Sunday, 6 April 2025

TAKAITACCEN TARIHIN AUWAL ZAKARI MUHAMMAD AYAGI (BARDEN AYAGI)

TAKAITACCEN TARIHIN AUWAL ZAKARI MUHAMMAD AYAGI (BARDEN AYAGI)

PA Media and Publicity to the Deputy National President Nigerian Labour Congress/National President Medical and Health Workers Union of Nigeria 

An haifi Auwal Zakari Ayagi (Barden Ayagi) ranar Alhamis 23/09/1976 a gida mai lamba 291 da ke Unguwar Ayagi cikin karamar hukumar Dala.

Karatun Alkur’ani: Auwal ya fara karatun Alkur’ani mai tsarki a makarantar Allo, karkashin Mal. Yahaya wanda aka fi sani da Alhajin Makaranta, ya sauke Alkur’ani mai tsarki cikin 1988, daga cikin malaman sa na Alkur’ani akwai Alhaji Baba Ayagi, Mallam Idi, Mallam Zangi, Mallam Ado, da Malam Uzairu.

Karatun Addini: Auwal Zakari yafara karatun Addini wato karatun Zaure a wajen Mallam Zangi, inda ya fara da karatun litatttafan fiqhu, Tauhidi, hadisi da sauransu, daga nan yaci gaba da karatun Addini wajen Marigayi Mallam Abdulhadi Aminu, da Mal Nasir (Maisunan Mallam) sai Marigayi Ustaz Auwal Isa Yakasai wanda a wajensa ne ya karanci littafai da dama cikin harda Tafsiri, Fiqhu, Tauhidi, Hadisi, Sirah, Tajweed, Balaga, Lugga, da sauransu.

Karatun Boko (Ilimin Zamani): Auwal Ayagi Ya fara karatun san a Boko a Makarantar Kofar Kabuga Special Primary School inda ya kamala cikin 1990, daga nan ya shiga Government Secondary School Goron Dutse daga 1990 zuwa 1996, bayan kammala Makarantar gaba da primary ya fara karatun NCE a FCE Kano, amma sai ya canja zuwa makarantar kiwon Lafiya ta School of Hygiene Kano daga 1997 zuwa 1999, inda ya zamu shaidar certificate kan kula da tsaftar Muhalli, daga nan yaci gaba duk dai a makarantar cikin 2000 zuwa 2002 ya samu shaidar Diploma duk dai a kan tsaftar Muhalli.

Ya samu shaidar Advance Diploma kan Gudanarwa wato Advance Diploma in Public Administration daga Kaduna polytechnic a shekara ta 2008, Sannan ya Karanta Diploma in Computer Science daga 2009-2010.

Barden Ayagi ya shiga Jami'ar Maryam Abacha American University da take Maradi a Jamhuriyar Niger, inda ya karanci Bsc Environmental Health and Sefety daga shekarar 2016 zuwa 2019,  ya cigaba da Digiri na biyu (MSc Public Health) a National open University.

Aikace Aikace: Kafin ya fara aikin Gwamnati ya yi Sana'oi da da dama, da kasuwanci, ya yi kasuwanci a kasuwar Kantin kwari a 1995, sai kasuwar Singer nanma ya taba kasuwanci a gidan batir daga 1996 zuwa 1998, daganan ya koma kasuwar Sabon gari Jan bulo a 1999.

Ya tan taba aikin wucin gadi da jaridar Bahaushiya, wace take wani bangare ce a cikin jaridar "Fim Mafazine" inda yake yi musu sharhin finafinai cikin 1999 zuwa 2002, tare da Ashafa Murnai Barkiya, daga nan ya shiga sana'ar daukar Hoto wato "Photography" inda har ya zama Mataimakin Jami'in yada labarai na kungiyar Kwararrun Masu daukan hoto ta Jihar Kano, (Proffessional Photograghy Union of Nigeria PPU) a shekara ta 2002.

Bayan ya kammala karatun sa kuma, sai ya fara aiki a matsayin ma’aikacin wucin gadi a Sashin Lafiya na karamar Hukumar Dala cikin shekara ta 1999 zuwa 2005, ya zauna a Fuskar Arewa Health Unit, da Makarantar Firamary ta Yalwa a Matsayin Jami’i mai kula da Lafiyar Dalibai. Ya zama cikakken ma’aikaci duk dai a wannan sashi na Lafiya a watan June na 2005.

Mukamai: ya fara a matsayin Ma’aikaci a Asibitin Adakawa, daga nan ya rike mukamin mataimakin Incherge a Fuskar Arewa Health Unit, sannan ya zama Shugaba wato Incherge duk dai a wurin daga 2006 zuwa 2008, Sannan ya samu ci gaba zuwa Jami’i mai kula da Alluran rigakafi na Karamar Hukumar Dala wato Cold Chain Officer (CCO) cikin 2008 zuwa 2013, sannan ya samu canjin aiki daga Karamar Hukumar Dala zuwa Gundumar Dawakin Tofa a matsayin Jami’in Kula da Alluran rigakafi na Gundumar Dawakin Tofa wato (Zonal CCO a Dawakin Tofa Zone) a shekara ta 2013.

Kungiyoyi: Ya zama mamba a kungiyoyi da dama, wasu kuma ya rike mukamai a cikin su, ga kadan daga ciki:

1. Al’azmiyyah Islamic Foundation daga 1998 to Date as National President/Founder

2. Kofar Kabuga Youth Development Association daga 1998-1999 Chairman sai kuma daga 1999-2004 as Secretary, da kuma 2004 to date as  Asst. Health Secretary. 

3. Professional Photographers Union of Nig. Kano State Branch from 2000-2004 as Asst. PRO

4. Environmental Health Officers Association of Nig. Dala LGA Branch as Vuce Chairman

5. Environmental Health Officers Association of Nig. Dala LGA Branch as Chairman

6. Dala Health Foundation from 2008-to date as Secretary. General.

7. Kano State Lafiya Jari Dala LGA Branch feom 2010 to Date as Chairman

8. Kabuga Readers Association as Adviser

9.  Goron Dutse Old Boys Association Class 96 GDOBA’96 from 2008 to Date as Chairman

10. Gidauniyar Tallafawa Marayu ta Jihar Kano 2013 to date as Treasure

Kungiyoyi: Ya samu shaidun yabo daga wurare da dama ciki har da

1.  Environmental Health Officers Association of Nig. Dala LGA Branch a 1999 -Certificate of Excellent

2. Almu’amamalat Hausa News Paper and Magazine in 2013 - Certificate of Commendation

3. Gidauniyar Tallafawa Marayu daga Tude a 2020

5. Shafin Zamantakewa a 2021

Zumunta Social Network of Nigeria a 2021

Har ila yau ya zama Online Editor na Jaridar Dala A Yau, kuma ya rike mukamai da dama a kungiyoyin social media ciki har da Zumunta Group, Dala Social Network, Zamantakewa, Matasan Zamanni social Network da Sauransu da dama.

Comrade Auwal Ayagi ya Zama Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kungiyar Kwadago na jihar Kano a kan kafofin sadarwa (PA Media and Publicity) a Shekara ta 2016. Ya samu ci gaba zuwa PA din Mataimakin Shugaban Kungiyar Kwadago na Kasa NLC, kuma Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Lafiya na Kasa MHWUN a 2023.

Ayagi yana sha’awar rubuce rubuce da bincike,.don ya rubuta littattafai da dama, ciki har da Alusmaniyyun (2002), Al-Usmaniyya (2024), Koyon Computer a Saukake (2025), Riba da Illolinta a musulunci (2025), Tasirin azimi ga Lafiya (2025) Kuma yana Sha'awar kallace kallace, yana da Aure da ‘ya’ya Uku, yana zune a Unguwar Rijiyar Zaki a halin yanzu.


Saturday, 5 April 2025

MAGUNGUNAN DA DINYA TAKE YI


KO KA SAN  MAGANIN DA DINYA KE IYA YI?

Na san mai karatu ya san abinda ake kira DINYA, wani irin yayan itace da yanzu sai a kauye a kan samu.

Muna yara mun sha dinya kusan a kullun muka je jeji. Amma ko mai karatu ya san dinya na daga cikin yayan itatuwan da ke da matukar amfani wajen yin magungunan cututtuka daban daban? Dinyan kansa, da kwallonsa da kuma ganyensa dukkansu magunguna ne masu amfani a jikinmu. Allah Ya mana arzikin magunguna, amma kash mun makale kan maganin bature ba tare da yin bincike da bunkasa namu ba da Allah Ya mana su iriiri a kewaye da mu. Yanzu dai tun yaushe rabonka ko rabonki da  shan dinya? Ga kadan daga cikin maganin ko amfanin da dinya key i a jikinmu.

CIWON SUGAR
A raba kwallon dinyan da tuwon kwallon  Sai a shanya kwallon a rana har zuwa kwanaki uku zuwa hudu har su bushe. Idan  sun bushe sai  a fasa kwallon a dauko dan cikin kwalon wanda launinsa korekore ne. Daga nan sai a farfasa wadannan yayan cikin kwallon a shanya su  na yan kwanaki a rana har su bushe.
Sai kuma a nika su su zama gari.
Sai kuma a ajiye garina kwalba a rufa sosai.  Za a dauki ruwa kofi guda  sannan a dauki cokalin tea na garin a zufa a ciki a gauraya  a rinka sha da safe kafin a karya kumallo.

1. Ganyen dinya babban magani ne na attini wato kashin jini.Kuma yana iya hana sake kamuwa da cutar har na tsawon lokaci.

2  Ganyen dinya  yana matukar maganin   (kidney stones)  wato dutsen koda.. A samu ganyen dinya kimanin nauyin gram 10 zuwa 15 a wanke.sai a matse ruwansa  a sanya kwayan bakin barkono guda uku a cikin ruwan a rinka sha  sau biyu a rana. Na tsawon kwanaki.

3, Ganyen dinya na dauke da sinadarin da ke hana cutar daji/ cancer  a jikin mutum kuma na  hana kari girma a jiki.
4.Idan kana zazzabin da ya wuce kwanaki uku, sai ka jika ganyen kana sha domin yana rage zafin jiki .

5. yana taimakawa wajen sa jini ya rinka gudana sosai a jikin mutum, wannan na taimakawa zuciya kwarai kuma ya magance kumburi a sakamakon rashin gudanar jini yadda ya kamata.

6. Idan kana da matsala a bakinka kamar wanda ke hanaka cin abinci ko zaizayewar fatan cikin baki, sai ka rinka wanke bakinka da ruwan ganyen dinya. Yana warkar da shi cikin lokaci kankani.kuma ya kara maka karfin hakora da dasorinka.. Ka tsinki ganyen dinya guda biyar zuwa shida ka matse ruwan kana kurkure bakinka .

7. Ganyen dinya na matukar maganin hawan jini domin ganyen na dauke da wani sinadarin da ke saukar da hawan jini

8. mace mai matsalar rashin haihuwa saboda matsaloli a mahaifarta, tana iya matse ruwan ganyen  ta sanya zuma a ciki tana sha..

9. Wanda yak e da basir yana iya matse ruwan ganyen dinya ya sanya ganyen (CHUTNEY) da na (JAGGERY) da kofi daya na madarar shanu a rinka sha na sati guda  yana taimakawa wajen basir da ke fitar da jini.

10. A cewar masana da suka yi bincike na kasar India, sun tabbatar da cewar in aka hada ganyen dinya da da yayan dinya fatar dinyan ana sha, yana maganin ciwon sugar kuma yana hana matsalar da ta kan faru na kasha karfin ido wa masu wannan ciwon na sugar.

11.Idan kina da kuraje a fuska, ana iya daka yaya/kwallon  dinyaa gauraya da madaran shanu sai a shafe fuska da shi kafin a kwanta sai a barshi sai da safe a wanke . yin hakan a kai a kai yana magance kurajen fuska.

12. Dinya yana da amfani wa masu karancin jini domin yana kunshe da sinadarin iron sosai da kuma vitamin C

13. Dinya da ya kai nauyin gram dari na dauke da  sinadarin potassium da ya kai mg55 wannan adadin ya isa ya tiamaka wajen ciwon zuciya, hawan jini da stroke, in an jibinci shan dinya gwargwado ba a wuce gona da iri ba yana taimakawa wajen hana toshewar hanyoyin jini. Kuma na taimakawa wajen hana kamuwa da cutar hanta saboda yana kunshe da sinadarin da ake kira (POLYPHENOL)

A KULA.
Masu ciki da masu shayarwa kada su yi amfani da dinya.

Kada mutum ya sha dinya kafin da kuma bayan an masa tiyata domin yana rage karfin hawan jini. Wadannan mutane su kaurace wa shan dinya na makonni biyu akalla kafin da kuma bayan an musu aiki.

A kauracewa shan dinya in cikinka ba komai.

A kaurace wa shan madara bayan an sha dinya.

A kaurace wa shan dinya da yawan gaske a lokaci guda.domin zai haddasa matsala a makoshi/makogwaroda kirji kuma zai iya sa tari da kuma tara majina a kirji.

(TUNTUBI LIKIYANKA KAGIN KA SOMA AMFANI DA KOWANE MAGANI)
source: Balarabe Shehu Illela fcbk handle


AL-USMAIYYUN (Littafi Na Daya) 2002


AL-USMANIYYUN

Littafin Daya Qunshi Tarihi Da Zuriyar

Malam Shehu Usman Hussaini Ayagi

Xan Asalin Garin Kumurya Dake

Qaramar Hukumar Bunkure Jihar Kano

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Wanda ya rubuta

 

AUWALU ZAKARIYYA MUHAMMAD USMAN AYAGI

 

 

 

 

Haqqin Mallaka (M) Al-Azmiyyah Ventures

 

 

An fara bugu wa 2002/1423

 

 

Sadaukarwa

Na sadaukar da wannan Littafi ga iyayena Alhaji Zakari Muhammad Usman Ayagi (Alh Amasha) da Mahaifiyata Hajiya Rakiya Usaini Lawan (Inna) Allah ya qara mata Lafiya. Da kuma xaukacin Musulmi musamman masu sada Zumunchi da umarni da sadashi

 

 

TSARA RUBUTU A COMPUTER

Beta Bussiness Centre, Kabuga

B.U.K Road, Kano

 

 

BUGAWA

Al-Azmiyyah Printers A Division of Al-Azmiyyah Ventures, Kogar Kabuga Quarters

POBox 13808 Kano.

E-mail: alazmiyya@gmail.com

 

Ta’aliqi

Ina godiya ga Allah Tabaraka wa Ta'ala, daya wajabta sadar da zumunci da kuma bada lada mai xibbin yawa ga duk wanda ya sadardabshi, da kuma yabo da salati ga Shugabamınu Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa da 'ya'yan Gidansa.

Bayan Haka haqiqa wannan littafi ya qunshi tarihin Malam Usman Kumurya, Dan Malam Husaini Dan Uwan Malam Hasan. Dukkansu haifaffun Kumurya ne, domin shi Malam Usman wanda aka fi sani da Malam Shchu, wanda dalilin haka ne ma, ake cewa da mahaifina Malam ldi xan Shchu, Mahaifinsa an haife sune su biyu kamar yadda Tarihi ya nuna, wato 'Yan Tagwayc, sai dai wanda ya haifi Mallam Usman Kumurya shi ne Malam Husaini Kumurya.

Hakika wannan tunani da wannan xa namu mai albarka yayi na binciko asalin mu, (wato Auwalu Zakari Muhd Usman Ayagi) da tushemu yana da kyau kwarai, Saboda Malaman Tarihi sun ce "Tarihi Mudubi nc na Al'ummar da suka shige" Ta inda za'a san irin rayuwar da suka yi.

To hakika mu sai muce san barka domin rayuwar magabatanmu rayuwa ce ta ilimi da cinikayya: kuma mu 'yan-Kano ne lyaye da Kakanninmu.

Saboda da haka wannan littafi ya na da kyau, ya kuma kunshi haqiqanin Zuriyar Malam Usman Kumurya 'ya'yansa da jikokinsa na wajen 'yaya mata da na wajan 'ya'ya maza da 'yayansu, da kuma suma 'yayansu.

A qarshe nake cewa Allah yayi wa zuriyar Malam Usman Kumurya Albarka, ya kuma haxa kansu, Amin summa Amin.

Husaini Idi Dan-Shehu Ayagi

Shugaban Makarantar Primary Ta

Danlami Ibrahim Islamiyya Ayagi

09-08-2002

 


 

Godiya

Da sunan Allah mai yawan Rahama mai yawan Jinkai.Tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da Alayensa da Sahabbansa baki daya.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai, da ya bani dama harna rubuta wannan littafi.

Bayan godiya ga Allah da salati ga Annabi (SAW) dole ne iny godiya ga wasu mutane saboda irin kwarin gwiwa. da shawarwari da suka bani wajen wallafa wannan littafi da kuma tarihai da suka bani da kuma sunayen da suka taimakamin wajen zakulowa.

Da farko dole ne in mika cikakkiyar godiya ta ga babbar jikar Mal. Usman wato Hajiya Jummai saboda irin tarihan da ta rinqa bani, da shawarwari da dama. Sannan ina mika godiya ta ga mahaifina Alh. Zakari Muhd (Amasha) da mahaifiyata suma saboda shawarwarin da suka bani.

Har ilayau ina mika godiya ga mutanen kul-kul, Iyalan Baba Uba Musamman dansa Ibrahim, sannan da mutancn Zariya kamar Baba Sani, Ladi, Shchu da sauransu, sannan godiya ta musamman ga Baba Yalwa da Hassan da Husaini da Safiya da Haj. Karama, da Lami, da kuma gabaxayan mutancn Fagge kamar su Ladidi, Zulaihat da Maimuna, da sauransu. Kai dama wanda duk ya taimaka da farin-cikinsa ko shawararsa, da duk abokaina da Malamaina da dalibaina da suka taimaka wajen fitowar wannan Littafi.

Daga karshe ina mika cikakkiyar godiya dayabo da jinjina ga Gwarzo na kuma Masani akan aikin sa Abdulkadir Ali Ahmad Kabara wanda da cikakkiyar gudummawarsa da nuna qwarewarsa ne wannan Littafi ya samu fitowa, dakuma Malamina Mai tarbiyata Wato Malam Auwalu Isa Yakasai Da kuma Malam Maisunan Malan Allah ya saka musu da Alheri, kuma Allah ya cika musu burinsu a duniya da Lahira.

Wassalamu Alaikum Warahmatullah

Auwal Zakari Muhammad Ayagi

Al-Azmiyyah Ventures

No. 852 Kofar Kabuga,

Kano State.

 

Gabatarwa

Da sunan Allah mai Rahma Mai jinkai, Ubangiji Mahaliccin Sammai da qassai, tsira da Aminci su tabbata ga Annabinmu Annabin Rahma, shugabanmu Annabi Muhammadu (SAW) Allalh ya qara tsiransa ga sahabbansa da Alayensa da masoyansu da mabiyansu har zuwa ranar Al-qiyama, Innamal A'amalu Binniyati, wa'inn ma likulli Imri'in ma nawa (Hadis Ash-sharif).

Bayan haka acikin wannan dan taqaitacccn littafi wanda ya qunshi Tarihi da kasuwanci da zuriyar Mal. Usman da na wallafa, nayi shine musamman don ganin na zaburar da jama'a (musamman zuriyarsa) zuwa ga sada zumunci, musamman domin ganin yadda jama'ar wannan zamani sukai sako-sako da zumunci, sai kaga dan'uwa da dan'uwa sun hadu amma basu san ccwa su 'yan-uwa ba ne.

Kuma gashi Allah da Manzon Allah (SAW) sun yi umarni da lallÄ…i mu sada zumunci kuma mu guji yanke shi. Kamar yadda Manzon Allah yace:- "MAI YANKE ZUMUNCI BAZAI SHIGA ALJANNA BA"

Sannan yace: - YANA DAGA MANYA-MANYAN FALALOLI KA SADAR DA ZUMUNCI GA WANDA YA YANKE MAKA"

Har ila yau ya kara da cewa:- "HAQIQA ARRAHIM (Wato zumunci) TSAGI NE DAGA SỤNAN ALLAH ARRAHMAN (wato mai yawán Rahma) ALLAH YACE: WANDA YA SADA SHI (Zumunci) ZAN SADASHI DA RAHAMA WANDA YA YANKE SHI (Zumunci) ZAN YANKE SHI DAGA RAHMA".

Har ilayau dai yace:- "ABUBUWA HUDU ( SUNA DAGA TASKOKIN ALJANNA: -

1. SIRRINTA YIN SADAKA

2. BOYE MUSIBA

3. SADA ZUMUNCI

4. FADIN "LAHAULA WALA KUWATA ILLA BILLAHI'

Da sauran Hadisai da dama, kuma ya tabbata cikin Hadisin Annabi cewa: "Kasan Allah kafin ka bauta masa" saboda haka wanda duka bai san 'yan-uwan sa ba, to bazai iya sada zumunci ba, don haka na himmatu wajen wallafa wannan littafi da fatan Allah (SWT) ya sa wannan littafi ya zama sila ko wata hanya ta sada zumunci, kuma ya zama izna ko jankunnc ga masu yanke zumunci, su dawo ga sadashi, Allah (SWT) ya sakamu cikin masu sada zumunci kuma ya sadamu da Rahamarsa, ya shiryar

da masu yake zumunci su zama daga cikin masu sada zumunci don su sami Rahmar Ubangiji, Amin.

Auwal Zakari Muhd Ayàgi

ABUBUWAN DA KE CIKI

ABUBUWAN DA KE CIKI                    Shafi

Shafin Farko ………….…………………………..…1

Sadaukarwa……………………….……,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,2

Ta’aliqi……………………………………,,,,,,,,,,,… 3

Godoiya…………………………………,,,,,…,,…4

Abubuwan da ke ciki……………………………,,…7

Gabatarwa…………………………………………,..8

Babi Na Farko:

Taqaitaccen Mal. Usman………………,,,,,,.…,…. 10

Matansa……………………………………,………11

‘Ya’yansa……………………………………...,,….12

Jikokinsa,,,………,,,,,,,,…………………/….,,,,,,,..,14

‘Ya’yan Jikokinsa …………………..…,,,……,,…17

Tattava Kunnensa…,,………,,,,,,,,,…………….… 20

‘Yayan Tattava Kunnensa ……,,,,, ………….……27

Babi Na Biyu

Kammalawa……,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,29Fadakarwa………………………….,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,30

 

 

 

 

 

 

 

 

BABI NA FARKO

Kasuwanci A Zamanin Da

Kano ta Dabo Tumbin Giwa, Yaro koda me kazo an fika. Wannan shi ne kirarin da ke yiwa Kano, saboda shahararta ta kowanne bangare musamman kasuwanci, don haka ne ma ake cewa da Kano cibiyar kasuwanci wato (Center of Commance) kamar yadda yake a rubuce a kowacce lambar mota ta Kanon. To duk wannan ya samo asaline tin zamanin daya shuxe, lokacin da ba jiragc, ba motoci ba kekuna sai jakuna da dawakai da Raquma sama da shekaru dubu da suka wuce.

Daga cikin sana'o'in da Kano ta shahara da su a a zamanin da can, sun hada da Noma, Saqa, qira, Fatauci, Kiwo, Gini da sauransu. To amma Noma da fatauci sune suka fi shahara a wancan zamanin, don a da ance Kano ba abin da zai fara zuwa zuciyarka, sai Dalar Gyada, Kano ta shahara sosai da wannan sana'a.

Haka ma fatauci daxaxxiyar sana'ace ta mutanen Kano, Fatauci ya kasu daban-daban akwai gajcren Fatauci, inda mutum zai tafi kusa da garinsu yayyo siyayya ya dawo garinsu ya sayar, akwai kuma wanda zai tafi gari mai nisa, ya kwashe watanni ko shekaru, wasu ma in suka tafi sun tafi Kenan, acan zasu yi aure su hayayyafa, don hakane ma ba garin da zakaje ba ka ga Bahaushe ba, to wannan ya samo asali ne ta hanyar Fatauci. Galibi fatauci ana yinsa ne ta hanyar Ayari a karkashin jagoracin Madugu, dole ne ya zama shi Madugun yafi kowa shiri sabo da hatsarin da ke cikin sana'ar kamar Yan-Fashi, Barayi, Almatsutsai Namun Daji da suke kan hanyar. Har hausawa kan yi masa kirari da "Madugu Uban Tafiya".

 

 

BABI NA BIYU

Taqaitaccen Tarihin Mal. Usman

Malam Usman wanda aka fi sani da Shehu, cikakken sunansa shine Shehu Usmanu dan Hussaini Mutumin Garin Kumurya.

An haife shi a wani garı mai suna Kumurya wanda a yanzu yake cikin karamar hukumar Bunkure ta jihar Kano. Malam Usmanu ya taso cikin karatun Addinin Mlusulunci, sannan kuma ya na sana'ar Noma (Kamar yadda ta shahara a wancan zamanin) Allah ya daukaka Mal. Usman a wannan sana'ar ta Noma, inda ya mallaki nanya-manyan gonaki, kuna yake noma su.

A inda daga bisani ya fara sana'ar fatauci ta hanyar siyan kayayyaki ya tafi dasu wadansu garuruwan ya sayar ya sayo wasu acan ya kai garinsu. Har daga baya sai ya fara barin kasar Kano ya na wannan tafiye-tafiye ne ta hanyar Ayari na Fatake, suna wannan Fataunci ne akan Jakuna, zasu dorawa Jakunan Kaya su kuma su bisu a kasa, suna daukan watanni kafin su isa, da sunje sun siyar sai su sayo wadanda akce bukata a wannan garin su tawo da su. Idan sun iso sukan yada Zango a wani guri mai yawan ruwa da bishiyoyi, su tsaya su wanke jikinsu, su ba Jakunansu ruwa suyi kiwo, su huta saboda gurin ya yi kama da can kudancin kasarnan inda suke zuwa wato Kurmi, to in sun tsaya su na hutawa, sai Jama'a su dinga zuwa suna sayan kayayyaki, abin ya na ci gaba, wasu ma anan kayansu suke karewa sai su koma.

Ana halin haka saí ya zama kamar Al-ada da Sun dawo sai su ce, mu tafi Kurmin Kano, to da zarar sun zo sai Mal. Usman ya wuce gidan wani Abokinsa ya sauka da yake a wata unguwa kusa da wannan Kurmin mai suna Mararraba, in ya siyar da kayansa da wuri sai ya yi sauri yaje garinsu Kumurya ya dawo kafin ayari ya tashi.

Ana cikin wannan hali sai wannan Abokin nasa ya bashi shawarar cewa kamata ya yi, ya sa yi gida a nan kusa da Kurmin, shi ma, idan suka sauka, sai ya sauka a gidansa, idan ayari ba zai tashi da wuri ba, sai yaje Kumurya garisu, in kuma da wuri zasu tashi, shi ke nan sai ya koma, sai Mal. Usman yai na'am da wannan shawarar kuma ya danka komai a hannun abokin na sa, akan ya nemo masa gida, idan ya dawo sai ya bashi kudin (a lokacin ana lissafi da keso ne, ba Naira ba) haka kuwa aka yi, yana dawowa, sai ya samu Abokin nasa ya sai mai gida akusa da unguwarsu a wata unguwa mai suna Ungwar Ayagi, suka je ya ga gida ya yi farin-ciki, da ya sai da kayansa ya kawo kudin sa ya bashi, inda daga baya sai ya debo iyalansa ya dawo dasu gidansa. To wamman shine dalilin zamansa a Unguwr Ayagi.

A wani Labarin kuma cewa akayi, ya zo cikin Kano ne neman Ilimin Addini, bayan ya Sauke Alkur’ani a can Kumurya, sai ya shigo Birni qarin neman Ilim, yana neman Ilimin ne ya fara sana’ar Fatauchi, har ya sa aka nema masa gidan ya siya, ya xebo iyalan sa suka dawo.

Haka Mal. Usman ya cigaba da wannan sana'a har lokacin da girma ya zo masa, sai ya dene Fatauci ya zauna a gidansa daya siya ya cigaba da kasuwanci a wannan waje, wanda a yanzu akewa lakabi da kasuwar Kurmi har zuwa lokacin da Allah ya karbi ransa, Allah, ya jikan sa da Rahamrsa Amin.

 

BABI NA UKU

ZURI’AR MAL. USMAN

Kusan wannan shine maqasudin rubuta wannan littafi, domin Allah ya albarkanci Mal. Usman da zuriya masu yawa, ko da yake sai da haifi ‘ya’ya takwas suna rasuwa, sai ta Taran ce Ayashe ta tsaya,. Don haka na kasa wannan kasha gida shida, kamar yadda zai zo a qasa.

 

 

 

Kashi na Farko

Matansa

 

Mal. Usman ya rasu ya bar Mata Huxu kamar haka:

1.              Fadimatu

2.              Hassana

3.              Hassana (Iya Masa)

4.              Amina (Aisa)

Kashi na Biyu

‘Ya’yansa

Mal. Usman ya rasu yabar ‘ya’ya ne guda Bakwai a raye, amma kafin ya rasu ya binne wasu da dama kamar yadda ita Hajiya Jummai ta tabbatar min, amma bakwai (7) sune wadanda ya rasu ya bari a duniya.

‘Ya’yansa sune kamar haka:

1.              Aishatu Usman (Ayashe)

2.              Hauwa’u Usman (Inna ta Fagge)

3.              Muhammad Usman (Baba Mai Goro)

4.              Amina Usman (Inna Amina)

5.              Sulaiman Usman (Baba Mai Lemo)

6.              Idris Usman (Idi Dan Shehu)

7.              Furera Usman (Hajyan Anchau)

Wadannan sune ‘ya’yan Mal. Usman guda bakwai, a inda daga cikin Mazan wasu sun gajeshi a sana’arsa ta fatauci.Kamar Muhammad yayi Sana’ar fatauci a Ikko inda ya zauna acan har yayi aure ya haifi wasu daga ‘ya’yansa a can, har sai da ya rike sarkin Hausawan acan iko ko Shagamu.

Allah ya jiqansu Ameen.

Kashi Na Uku

Jikokinsa

Yayan Aishatu Usman (Ayashe)

1. Hauwa’u (Hajiya Jummai)

2. Atine      (Tarasu)

‘Ya’yan Hauwa Usman (Inna ta Fagge)

2. Musa               (Ya Rasu)

‘Ya’yan Amina Usman

1. Sa’idu    (Baba Na Kafi) Ya Rasu

2. Abubakar (Uba na Kul-kul) Ya Rasu 9/12/2002

‘Ya’yan Furaira Usman

1.              Abubakar (Garba Kyauta)

‘Ya’yan Sulaiman Usman (Mai Lemo)

 1,      Garba        (Uban Kano)

2.              Inuwa          (Ya Rasu)

3.              Idris            (Dan Zaria) ya Rasu

4.              Fatima         (Jummai)    

5.              Muhammadu Sani

‘Ya’yan Muhammad Usman (Mai Goro)

1.              Zakariyya    (Amasha)

2.              Sadiya         (Asabe) Ta Rasu

‘Ya’yan Idris Usman (Idi Dan Shehu)

1.              Aisha          (Inna Yalwa)

2.              Saude          (Ta Rasu)

3.              Hassan       

4.              Hussaini     

Wadannan sune jikokin Mal. Usman Goma sha Bakwai (17), Goma (10) suke raye, Allah ya gafartawa wadanda suka rasu Amin.

Kashi Na Hudu:

‘Ya’yan Jikokinsa

Jikokin Aishatu Usman (Ayashe)

Yayan Hauwa’u (Hajiya Jummai)

1. Zulaihat (Yar Mallam)  Ta rasu

2. Sadiya (Hajiya Karama)

3. Sadiya (Lami)

‘Ya’yan Atine

Tarasu kafin ta haihu

Jikokin Hauwa’u Usman (inna ta fagge)

Yayan Musa (Baba na Fagge)

1.              Nasidi                             7. Ruqayya

2.              Ishak (Alh. Maikudi)      8. Ibrahim

3.              Isa                                   9. Idris (Dantalata)

4.              Adamu                           10. Usamatu

5.              Kadija  (Gambo)             11. Aliyu

6.              Fatima (Asabe)                12. Abdulkadir

 

Jikokin Amina Usman

‘Ya’yan Sa’idu (Baba Agwa)

1.              Auwalu (Lawan)  

2.              Adamu                 

3.              Zulaiha

4.              Abubakar

‘Ya’yan Abubakar (Uba Na Kul-Kul)

1.              Habiba                  6.Binta

2.              Dauda                   7. Ibrahim

3.              Furera (Laraba)     8. Musa

4.              Aliyu                              9. Amina

5.              Auwalu                

       

Jikokin Furaira Usman

‘Ya’yan Abubakar (Garba Kyauta)

1.              Furaira (Mammy) 

2.              Sulaiman (Abba)  

3.              Saliha (Ummi)     

4.              Hadiza (Baby)      

5.              Abdulmumin       

6.              Hafsatu

* Yayan Abubakar Sune Yayan Jummai

*Suna Zaune a Banzazzau Kusa da Gidan Kogi, Zaria Jihar Kaduna

Jikokin Sulaiman Usman (Mai Lemo)

Yayan Inuwa Sulaiman Usman

1.              (Ladi) Tarasu                  6. Maryam (Mama)

2.              Shehu                             7. Tukur

3.              Umar                                        8. Adamu

4.              Tanimu                           9. Musa

5.              Rukayya (Gaje)               Hadiza

                 

‘Ya’yan Idris Sulaiman Usman (Dan Zaria)

1.              Maryam     

2.              Bashari       

3.              Tukur         

4.              Hauwa

Yayan Jummai Sulaiman Usman

1.              Furaira (Mammy)

2.              Sulaiman (Abba)  

3.              Saliha (Ummi)     

4.              Hadiza (Baby)      

5.              Abdulmumin       

6.              Hafsatu

v   Yayan Jummai Sune Yayan Abubakar

Jikokin Muhammad Usman (Mai Goro)

Yayan Zakariyya Muhammad Usman

1.              Muhammad Auwal        

2.              Muhammad Sani

3.              Muhd. Salisu       

4.              Rukayya (Lami)   

5.              Hauwa’u (Hajiya)

6.              Muhd. Rabi’u      

7.              Saifullahi             

8.              Abdulrashid         

9.              Zakariyya (Halifa)

10.         Aliyu (Baffa)

 

Jikokin Idris Usman (Idi Dan Shehu)

‘Ya’yan Saude Idris Usman

1.              Aishatu (Yar yaye)                   5. Abdulrashid (Yarasu)

2.              Rabi’u                            6. Suwaiba (Ta Rasu)

3.              Misbahu                         7. Ummahani

4.              Asma’u                          8. Hauwa (Jummai)

‘Ya’yan Hassan Idris Usman

1.              Idris (Halifa)        

2.              Usman                 

‘Ya’yan Husaini Idris Usman (Yarasu)

1.                 Aisha (Ummi)     

2.                 Muammadu        

3.                 Fatima

Wadannan Sune Yayan Jikokin Mal. Usman, wadanda suka rasu Allah ya gafarta musu Amin.

 

 

 

Kashi Na Biyar

Tattaba Kunnensa

‘Ya’yan Jikokin Aishatu Usamn (Ayashe)

Jikokin Hauwa’u (Haj. Jummai)

‘Ya’yan Zulai (Yar Mallam)

1.              Ibrahim                

2.              Safiyya                

Yayan Sadiya (Hajiya Karama)

1.              Jamila          (Ta Rasu)    6. Abadiyya

2.              Yasin          (Yarasu)      7. Ubayyu

3.              Kudsiyya                        8. Wasilu

4.              Mujibur-Rahman           9. Saddiqa

5.              Mansulu                        

Ya’yan Sadiya (Lami)     

1.              Tijjani                            6.Aisha                

2.              Abubakar                        7. Kabiru

3.              Salamatu                         8. Aminu

4.              Fatima                            9. Aminu

5.              Bilkisu                                              

‘Ya’yan Jikokin Hauwa Usman (Inna Ta Fagge)

Jikokin Musa (Baba Na Fagge)

‘Ya’yan Nasidi

1.              Jamila (Tarasu)

2.              Maryam (Tarasu)

 

‘Ya’yan Ishak Musa (Alh. Maikudi Sarkin Fata)

1.              Hauwa (Maituwo) Tarasu 12. Ruqayya

2.              Binta (Ladidi)                 13. Hadiza

3.              Bashir                             14. Muhd (Yaya)

4.              Hauwa (Maijidda)           15. Ishaq (Alhaj)

5.              Aisha (Mai Riga)            16. Ibrahim

6.              Babangida                      17. Amina

7.              Ahmad                           18. Mahmud

8.              Habiba                            19. Hauwa (Momy)

9.              Musa (Abba)                   20. Aisua

10.         Zulaihat                          21. Bulyaminu

11.         Abdul-Hamidu               22. Nuraddin

‘Ya’yan Isa Musa

1)             Hannatu                          7. Khalil

2)             Jamila                             8. Isa (Babannan)

3)             Aminu                           9. Fatima

4)             Musa (Abba)                  10. Muhammad

5)             Ishak (Alhaji)                  11. Rabi

6)             Zainab                            12. Zakariyya

‘Ya’yan Adamu Musa

1.              Hauwa’u               4. Musa

2.              Aisha                    5. Muhammad

3.              Umar                     6. Abubakar

‘Ya’yan Khadija (Gambo) Musa

1.              Auwalu                 4. Fatihu

2.              Ibrahim                 5. Sulaiman

3.              Maryam                6. Aisha

‘Ya’yan Fatima (Asabe) Musa

1.              Maimuna              4. Faisal

2.              Rabi’u                  5. Muhd Sani

3.              Aina’u                  6. Umar

Ya’yan Rukayya Musa

1.              Kabiru                  4. Idris

2.              Halima                  5. Salmanu

3.              Aisha                    6. Sukairaju

‘Ya’yan Ibrahim Musa

1.              Hafsiyya     

2.              Abdullahi

3.              Furaira

4.              Usman

5.              Binta (Ummi)

 

‘Ya’yan Jikokin Amina

Jikokin Sa’idu (Baba Agwa)

Ya’yan Lawan Sa’idu

1.              Maryam

2.              Zubaida

3.              Zahara’u

Ya’yan Adamu Sa’idu

1.              Hamza        

2.              Saidu (Abba)                 

3.              Furera (Balaraba) 

‘Ya’yan Zulai Sa’idu

1.              Salisu

‘Ya’yan Abubakar Sa’idu

1.              Ibrahim (Halifa)

Jikokin Abubakar (Uba Na Kul-Kul)

Yayan Habiba Abubakar

1.              Saadiku                5. Hauwa’u (Ummi)      

2.              Fatihu                             6. Ibrahim

3.              Kamalu                 7. Aba Yazid

4.              Alawiyya              8. Sadiya

‘Ya’yan Dauda Abubakar

1.              Abdulrahaman

2.              Mustafa

Yayan Furaira Abubakar (Laraba) (09039151977)

1.              Zahara’u     

2.              Yakuba      

3.              Aminu       

4.              Shamsuddin         

5.              Mikidaru    

6.              Marakisiyya

7.              Maryam     

8.              Amina        

Yayan Binta Abubakar

1.              Aminu

2.              Zainab (Ummi)

3.              Aisha                    (08104066354)

‘Ya’yan Jikokin Sulaiman Usman

Jikokin Inuwa Sulaiman Usman

‘Ya’yan Amina (Ladi) Inuwa Sulaiman Usman

1.               Amina

2.               Abubakar

3.               Sadiya

4.               Hauwa

5.               Muzakkir

‘Ya’yan Tukur (Alhaji) Inuwa Sulaiman

1.              Amina

2.              Abubakar (Halifa)

‘Ya’yan Adamu Inuwa Sulaiman

1.              Muhd. Inuwa (Alhaji)

‘Ya’yan Hadiza Inuwa Sulaiman Usman

1.              Samha         (07032099857)

2.              Aminu

‘Ya’yan Rukayya (Gaje) Inuwa Sulaiman

1.              Sa’idu

2.              Sumayya

3.              Badamasi (Halifa)

‘Ya’yan Maryam Inuwa Sulaiman Usman

1.              Imran

2.              Asma’u

‘Ya’yan Jikokin Muhammad Usman

Jikokin Zakariyya Muhammad Usman

‘Ya’yan Rukayya Zakari Muhammad Usman

1.              Hafasat                 

2.              Sadiyya               

‘Ya’yan Jikokin Idris Usman

Jikokin Saude Idris Usman

‘Ya’yan Aishatu (Yaryaye)

1.              Amina                 

2.              Zainab                 

‘Ya’yan Rabi’u

1.              Fiddausi     

2.              Fatima (Momy)

3.              Habiba

‘Ya’yan Misbahu

1.              Rukayya    

‘Ya’yan Asma’u

1.              Fatima  (Ummi)

2.              Aisha         

3.              Sa’adatu     

4.              Khadija      

‘Ya’yan Ummahani

1.              Abdulhamid

‘Ya’yan Hauwa (Jummai)

1.              Aisha (Tarasu)

Wadannan sune tattaba kunnensa.

 

 

 

KASHI NA SHIDA

YA’YAN TATTABA KUNNENSA

Tataba Kunnen Aisha Usman

‘Ya’yan Jikokin Hauwa (Haj. Jummai)

Jikokin Zulai (Yar Malam)

‘Ya’yan Ibrahim

1.              Abubakar             

2.              Abdulrahman       

‘Ya’yan Safiya

1.              Hafsat                    5. Sahlat

2.              Aisha                    6. Umar

3.              Ramlatu                7. Maimunatu

4.              Muhammad                   

Jikokin Sadiya (Haj. Karama)

‘Ya’yan Kudsiyyah

1.              Amina

2.              Ahmad

3.              Muhammad

Jikokin Sadiya (Lami)

‘Ya’yan Salamatu (Magajiya)

1.              Mariya

  

Tattaba Kunnen Hauwa’u Usman

Yayan Jikokin Musa na Fagge

Jikokin Ishak (Alh. Maikudi)

‘Ya’yan Hauwa (Maituwo)

1.              Abubakar (Abba)           4. Shafa’atu

2.              Zahara’u                         5. Mubarak

3.              Maryam                          6. Najib

‘Ya’yan Binta Ishak Musa (Ladidi)

1.              Maryam (Ummi)

2.              Idris

3.              Muhammad Sani

4.              Hasiya                 

5.              Hauwa (Mamy)    

‘Ya’yan Bashir Ishak Musa

1.              Ishak (Khalifa)

2.              Salihu

3.              Muhammad Arab

‘Ya’yan Hauwa Ishak Musa (Maijidda)

1.              Khadija (Yariny)

2.              Ishak (Amir)

‘Ya’yan Aisha Ishak Musa (Meriga)

1.              Ahmad

2.              Muhammad

Jikokin Isa Musa

‘Ya’yan Hannatu Isa Musa

1.              Bashir

‘Ya’yan Jamila Isa Musa

1.              Rumasa’u

2.              Rabi

Jikokin Rukayya Musa

‘Ya’yan Kabir

1.              Adamu

Tattaba Kunnen Amina

Yayan Jikokin Sa’idu

Jikokin Lawan

‘Ya’yan Maryam

1.              Rabi’a

‘Ya’yan Jikokin Abubakar (Uba)

Jikokin Furere Abubakar (Laraba)

‘Ya’yan Zahara’u

1.              Bilkisu

2.              Salisu

Wadannan sune Yayan Tattaba Kunnensa

 

  

 

FADAKARWA

lna fadakar da sauran dangi cewa duk wanda yaga wani gyara ko kuskuren arubuta suna ko ragi ko qari na wasu Sunayen., ko yake da wani karin bayani da zai daxa kyautata littafin da ya sanar da ni cikin gaggawa, in za'a buga na biyu sai a shigar da su.

Da fatan Abin da nayi Allah ya karba, ya mika ladan ga shi Shehu Usman da ‘ya’yayensa da jikokinsa da suka rigamu gidan gaskiya, muma in munzo cikawa, Allah ya sa mu cika da Imani, Amin. Abin da aka yi na kuskure kuma Allah ya yafe mana, Amin.

 

KAMMALAWA

Alhamdulillahi, Alhamulillahi, Godya ta tta ga Ubangijin da ya halicci hallita ya kuma daidaitata, snnan ya sanya mata tsarin da zata tafi a kansa, kuma ya wajabta zumunci ya sanya lada mai dinbun yawa ga wanda ya sadar da shi, Tsira da amini su qara tabbata ga fiyayycn halitta, wanda ya tsamo mu daga duhun vata, zuwa hasken shiriya na Addinin Musulunci, Annabi ma’abocin cikar kalama da sada zumunci, shugaban da yake cewa: ‘Wanda yake so Allah ya yalwata masa (a cikin rayuwar sa), kuma a qara masa acikin arzikinsa, to yabi iyayen sa, kuma ya sadar da zumunci'  Sallallahu alaihi wasallam, Manzo yayi gaskiya. Allah cikin salatin ka hada da iyalan gidan sa, da sahabbansa baki daya.

Bayan haka, ina mai daxa godewa Allah daya bani damar kammala wannan litafi dana fara rubutawa Ranar 20-02-2001 zuwa yau Albamis 01-08-2002.

ALHAMDULILLAH

Sai Mun Haxu a Littafi Na Biyu

AUWAL ZAKARI MUHD AYAGI

(2 JUMADA THANI 1423)

01-AUGUST 2002