HUJJOJIN
MAULUDI DAGA LITATTAFAN WAHABIYYA
Daga Muhammad Sani
Zakariyya, Kwamitin nazari da bincike na
Mu’assasatush-Shaikh Khamis Alkhairiyya K/Kabuga, Kano State Nigeria.
Godiya ga wanda ya zabi Annabi
Muhammadu ya zama Annabi lokacin Annabi Adamu yana tsakanin ruwa da yunbu.
Gaisuwa ga wanda bayyanarsa ta zama rahama ga talikai da ahlin gidansa da
sahabbansa da wadanda suka bi shi da kyawawan aiki.
Da yawa malamai suna fito da hujjoji
da suke nuna halarcin Maulidi domin kara karfafa gwiwar masoya Annabi (SAW)
bisa hidima da suke a wannan wata na Mauludi; Sai na ga ya dace na fito da
hujjojin yin mauludin daga cikin litattafan su masu inkarin Mauludin domin ya
zama hujja a kansu idan sun ce bata ne to malamansu ne suka fara; Idan kuwa sun
ce bidi’a ne to ya ya suke da shaihunansu?
Bari mu fara da babban shehun na su wanda shi
ne abin koyin su wato SHAIKUL ISLAM AHMAD IBN TAIMIYYA wanda ya rayu a karni na
shida zuwa na bakwai, ku ga abin da yake cewa akan Mauludi.
“Haka abin
da sashen mutane suka farar da shi don koyi da kirista a haihuwar Annabi isa AS
ko kuma domin kauna ga Annabi (SAW) da girmamashi. Hakika, Ubrangiji zai ba su
lada a bisa wannan soyayyar da kuma ijtihadin da suka yi, ba a bisa bidi’ar da
suka yi ba ta rikar mauludin Annabi (SAW) kamar idi tare da cewa malamai sun
sami sabani bisa mauludi”.
IBN
TAIMIYYA YANA YABON MASU MAULUDI DA KYAKKYAWAR MANUFA
Hakika dai Shehul Islam Ibn Taimiyya ya ci gaba da
yabon masu Mauludi da tabbatar musu da lada mai girma da kuma kawo hujja da
cewa mauludin bidi’a ce mai kyau ga Mazhabin Imamu Ahmad ga dai abin da yake
cewa:
“Lallai
girmama Mauludi da rikonsa ya zama wani taro. Hakika a cikin mutane akwai masu
yin hakan, lada mai girma kuma ya kasance a tare da su, saboda me? Saboda
kyakkyawar manufarsu da kuma girmamawarsu ga Annabin Allah (SAW).
Malamin ya
ci gaba da cewa:
Kamar yadd
aya ce a baya wani abun ya na zama mai kyau ga sashen mutane wanda zai iya zama
mummuna ga munin mai taka-tsantsan, saboda haka aka ce da Imamu Ahmad don
Hambali menene hukumcin wani shugaba da ya fitar da kudi dinare dubu domin buga
Alkur’ani? Sai ya ce ku kyale shi wannan abin da ya yi shi ya fi a cikin abin
da ake ciyarwa na dinare. Tare da cewa makaruhi ne a Mazahabar shi Imamu Ahmad
din kawata alkur’ani.
To ‘yan uwa
wannan fa shi ne babban shehin wanda
daga gareshi ne dukkan akidar wahabiyya, salafiyya, sunniyya, izala ta fito
dubi inda da bakinsa yake fadar hujjar mauludi. Da sakamakon mai yinsa. (Don
Karin bayani dubi littafin Iktida’usiradal mustakin shafi na 312-317).
To, daga dai kin gaskiya sai bata, yakamata
masu makauniyyar biyayya su sake nazari su ji abin da malamansu suke fada ko sa
gane abin da iyayen gidansu na yanzu suke musu ‘yar burun-burun.
YADDA SHEIKH IBN KASIR YA FAHIMCI
MAULUDI
Shi ne
sheikh Abil fadal Alhafiz Ibn Kasir ya fadi ra’ayinsa ga Mauludi wanda azahiri
ma yana nuna halaccin yin mauludin kuma ya goyi bayan masu yinsa cikin
littafinsa ‘ALBIDAYA-WANNIHAYA’ mujalladi na bakwai shafi na dari da Ishirin da
uku (123) inda yake yabon Sarkin Muzaffar kan hidima da yake yi a watan
Mauludi.Ga dai abin da yake cewa:
Sarkin
muzaffar ya kasance yana yin Mauludi mai girma a cikin watan Rabiul
Awwal.Yana yin gagarumin taro, kuma ya
kasance mutum ne jarumi, mai Juriya, mai tunani adali, Allah ya jikansa yasa
Aljanna makomarsa.
Ibn kasir
ya ci gaba da cewa
Hakika
shehu Abdul Khadab Ibn Dahiyya ya wallafa littafi mujalladi a kan
Mauludi ya sa masa suna ATTANWIR FI MAULIDIL BASHIRIN NAZIR. Sai Sarki ya sa
aka ba shi dinare dubu saboda abin da ya yi.
IBN KASIR
YANA JINJINA WA SARKI MUSAFFAR SABODA CIYARWAR DA YAKE A RANAR MAULUDI
Ibn kasir ya yaba wa Sarki muzaffar
saboda irin ciyarwar da yake da hidima ga jama’a domin tunawa da ranar haihuwar
shugaban halitta (SAW) ga abin da Ibn Kasir yake cewa:
An rawaito
daga sashin wadanda suka halarci mauludin Sarki Muzaffar ya ce: Sarki Muzaffar
yana fito da nau’in abinci kamar farfesun naman kai sama da guda dubu biyar da
soyayyun kaji dubu goma da kabakin man shanu ko curi guda dubu goma kayan
taba-ka-lashe sama da dubu talatin, ya ce manyan malamai masana da sufaye suna
halartar mauludin tare da shi. Sarki Muzaffar ya kasance kowacce shekara yana
kashe dinare dubu dari uku domin hidima ga mauludi.
To duba ya kai dan uwa yadda Ibn
Kasir yake yabon wannan Sarki, wanda wannan Sarki shi ne Sirikin baban
mujahidin nan da ya kwato baitul Mukaddas wato SALAHUDDIN AL AYUBIY (RTA). Shi
kuwa Ibn kasir kowa ya san shi; Shi ne babban waziri kuma babban almajirin Ibn
Taimiyya, masoyinsa wanda ya karfafa akidarsa, to amma ga abin da yake cewa
game da Mauludin, kai hasali ma shi Ibn kasir ya yi littafi a kan mauludi mai
suna: MAULUDI RASULULLAHI (SAW) wanda har sashin ‘yan uwa suna karanta shi a
dararren mauludin domin ya yi shi ne a tsarin irin litattafan da ake karantawa
a dararen mauludi kamar Barzanji, Kamalul fatahi, Faidul Ahmad, Mauludul kabari
da sauransu. Ga ma abin da yake cewa a farkon littafin:
‘Bayan
haka, wannan ambaton wani abu ne daga ambaton Hadisai da kissoshi da suke da
dangantaka da haihuwar Annabi SAW) wanda aka cirosu da ingancinsu daga malaman
Hadisi masana kwararru. Abin da muke nufi a nan lallai daren haihuwar Annabi
(SAW) ya kasance dare ne mai girman daraja mai albarka da amfanarwa ga
muminai…”.
A cikin
mukaddamar wannan littafi ne malamin ya yi tahakkin littafin Sheikh Salahuddin
Almunjid wanda shi ma salafiyi ne yake cewa:
Abin lura
da rubuta wannan littafi da Ibn Kasir ya yi, cewa su mutanen Sham sun kasance
suna taron mauludi a masallacin Hambila a masallacin da Ibn Taimiyya yake
karatu. Saboda haka shi ladanin masallacin wanda shi malami ne kuma almajirin
Ibn Taimiyya ya nemi Ibn kasir ya rubuta masa littafi kan mauludi da za su rinka karantawa, sai
Ibn kasir ya rubuta musu wannan littafin.
Saboda
haka, wannan littafi da Ibn kasir ya yi yana nuna cewa ya yarda da halarcin
Mualudin baya ganin laifin yinsu. Inji fa shi Sheikh Salahuddin Almunjid
Assalafi.
To dan uwa
da kake takama da kai salafi ne kake haramta mauludi ga abin da malaman
malamanka suke fadi ga mauludi.
MALAMAN HADISI DA SUKA YI
LITATTAFAI A KAN MAULID
Masu musun
mauludin suna cewa wai salaf ba su yi ba. Wai su wane ne salaf din? ga malamai
masana Hadisi wadanda duniyar ilimi ta tabbatar da su sun yi litattafai a kan Mauludi misalinsu
sune:
1.
ALHAFIZ IBN NASIRIDDIN ADDIMASHKIY (777-842) ya
kasance yana girmama Ibn Taimiyya yana sonsa amma ya yi littafi a kan Mauludi mai suna:
JAMI’UL ASAR FI MAULUDI NABIYIL MUKHTAR Mujalladi uku da kuma ALLAFAZU RAIK FI
MAULIDI KHAIRUL KHALIK.
2.
ALHAFIZUL IRAKI 9725-808) mawallafin Alfiya ta hadisi
kuma babban Malami a fannin shi ma ya yi littafi a kan mauludi mai suna AL MAURIDUL HANA FIL
MAULIDIS-SANA.
3.
ALHAFIZ ASSHAUKANIY (831-902) shi ma ya yi littafi a kan mauludi kamar yadda
mai Kashifuz-zunin ya ambata.
4.
ALHAFIZ MULLA ALIYUL KHAIRI 91014) ya yi littafi a kan mauludi mai suna
ALMAURIDUR RAWI FI MAULUDIN-NABAWI
5.
AL HAFIZ IBN KASIR 9774) ma’abocin tafsir mai yawan
Ilimi kuma almajirin Ibn Taimiyya (Kamar yadda muka fada a baya) shi ma ya yi
littafi a kan
mauludi mai suna MAULIDI RASULULLAHI (SAW) tahakikin Salahuddin Almunjid.
Kadan kenan
daga malaman Sunna-salaf da suka yi littattafai a kan mauludi.
SHEIKH
USAIMIN DA MAULID
Shi ma
Sheikh Usaimin (Muhammad Ibn Dalha Al-usaimin) daya daga malaman Wahabiyya ne
na baya-baya kuma masu tsananin suka ga mauludi, Allah ya sa ya yi bayani kan mauludi. Haka kuwa
ya faru ne a tambayar da aka yi masa a kan
halarcin mauludi bayan ya haramta shi, sai kuma
ya yi subutar baki gaskiya ta fito. Ga abin da yake cewa:
“Babu
kokwanto cewa wadanda suke taron mauludin Annabi (SAW) suna yin haka ne domin
girmama Annabi (SAW) da kuma bayyana soyayyarsa da kuma karfafa himma domin
motsa ‘adifa’ (karsashi) na son Annabi (SAW) sababin wannan taro. To dukkan
wadannan abubuwa ibada ne domin son annabi (SAW) Ibada ne; kai bari ma Imani ba
ya cika sai mutum ya zamo yana son Annabi SAW fiye da kansa da ‘ya’yansa da
iyayensa da mutane baki daya, kuma shi ma girmama Annabi SAW Ibada ne, haka
kuma motsa adifa a kan Annabi (SAW) yana cikin addini saboda a cikinsa akwai
karantuwa izuwa bin shari’arsa (Saboda haka yin taro na mauludin Annabi (SAW)
domin neman kusanci izuwa ga Allah da kuma girmamawa ga Annabi (SAW) ibada ne.
to idan kuwa ya kasance ibada ne har abada ba ya halarta a kagi wani abu cikin
Addinin Allah da ba ya cikinsa (saboda wannan dalilai da ya kawo ya ce, wai
Mauludi bidi’a ce muharrama).
Dan uwa
dubi inda Allah ya sa ya rinka zubo hujjojin mauludi da kuma yaba wa mai yin
maulidi amma akarshe sai ya ce wai bidi’a ce. Allah ya shirye mu mai so karin
haske sai ya nemi wadannan litattafai:
1.
Ikitida’us siradil mustakin muhalifatu Ashabul jahin
(92-317).
2.
Fatawal Akida (382-384)
3.
Al biday wannihaya mujalladi na bakwai shaf 9123-124)
Allah ya sa
mu gane gaskiya gaskiya ce; ya sa mu yi aki da ita ya sa mu gane karya karya
ce, ya sa mugujeta.
Daga dan uwanku a musulmi
Muhammad
Sani Zakariyya
A madadin kwamitin Nazari da
Bincike na Mu’assasatush-Sheik
Khamis Alkhairiyyah
Kofar Kabuga, Kano, Nijeriya
Aslm malan dan allah kadaina wahalar da kanka akan abinda bayada amfani. Koda dukkanin malaman duniya suka goyi bayan maulidi idan har basuda hujja ta shari'a to wallahi aikin banzane idan kanaso mugane maulidi to kakawo aya ko hadisi kaitsaye akan maulidi to shikenan zamu yarda.
ReplyDelete