LAILATUL KAD'RI. Lailatul Kadri dare ne Mai matukar albarka a cikin Watan Ramadan , shine daren da Yafi watanni dubu alfarma. Ana Tsammanin daren Lailatul kadri ne a Goman karshe na Watan Ramadhan, musamman an fi sa rai a Dararen mara (wutri). Wato daren 19, 21, 23, 25, 27, 29. An ruwaito Cewa, Idan Goman karshe na Ramadhan ya shigo, Manzon Allah Mai tsira da Aminci yakan tashi da iyalansa (Da dddare), yakan Kara yawan ibada da Neman kusanci ga Allah Ta'ala ta Hanyar salloli, zikiri, da karatun al-kur'ani. Da aka tambayi Manzon Allah Mai tsira da Aminci Cewa, "Me ya kamata mutum ya Roka adaren Lailatul kadri? Sai yace, "Kuce, Ya ubangiji! Kaine Mai afuwa, kana son afuwa, kayi mana afuwa!" Tirmiziy ne ya ruwaito. Ya Yan Uwa Musulmi Watan Ramadan ya kusa wucewa, babu Wanda yake da tabbacin kaiwa wani ramadan na gaba a cikin mu, Dan Haka mu Dage da ibada, mu gayawa Allah bukatan mu, Allah zai amsa mana cikin ikon sa.
LAILATUL KAD'RI.
ReplyDeleteLailatul Kadri dare ne Mai matukar albarka a cikin Watan Ramadan , shine daren da Yafi watanni dubu alfarma. Ana Tsammanin daren Lailatul kadri ne a Goman karshe na Watan Ramadhan, musamman an fi sa rai a Dararen mara (wutri). Wato daren 19, 21, 23, 25, 27, 29.
An ruwaito Cewa, Idan Goman karshe na Ramadhan ya shigo, Manzon Allah Mai tsira da Aminci yakan tashi da iyalansa (Da dddare), yakan Kara yawan ibada da Neman kusanci ga Allah Ta'ala ta Hanyar salloli, zikiri, da karatun al-kur'ani.
Da aka tambayi Manzon Allah Mai tsira da Aminci Cewa, "Me ya kamata mutum ya Roka adaren Lailatul kadri? Sai yace, "Kuce, Ya ubangiji! Kaine Mai afuwa, kana son afuwa, kayi mana afuwa!" Tirmiziy ne ya ruwaito.
Ya Yan Uwa Musulmi Watan Ramadan ya kusa wucewa, babu Wanda yake da tabbacin kaiwa wani ramadan na gaba a cikin mu, Dan Haka mu Dage da ibada, mu gayawa Allah bukatan mu, Allah zai amsa mana cikin ikon sa.
Jazakal Laahu Khairan min khairi jazaaa'iH
ReplyDelete