Monday, 28 January 2013

GULMA DA ILLOLINTA

GULMA DA ILLOLINTA
Da sunan Allah mai yawan Rahama Mai yawan jinkai, gaisuwa da yabo su kara tabbata ga manzon Allah (SAW) da Alayansa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka na yi kokari gabatar da wannan takaitaccen bayani ne sabo da ganin yanda yan uwa mata da maza muke cikin wannan mummunan dabi'a ta gulma, a inda ada mata kadai akasani da gulma amma yanzu har mazanma suna neman su kere matan, dafatan Allah zai amfanar damu mu gane mu kauce mata.
MENENE GULMA?
Gulma a shar'ance tana nufin mutum ya dauki maganar wani ya kaiwa wani da nufin hada husuma a tsakaninsu, ko cutarwa, amma idan da nufin alhairi aka kai babu laifi.
HUKUMCIN GULMA A MUSULCI
Gulma haramun ce da nassin Alkur'ani da Hadisan Shugaba Alaihissalam, kuma dayace daga cikin manyan zunubai.
Daga cikin dalilai na haramcin Gulma akwai fadi Allah (SWT) cikin littafinsa mai tsarki cikin suratulKalam Aya ta 11 cewa: "MAI YAWAN AIBATA MUTANE, MAI YAWAN GULMA (TSAKANIN MUTANE)" Har iala yau da fadinsa "SHIN DAYAN KU YANA SON YA RIKA CIN NAMAN DAN'UWANSA ALHALI YANA MUSHE? TO KUN KYAMACI HAKA...(HUJRAAT:12)
Sannan kuma Manzo (SAW) yce: "DUKKAN MUTUM ANNAMIMI (MAI GULMA, MAIHADA HUSUMA DA TSAKANIN MUTANE BAZAI SHIGA   ALJANNA BA" ( Buhari Da Muslim)
Wata rana manzon Rahama ya wuce wasu Kaburbura Biyu, sai yace ana yiwa na cikin Kaburburan azaba a halin yanzu, kuma su awajensu ba akan wani babban laifi bane, lokacin da suke aikata laifukan sun ganin ba manya bane, daya daga cikin su ya kasanci in yayi Fitsari baya tsarkaka, wato idan ya gama fitsari baya bari ya dige gaba dayansa sai ya rika a jikin sa ba tare da rashin lafya ko wani uzuri ba, na biyun kuma ya kasance mai yawan yawo tsakanin mutane da annamimanci" (Buhari da Muslim)
Sannan Manzo Alaihissalam yace: " Zaka samu daga cikin mafiya sharri a cikin mutane, sune masu fuska biyu wadanda zasu zowa wadannan mutane da wata fuska sannan su ewa wadannan da wata fuskar" (Buhari da Muslim ne suka rawaito)
Har ila yanzo Manzo yace: "Dukkan wanda ya kasance yana da harshe biyu a gidan duniya (wato Magulmaci) to Allah zai sanya masa harshe biyu na wuta a ranar Alkiyama" (Abu dawud ne ya rawaito:4873)
Sannan Ka'ab yana cewa: "Ku tsoraci annamimanci (wato Gima) domin ma'abocinta baya hutawa daga azabar Kabari.
Mansur ya rawaito daga Mujahd dangane da matar abi Lahab wadda asalin sunanta Arwa, sannan ana mata Alkunya da Ummu Jamil inda allah Madaukakin sarki ya ke cewa: "Da matarsa ina nufin magulmaciya" (Suratul Madas aya ta 4)
wannan mata Mummunace mai ido daya amma ba'abin da ta ke yi da shi sai zunden Manzon Allah(SAW) da tsara baitocin waka don keta alfarmar sa.
HALAYEN MAGABATA A LOKACIN DA AKA JE MUSU DA GULMA
An rawaito cewa wata rana wani mutum ya je wajen Umar Ibn Abdul'aziz ya kai masa Gulmar wani mutum, sai umar Ibn Abdul'aziz yace masa: Yakai wannan mutum idan naga dama zan duba lamarinka, idan ka kasance mai gaskiya, to kana daga cikin wanda Allah yake cewa: "Idan fasiki yazo muku da wani zance to ku yi binciki.." (Hujurat:6 ). Idan kuma ka kasance makryaci, to kana daga cikin wadanda Allah yake cewa: " Mai yawan aibata Mutane, mai yada Gulma" (tsakanin mutane) Kalam: 11.
Inaga dama in yafe maka, sai wannan mutum yace: Kayafe min ya sarkin muminai, bazan sake aikata haka ba.
Wani mutum yazo waje aliyu dan Hussain (RTA) yace masa: Wane ya zageka, kuma yace kaza da kaza, sai yace: zanje wajensa, sai suka tafi wajensa tare da tsammanin zaije ne ya kare kansa< lokacin da suka isa wurinsa, sai yace: Ya dan'uwa na idan abin da ka fada tare dani gaskiyane, to allah ya gafarta mini, idan kuma abin da kafada gane dani ba gaskiya bane , to allah ya gafarta maka.
ABN DA AKE SO KA AIKATA LOKACIN DA A KA ZO MAKA DA GULMA
A kwai abubuwa da dama da akeso ka aikata lokacin da wani ya zo maka da Gulma, kadan daga ciki sune:
1.       Kada ka gaskata labarin da aka zo maka, domin wanda yazo da labarin ya zama Annmimi, fasiki, kuma mai mayar da alheri.
2.      Ka hana wanda ya kawo maka Gulmar ci gaba da Gulmar, kuma kayi masa nasiha sannan ka kyamaci aikata hakan.
3.      Ka nuna masa kaji haushin sa domin Allah, don Allah yana fushi da aikinsa, kuma yin fushi domin allah wajibi ne.
4.     kada kayi mummunar zato dangane ga wanda aka kawo maka gulmarsa, donin Allah (SWT): KU NI SANCI MAFI YAWA DAGA CIKN ZATO.." (Hujurat:12)
5.     kada mutun yace zai yi bincike don gano abin da aka fada masa  karya ce gaskiya ne, domin Allah(SWT) tace: "Kuma kada kuyi bincike.." (Hujurat:12).
6.     Kada mutun yaci gaba da labartarwa da wasu abin da aka kawo masa na gulma, domin shima sai ya koma matsayin wanda yazo masa da gulman.
Wadannan sune kadan daga bayanai akan Gulwa, da fatan Allah ya karemu daga aikata wannana mummunan dabi'a, ya shiryemu da dukkan musulmi baki daya.
Wassalamu alaikum warahamatullah. 


2 comments:

  1. Allah yasakwa malam da alherinsa ya kara basira da karfin gwiwar fadakar damu gaskiya. mukuma Allah ya bamu ikon daukar gaskiya ya tsaremu daga sharrin shaidan la'ananne.

    ReplyDelete