaka samun maqwabci irin Mal. Bashir ba a ko ina ba, ba dai ka ga Mal. Bashir shi da wani su na rigima ba, Mal. Bashir Mutum ne mai son zaman lafiya da kare dukkanin haqqin mai haqqi.

Mal. Bashir ya tava baiwa maqwabtansa wani labari lokacin da su ka tafi bautar kasa a jahar Dalta, cewa ya tava musulintar da wani kafuri, to a garin akwai yahudawa waxanda ba sa yin addini sai addinin hindu, to a cikin yahudawan nan akwai wani, wanda kullum ya na ganin Mal. Bashir ya na yin Sallah, sai ya ke tambayarsa cewa: wai me ka ke yi haka?, sai Mal. Bashir ya ke ce masa: Au kai ba ka san wannan addinin ba?, sai ya ce da shi: ey, ban san shi ba, sai Mal. Bashir ya ce masa: wannan shi ne Addinin da Allah ya umarce mu da mu yi, sai bayahudan ya ce da shi: Idan ka yi wannan shi ne ka yi addinin gaskiya?, sai Mal. Bashir ya ce da shi: tabbas wannan shi ne addinin gaskiya!!!. Sakamakon haka ne sai wannan bayahuden yayi sha'awar addinin musulinci, sai kuwa Mal. Bashir ya fara koya masa al'amuran addinin musulinci a voye, duk ranar Juma'a idan za su je masallaci sai ya biya xari uku na mota sannan zai je masallaci saboda a garin da ya ke babu masallaci, haka dai Mal. Bashir ya qoqarin rabo wannan mutumi da garinsu bayan sun gama bautar kasar, wannan bawan Allah ya karbi Musulinci sanadiyyar Mal. Bashir ALLAHU AKBAR. [9]

Mal. Bashir ya na son kyautatawa mutane, a yadda mu ka samu labari cewa a cikin abokansa akwai wanda duk sanda Mal. Bashir ya karvi Al'bashinsa ya na xauki wani abu daga cikin kuxin ya ba shi saboda tausayi da jinkan marar sa karfi.

Maqwabcinsa Yusi mai awo idan wata ma'amulla ta mutunci ta haxa su da Mal. Bashir ya kan kyautata masa sosai, sannan idan ya yi wani abu wanda ba dai-dai ba Mal. Bashir ya kan kira shi gefe ya ce masa ya dinga haquri da lamarin duniya.

Allah ka jikan Mal. Bashir da Rahma, mu ma idan ta mu ta zo ka sa mu cika da Imani Al'barkar Shugaba Salalllahu alaihi wasallam Amin summa Amin.

FA'IDAH

Lallai zai dace a ce kafin a kamma wannan littafi a kawo kadan daga bayanan da ke cikin littafinsa da ya wallafa mai suna) inda a muqaddamar littafi ya fara da cewa:

"Na ga cewa babu makawa a gare ni da na xan rubuta wani abu wanda Allah zai warkar da qirazan Muminai da shi, ya tafi da ruxi da shi, don magantar abin da ya zo daga shashin malaman karshen zamani, kamar xan Baaz da sauran waxanda su ka jibince shi su ka mara masa baya (wajen tsaurin kansu a hakkin Annabi) a inda su ke cewa: Annabi (SAW) ba abin halitta ne daga haske ba, su na nufin wai babu haske tare da Annabi (SAW) sannan babu wani haske da ya ke haskaka daga gare shi (SAW), wai bari ma dai shi abin halitta ne daga ruwan maniyyi rarrauna (wal'iyaazu billah), saboda haka dole na rubuta littafi don raddi a gare su cikin hakan don kariya ga Annabi (SAW)."

Sannan ya rufe littafinsa mai al'barka da fadinsa cewa:

 (1). Ya Ma'aikin Allah wannan shi ne xan qanqanin qoqarina da 'yar iyawata! cikin kariya game da haskenka mai al'barka wanda Allah ya halicce shi tun kafin ya halicci dukkanin halitta, ya Rasulallahi kai yo baiwa kai yo madadi a gare ni da malamaina da shehunaina da abokaina da Iyayena maza da iyayena mata da 'ya'yana da dukkanin masoya shugaban kasantattu (masoyanka kenan ya ma'aikin Allah), ya hasken shuhudi (kai min haka) daga baye-bayenka da kulawarka da haskake-haskakenka har izuwa sanda za mu haxu da kai a ranar halartar bayin (ranar al'kiyama) mu na kuvutattu (daga azaba) masu rabauta (da al'jannah da ni'imominta).

(2). Ya Allah ka sanya hasken Annabinka a zukatanmu, ka sanya hasken Annabinka a harasanmu, ka sanya hasken Annabinka a cikin jinmu, ka sanya hasken Annabinka a magannenmu, ka sanya hasken Annabinka a damanmu, ka sanya hasken Annabinka a hagunmu, ka sanya hasken Annabinka a samanmu, ka sanya hasken Annabinka a qasanmu, ka sanya hasken Annabinka a gabanmu, ka sanya hasken Annabinka a bayanmu, ka sanya hasken Annabinka a rayukanmu, ka game mu da Annabi naka Shugabanmu hasken majivincinmu al'amuranmu Muhammadu (SAW).

 

KAMMALAWA

Mu na godiya ga Allah Subhanahu wa Ta'ala da ya ba mu ikon kamala wannan littafi mai al'barka mai suna "Tarihin Mal. Bashir Haladu (Al'kaumu), wanda ya qunshi tarihin rayuwarsa tun daga haihuwa zuwa rasuwarsa a takaice. Allah ya ji kansa da Rahma.

MASAMAR BAYANAI:

·        Mahaifinsa Alh. Haladu Umar.

·        Mahaifiyarsa Hajiya Halimatu Idris.

·        Matarsa Aminatu Mukhtar Umar.

·        Iyalan Marigayi Mal. Auwali Isa Yakasai.

·        Yusuf Abdullahi (Yusi Mai Awo)

·        Salisu Muhammad Abubakar (Salisu A1)

DUBA AIKI: Mal. Abdullahi Sabi'u (Baballe).

AL'HAMDU LILLAHI

***



[1] - Wannan kasidarsa ce kuma it ace bakandamiyarsa ya na sonta sosai da sosai.

[2] - Ita ma wannan kasidar tasa ce, kuma ya na sonta sosai.

[3] - Ita ma wannan kasidar tasa ce, kuma ya na sonta sosai.

[4] - Abin da wannan baiwar Allah wato matar shi Mal. Bashi ta ke fax, halaye ne da dukkanin wata mace ta ke al'faharin da cewa mijinta ya na dasu masamman idan ya rasu. To abin tambaya a nan shi ne ina hankalin matan ya ke tafiya ba su maida hankali wajen samun mazaje irin su Mal. Bashir?.

Wani Shahabi ya na cewa: mu na godiya ga Allah wanda ya sa mawadata (masu kuxi) su ke sha'awar rayuwarmu a lokacin mutuwa, mu kuma ba mu sha'awar rayuwarsu a lokacin mutuwa!.

[5] - Dama ita kadiriyyah haka ta ke. Haka ne koyarwarta.

[6] - Wannan gado ne daga Shehunai irin su shehu Usmanu Dan Fodio (RTA).

[7] - Bayan wannan akwai wanda ya kamala rubutawa amma ba a buga ba, sannan akwai wadanda ya ke kan rubuta su. Wannan littafi ne da ya rubuta shi a kan bayanin hasken Manzon Allah, kuma sanda a ke masa aikin buga wannan littafi ya nuna tsananin dokinsa wajen a kammala wannan aikin littafin ya fita, haka kuwa a ka yi, littafin ya fita ya shiga hannun masoyan Annabi Salalllahu alaihi wasallam masamman malamansa kusan ya baiwa duk wanda ya kamata kwafi daya kyauta.

[8] - "Uwa uba, Mal. Bashir ya samu wasu abubuwa daga Mal. Auwalu kamar haka:

•     Tarbiyyah Diniyyah Muhammadiyyah.

•     Kishin masharabi.

•     Yarda da amincewa.

•     Fadar gaskiya ba kumbiya-kumbiya.

[9] - "A wani Hadisi Annabi (s.a.w) ya ce: Allah ya shiryi Mutum Daya ta dalilinka shi ya fi al'khairi daga a ba ka jajayen rakuma (Kamar a ce Motocin jifjifai ke nan a yanzu). 

No comments:

Post a Comment