Addu’a takobin mumini
Daga www.sautulazimiyyah.blogspot.com
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah, Ubagijin halittu baki daya. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu sallallaahu alaihi wasallam, tare da alayensa da sahabbansa baki daya, da duk wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar karshe. Bayan haka, a yau inaso in dan yi tsokaci ne a kan addu’a a matsayinta na takobin mumini. Za mu ga ma’anarta da falalarta da lokuta da guraben da ake karbarta, sannan da ladubbanta. Haka nan akwai nau’in wadanda ake karba musu addu’a da kuma wadanda ba a karba musu ko kuma ake jinkirta musu.Sannan da bayanan a kan dalilan dasuke sawa ba a karbar addu’a duk daga abin da aka cirato daga zantuka da bayanan magabata na kwarai, Allah Ya jikansu da rahama. Sai kuma wani waige a kan Istikharah. Bismillah!MA’ANARTA A Larabce addu’a na nufin kiran wani, ko neman miko wani abu. Suna cewa: da’aa bil kitabi, ma’ana ya nemi a miko masa littafi. A isdilahi kuma addu’a tana nufin tarin kalmomin yabon Ubangiji, masu nuni ga neman wani abu daga gare Shi, ko neman tsarin wani abu (sharri) daga gare Shi.FALALARTA“An karbo daga dan Abbas, Allah Ya yarda da shi cewa Yahudawan Madina sun tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) suka ce: ‘Ta yaya Ubangijinmu Zai ji addu’armu, bayan kai kana zaton cewa tsakaninmu da sama kimanin tafiyar shekara dari biyar ne. Kuma tsakanin kowace sama da ’yar uwarta ma haka ne ?’ Sai Allah Ya saukar da: “Duk lokacin da bayiNa suka tambaye ka game da Ni, to Ni Makusanci ne. ina amsa addu’ar mai roko in ya roke Ni.” Bakara aya ta 186 ( daga Algunya ta Sidi Abdulkadir Shafi Na 373).Ma’aiki, sallallahu alaihi wasallam, ya ce “Addu’a ita ce ibada.” Kamar yadda aka fitar a littafin Riyadhussalihin na Imam Nawawi a Kitabul – da’awati . A wata riwayar kuma ya ce: “Hakika Ubangiji na mu’amala irin ta jin kunya. Idan bawa ya buda hannu ya roke Shi, Ya ki amsa masa, ko dai ya gaggauta masa a amsawar tun a duniya, ko ya jinkirta masa sai a ran kiyama.”LOKUTA DA GURABEN AMSA ADDU’AAna karba (amsa) addu’a a wurare da lokuta da kuma guraben yanayi kamar haka:1- Yayin sujjada. 2- Lokacin alwala.3-Lailatul kadri. 4- Yayin saukar ruwan sama.5- Tsakar dare. 6- Tsakanin kiran sallah da ikama.7- Ranar Juma’a 8- Ranar Arfa.9- Yayin kiran sallah. 10- Bayan kiran sallah. 11- Bayan jifan shaidan. 12- A Safa da Marwa.13- Sallolin farilla. 14- Watan Rajab.LADUBBAN ADDU’A Yana daga cikin ladubban addu’a mutum ya kasance yana da:1- Ikhlas – wato ya kasance yana da tsarkin zuciya, ya fuskanci Allah kadai a cikin abin da yake bukata. 2- Kyakyawan zaton amsa ta. 3- kankan da kai da sassauta sauti.4- Shiga (suturarsa) da ci da shansa su kasance na halal. 4- Fuskantar alkibla. 5- Naci a addu’ar. 6- Cudanyata da yabon Ubangiji da kirari gare Shi.7- Salatin Annabi farko da tsakiya da karshe.8- Fadada abin nema ga sauran musulmai. 9- Yin ta a tsanani da walwala. 10- Halarto zunubi da bayyana tuba.11- Bijiro ni’imomi da bayyana godiya ga Allah.12- daga hannu sama da shafar fuska da shi bayan addu’ar.WADANDA BA A KIN AMSA ADDU’ARSU1- Mai azumi yayin buda baki. 2- Wanda aka zalinta.3- Shugaba nagari. 4- Matafiyi kan yardar Allah.DALILIN kIN AMSA ADDU’AWofintar addu’a ga ladaban amsa ta na jawo kin amsa ta. An tambayi Shehi Ibrahim dan Adhama, Allah Ya yi masa rahama, cewa ‘ko me ya sa muke rokon Allah ba Ya amsa mana?’ Sai ya ce saboda :-1- Kun san sunnar Ma’aiki, sallallahu alaihi wasallam, ba ku bi.2- Kun san Alkur’ani ba ku aiki da shi.3- Kuna cin ni’imomin Ubangiji ba ku godiya. 4- Kun san Aljanna ba ku nemanta.5- Kun san wuta ba ku tsoranta.6- Kun san shaidan kuna binsa. 7- Kun san mutuwa ba ku yi mata tanadi ba.8- Kun san mamata ba ku tunawa da su.9- Kun bar abinku kun shagalta da na mutane.Haka nan Allah Yakan jinkirta wa bawa addu’rsa don soyayya, kamar yadda hadisi ya bayyana cewa, “Bawa kan roki Allah Ya biya masa da wuri, saboda ba Ya son jin muryarsa; wani (bawan kuma) ya roka a jinkirta masa, saboda son jin muryarsa da Allah Yake .”TSAWAITA ADDU’A KO TAKAITA TANana A’ishah, Allah Ya yarda da ita, ta ce Manzon Allah, sallallahu alaihi wasallam, yana son dunkulalliyar addu’a, yana barin watanta (ma’ana ba ya tsawaita mai wuce haddi), kamar yadda aka fitar a littafin Riyadhussalihina a Kitabul da’awati shafi na 264).ISTIKHARAH Wannan na nufin neman zabin Allah kan wani al’amari da bawa yake so ko zai aikata.Sayyadina Jabir, Allah Ya kara masa yarda, ya ce “Ma’aikin Allah, sallallahu alaihi wasallam, ya kasance yana koya mana istikhara a duk al’amari , tamkar sura daga Alkur’ani. Yana cewa, ‘idan dayanku ya nufi wani al’amari, sai ya yi sallar nafila raka’a biyu, sai ya ce: Allahumma inni astakhiruka bi ilmika wa astakdiruka bi kudratika wa as’aluka min fadlikal azim fa innaka takdiru wala akdiru wa ta’alamu wala a’alamu wa anta allamul guyub; allahumma in kunta ta’alamu anna hazal amra khairun li fi dini wa ma’ashi wa akibati amri fakdirhu li wa yassirhu li summa barik li fihi; wa in kunta ta’alamu anna hazal amra sharrun li fi dini wa ma’ashi wa akibati amri fasrifhu anni wasrifni anhu wakdir liyal khaira haisu kana summa ardhini bihi (sai mutum ya ambaci bukatarsa) – Imamul Bhukari. Tabbas Allah na fushi da bawanSa in ba ya rokonSa. Allah Ka daukaka Musulunci da musulmai, Ka rusa kafirci da kafirai. Ka yalwata mu da soyayyar Ma’aikinmu, sallallahu alaihi wasallam, Ka sa al’amarinmu ya kasance a ranar mutuwarmu muna masu cikawa da kalmar la’ilaha illallah muhammadur rasulullah
No comments:
Post a Comment