KO KA SAN MAGANIN DA DINYA KE IYA YI?
Na san mai karatu ya san abinda ake kira DINYA, wani irin yayan itace da yanzu sai a kauye a kan samu.
Muna yara mun sha dinya kusan a kullun muka je jeji. Amma ko mai karatu ya san dinya na daga cikin yayan itatuwan da ke da matukar amfani wajen yin magungunan cututtuka daban daban? Dinyan kansa, da kwallonsa da kuma ganyensa dukkansu magunguna ne masu amfani a jikinmu. Allah Ya mana arzikin magunguna, amma kash mun makale kan maganin bature ba tare da yin bincike da bunkasa namu ba da Allah Ya mana su iriiri a kewaye da mu. Yanzu dai tun yaushe rabonka ko rabonki da shan dinya? Ga kadan daga cikin maganin ko amfanin da dinya key i a jikinmu.
CIWON SUGAR
A raba kwallon dinyan da tuwon kwallon Sai a shanya kwallon a rana har zuwa kwanaki uku zuwa hudu har su bushe. Idan sun bushe sai a fasa kwallon a dauko dan cikin kwalon wanda launinsa korekore ne. Daga nan sai a farfasa wadannan yayan cikin kwallon a shanya su na yan kwanaki a rana har su bushe.
Sai kuma a nika su su zama gari.
Sai kuma a ajiye garina kwalba a rufa sosai. Za a dauki ruwa kofi guda sannan a dauki cokalin tea na garin a zufa a ciki a gauraya a rinka sha da safe kafin a karya kumallo.
1. Ganyen dinya babban magani ne na attini wato kashin jini.Kuma yana iya hana sake kamuwa da cutar har na tsawon lokaci.
2 Ganyen dinya yana matukar maganin (kidney stones) wato dutsen koda.. A samu ganyen dinya kimanin nauyin gram 10 zuwa 15 a wanke.sai a matse ruwansa a sanya kwayan bakin barkono guda uku a cikin ruwan a rinka sha sau biyu a rana. Na tsawon kwanaki.
3, Ganyen dinya na dauke da sinadarin da ke hana cutar daji/ cancer a jikin mutum kuma na hana kari girma a jiki.
4.Idan kana zazzabin da ya wuce kwanaki uku, sai ka jika ganyen kana sha domin yana rage zafin jiki .
5. yana taimakawa wajen sa jini ya rinka gudana sosai a jikin mutum, wannan na taimakawa zuciya kwarai kuma ya magance kumburi a sakamakon rashin gudanar jini yadda ya kamata.
6. Idan kana da matsala a bakinka kamar wanda ke hanaka cin abinci ko zaizayewar fatan cikin baki, sai ka rinka wanke bakinka da ruwan ganyen dinya. Yana warkar da shi cikin lokaci kankani.kuma ya kara maka karfin hakora da dasorinka.. Ka tsinki ganyen dinya guda biyar zuwa shida ka matse ruwan kana kurkure bakinka .
7. Ganyen dinya na matukar maganin hawan jini domin ganyen na dauke da wani sinadarin da ke saukar da hawan jini
8. mace mai matsalar rashin haihuwa saboda matsaloli a mahaifarta, tana iya matse ruwan ganyen ta sanya zuma a ciki tana sha..
9. Wanda yak e da basir yana iya matse ruwan ganyen dinya ya sanya ganyen (CHUTNEY) da na (JAGGERY) da kofi daya na madarar shanu a rinka sha na sati guda yana taimakawa wajen basir da ke fitar da jini.
10. A cewar masana da suka yi bincike na kasar India, sun tabbatar da cewar in aka hada ganyen dinya da da yayan dinya fatar dinyan ana sha, yana maganin ciwon sugar kuma yana hana matsalar da ta kan faru na kasha karfin ido wa masu wannan ciwon na sugar.
11.Idan kina da kuraje a fuska, ana iya daka yaya/kwallon dinyaa gauraya da madaran shanu sai a shafe fuska da shi kafin a kwanta sai a barshi sai da safe a wanke . yin hakan a kai a kai yana magance kurajen fuska.
12. Dinya yana da amfani wa masu karancin jini domin yana kunshe da sinadarin iron sosai da kuma vitamin C
13. Dinya da ya kai nauyin gram dari na dauke da sinadarin potassium da ya kai mg55 wannan adadin ya isa ya tiamaka wajen ciwon zuciya, hawan jini da stroke, in an jibinci shan dinya gwargwado ba a wuce gona da iri ba yana taimakawa wajen hana toshewar hanyoyin jini. Kuma na taimakawa wajen hana kamuwa da cutar hanta saboda yana kunshe da sinadarin da ake kira (POLYPHENOL)
A KULA.
Masu ciki da masu shayarwa kada su yi amfani da dinya.
Kada mutum ya sha dinya kafin da kuma bayan an masa tiyata domin yana rage karfin hawan jini. Wadannan mutane su kaurace wa shan dinya na makonni biyu akalla kafin da kuma bayan an musu aiki.
A kauracewa shan dinya in cikinka ba komai.
A kaurace wa shan madara bayan an sha dinya.
A kaurace wa shan dinya da yawan gaske a lokaci guda.domin zai haddasa matsala a makoshi/makogwaroda kirji kuma zai iya sa tari da kuma tara majina a kirji.
(TUNTUBI LIKIYANKA KAGIN KA SOMA AMFANI DA KOWANE MAGANI)
source: Balarabe Shehu Illela fcbk handle
No comments:
Post a Comment