Monday, 28 January 2013

GULMA DA ILLOLINTA

GULMA DA ILLOLINTA
Da sunan Allah mai yawan Rahama Mai yawan jinkai, gaisuwa da yabo su kara tabbata ga manzon Allah (SAW) da Alayansa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka na yi kokari gabatar da wannan takaitaccen bayani ne sabo da ganin yanda yan uwa mata da maza muke cikin wannan mummunan dabi'a ta gulma, a inda ada mata kadai akasani da gulma amma yanzu har mazanma suna neman su kere matan, dafatan Allah zai amfanar damu mu gane mu kauce mata.
MENENE GULMA?
Gulma a shar'ance tana nufin mutum ya dauki maganar wani ya kaiwa wani da nufin hada husuma a tsakaninsu, ko cutarwa, amma idan da nufin alhairi aka kai babu laifi.
HUKUMCIN GULMA A MUSULCI
Gulma haramun ce da nassin Alkur'ani da Hadisan Shugaba Alaihissalam, kuma dayace daga cikin manyan zunubai.
Daga cikin dalilai na haramcin Gulma akwai fadi Allah (SWT) cikin littafinsa mai tsarki cikin suratulKalam Aya ta 11 cewa: "MAI YAWAN AIBATA MUTANE, MAI YAWAN GULMA (TSAKANIN MUTANE)" Har iala yau da fadinsa "SHIN DAYAN KU YANA SON YA RIKA CIN NAMAN DAN'UWANSA ALHALI YANA MUSHE? TO KUN KYAMACI HAKA...(HUJRAAT:12)
Sannan kuma Manzo (SAW) yce: "DUKKAN MUTUM ANNAMIMI (MAI GULMA, MAIHADA HUSUMA DA TSAKANIN MUTANE BAZAI SHIGA   ALJANNA BA" ( Buhari Da Muslim)
Wata rana manzon Rahama ya wuce wasu Kaburbura Biyu, sai yace ana yiwa na cikin Kaburburan azaba a halin yanzu, kuma su awajensu ba akan wani babban laifi bane, lokacin da suke aikata laifukan sun ganin ba manya bane, daya daga cikin su ya kasanci in yayi Fitsari baya tsarkaka, wato idan ya gama fitsari baya bari ya dige gaba dayansa sai ya rika a jikin sa ba tare da rashin lafya ko wani uzuri ba, na biyun kuma ya kasance mai yawan yawo tsakanin mutane da annamimanci" (Buhari da Muslim)
Sannan Manzo Alaihissalam yace: " Zaka samu daga cikin mafiya sharri a cikin mutane, sune masu fuska biyu wadanda zasu zowa wadannan mutane da wata fuska sannan su ewa wadannan da wata fuskar" (Buhari da Muslim ne suka rawaito)
Har ila yanzo Manzo yace: "Dukkan wanda ya kasance yana da harshe biyu a gidan duniya (wato Magulmaci) to Allah zai sanya masa harshe biyu na wuta a ranar Alkiyama" (Abu dawud ne ya rawaito:4873)
Sannan Ka'ab yana cewa: "Ku tsoraci annamimanci (wato Gima) domin ma'abocinta baya hutawa daga azabar Kabari.
Mansur ya rawaito daga Mujahd dangane da matar abi Lahab wadda asalin sunanta Arwa, sannan ana mata Alkunya da Ummu Jamil inda allah Madaukakin sarki ya ke cewa: "Da matarsa ina nufin magulmaciya" (Suratul Madas aya ta 4)
wannan mata Mummunace mai ido daya amma ba'abin da ta ke yi da shi sai zunden Manzon Allah(SAW) da tsara baitocin waka don keta alfarmar sa.
HALAYEN MAGABATA A LOKACIN DA AKA JE MUSU DA GULMA
An rawaito cewa wata rana wani mutum ya je wajen Umar Ibn Abdul'aziz ya kai masa Gulmar wani mutum, sai umar Ibn Abdul'aziz yace masa: Yakai wannan mutum idan naga dama zan duba lamarinka, idan ka kasance mai gaskiya, to kana daga cikin wanda Allah yake cewa: "Idan fasiki yazo muku da wani zance to ku yi binciki.." (Hujurat:6 ). Idan kuma ka kasance makryaci, to kana daga cikin wadanda Allah yake cewa: " Mai yawan aibata Mutane, mai yada Gulma" (tsakanin mutane) Kalam: 11.
Inaga dama in yafe maka, sai wannan mutum yace: Kayafe min ya sarkin muminai, bazan sake aikata haka ba.
Wani mutum yazo waje aliyu dan Hussain (RTA) yace masa: Wane ya zageka, kuma yace kaza da kaza, sai yace: zanje wajensa, sai suka tafi wajensa tare da tsammanin zaije ne ya kare kansa< lokacin da suka isa wurinsa, sai yace: Ya dan'uwa na idan abin da ka fada tare dani gaskiyane, to allah ya gafarta mini, idan kuma abin da kafada gane dani ba gaskiya bane , to allah ya gafarta maka.
ABN DA AKE SO KA AIKATA LOKACIN DA A KA ZO MAKA DA GULMA
A kwai abubuwa da dama da akeso ka aikata lokacin da wani ya zo maka da Gulma, kadan daga ciki sune:
1.       Kada ka gaskata labarin da aka zo maka, domin wanda yazo da labarin ya zama Annmimi, fasiki, kuma mai mayar da alheri.
2.      Ka hana wanda ya kawo maka Gulmar ci gaba da Gulmar, kuma kayi masa nasiha sannan ka kyamaci aikata hakan.
3.      Ka nuna masa kaji haushin sa domin Allah, don Allah yana fushi da aikinsa, kuma yin fushi domin allah wajibi ne.
4.     kada kayi mummunar zato dangane ga wanda aka kawo maka gulmarsa, donin Allah (SWT): KU NI SANCI MAFI YAWA DAGA CIKN ZATO.." (Hujurat:12)
5.     kada mutun yace zai yi bincike don gano abin da aka fada masa  karya ce gaskiya ne, domin Allah(SWT) tace: "Kuma kada kuyi bincike.." (Hujurat:12).
6.     Kada mutun yaci gaba da labartarwa da wasu abin da aka kawo masa na gulma, domin shima sai ya koma matsayin wanda yazo masa da gulman.
Wadannan sune kadan daga bayanai akan Gulwa, da fatan Allah ya karemu daga aikata wannana mummunan dabi'a, ya shiryemu da dukkan musulmi baki daya.
Wassalamu alaikum warahamatullah. 


Friday, 25 January 2013

BAYANI KAN AZUMIN WATAN RAJAB


BAYANI KAN AZUMIN WATAN RAJAB
Daga Auwal zakari Ayagi
Shugaban kungiyar Al'azmiyya Islamic Foundation Kano State
emai:
auwalzakari@gmsai.com
website: htp//: www.sautulazimiyyah.blogspot.com

Da sunan Allah mai yawan Rahama Mai yawan jinkai, gaisuwa da yabo su tabbata ga ma'aikin Allah (SAW) da alayensa da shabbansa baki daya.

Bayan haka shi Azumin Rajab sunna ne daga cikin sunnonin Annabi (SAW) da ya kwadaita da yinsa, kamar yadda ya tabbata a hadisin Mujibatul Bahiliyya.

Amma kafin mu shiga cikin wannan Maudu'i, zanso yan'uwa su fahinci wasu abubuwa kamar haka:

Sunnar Annabi (SAW) tana nufin duka wani abu da aka jinginashi ga annabi (SAW) Maganace ko aiki, ko tabbatarwa (Takrir) ma'ana ya tabbatar da wani daga cikin sahabbansa bisa ga abin da ya aikata ta hanyar yaba masa ko yin shiru lokacin da ya aikata.

Akwai Sunnoni da ambatonsu yake zuwa karara kamar falalar yawaita azumin sha'aban, Litinin da Alhamis, da sauransu, akwai kuma Sunnoni da ambatonsu yake zuwa adunkule kamar Azumtar watanni masu alfarma.
Watanni masu alfarma sune:

Watannin Zulka'ada, Zulhhijja, Almuharram da kuma Rajab. kamar yadda Iman Ahmad ya kawo a Musnad da Abu Dawud da Ibn Majah da Baihaki, idan mukayi duba ga gabar karshe wato Azumtar watanni masu alfarma zamu ga Hadisi ya tabbata da Sanadi ingantacce kuma Alhafiz Ibn Hajar ya tabbatar da ingancinsa a "Tabyinul ajab" cewa: "Wani mutum ya zo wajen Annabi SAW) sai yace yarasululluhi nine mutimin da na zo maka shekarar da ta wuce (Annbi (SAW) bai gane shi ba) sai Ma'aiki (SAW) yace na ga ka canza duk ka reme? Sai yace ya rasulullahi tin da nazo wajenka ban kara cin abinci da rana ba domin ina ta yin Azumi, sai Annabi(SAW) yace amma kaba kanka wahala, ka Azumci Ramadhan bayansa kuma sai a kowanne wata kayi Azumi daya, sai shi mutumin yace Ya rasulullahi ka karamin ina da karfin da zanyi fiye da haka, sai Annabi (SAW) yace bayan ka azumci watan Ramadhan to a kowanne wata sai ka Azumci Ranaku biyu, sai ya kara cewa Ya rasulullahi a karamin ina da karfi, Sai Annabi (SAW) tace ka azumci ranaku masu alfarma sai ka barshi haka, Annabi (SAW) yana nuni da hannunsa idan ya dunkulesu sai ya bude. Wannan Hadisi Hasani ne kamar yadda Ibn Hajar ya kawo a littafinsa (Tabiyunyi Ajab).

Sayyid Sabik ya fada a Fikhus-sunnah Azumtar watanni masu alfarma, sai yace watanni masu alfarma sune: Zulka'adah, Zulhijjah, Almuharram da kuma Rajab, yace anaso ayawaita azumi a cikinsu sai ya kafa hujja da Hadin Bahili wanda muka ambata a baya, sannan yace Azumin watan Rajab bashi da wata falala da ta wuce wannan inganci bisa mabayyani, shi dai Rajab yana cikin watanni masu Alfarma" (Fikihun Hadisi)

A cikin wannan Hadisi na bahili Za'a iya fahintar abubuwa kamar haka:

1. Yanda sahabbai suke tasirantuwa da zama da Annabi (SAW) domin shi wannan yazo wajen Annabi (SAW) ne a shekarar farko da ya kwankwadi madarar Imani, zuciyarsa ta tsarkaka tun da yaje wajen annbi (SAW) bai kara cin abinci ba da rana sai ya lazimci Azumi.

2. Yanda Annabi (SAW) yake tausasawa al'umma, domin ya ga yanda wannan sahabi ya canza har bai gane shi ba, shi yasa ya hana shi wannan Azumi.

3. Hani karara bisa Azumin da zai galabaitar da mutum ya wahalar da shi.

4. Umarni da kwadaitarwa bisa Azumin da mutum zai iya bayan na Ramadan.

5. Yin Azumi ya danganta da irin yanayin mutum ne, wanda zai iya yi da yawa domin yana da lafiya da karfi sai yayi, wanda kuma ba zai iyaba, shari'a tayi masa rangwame.

6. Annabi (SAW) ya umarce shi da ya Azumci Ramadan da watanni masu alfarma idan muka hada zamu ga ashekara zai iya yin Azumin wata hudu.

7. Akwai hujja karara ta Azumtar Rajab gaba dayansa ga mai iko cikin wannan Hadisi, domin Annabi (SAW) cewa yayi da shi ka Azumci watanni masu alfarma kamar yadda ya tabbata a Hadisin, t
un da babu wani nassi ingantacce da ya fito karara ya hana azumin watan Rajab. Ba wai wannan hadisi kadai ne yayi magana kan falala da hujjar azumtar Rajab ba, a'a akwai hadisin korama, da gida da yake magana kan gidan da Allah ya tanadarwa masu azumtar Rajab da sauran su, duk da cewa akwai wadanda basu ingantaba a cikin hadisan kamar yadda Alhafiz Ibn hajar Al'askalani ya fada cikin Tabiyul Ajab sai dai akwai tsokaci anan, tsokacin kuwa shine, shi hadisi Da'if ana aiki dashi wajen ayyukan neman falala (kamar shi a zumin Rajab din) ko tabbatar da matsayi da daraja ga wani daga bayin Allah ko kwadaitarwa kan wani lamari da shari'a take umarni ko tsoratarwa kan aikata wani abu da tayi hani da shi. Wannan magana malaman Hadisi sun hadu akan haka kamar yadda Imamul Nawawi ya kawo cikin Littafin sa 'Ibahatul Kiyam'.

Daga malaman da suka tabbatar da haka akwai Imamu Ahalul sunna Ahmad Ibn Hambali da Imam Ibn Sayyidi-nas da imam Al'iraky, da Shehul Islam Zakariyyal Ansari da Imam Shakh-khawi da Alhafiz Ibn Hajar Al'askalani, da Imam Ibn Humam Al'hanafy, da Imam Ibn Adiy, da imam Khadib Al'bagadadi da sauransu.

FADAKARWA
Yakamata musan cewa azumin Rajab da ake cewa azumin tsofaffi ba ana nufin sai tsoho bane zai yi ba, sam wannan kalma isdilahi ce ko sara ce ta hausawa kawai, Azumin Rajab na dukkan Musulmi ne ma son alhairi da falala, shi wannan suna ya samo asaline domin yayan hausawa sun taso sunga iyayensu da kakannin su suna yi sai suka samasa wannan suna, kamar yadda suke kiran azmin ramadan da azumin duk gari, ai kaga a garin akwai wadanda ba Musulmi ba, a Musulmin ma akwai wadanda shari'a tayi musu rangwame kamar marasa lafiya da tsofaffi da masu jinin haila ko na biki da masu shayarwa ko goyon ciki idan azumin zai wahalar da su ko baza su iyaba.

Lalai ya kamata kamar yadda muke azumtar watan Rajab mu dinga azumtar Sha'aban haka ko fiye da hakan, domin ya tabbata a hadisin Buhari da Muslim Nana Aisha tace: Annabi (SAW) yana azumtar kusan dukkan Sha'aban" amma sai kaga yan'uwa suna rafkana ana gama Rajab sai a daina, a'a kaka ba dai dai bane.

Hakannan akwai azumi da yawa da ya tabbata daga Ma'aiki (SAW) kamar azumin ranar Litinin da Alhamis, da azumin ranakun 13 da 14 da 15 na kowanne wata, da azumtar kwanaki 6 a Shawwal, da kwanaki 10 na Muharram, da na ranar Tasu'a da Ashura, da azumin Annabi Dawud yau kayi gobe ka sha, da azumin Gwauraye wato wadanda basu samu damar yin auruba, da dai sauransu.

Domin Annabi alaihissalam yace: wanda ya azumci wani yini domin neman yar dar Ubangiji, Allah zai (SWT) zai zai nisanta fuskarsa daga wutar Jahannama na tsawon shekara guda.

Allah ya bamu dacewa ya karbi dukkan Ibadun mu don Alfarmar shugaban masu Azumi (SAW).

Wassalamu alaikun warahamatullah

Tuesday, 15 January 2013

ALAZMIYYA ISLAMIC FOUNDATIN Shafin Farko

Da sunan Allah Mai yawan Rahama Mai jin kai
Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad SAW