AL-USMANIYYUN
Littafin Daya Qunshi Tarihi Da Zuriyar
Malam Shehu
Usman Hussaini Ayagi
Xan Asalin Garin
Kumurya Dake
Qaramar Hukumar
Bunkure Jihar Kano
Wanda ya rubuta
AUWALU ZAKARIYYA
MUHAMMAD USMAN AYAGI
Haqqin Mallaka (M) Al-Azmiyyah Ventures
An fara bugu wa 2002/1423
Sadaukarwa
Na sadaukar da
wannan Littafi ga iyayena Alhaji Zakari Muhammad Usman Ayagi (Alh Amasha) da Mahaifiyata
Hajiya Rakiya Usaini Lawan (Inna) Allah ya qara mata Lafiya. Da kuma xaukacin Musulmi musamman masu sada
Zumunchi da umarni da sadashi
TSARA
RUBUTU A COMPUTER
Beta Bussiness
Centre, Kabuga
B.U.K Road, Kano
BUGAWA
Al-Azmiyyah Printers A Division of Al-Azmiyyah Ventures, Kogar Kabuga Quarters
POBox 13808 Kano.
E-mail:
alazmiyya@gmail.com
Ta’aliqi
Ina godiya ga
Allah Tabaraka wa Ta'ala, daya wajabta sadar da zumunci da kuma bada lada mai
xibbin yawa ga duk wanda ya sadardabshi, da kuma yabo da salati ga Shugabamınu
Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa da 'ya'yan Gidansa.
Bayan Haka haqiqa
wannan littafi ya qunshi tarihin Malam Usman Kumurya, Dan Malam Husaini Dan
Uwan Malam Hasan. Dukkansu haifaffun Kumurya ne, domin shi Malam Usman wanda
aka fi sani da Malam Shchu, wanda dalilin haka ne ma, ake cewa da mahaifina
Malam ldi xan Shchu, Mahaifinsa an haife sune su biyu kamar yadda Tarihi ya
nuna, wato 'Yan Tagwayc, sai dai wanda ya haifi Mallam Usman Kumurya shi ne
Malam Husaini Kumurya.
Hakika wannan
tunani da wannan xa namu mai albarka yayi na binciko asalin mu, (wato Auwalu
Zakari Muhd Usman Ayagi) da tushemu yana da kyau kwarai, Saboda Malaman Tarihi
sun ce "Tarihi Mudubi nc na Al'ummar da suka shige" Ta inda za'a san
irin rayuwar da suka yi.
To hakika mu sai
muce san barka domin rayuwar magabatanmu rayuwa ce ta ilimi da cinikayya: kuma
mu 'yan-Kano ne lyaye da Kakanninmu.
Saboda da haka
wannan littafi ya na da kyau, ya kuma kunshi haqiqanin Zuriyar Malam Usman
Kumurya 'ya'yansa da jikokinsa na wajen 'yaya mata da na wajan 'ya'ya maza da
'yayansu, da kuma suma 'yayansu.
A qarshe nake
cewa Allah yayi wa zuriyar Malam Usman Kumurya Albarka, ya kuma haxa kansu,
Amin summa Amin.
Husaini Idi
Dan-Shehu Ayagi
Shugaban
Makarantar Primary Ta
Danlami Ibrahim
Islamiyya Ayagi
09-08-2002
Godiya
Da sunan Allah mai
yawan Rahama mai yawan Jinkai.Tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad
(SAW) da Alayensa da Sahabbansa baki daya.
Godiya ta tabbata
ga Allah Ubangijin Talikai, da ya bani dama harna rubuta wannan littafi.
Bayan godiya ga
Allah da salati ga Annabi (SAW) dole ne iny godiya ga wasu mutane saboda irin
kwarin gwiwa. da shawarwari da suka bani wajen wallafa wannan littafi da kuma
tarihai da suka bani da kuma sunayen da suka taimakamin wajen zakulowa.
Da farko dole ne
in mika cikakkiyar godiya ta ga babbar jikar Mal. Usman wato Hajiya Jummai
saboda irin tarihan da ta rinqa bani, da shawarwari da dama. Sannan ina mika
godiya ta ga mahaifina Alh. Zakari Muhd (Amasha) da mahaifiyata suma saboda
shawarwarin da suka bani.
Har ilayau ina
mika godiya ga mutanen kul-kul, Iyalan Baba Uba Musamman dansa Ibrahim, sannan
da mutancn Zariya kamar Baba Sani, Ladi, Shchu da sauransu, sannan godiya ta
musamman ga Baba Yalwa da Hassan da Husaini da Safiya da Haj. Karama, da Lami,
da kuma gabaxayan mutancn Fagge kamar su Ladidi, Zulaihat da Maimuna, da
sauransu. Kai dama wanda duk ya taimaka da farin-cikinsa ko shawararsa, da duk
abokaina da Malamaina da dalibaina da suka taimaka wajen fitowar wannan
Littafi.
Daga karshe ina
mika cikakkiyar godiya dayabo da jinjina ga Gwarzo na kuma Masani akan aikin sa
Abdulkadir Ali Ahmad Kabara wanda da cikakkiyar gudummawarsa da nuna qwarewarsa
ne wannan Littafi ya samu fitowa, dakuma Malamina Mai tarbiyata Wato Malam
Auwalu Isa Yakasai Da kuma Malam Maisunan Malan Allah ya saka musu da Alheri,
kuma Allah ya cika musu burinsu a duniya da Lahira.
Wassalamu Alaikum
Warahmatullah
Auwal Zakari
Muhammad Ayagi
Al-Azmiyyah Ventures
No. 852 Kofar Kabuga,
Kano State.
Gabatarwa
Da sunan
Allah mai Rahma Mai jinkai, Ubangiji Mahaliccin Sammai da qassai, tsira da
Aminci su tabbata ga Annabinmu Annabin Rahma, shugabanmu Annabi Muhammadu (SAW)
Allalh ya qara tsiransa ga sahabbansa da Alayensa da masoyansu da mabiyansu har
zuwa ranar Al-qiyama, Innamal A'amalu Binniyati, wa'inn ma likulli Imri'in ma nawa
(Hadis Ash-sharif).
Bayan haka
acikin wannan dan taqaitacccn littafi wanda ya qunshi Tarihi da kasuwanci da
zuriyar Mal. Usman da na wallafa, nayi shine musamman don ganin na zaburar da
jama'a (musamman zuriyarsa) zuwa ga sada zumunci, musamman domin ganin yadda
jama'ar wannan zamani sukai sako-sako da zumunci, sai kaga dan'uwa da dan'uwa
sun hadu amma basu san ccwa su 'yan-uwa ba ne.
Kuma gashi
Allah da Manzon Allah (SAW) sun yi umarni da lalląi mu sada zumunci kuma mu guji
yanke shi. Kamar yadda Manzon Allah yace:- "MAI YANKE ZUMUNCI BAZAI SHIGA
ALJANNA BA"
Sannan yace:
- YANA DAGA MANYA-MANYAN FALALOLI KA SADAR DA ZUMUNCI GA WANDA YA YANKE
MAKA"
Har ila yau
ya kara da cewa:- "HAQIQA ARRAHIM (Wato zumunci) TSAGI NE DAGA SỤNAN ALLAH
ARRAHMAN (wato mai yawán Rahma) ALLAH YACE: WANDA YA SADA SHI (Zumunci) ZAN
SADASHI DA RAHAMA WANDA YA YANKE SHI (Zumunci) ZAN YANKE SHI DAGA RAHMA".
Har ilayau
dai yace:- "ABUBUWA HUDU ( SUNA DAGA TASKOKIN ALJANNA: -
1. SIRRINTA YIN SADAKA
2. BOYE MUSIBA
3. SADA ZUMUNCI
4. FADIN "LAHAULA WALA KUWATA ILLA BILLAHI'
Da sauran Hadisai da dama, kuma ya tabbata cikin Hadisin Annabi cewa:
"Kasan Allah kafin ka bauta masa" saboda haka wanda duka bai san
'yan-uwan sa ba, to bazai iya sada zumunci ba, don haka na himmatu wajen
wallafa wannan littafi da fatan Allah (SWT) ya sa wannan littafi ya zama sila
ko wata hanya ta sada zumunci, kuma ya zama izna ko jankunnc ga masu yanke
zumunci, su dawo ga sadashi, Allah (SWT) ya sakamu cikin masu sada zumunci kuma
ya sadamu da Rahamarsa, ya shiryar
da masu yake
zumunci su zama daga cikin masu sada zumunci don su sami Rahmar Ubangiji, Amin.
Auwal Zakari
Muhd Ayàgi
ABUBUWAN DA KE
CIKI
ABUBUWAN DA KE CIKI Shafi
Shafin Farko ………….…………………………..…1
Sadaukarwa……………………….……,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,2
Ta’aliqi……………………………………,,,,,,,,,,,…
3
Godoiya…………………………………,,,,,…,,…4
Abubuwan
da ke ciki……………………………,,…7
Gabatarwa…………………………………………,..8
Babi Na Farko:
Taqaitaccen Mal. Usman………………,,,,,,.…,….
10
Matansa……………………………………,………11
‘Ya’yansa……………………………………...,,….12
Jikokinsa,,,………,,,,,,,,…………………/….,,,,,,,..,14
‘Ya’yan Jikokinsa …………………..…,,,……,,…17
Tattava Kunnensa…,,………,,,,,,,,,…………….…
20
‘Yayan Tattava Kunnensa ……,,,,, ………….……27
Babi Na Biyu
Kammalawa……,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,29Fadakarwa………………………….,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,30
BABI NA FARKO
Kasuwanci A
Zamanin Da
Kano
ta Dabo Tumbin Giwa, Yaro koda me kazo an fika. Wannan shi ne kirarin da ke
yiwa Kano, saboda shahararta ta kowanne bangare musamman kasuwanci, don haka ne
ma ake cewa da Kano cibiyar kasuwanci wato (Center of Commance) kamar yadda
yake a rubuce a kowacce lambar mota ta Kanon. To duk wannan ya samo asaline tin
zamanin daya shuxe, lokacin da ba jiragc, ba motoci ba kekuna sai jakuna da
dawakai da Raquma sama da shekaru dubu da suka wuce.
Daga
cikin sana'o'in da Kano ta shahara da su a a zamanin da can, sun hada da Noma,
Saqa, qira, Fatauci, Kiwo, Gini da sauransu. To amma Noma da fatauci sune suka
fi shahara a wancan zamanin, don a da ance Kano ba abin da zai fara zuwa
zuciyarka, sai Dalar Gyada, Kano ta shahara sosai da wannan sana'a.
Haka
ma fatauci daxaxxiyar sana'ace ta mutanen Kano, Fatauci ya kasu daban-daban
akwai gajcren Fatauci, inda mutum zai tafi kusa da garinsu yayyo siyayya ya
dawo garinsu ya sayar, akwai kuma wanda zai tafi gari mai nisa, ya kwashe
watanni ko shekaru, wasu ma in suka tafi sun tafi Kenan, acan zasu yi aure su
hayayyafa, don hakane ma ba garin da zakaje ba ka ga Bahaushe ba, to wannan ya
samo asali ne ta hanyar Fatauci. Galibi fatauci ana yinsa ne ta hanyar Ayari a
karkashin jagoracin Madugu, dole ne ya zama shi Madugun yafi kowa shiri sabo da
hatsarin da ke cikin sana'ar kamar Yan-Fashi, Barayi, Almatsutsai Namun Daji da
suke kan hanyar. Har hausawa kan yi masa kirari da "Madugu Uban
Tafiya".
BABI NA BIYU
Taqaitaccen
Tarihin Mal. Usman
Malam
Usman wanda aka fi sani da Shehu, cikakken sunansa shine Shehu Usmanu dan
Hussaini Mutumin Garin Kumurya.
An
haife shi a wani garı mai suna Kumurya wanda a yanzu yake cikin karamar hukumar
Bunkure ta jihar Kano. Malam Usmanu ya taso cikin karatun Addinin Mlusulunci,
sannan kuma ya na sana'ar Noma (Kamar yadda ta shahara a wancan zamanin) Allah
ya daukaka Mal. Usman a wannan sana'ar ta Noma, inda ya mallaki nanya-manyan
gonaki, kuna yake noma su.
A
inda daga bisani ya fara sana'ar fatauci ta hanyar siyan kayayyaki ya tafi dasu
wadansu garuruwan ya sayar ya sayo wasu acan ya kai garinsu. Har daga baya sai
ya fara barin kasar Kano ya na wannan tafiye-tafiye ne ta hanyar Ayari na
Fatake, suna wannan Fataunci ne akan Jakuna, zasu dorawa Jakunan Kaya su kuma
su bisu a kasa, suna daukan watanni kafin su isa, da sunje sun siyar sai su
sayo wadanda akce bukata a wannan garin su tawo da su. Idan sun iso sukan yada
Zango a wani guri mai yawan ruwa da bishiyoyi, su tsaya su wanke jikinsu, su ba
Jakunansu ruwa suyi kiwo, su huta saboda gurin ya yi kama da can kudancin
kasarnan inda suke zuwa wato Kurmi, to in sun tsaya su na hutawa, sai Jama'a su
dinga zuwa suna sayan kayayyaki, abin ya na ci gaba, wasu ma anan kayansu suke
karewa sai su koma.
Ana
halin haka saí ya zama kamar Al-ada da Sun dawo sai su ce, mu tafi Kurmin Kano,
to da zarar sun zo sai Mal. Usman ya wuce gidan wani Abokinsa ya sauka da yake
a wata unguwa kusa da wannan Kurmin mai suna Mararraba, in ya siyar da kayansa
da wuri sai ya yi sauri yaje garinsu Kumurya ya dawo kafin ayari ya tashi.
Ana
cikin wannan hali sai wannan Abokin nasa ya bashi shawarar cewa kamata ya yi,
ya sa yi gida a nan kusa da Kurmin, shi ma, idan suka sauka, sai ya sauka a
gidansa, idan ayari ba zai tashi da wuri ba, sai yaje Kumurya garisu, in kuma
da wuri zasu tashi, shi ke nan sai ya koma, sai Mal. Usman yai na'am da wannan
shawarar kuma ya danka komai a hannun abokin na sa, akan ya nemo masa gida,
idan ya dawo sai ya bashi kudin (a lokacin ana lissafi da keso ne, ba Naira ba)
haka kuwa aka yi, yana dawowa, sai ya samu Abokin nasa ya sai mai gida akusa da
unguwarsu a wata unguwa mai suna Ungwar
Ayagi, suka je ya ga gida ya yi farin-ciki, da ya sai da kayansa ya kawo
kudin sa ya bashi, inda daga baya sai ya debo iyalansa ya dawo dasu gidansa. To
wamman shine dalilin zamansa a Unguwr Ayagi.
A
wani Labarin kuma cewa akayi, ya zo cikin Kano ne neman Ilimin Addini, bayan ya
Sauke Alkur’ani a can Kumurya, sai ya shigo Birni qarin neman Ilim, yana neman
Ilimin ne ya fara sana’ar Fatauchi, har ya sa aka nema masa gidan ya siya, ya
xebo iyalan sa suka dawo.
Haka
Mal. Usman ya cigaba da wannan sana'a har lokacin da girma ya zo masa, sai ya
dene Fatauci ya zauna a gidansa daya siya ya cigaba da kasuwanci a wannan waje,
wanda a yanzu akewa lakabi da kasuwar Kurmi har zuwa lokacin da Allah ya karbi
ransa, Allah, ya jikan sa da Rahamrsa Amin.
BABI NA UKU
ZURI’AR MAL.
USMAN
Kusan
wannan shine maqasudin rubuta wannan littafi, domin Allah ya albarkanci Mal.
Usman da zuriya masu yawa, ko da yake sai da haifi ‘ya’ya takwas suna rasuwa,
sai ta Taran ce Ayashe ta tsaya,. Don haka na kasa wannan kasha gida shida,
kamar yadda zai zo a qasa.
Kashi na Farko
Matansa
Mal. Usman ya rasu ya bar Mata Huxu kamar haka:
1.
Fadimatu
2.
Hassana
3.
Hassana (Iya Masa)
4.
Amina (Aisa)
Kashi
na Biyu
‘Ya’yansa
Mal. Usman
ya rasu yabar ‘ya’ya ne guda Bakwai a raye, amma kafin ya rasu ya binne wasu da
dama kamar yadda ita Hajiya Jummai ta tabbatar min, amma bakwai (7) sune
wadanda ya rasu ya bari a duniya.
‘Ya’yansa sune kamar haka:
1.
Aishatu Usman (Ayashe)
2.
Hauwa’u Usman (Inna ta Fagge)
3.
Muhammad Usman (Baba Mai Goro)
4.
Amina Usman (Inna Amina)
5.
Sulaiman Usman (Baba Mai Lemo)
6.
Idris Usman (Idi Dan Shehu)
7.
Furera Usman (Hajyan Anchau)
Wadannan sune ‘ya’yan Mal. Usman guda
bakwai, a inda daga cikin Mazan wasu sun gajeshi a sana’arsa ta fatauci.Kamar
Muhammad yayi Sana’ar fatauci a Ikko inda ya zauna acan har yayi aure ya haifi
wasu daga ‘ya’yansa a can, har sai da ya rike sarkin Hausawan acan iko ko
Shagamu.
Allah ya jiqansu
Ameen.
Kashi Na Uku
Jikokinsa
Yayan
Aishatu Usman (Ayashe)
1. Hauwa’u
(Hajiya Jummai)
2. Atine (Tarasu)
‘Ya’yan
Hauwa Usman (Inna ta Fagge)
2. Musa
(Ya Rasu)
‘Ya’yan
Amina Usman
1. Sa’idu
(Baba Na Kafi) Ya Rasu
2. Abubakar
(Uba na Kul-kul) Ya Rasu 9/12/2002
‘Ya’yan
Furaira Usman
1.
Abubakar (Garba
Kyauta)
‘Ya’yan
Sulaiman Usman (Mai Lemo)
1, Garba
(Uban Kano)
2.
Inuwa (Ya Rasu)
3.
Idris (Dan Zaria) ya Rasu
4.
Fatima (Jummai)
5.
Muhammadu Sani
‘Ya’yan
Muhammad Usman (Mai Goro)
1.
Zakariyya (Amasha)
2.
Sadiya (Asabe) Ta Rasu
‘Ya’yan
Idris Usman (Idi Dan Shehu)
1.
Aisha (Inna Yalwa)
2.
Saude (Ta Rasu)
3.
Hassan
4.
Hussaini
Wadannan sune
jikokin Mal. Usman Goma sha Bakwai (17), Goma (10) suke raye, Allah ya
gafartawa wadanda suka rasu Amin.
Kashi Na Hudu:
‘Ya’yan
Jikokinsa
Jikokin
Aishatu Usman (Ayashe)
Yayan Hauwa’u (Hajiya Jummai)
1. Zulaihat
(Yar Mallam) Ta rasu
2. Sadiya
(Hajiya Karama)
3. Sadiya
(Lami)
‘Ya’yan
Atine
Tarasu
kafin ta haihu
Jikokin
Hauwa’u Usman (inna ta fagge)
Yayan Musa (Baba na Fagge)
1.
Nasidi 7. Ruqayya
2.
Ishak (Alh. Maikudi) 8. Ibrahim
3.
Isa 9. Idris (Dantalata)
4.
Adamu 10. Usamatu
5.
Kadija (Gambo) 11.
Aliyu
6.
Fatima (Asabe) 12.
Abdulkadir
Jikokin
Amina Usman
‘Ya’yan Sa’idu (Baba Agwa)
1.
Auwalu (Lawan)
2.
Adamu
3.
Zulaiha
4.
Abubakar
‘Ya’yan
Abubakar (Uba Na Kul-Kul)
1.
Habiba 6.Binta
2.
Dauda 7.
Ibrahim
3.
Furera (Laraba) 8. Musa
4.
Aliyu 9. Amina
5.
Auwalu
Jikokin
Furaira Usman
‘Ya’yan Abubakar (Garba Kyauta)
1.
Furaira (Mammy)
2.
Sulaiman (Abba)
3.
Saliha (Ummi)
4.
Hadiza (Baby)
5.
Abdulmumin
6.
Hafsatu
* Yayan Abubakar Sune Yayan Jummai
*Suna Zaune a Banzazzau Kusa da Gidan
Kogi, Zaria Jihar Kaduna
Jikokin
Sulaiman Usman (Mai Lemo)
Yayan Inuwa Sulaiman Usman
1.
(Ladi) Tarasu 6. Maryam (Mama)
2.
Shehu 7. Tukur
3.
Umar 8. Adamu
4.
Tanimu 9. Musa
5.
Rukayya (Gaje) Hadiza
‘Ya’yan
Idris Sulaiman Usman
(Dan Zaria)
1.
Maryam
2.
Bashari
3.
Tukur
4.
Hauwa
Yayan
Jummai Sulaiman Usman
1.
Furaira (Mammy)
2.
Sulaiman (Abba)
3.
Saliha (Ummi)
4.
Hadiza (Baby)
5.
Abdulmumin
6.
Hafsatu
v
Yayan Jummai Sune Yayan
Abubakar
Jikokin
Muhammad Usman (Mai Goro)
Yayan Zakariyya Muhammad Usman
1.
Muhammad Auwal
2.
Muhammad Sani
3.
Muhd. Salisu
4.
Rukayya (Lami)
5.
Hauwa’u (Hajiya)
6.
Muhd. Rabi’u
7.
Saifullahi
8.
Abdulrashid
9.
Zakariyya (Halifa)
10.
Aliyu (Baffa)
Jikokin
Idris Usman (Idi Dan Shehu)
‘Ya’yan Saude Idris Usman
1.
Aishatu (Yar yaye) 5. Abdulrashid (Yarasu)
2.
Rabi’u 6.
Suwaiba (Ta Rasu)
3.
Misbahu 7.
Ummahani
4.
Asma’u 8.
Hauwa (Jummai)
‘Ya’yan
Hassan Idris Usman
1.
Idris (Halifa)
2.
Usman
‘Ya’yan Husaini Idris Usman (Yarasu)
1.
Aisha (Ummi)
2.
Muammadu
3.
Fatima
Wadannan
Sune Yayan Jikokin Mal. Usman,
wadanda suka rasu Allah ya gafarta musu Amin.
Kashi Na Biyar
Tattaba
Kunnensa
‘Ya’yan
Jikokin Aishatu Usamn (Ayashe)
Jikokin Hauwa’u (Haj. Jummai)
‘Ya’yan Zulai (Yar Mallam)
1.
Ibrahim
2.
Safiyya
Yayan Sadiya (Hajiya Karama)
1.
Jamila (Ta Rasu) 6. Abadiyya
2.
Yasin (Yarasu) 7. Ubayyu
3.
Kudsiyya 8.
Wasilu
4.
Mujibur-Rahman 9.
Saddiqa
5.
Mansulu
‘Ya’yan
Sadiya (Lami)
1.
Tijjani 6.Aisha
2.
Abubakar 7.
Kabiru
3.
Salamatu 8.
Aminu
4.
Fatima 9. Aminu
5.
Bilkisu
‘Ya’yan
Jikokin Hauwa Usman (Inna Ta Fagge)
Jikokin
Musa (Baba Na Fagge)
‘Ya’yan Nasidi
1.
Jamila (Tarasu)
2.
Maryam (Tarasu)
‘Ya’yan Ishak Musa (Alh. Maikudi Sarkin
Fata)
1.
Hauwa (Maituwo) Tarasu 12.
Ruqayya
2.
Binta (Ladidi) 13.
Hadiza
3.
Bashir 14. Muhd (Yaya)
4.
Hauwa (Maijidda) 15.
Ishaq (Alhaj)
5.
Aisha (Mai Riga) 16.
Ibrahim
6.
Babangida 17.
Amina
7.
Ahmad 18. Mahmud
8.
Habiba 19. Hauwa (Momy)
9.
Musa (Abba) 20.
Aisua
10.
Zulaihat 21.
Bulyaminu
11.
Abdul-Hamidu 22.
Nuraddin
‘Ya’yan
Isa Musa
1)
Hannatu 7.
Khalil
2)
Jamila 8.
Isa (Babannan)
3)
Aminu 9.
Fatima
4)
Musa (Abba) 10. Muhammad
5)
Ishak (Alhaji) 11.
Rabi
6)
Zainab 12.
Zakariyya
‘Ya’yan Adamu Musa
1.
Hauwa’u 4. Musa
2.
Aisha 5.
Muhammad
3.
Umar 6.
Abubakar
‘Ya’yan Khadija (Gambo) Musa
1.
Auwalu 4. Fatihu
2.
Ibrahim 5. Sulaiman
3.
Maryam 6. Aisha
‘Ya’yan Fatima (Asabe) Musa
1.
Maimuna 4. Faisal
2.
Rabi’u 5. Muhd Sani
3.
Aina’u 6. Umar
Ya’yan Rukayya Musa
1.
Kabiru 4. Idris
2.
Halima 5. Salmanu
3.
Aisha 6. Sukairaju
‘Ya’yan Ibrahim Musa
1.
Hafsiyya
2.
Abdullahi
3.
Furaira
4.
Usman
5.
Binta (Ummi)
‘Ya’yan
Jikokin Amina
Jikokin
Sa’idu (Baba Agwa)
Ya’yan Lawan Sa’idu
1.
Maryam
2.
Zubaida
3.
Zahara’u
Ya’yan Adamu Sa’idu
1.
Hamza
2.
Saidu (Abba)
3.
Furera (Balaraba)
‘Ya’yan Zulai Sa’idu
1.
Salisu
‘Ya’yan Abubakar Sa’idu
1.
Ibrahim (Halifa)
Jikokin Abubakar (Uba Na Kul-Kul)
Yayan Habiba Abubakar
1.
Saadiku 5. Hauwa’u (Ummi)
2.
Fatihu 6. Ibrahim
3.
Kamalu 7. Aba Yazid
4.
Alawiyya 8. Sadiya
‘Ya’yan Dauda Abubakar
1.
Abdulrahaman
2.
Mustafa
Yayan Furaira Abubakar (Laraba)
(09039151977)
1.
Zahara’u
2.
Yakuba
3.
Aminu
4.
Shamsuddin
5.
Mikidaru
6.
Marakisiyya
7.
Maryam
8.
Amina
Yayan Binta Abubakar
1.
Aminu
2.
Zainab (Ummi)
3.
Aisha (08104066354)
‘Ya’yan
Jikokin Sulaiman Usman
Jikokin
Inuwa Sulaiman Usman
‘Ya’yan Amina (Ladi) Inuwa Sulaiman Usman
1.
Amina
2.
Abubakar
3.
Sadiya
4.
Hauwa
5.
Muzakkir
‘Ya’yan Tukur (Alhaji) Inuwa Sulaiman
1.
Amina
2.
Abubakar (Halifa)
‘Ya’yan Adamu Inuwa Sulaiman
1.
Muhd. Inuwa (Alhaji)
‘Ya’yan Hadiza Inuwa Sulaiman Usman
1.
Samha (07032099857)
2.
Aminu
‘Ya’yan Rukayya (Gaje) Inuwa Sulaiman
1.
Sa’idu
2.
Sumayya
3.
Badamasi (Halifa)
‘Ya’yan Maryam Inuwa Sulaiman Usman
1.
Imran
2.
Asma’u
‘Ya’yan Jikokin Muhammad Usman
Jikokin Zakariyya Muhammad Usman
‘Ya’yan Rukayya Zakari Muhammad Usman
1.
Hafasat
2.
Sadiyya
‘Ya’yan Jikokin Idris Usman
Jikokin Saude Idris Usman
‘Ya’yan Aishatu (Yaryaye)
1.
Amina
2.
Zainab
‘Ya’yan Rabi’u
1.
Fiddausi
2.
Fatima (Momy)
3.
Habiba
‘Ya’yan Misbahu
1.
Rukayya
‘Ya’yan Asma’u
1.
Fatima (Ummi)
2.
Aisha
3.
Sa’adatu
4.
Khadija
‘Ya’yan Ummahani
1.
Abdulhamid
‘Ya’yan Hauwa (Jummai)
1.
Aisha (Tarasu)
Wadannan sune tattaba kunnensa.
KASHI NA SHIDA
‘YA’YAN
TATTABA KUNNENSA
Tataba Kunnen Aisha Usman
‘Ya’yan Jikokin Hauwa (Haj. Jummai)
Jikokin Zulai (Yar Malam)
‘Ya’yan Ibrahim
1.
Abubakar
2.
Abdulrahman
‘Ya’yan Safiya
1.
Hafsat 5.
Sahlat
2.
Aisha 6.
Umar
3.
Ramlatu 7.
Maimunatu
4.
Muhammad
Jikokin
Sadiya (Haj. Karama)
‘Ya’yan Kudsiyyah
1.
Amina
2.
Ahmad
3.
Muhammad
Jikokin
Sadiya (Lami)
‘Ya’yan Salamatu (Magajiya)
1.
Mariya
Tattaba
Kunnen Hauwa’u Usman
Yayan
Jikokin Musa na Fagge
Jikokin
Ishak (Alh. Maikudi)
‘Ya’yan Hauwa (Maituwo)
1.
Abubakar (Abba) 4. Shafa’atu
2.
Zahara’u 5.
Mubarak
3.
Maryam 6. Najib
‘Ya’yan Binta Ishak Musa (Ladidi)
1.
Maryam (Ummi)
2.
Idris
3.
Muhammad Sani
4.
Hasiya
5.
Hauwa (Mamy)
‘Ya’yan Bashir Ishak Musa
1.
Ishak (Khalifa)
2.
Salihu
3.
Muhammad Arab
‘Ya’yan Hauwa Ishak Musa (Maijidda)
1.
Khadija (Yariny)
2.
Ishak (Amir)
‘Ya’yan Aisha Ishak Musa (Meriga)
1.
Ahmad
2.
Muhammad
Jikokin
Isa Musa
‘Ya’yan Hannatu Isa Musa
1.
Bashir
‘Ya’yan Jamila Isa Musa
1.
Rumasa’u
2.
Rabi
Jikokin Rukayya Musa
‘Ya’yan Kabir
1.
Adamu
Tattaba Kunnen Amina
Yayan Jikokin Sa’idu
Jikokin Lawan
‘Ya’yan Maryam
1.
Rabi’a
‘Ya’yan Jikokin Abubakar (Uba)
Jikokin
Furere Abubakar
(Laraba)
‘Ya’yan Zahara’u
1.
Bilkisu
2.
Salisu
Wadannan sune Yayan Tattaba
Kunnensa
FADAKARWA
lna fadakar da sauran dangi cewa duk wanda
yaga wani gyara ko kuskuren arubuta suna ko ragi ko qari na wasu Sunayen., ko
yake da wani karin bayani da zai daxa kyautata littafin da ya sanar da ni cikin
gaggawa, in za'a buga na biyu sai a shigar da su.
Da fatan Abin da nayi Allah ya karba, ya
mika ladan ga shi Shehu Usman da ‘ya’yayensa da jikokinsa da suka rigamu gidan
gaskiya, muma in munzo cikawa, Allah ya sa mu cika da Imani, Amin. Abin da aka
yi na kuskure kuma Allah ya yafe mana, Amin.
KAMMALAWA
Alhamdulillahi, Alhamulillahi, Godya ta
tta ga Ubangijin da ya halicci hallita ya kuma daidaitata, snnan ya sanya mata
tsarin da zata tafi a kansa, kuma ya wajabta zumunci ya sanya lada mai dinbun yawa
ga wanda ya sadar da shi, Tsira da amini su qara tabbata ga fiyayycn halitta,
wanda ya tsamo mu daga duhun vata, zuwa hasken shiriya na Addinin Musulunci,
Annabi ma’abocin cikar kalama da sada zumunci, shugaban da yake cewa: ‘Wanda yake so Allah ya yalwata masa (a cikin
rayuwar sa), kuma a qara masa acikin arzikinsa, to yabi iyayen sa, kuma ya
sadar da zumunci' Sallallahu alaihi
wasallam, Manzo yayi gaskiya. Allah cikin salatin ka hada da iyalan gidan sa,
da sahabbansa baki daya.
Bayan
haka, ina mai daxa godewa Allah daya bani damar kammala wannan litafi dana fara
rubutawa Ranar 20-02-2001 zuwa yau
Albamis 01-08-2002.
ALHAMDULILLAH
Sai
Mun Haxu a Littafi Na Biyu
AUWAL
ZAKARI MUHD AYAGI
(2
JUMADA THANI 1423)
01-AUGUST
2002
No comments:
Post a Comment