BAYANI A KAN SAKAMAKON MAI WASA DA SALAH
Daga Auwal Zakari Muhammad Ayagi GSM
07090987314, 07038775781,
Website: www.sautulazimiyyah.blogspot.com
Da sunan Allah mai yawan Rahama mai yawan jinkai, tsira da Aminci su
kara tabbata ga Shugaban Halitta, Annabin da Ubangijin Sa ya gayyace shi
fadarsa su ka gana, ya ba shi Salloli biyar, kuma ya umarce mu da mu rinka
aikatasu a kowacce rana, tare da kiyayesu ba tare da tauyesu ba balle a barsu
dungurumgun, sannan Ubangiji ya tanadi babban rabo ga mai kulawa da su kamar
yadda ya yi umarni, haka-zalika ya yi tanadin azaba ga wanda baya zuwa da su
kamar yadda ya yi umarni, tsiran Ubangiji ka hada da sahabbansa da suka bishi
da kyautatawa tare da kiyaye Sallah, da yinta a kan lokacinta cikin jam’i ba
tare da sun tauye ta da komai ba, da matayensa da yayayensa da dukkan wadanda
suka bishi da kyautatawa tare da kiyaye hukumce-hukumcen Sallah har zuwa ranar
Alkiyama.
Bayan
haka, da yardarm Allah zan gabatar da
Muhadara Maitaken: SAKAMAKON MAI WASA DA
SALAH da fatan Allah yayi mana jagoranci, yasa mu fadaka mukiyaye, abin da
akji na daidai daga Allah ne, na Kuskure kuwa daga gare nine, WAMA
FAUFIQI ILLA BILLAH, WALAHAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH.
SALLAH GINSHIKIN ADDINI
Ya yan
uwa Musulmi, mu sani cewa Sallah ita ce ginshikin Addini, duk wanda ya tsayar
da ita, tare da ba da hakkokinta, to hakika ya tsayar da addini, wanda kuwa ya
tauyeta, to ya tauye addini, domin yana daga manya-manyan musiba wulakantu
Sallah, da tauyeta da rashin yinta a cikin jam’i.
MAI TOZARTA SALLAH DA SANNU ZAI HADU DA AZABA
Ubangiji
mai girma da daukaka yana cewa cikin Littafi mai girma, a cikin Suratul Maryam
aya ta Hamsin da tara zuwa sittin (59- 60)
SAI
WADANSU YAN BAYA SUKA MAYE A BAYANSU SUKA TOZARTA SALLAH, KUMA SUKA BI
SHA’AWOWINSU, TO DA SANNU ZASU HADU DA AZABA, FACE WANDA YA TUBA, KUMA YA YI
IMANI, KUMA YA AIKATA AIKI NA KWARAI TO WADANNAN ZA SU SHIGA ALJANNA KUMA BA ZA
A ZALUNCESU DA KOMAI BA.
MENENE TOZARTAR SALLAH
Ibn
Abbas (RTA) ya ce, ba ana nufin tozarta sallah shi ne barin sallah baki daya ba,
a’a ana nufin jinkirtata daga lokacinta.
Sa’id
Ibn Musayyib Allah ya kara yarda a gareshi, shugaban tabi’ai ya ce, tozartar
sallah shi ne kin sallar azahar har lokacin sallar la’asar ya shiga, ko kin
sallar la’asar har lokcin sallar magariba ya shiga, ko kin sallar magariba har
lokacin sallar isha’i ya shiga, ko kin sallar isha’i har ketowar alfijir.
MASU SHAGALA DA GA SALLARSU ZA SU HADU DA
AZABA
Har
ila yau, Ubangiji mai girma da daukaka yana fada cikin wata ayar daban cewa:
"TSANANIN
AZABA YA TABBATA GA MASALLATA WADANDA SUKE MASU SHAGALA DAGA SALALRSU" (Ai masu gafala daga gareta masu wulakanta ta) suratul ma’un Aya ta
Hudu.
Sa’ad
Ibn Abi Wakkas (RTA) ya ce: na tambayi Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su
kara tabbata a gareshi, a kan wadanda suke masu shgala daga sallarsu, ya ce
shagala daga sallah shi ne jinkirta lokaci, ma’ana kin yin sallah a kan lokacin
har lokacin sallar gabe ya shiga.
An
kirasu masallata sai dai kuma ga shi suna wulakanta ta, tare da jinkirta ta
daga lokacin ta, Allah ya yi musu alkawarin ‘WAILU’ shi wailu wata
Tsananin Azaba ce, a wata fadar kuma an ce wani rami ne a cikin wutar Jahannama da za a saka dukkan
duwatsun duniya a cikin sa da sun narke saboda tsananin zafin da yake cikinsa.
To nan ne mazaunin masu wulakanta Sallah ko jinkirta ta daga barin lokacinta,
sai dai wanda ya tuba ya yi nadama a bisa aikinsa na baya.
DUKIYA DA ‘YA’YA SUKAN SA MUTUM YA ZAMA
HASARARRE
Ubangiji
mai girma da daukaka ya fada a cikin wata aya cewa:
“YA KU
WADANDA KUKA YI IMANI, KADA DUKIYOYINKU DA ‘YA’YANKU SU SHAGALTAR DA KU DAGA
AMBATON ALLAH, WANDA YA YI HAKA YA NA DAGA MASU HASARA (Suratul Munafikun aya ta 9).
Masu
fassara suka ce: Abin da ake nufi da ambaton Allah a cikin wannan ayar shi ne Salloli
biyar, duk wanda dukiyarsa da kasuwancinsa, ko tarin ‘ya’yansa suka shagaltar
da shi daga sallah, to ya zama hasararre, yana tare da masu hasara.
SALLAH ITA CE FARKON HISABI
Manzon
Allah Alaihis-salam ya fada cikin hadisin da Tirmizi ya rawaito cewa:
“FARKON
ABIN DA ZA A YI WA BAWA HISABI DA SHI A RANAR ALKIYAMA DAGA AYYUKANSA SHI NE
SALLAH, IDAN TA INGANTA, TO HAKIKA YA RABAUTA YA TSIRA, AMMA IN TA TAWAYA TO
HAKIKA YA TABE YA YI HASARA.
KIN SALLAH DA KIN CIYARWA KAN TSUNDIMA BAWA
WUTAR SAKAR
Ubangiji
ya fada cikin Suratul Mudassir aya ta 42-48, yana mai bayar da labarin ‘yan
wuta cewa:
“ME YA SHIGAR DA KU CIKIN SAKAR? SAI SUKA CE
‘BA MU KASANCE CIKIN MASU SALLAH BA, KUMA BA MU ZAMO CIKIN MASU CIYAR DA
MATALAUTA BA, KUMA MUN KASANCE MUNA KUTSAWA TARE DA MASU KUTSAWA, MUN KASANCE MUNA
KARYATA RANAR SAKAMAKO HAR GASKIYA (wato mutuwa) TA ZO MANA, SABODA HAKA, CETON
MAI CETON MASU CETO BA ZAI AMFANE SU BA!
BARIN SALLAH KAFIRCI NE
Manzon
Allah tsira da Aminci ya kara tabbata a gareshi ya ce: “ALKAWARIN DAKE TSAKANINMU DA
TAKANINSU SHI NE SALLAH, WANDA YA BARTA HAKIKA YA KAFURTA (Iman Ahmad
da wadansu). Ya zo a cikin Sahihu Buhari cewa, Manzon Allah, (SAW) ya ce: Wanda
sallar la’asar ta kuburce masa, hakika ayyukansa sun baci”.
Har
ila yau, Shugaba Alaihis salam ya ce: An umarceni in yaki mutane har sai sun
tabbatar babu abin bauta wa sai Allah, sannan su tsayar da sallah, su bayar da
zakka, idan har suka aikata haka, jininsu ya kubuta daga gareni, da dukiyoyinsu
sai da hakkinta (hakkinta shi ne wanda ya kashe shi ma a kashe shi, ko bazawari
matsinaci; ko wanda ya bar addini duk za a kashesu) sakamakon yana gun Ubangiji
(Buhari da Muslim).
MAI WASA DA SALLAH ZA A TASHE SHI TARE DA
FIR’AUNA
Manzon
Rahama Alaihissalam ya ce: “Wanda ya kiyaye sallah za ta zamo haske da kubuta a
gareshi ranar alkiyama, wanda baya kiyayeta kuwa ba za ta zamo haske ba agare
shi; ba za ta zamo kubuta agershi ba, Ranar Alikiyama zai zamo tare da Fir’auna
da Hamana da Ubayyid Dan Kha’ab. Ma’ana zai tashi ranar Alkiyama tare da wanda
aikinsa ya zamo makamancin ayyukansu, zai zamo kamar mai bin su ne.
Sashin
Malamai sun ce: Hakika za a tashi mai barin Sallah tare da mutanan Hudu, domin
cewa yana shagaltuwa ga barin sallar ne bisa dalilin tarin dukiyarsa, ko
mulkinsa ko bisa taimakawa mai mulki (Wazirci) ko kasuwancinsa. Wanda dukiyarsa ta shagaltar da shi da barin
sallah za a tasheshi tare da Karuna,
wanda kuwa mulkinsa ya shagaltar da
shi ga barin sallah,i za a tasheshi da Fir’auna.
Wanda wazircinsa ya shagaltar dashi
ga barin sallah, shi kuma za a tasheshi da Hamana,
amma wanda kasuwancinsa ya shagaltar
da shi har yake barin sallah, za a tashe shi da Ubayyi da khalaf, (Attajirin kafirinnan na maka).
Imam
Baihaki (RTA) ya rawaito cewa Umar Dan Khaddab (RTA) ya ce: “wani mutum ya zo
wajen shugaba Annabi Alaihis Salam ya ce: Ya rasululahi, wanne aiki ne mafi
soyuwa a wajen Allah a musulunci? Sai Manzon ya ce: SALLAH A KAN LOKACINTA, wanda ya bar sallah babu addini a gareshi,
sallah ginshikin addini ce”.
JINKIRTA SALLAH BABBAN LAIFI NE
Jinkirta
sallah ga barin lokacinta da gangan alhali mutum yana da ikon da zai yi ta a
lokacinta, kuma ba tare da wani Uziri ba, ko wani rangwame da aka yi masa na
jinkirta ta ko gabatar da ita ba, misali kamar matafiyi da makamantansu, babban
laifi ne wanda shirka ce kadai ta fishi. Domin Annabi Alaihis-salam y ace: ‘Wanda
ya hadu da Ubangiji yana mai tozarta Sallah, Allah ba zai karbi dukkan kyawawan
ayyukansaba” Ibn Jauzi (RTA) ya ce: “BABU WANI ZUNUBI Mafi girma bayan
shirka kamar jinkirta sallah ga barin lokacinta, da kashe mumini ba tare da
hakki ba”.
Sahabban
shugaba alaihis-salam sun kasance basa ganin wani abu da barinsa kafirci ne
kamar sallah. An tambayi Imam Aliyu (RTA) game da wata mace da bata yin sallah,
sai y ace: wanda baya sallah kafiri ne. shi kuma Ibn Mas’ud (RTA) ya ce: ‘wanda
baya sallah babu addine tare da shi”. Shi kuma Ibn Abbas (RTA) cewa yayi:
‘wanda ya bar Sallah daya da gangam zai hadu da Ubangiji yana mai fushi das hi,
Ibrahimul-Nakha’iyyu (RTA) ya ce: wanda ya bar sallah hakika ya kafirta.
FARKON TAMBAYA A KABIRI SALLAH
Aunu
dan Abdullah (RTA) ya ce: idan aka shgiar da bawa kabarinsa farkon abin da za a
tambaya shi shi ne sallah. Idan ta kyautata sai a duba sauran ayyukansa, amma
idan ba ta kyautata ba, ba za a duba sauran ayyukansa ba, don haka yana da kyau
mu zamo masu kyautata sallolinmu domin duk kyawun ayyukan mutum, in har ba ya
kyautata sallarsa, a lahira, ko kallon ayyukan ba za a yi ba, sallar dai ita ce
farkon abin duba in ta inganta to ya haye in kuwa bata inganta ba, duk kyawun
ayyukansa baza su amfane shi da komai ba.
Shugaba
Annabi (SAW) ya ce: Idan bawa ya yi sallah a farkon lokacinta za a hau da ita
sama tana haske, har sai ta isa ga al’arshi, sai ta yi ta nema wa mai ita
gafara har zuwa ranar Alkiyama,a tana mai fadi: Allah ya kiyaye ka kamar yadda
ka kiyayeni. Amma idan ya yi sallar ba a cikin lokacinta ba, za a hau da ita
sama tana mai duhu, idan taje ga al’arshi za’a cukur-kudeta a jefi fuskar mai
ita da sallar, tana mai cewa Allah ya tozartaka kamar yadda ka tozartani”.
MUTANE UKU ALLAH BA YA KARBAR SALLARSU
Mutane
uku Ubangiji ba ya karbar sallolinsu, kamar yadda Abu Dawud ya rawaito cikin
sunnaninsa daga Abdullahi dan Amru dan Asin (RTA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya
ce: ‘uku Allah ba ya karbar sallolinsu
Ya zo
daga gare shi har ila yau ya ce: ‘wanda ya hada tsakanin salloli biyu ba tare
da wani uziri ba, to Hakika ya zo da wata kofa mai girma daga kofofin
manya-manyan laifuka.
Allah
ya gafarta mana ya shiryemu, domin ya zama wajibi a garemu mu tsaya mu yi duba
cikin yadda muke salloli domin mu kawo gyara cikin gaggawa kafin lokaci ya kure
mana. Allah ya sa mu dace.
YAUSHE ZA A UMARCI KANANAN YARA YIN SALLAH
Abu
Dawud ya rawaito Hadisi cikin Sunan cewa Manzon Allah (SAW) ya ce: ‘KU UMARCI
YARA DA YIN SALLAH IDAN SUKA ISA SHEKARA BAKWAI; IDAN SUKA KAI SHEKARA GOMA KU
DAKESU A KANTA’.
Umarni da yin Sallah a shekara bakwai shi zai sa su kiyayeta tare lura
da lokutanta, tare da sanin girman Sallar tun suna kanana; amma sai Ma’aiki ya
ce, idan sun kai shekara goma za a dokesu idan suka ki yin Sallar. Ya zo cikin
wata ruwayar cewa: Ku UMARCI ‘YA’YANKU DA YIN SALLAH TUN SUNA SHEKARA BAKWAI,
KU DOKESU A KANTA IN SUN KAI SHEKARA GOMA, KU KUMA RABA TSAKANINSU A WAJEN
KWANCIYA’. Raba wajen kwanciya shi ne kada yaro namiji ya kwanta tare da ‘yar
uwarsa mace a kan shinfida daya, idan suka kusanci balaga.
Imam Abu Sulaiman Haddabi (RTA) ya
ce: wannan Hadisi yana shiryatarwa a kan tsanantawa a gare shi, idan ya balaga,
idan har ya bar Sallar.
Sashin Abokan Imamu shafi’i Allah ya
kara yarda a garesu sun kasance suna ganin za a kashe wanda ya bar Sallah da
gangan in har ya balaga, amma idan bai kai lokacin balaga ba ya cancanci duka,
wannan yana shiyatarwa kan cewa za a umarci kananan yara da Sallah lokacin da
suka kai shekara bakwai. In kuma suka kai goma za a dokesu in suka ki yin
Sallah.
SABANIN MALAMAI KAN
HUKUMCIN MAI BARIN SALLAH
Malamai
sun yi sabani kan hukumcin mai barin Sallah. Imam Malik da Imam Shafi’I da Imam
Ahmad sun ce, za a zare ran mai barin Sallah da takobi, sannan sai suka yi
sabani a kan kafircinsa idan har ya bar Sallar ne ba tare da uziri ba har
lokacinta ya fita. Malam Ibrahimal Naha’iyyu da Malam Ayyubal Sahatinayi da
Malam Abdullah Dan Mubarak da Iman Ahmad Dan Hambali da Imam Ishak da Dan
Rahawayah sun ce: shi kafiri ne, suna masu kafa hujja da fadin Manzo
Alaihis-salam cewa: Alkawarin dake tsakaninmu da su (kafirai) Sallah, wanda ya
barta hakika ya kafirta, da fadin Alaihis-salam cewa: ‘Tsakanin Mutum da
kafirci barin Sallah”.
MAI
KIYAYE SALLAH UBANGIJI ZAI GIRMAMA SHI DA KARAMOMI GUDA BIYAR
Hakika
an rawaito a cikin Hadisi: ‘cewa wanda ya kiyaye Salloli ababen Rubutawa,
Ubangiji zai girmama shi da karamomi biyar:
1.
Za a dauke masa kuncin
rayuwa
2.
Za a dauke masa Azabar
Kabari
3.
Za a ba shi littafinsa a
hannun dama
4.
Zai shude siradi kamar
walkiya mai bicewa
5.
Zai shiga Aljanna ba tare
da Hisabi ba.
MAI
WASA DA SALLAH ZAI HADU DA UKUBOBI GOMA SHA HUDU
Amma
shi kuma mai wasa da Sallah zai hadu da ukubobi har goma sha hudu, ukubobi
biyar a duniya, uku a lokacin mutawa, uku a cikin kabari, uku lokacin da zai
fita daga kabari. Amma Ukubobin da zai hadu da su tun a Duniya
1.
Za a cire albarka a cikin
Rayuwarsa
2.
Za a shafe kamannin
Salihai daga fuskarsa
3.
Duk aikin da zai aikata
ba za a ba shi lada ba
4.
Addu’arsa ba zata daukaku
ba (ma’ana ba za a karbi addu’arsa ba)
5.
Ba shi da rabo a cikin
addu’o’in bayi nagari
Ukubobin
da za su same shi a lokacin mutuwarsa sune:
6.
Zai mutu wulakantacce
(wanda azaba da fitinar kabari suke jiransa)
7.
Zai mutu yana mai jin
yunwa,
8.
Zai mutu yana mai jin kishirwa koda za a
shayar da shi da kogunan Duniya ba za su raba shi da kishirwa ba
Ukubobin
da za su same shi a cikin kabarinsa sune:
9.
Za a kuntata kabarinsa
har sai hakarkaninsa sun saba wa juna
10.
Za a kunna wuta
akabarinsa yana jujjuyawa a kan garwashin wutar safe da dare
11.
Za a sanya macijiya a
cikin kabarinsa, mai suna Shuja’ul Akara’u.
Shuja’ul Akara’u: Idanunta na wuta ne, faratanta na bakin karfe, tsawon kowanne farce
kwatankwacin tsawon tafiyar kwana daya, za ta yi magana da mataccen tana cewa
ni ce Shuja’ul Akara’u, muryarta kamar tsawa, ta ce da shi: Ubangijina ya
umarce ni da in dokeka bisa ga tozarta Sallar Asuba da ka yi har rana ta fito,
in dokeka bisa ga tozarta Sallar Azahar da ka yi har lokacin La’asar ya shiga,
in dokeka bisa ga tozarta Sallar La’asar da ka yi har Sallar Magariba ta shiga.
Har ila yau, in dokeka bisa ga tozartar Sallar Magariba da ka yi har lokacin Sallar
Isha’i ya shiga, in kuma doke ka bisa ga tozartar Sallar Isha’i da ka yi har
lokacin Sallar Asubahi ta shiga, duk lokaciin da ta doke shi zai nitse a kasa
tsawon zira’i saba’in, ba zai gushe ba a cikin kasa ana mai yi masa azaba har
zuwa ranar Alkiyama.
Amma
musibu ukun da za su same shi a lokacin fitarsa daga kabarinsa sune
12.
Za a tsananta bincike a
gare shi
13.
Zai hadu da fushin
Ubangiji
14.
Zai shiga wuta
A wata
ruwayar ya zo cewa: zai zo ranar Alkiyama a fuskarsa an yi rubutu layi uku,
layi na farko an rubuta ya mai tozarta hakkin Ubangiji, layi na biyu kuma an
rubuta, ya wanda ya kebanta da fushin Ubangiji, a layi na uku kuma an rubuta
kamar yadda ka tozarta hakki Allah a Duniya a yau ka fita daga rahamar
Ubangiji.
An
rawaito daga Ibn Abbas Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: ranar Alkiyama za
a zo da wani mutum a tsayar da shi gaban Ubangiji, sai yace: a kaishi wuta, sai
ya ce ya Ubangiji saboda me? Sai Ubangiji yace: Saboda Jinkirta Sallah da kake
yi ga barin lokacinta, kuma ka hadu da ni kana makaryaci.
WANE NE SHAKIYYI ABIN HARAMTAWA?
Daga
Shugaba Annabi Alaihis-Salam, wata rana yace da Sahabbansa ‘Ya Ubangiji kada ka
bar Shakiyyi ko abin Haramtawa a cikinmu, sannan ya ce: shin kun san wane ne Shakiyyi
abin Haramtawa? Sai sukace wane ne ya Ma’aikin Allah, sai ya ce: MAI BARIN
SALLAH”
An
rawaito cewa farkon wanda a ranar Alkiyama za a fara bakanta fuskarsa shi ne
mai barin Sallah. A cikin wutar Jahannama da akwai wani kogo mai suna Mulkimu, cikinsa akwai macizai, kowacce
macijiya kaurinta ya yi girman wuyan rakumi, tsawonta kwatankwacin tafiyar
shekara, zata sari mai barin Sallah, dafinta zai rika yawo a cikin jikinsa har
shekaru saba’in, sannan namansa ya zagwanye.
BARIN
SALLAH SHI NE MAFI SHARRI FIYE DA ZINA DA KISAN KAI
Barin
Sallah shi ne laifi mafi girman sharri fiye da zina da kisan kai, kamar yadda
ya zo cikin wata Hikaya, cewa wata mata daga bani Isra’ila ta je wajen Annabi
Musa Alaihis-salam, sai ta ce da shi, ya Ma’aikin Allah ni na aikata laifi mai
girman gaske, ina mai tuba ga Allah, ina rokonka da ka rokamin Ubangiji da ya
gafartamin laifin da na yi ya karfi tubana, sai Annabi Musa ya ce da ita, wane
laifi kika aikata? Sai ta ce ya Annabin Allah Hakika ni na yi zina har na
haihu, da na haihu sai na kashe jaririn, sai Annabi Musa ya ce da ita, maza ki
fita ya fajira kada wuta ta sauko daga sama ta konemu saboda wannan babban
laifi naki, sai ta fita daga gare shi tana mai karyayyar zuciya. Sai Mala’ika
Jibrilu ya sauka, yace Ya Musa: Ubangiji yace da kai me ya sa ka juyar da mai
tuba. Shin ka san mafi sharri daga laifinta? Sai Annabi Musa yace: Ya Jibrilu
shin wane ne mafi sharri daga gareta? Sai ya ce: MAI BARIN SALLAH DA GANGAN
MAI WULAKANTA
SALLAH DA SANNU ZAI HADU DA AZABA
Mai wulakanta Sallah da jinkirtata ga barin
lokacinta da sannu zai hadu da Azabar Ubangiji da zarar an sanya shi a kabari.
Kamar yadda ya zo cikin Hikayar wata mata da ta rasu, wani dan Uwanta ya
halarci binne ta, bai sani ba sai jakar kudinsa ta fada cikin kabarin, kuma
babu wanda ya lura har aka rufe kabarin, sai daga baya ya tuna, sai ya juya ya
koma wajen kabarin bayan kowa ya tafi, sai ya hake kabarin yana hake shi sai ya
ga kabarin yana ci da wuta, sai ya yi sauri ya mayar da kasar ya rufe ya komo
gida yana mai kuka ya ce da mahaifiyarsu a halin damuwa: ya uwarmu bani labari
game da yar’uwata, me take aikatawa a lokacin rayuwarta na barna, sai ta ce:
mene ne ya sa kake tambaya? Sai ya ce: Ya mahaifiyarmu na ga kabarinta yana ci
da wuta. Sai ta fashe da kuka tana mai cewa ya Dana ‘yar uwarka ta kasance tana
wulakanta Sallah, tana jinkirtata ga barin lokacinta.
Wannan shi ne halin mai jinkirta
Sallah ina kuma ga wanda ba ya yin Sallah kacokan? Muna rokan Allah ya
taimakemu, mu zama masu kiyaye Sallah a kan lokacinta.
SAKAMAKON MASU TAUYE SALLAH BA SA CIKA RUKU’U KO SUJJADA
Tauye Sallah, shi ne kin cika wani
aiki na Sallah kamar kin cika ruku’u, ko kin cika sujjada da sauransu. Hakika
ya zo cikin fassarar fadin Ubangiji Madaukakin Sarki cikin Suratul Ma’un aya ta
biyar, cewa:
‘Tsananin
Azaba ya tabbata ga masallata, wadanda suke masu shagala a Sallarsu” shagala a Sallah shi ne tauye Sallah wajen kin yin cikakken ruku’u da
cikakkiyar sujjada. Ita ce Sallar da a zamanance ake cewa ‘YAR FAKI’.
Ya zo
cikin Buhari da Muslim an rawaito daga Abi Huraira Allah ya kara yarda a gare shi,
cewa, wani mutum ya shiga masallaci, Manzon Allah yana zaune a ciki, sai
mutumin ya yi Sallah, sannan ya zo ya yi sallama ga Manzo SAW sai ya juyar da
sallama a gare shi, sannan ya ce da shi koma ka yi Sallah don cewa ba ka yi
Sallah ba, sai ya koma ya sake Sallah kamar ta baya ya sake zuwa ya yi sallama
ga Shugaba Alaihis’salam, ya amsa sallamar ya sake cewa koma ka yi Sallah ba ka
yi Sallah ba, ya sake komawa ya yi Sallah kamar ta baya, ya sake sallama ga
Shugaba, har ila yau ya sake cewa koma ka yi Sallah ba ka yi Sallah, har sau
uku, sai ya ce a ta ukun, Na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ya Ma’aikin
Allah, ba zan iya yin fiye da wannan ba, ka ilimantar da ni, sai Manzo ya ce:
‘idan ka tashi don yin Sallah ka yi kabbara, sannan ka karanta abin da ya
sauwaka daga Alkur’ani, sai ka yi ruku’u har sai ka nutsu kana mai ruku’u, sai
ka dago har sai ka daidaita a tsaye, sai ka yi sujjada har sai ka nutsu kana
mai sujjada, sannan ka zauna har sai ka nutsu kana zaune, sai ka yi sujjada har
sai ka nutsu kana mai sujjada ka aikata haka a cikin dukkan Sallarka”.
BA A KARBAR SALLAR WANDA BA YA CIKA RUKU’U KO SUJJADA
Imam
Ahmad Allah ya kara yarda a gare shi ya rawaito daga Badariy (RTA) ya ce: Manzo
Alaihis-Salam ya ce: Ba a karbar Sallah ga wanda a cikin ruku’u da sujjada
bayansa ba ya daidaituwa.
Abu
Dawud da Tirmizi sun rawaito har ila yau, ya ce: Wannan Hadisi ne kyakkyawa
ingantacce. Ya zo a wata ruwayar cewa: ‘Har sai bayansa ya daidaitu a cikin
ruku’u da sujjada’.
Wannan
nassi ne daga Shugaba Annabi Alaihis-salam cewa: wanda yake Sallah bayansa ba
ya daidaituwa a ruku’u da sujjada, Sallarsa batacciya ce, wannan cikin Sallar
farilla, hakan nan da nutsuwa shi ne sanya kowacce gaba a birgenta.
WANE NE BARAWON DA YAKE SATA A CIKIN SALLAH?
Ya
tabbata daga Annabi Alaihis-salam, ya ce: mafi tsananin mutane sata shi ne
wanda yake sata a cikin Sallarsa, sai aka ce, ta ya ya zai yi sata a cikin
Sallarsa? Sai ya ce: Wanda ba ya cika ruku’unta ko sujjadarta, ba ya karatu a
cikinta”.
Imam
Ahmad ya rawiato Hadisi daga Ahmad Ibn Hambali daga Hadisin Abi Huraira Allah
ya kara yarda a gare shi, cewa, Shugaba Alaihis-Salam ya ce: Ubangiji ba ya
duba izuwa mutumin da bayansa ba ya mikewa tsakanin ruku’u da sujjada (Ubangiji
ba Ya karbar Sallarsa).
ZA’A BUGI FUSKAR MAI TAUYE SALLAH DA SALLARSA
An
karbo daga Umar dan haddabi (RTA) cewa shugaba Alahis-salam, ya ce: ‘Babu wai
mai yin sallah face yana tare da mala’iku guda biyu daya a damansa daya a
hagunsa. Ida ya cika sallarsa, sai a daukakata zuwa ga Ubangiji madaukakin saki,
amma idan ya tauyeta bai aika ta ba sai a doki fuskara da ita.
Har
ila yau shi ma Imam Baihaki ya rawaito Hadisi da sanadinsa daga Ubadatu dan Samit,
cewa Annabi Shugaba Alaihis-Salam ya ce: wanda ya yi Alwala ya kayutata
alwalars,a sannan ya tashi domin ya yi sallah ya cika Ruku’un ta da sujjadar
ta, ya kyautata karatunta, wanan sallar za ta ce: Ubangiji ka kiyayeshi, kamar
yadda ka kiyayeni, sannan sai a daukakata zuwa sama tana mai haske da
kyalkyali, za’a bude mata kufofin sama, har sai ta isa ga ubangiji sannan ta
nemi ceton mai ita (wanda ya cika sallar). Amma idan bai cika ruku’unta ba, bai
cika sujjadar ta ba, kuma bai kyautata
karatun ta ba, sai Sallar ya ce: Ubajgiji ka tozartashi kamar yanda ya
tozartani, sannan a daukaka ta zuwa sama tana mai tsananin duhu, sai a kulle
kofafin sama sai a ninninketa kamar yadda ake nannade tufafi sai bugi fuskar
mai ita da ita (sallar).
MAI TAUYE SALLAH A ZABA NA JIRANSA
An
karbo daga Salmanal farisi Allah ya kara yarda a gareshi ya ce: Annabi shugaba
AlaihisSalam ya ce: Sallah tana da ma’aunai guda biyu, wanda ya cikata za’a
cika masu ma’uninsa, amma wanda ya tauye ta hakika munsan sa cewa Ubangiji ya
fada cikin Suratul mudaffifin ayata (2) cewa:
Tsananin
azaba ya tabbata ga masu tauyewa (masu tauye ma’auni, ko mudu, ko Sallah) Allah
ya tanadar musu (wailu) shi wani rami ne a cikin wutar jahannama, wanda ita
kanta jahannamar tana neman tsari da zafin sa, Allah ya kiyayemu.
ANA SUJJADU A KAN GABOBI GUDA BAKWAI
An
karbo daga Ibn Abbas Allah ya kare yarda agareshi, cewa: Annabi Shugaba
Alaihis-Salam yace: idan dayanku zai yi sujjada ya sanya fuskarsa, da hancinsa
da hannunsa a kasa, doin cewa Ubagiji ya yi wahayi gareni da inyi sujjada a kan
gabbai guda bakwai, goshi, da hanci, da tafika biyu da guyoyi guda biyu da
cikin duga-dugai biyu.
Wanda
ya yi Sallah ba tare da bawa kowacce gaba hakkinta ba, wannan gabar za tai ta
la’antarsa har ya idar da Sallar.
RASHIN CIKA SALLAH BABBAR HASARACI
Wanda
baya cika sallah ya zama mai babbar hasara, domin duk shekarun da ya yi yana
sallah ba ta karbuwa, kamar yadda buhari ya rawaito daga Huzaifatul yaman Allah
ya kara yarda Agareshi cewa yayi ga wani mutum yana sallah baya cika ruku’un Sallarsa,
baya cika sujjadrta, sai Huzaifa ya ce da shi. Baka sallah da za ka mutu kana
wannan Sallar daka mutu ba akan ta farkin Annabi (SAW) ba, a wata ruwayar kuma
ta Abi Dawud cewa ya yi; Tin yaushe kake wannan Sallar? Sai ya ce: tin tsawon
shekaru Arba’in, sai ya ce tsawon shekaru Arba’in dinnan baka yin sallah da
dai, da zaka mutu da ka mutu ba kan tafarkin Annabi Alaihis salam ba.
SALLAH ITAC E FARKON HISABI
Hasanun
basar ya kasance yana cewa: Ya kai Dan Adam shin wanne abune mafi girma a
gareka, da Addininka, idan ka walakanta sallarka, ai ita ce farkon abin da za’a
tambaya daga ayyukanka ranar Alkiyama. Kamar yadda ya gabata daga fadin Manzo
Alaihis Salam cew: farkon abin da za’a fara yiwa bawa Hisabi dashi a Ranar
Alkiyama daga ayyukansa Sallah, in ta kyautatu, ya tsira ya rabauta, in kuma ta
baci ya tabe yayi hasara.
Idan
wani abu ya tawaya daga farillan bawa, Sai Ubangiji yace idan yana da wani abu
daga nafil-fili a cike masa inda ya tauye na daga farillarsa, haka ma sauran
ayyukansa za’a yi masa, don haka ake son mutum ya yawaita nafil-fili.
WANDA BAYA YIN SALLAH TARE DA JAMA’A YANA CIKIN NARKO MAI TSANANI
A nan
zamu ji abin da Allah ya tanada ga wanda baya halartar Sallar jami’i alhali
yana da ikon da zai halarta. Ubangiji mai girma da daukaka yana cewa:
‘RANAR
DA ZA’A YAYE KWAURI, KUMA A KIRASU ZUWA GAYIN SUJJADA, BAZASU IYA YIBA. SU FITO
DA IDANU KASKANTATTU, WULAKANCI YANA RUFESU LALLAI NE ADA SUN KASNACE ANA KIRANSU
ZUWA YIN SUJJADA, ALHALI KUWA SUNA LAFIYA LAU (SUKA KI YI)
’Suratul Kalam Aya ta 42-43).
Ibrahimal
tainiyyu yace: Abin da ake nufi a wannan aya shi ne kiransu zuwa Sallolin
farilla ta kiran Sallah da ikama. Sa’id bn Musayyib shi kuma ya ce: Sun zamo
suna jin fadin ‘HAYYA ALAS-SALA HAYYA
ALAL FALAH’ wato ku yi gaggawa zuwa sallah, ku yi gaggawa zuwa babban rabo,
basa amsawa alhali suna lafiyyayyu.
Ka’abul
ahabar ya ce: wannan aya bata sauka ba face ga wadnada suke kin halartar Sallah
tare da jama’a, shin wane narko ne mafi tsanani fiye da kin yin Sallah tare da
jama’a alhali da haliin yin hakan?
Yazo
cikin Sahihun muslim, cewa wani makaho ya je wajen manzon Allah (saw) Yace: ya
ma’aikin Allah, bani da dan jagora da zai yi min jagoranci zuwa masallaci sai
ya roki Manzon Allah da ya yi masa rangwame don ya rika yin sallarsa a gida,
sai Manzon Allah ya yi masa, yayin da ya bada baya sai Manzon Allah ya kirashi
ya ce masa, shin kana jin kiran sallah sai ya ce Na’am yana ji, sai Manzon
Allah ya ce ka amsa kiran, wato ya rinka zuwa masallacin babu rangwame. Abu
Dawud ya rawaito daga Amru dan Ummul maktum cewa shi yaje wajen Manzon Allah
tsira da amince su tabbata a gareshi ya ce ya ma’aikin Allah cewa madina tana
da yawan halittun kasa masu cutarwa kamar macizai da kunamai da makamantansu,
ga kuma dabbobi masu cutarwa, ni kuma ina da matsalar ido (bana gani) gidana
kuma yana nesa daga Masallci shin za’a min rangwame inyi Sallah a gida? Sai Manzon
Allah SAW yace: Shin kana jin kiran sallah? Sia yace yana ji sai Manzon Allah
ya ce: ka amsa domin ba zan iya yi maka rangwame ba?
To
wannan fa makaho ne yayi kukan bashi da dan jagora zai wahala zuwa masallaci
don Sallar jam’i, amma duk da wannan bai samu rangwamen yin ya yi sallar a
cikin gidansa ba, to ina kuma ga wnada yake gani sarai, to a nan babu wani
uzuri a tare da shi da har zai hanashi halartar Masallaci don yin sallar jam’i,
a kan wannan ne aka tambayi Ibn Abbas Allah ya kara yarda a gareshi, Kan wanda
yake tsayuwar dare, amma baya Sallah a cikin jama’a, baya sallar Jam’i, sai
yace: in har ya mutu a wannan halin to
shi dan wutane.
Abu
Huriara Allah ya kara yarda a gareshi yace: a cika kunnuwan mutum da narkarkiyar
dalma shi ya fi sauki a gareshi da yaji kiran Sallah ya ki amsawa.
Yan’uwa
mu duba Azabar da za’a ji yayin da aka sami dalma harkakkiya aka dura a kunnen
mutum, amma duk wannan mai sauki ce a kan azabar da za’ayi wa wanda ya ke jin karan
sallah amma baya tashi ya tafi Masallci don amsa kiran Allah.
BAZA A KARBI UZURIN TSORO KO RAHIN LAFIYA BA
WAJEN ZUWA MASALLACI
Haka
zilaka wanda yake fakewa da tsaron ko rashin lafiya yaki zuwa masallaci don
sallar jam’i shi ma ubangiji bazai karbi sallar da yayi a gida ba. Kamar yadda
aka rawaita daga Ibn Abbas Allah ya kara yarda a gareshi yace: Manzon Allah
tsira da Aminci su kara tabbata a gareshi ya ce: Wanda ya ji kiran Sallah sai
wani uzuri ya hane shi da ya amsa kiran (ya ki ya tafi masallaci don Sallar
jam’in) sai aka ce ya Ma’aikin Allah wanne uzuri? Sai yace tsoro ko rashin
lafiya, baza a karbi sallar da ya yi a gida ba.
MUTANE UKU ALLAH YA LA’ANCESU
Hakim
ya fita da hadisi daga Ibn abbas Allah ya kara yarda a tare da shi ya ce Manzon
Allah tsira da aminci tabbata a gareshi ya ce mutane uku Allah ya la’nace su:
1.
Wanda ya jagoranci mutane
alhali basa kaunarsu.
2.
Macen da ta kwana mijinta
yana fushi da ita.
3.
Sai kuma mutumin da yaji
kiran sallah yaki amsa kiran, wato yaki tafiya inda ake kiran sallar donyin
slalar jam’i).
BABU SALLAH GA MAKWABCIN MASALLACI
Sayyadi
Aliyu Allah ya girmama fuskarsa yace: babu sallah ga makocin masallaci face a
cikin masallacin, sai akace masa wanene makocin masallaci sai ya ce wanda ya ke
jin kiran sallah.
Idan
makai duba da wadannan hadisai zamu fahinci cewa babu wani uzuri ga mutumin da
yake jiyo sautin mai kiran Sallah yana kira zuwa ga babban rabo, wato sallah,
sannan ya toge a kofar gida, ko a cikin gidansa ba tare da ya tafi masallaci ba,
abin da ake so shi ne da zarar mutum ya ji kiran Sallah tafiya zuwa masallaci.
Kamar
yadda Imam Rabi’u dan Haisam ya ke yi, domin shi mutum ne wanda barin jikinsa
daya ya shanye amma duk da haka sai ya dogara ya tafi zuwa Masallaci don samaun
Sallar jam’i, sai akace da shi, ya Aba Muhammad bisa ga irin lalurar da take
tare daka,i ai kai an maka rangwame ka iya yin sallar ka a gidanka sai yace:
wannan abin da kuke cewa ne, ammai ni tayaya zanji mai kiran Sallah yana cewa,
‘kutaho zuwa Sallah, ku taho zuwa ga babban rabo’. Ai duk wanda yake da ikon
amsa wannan kiran, to lallai ya aikata ko da kuwa dan jan cikine.
Wannan
shi ne halin manyan bayanin Allah in har zasu iya ko da a wanne hali suke, za
kage sun kokarta sun tafi masallaci sashin salaf suna cewa; Babu wani mutum da
Sallar Jam’I zata tsere masa face akwai zunibi da zai same shi.
Abdullahi
dan Umar ya ce: wata rana Amru (RTA) ya tafi gonarsa, yayin da ya dawo sai ya
tarar mutane sun idar da sallar la’asar, a nan take sai Amru ya ce: ‘INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR-RAJIUN’ yana
fadi, yana cewa yau Sallar la’asar ta kubuce min a cikin jam’i, saboda haka
jama’a ku shaida na bayar da gonar sadaka ga muskinai (mabukata don ina fatan
ta zamo kaffara ga abin da na aikata na rashin samun sallar la’asar a cikin
jam’i.
To
‘yan Uwa Musulmi Hakika ya zama wajibi a garemu mu zamo masu kaucewa kin
halartar sallar jam’i, ya zama tilas a garemu, mu lazimci Masallatai, domin
akwai dan karamin misali, mudubi yanda a lokacin Azumi muke cika Masallatai
babu masa ka tsinke, amma da zaran watan ya wuce sai masallatai su yi
sako-sako, an dai na zuwa, shin me yake jawo haka?
Lallai
ne mu koma ga Ubangiji mu tuba mazamo masu kiyayye dukkan hukumce-hukumcen Sallah.
KAMMALAWA
Alhamdulillah
godiya ta tabbata ga Ubangiji da ya bani ikon kawo karanshen wadannan bayannan
da suka shafi Mas’aloli da hukunce hukuncen wadanda suke wasa da Sallah, da
kuma wadanda basa yin sallah a Jam’i.
Ina
rokon Allah Mai girma da Daukaka dukkan abin da nayi na kuskure ya gafarta min,
abin da nayi na daidai ladan yasa a mazanin Sayyadina Rasululallah, marasa
lafiya na musulmi Allah ya basu lafiya, wadanda muka rasa daga iyaye da yan’uwa
da dukkan ak’ummar Musulmi allah ya gafarta musu, dukkan masu bukatu na alheri
Allah ya biya musu, Allah ya samu cikin ceton sayyadina rasululalhi ranan
Alkiyama. Amin.
‘AKULU
KAULI HAZA, WA ASTAGFIRULLAH UWA LAKUM WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI TA’ALA
WA BARAKATUHU