Wednesday, 28 February 2018

GYARN GIDA

GYARAN GIDA.

Wannan bayani na samo shi ne daga shafin Facbook na Mal. Balarabe Shehu Illela, dafatan zamu amfana da bayanan da ya yi,  Malamin ya fara da cewa:

Sai ai min afuwa yan'uwa domin a harkar neman lafiya babu wani abin boyewa a jiki domin likitanka da lauyanka baka boye musu damuwarka. Kusan duk mutanenmu in suka zo kasar sin , zuwa wuraren gargajiyar kasar Sin shine kan gaba kan inda suke son zuwa. Wannan kuma ba laifi domin kula da lafiya ne kuma kyautata sunna ne.

Yau binciken da nay i kan gyaran zaman iyali ne a gargajiyance don haka duk wanda zai yi amfani da abubuwan da na fada ya tabbatar mai iyali ne kuma ban amince a yi amfani da bayanina ta wata hanyar da ba ta sunna ba.

Kasar Sin ta fi kowace kasa yawan jama’a a duniya kuma a kowace shekara ana haihuwar mutane sama da miliyan 18. Na barku da sauran bayanin. Amma ga kadan
daga cikin magungunan gargajiya da ake amfani da su da kuma yadda ake amfani da su.

1. A sami farar albasa guda daya a sa a injin markade a markade ta sannan a samo zuma mai inganci ba gauraye ba kimanin rabin yawan wannan albasa a kwaba su tare a gauraya , sai a samo kwalban glass wanda ana iya ganin cikinsa daga waje (transparent) sai a zuba wannan zuma da albasar a ciki a rufe.
Za a ajiye a kan taga ko duk wani wurin da zai rika samun hasken rana amma ba zafin rana ba, sai a ajiye shi har na tsawon kwana biyar kar a bude. Bayan kwana biyar sai a soma amfani da shi.
Za a sha cikin babban cokali daya da safe kafin a ci komai. Kuma ba za a ci kmai ba sai bayan minti 30. Haka za a yi ta sha har sai yak are. Akalla a yi mako guda ana sha. Rashin sha’awa ke hana kusantan iyali, domin jikin mutum akwai wani sinadari da ke sa sha’awa, wasu basu da shi da yawa . shan wannan maganin
gargajiya yana kara matukar sha’awa har a kai ga biyan bukata.

2. Wanda bai da kyamar tafarnuwa, sai ya samo tafarnuwa tsala uku ko hudu a daddatsa ta, sannan a samo zuma mai kyau cokali biyu ya zuba a kwaba. Sai a
sha da safe kafin cin abinci. Kullun ya zamo ana sha har na tsawon mako biyu ko uku. . wannan maganin gargajiya yana kara karfin namiji kwarai da gaske.

3. Sinawa kan yi amfani da Karas wajen magani. Ana yayyanka karas a sa zuma sannan a hada da danyen kwai a rinka sha. Wannan babban magani ne kwarai a bisa binciken likitocin gargajiyan.

4. kana iya cin danyen citta? To ka gwada ka sha mamaki a cewar likitocin gargajiya. Za ka dauki citta kamar girman karamin yatsarka, ka kankare sannan ka tauna
shi danyensa.. shim aba karamin taimakawa key i ba.

Mu kwana nan. Allah sa mu dace

NOTE/KULA. Mal. Balarabe yace: Ni ba likita bane don haka ka tuntubi likitanka kafin ka yi amfani da kowane irin magani