Sunday, 3 February 2013

BAYANI A KAN SAKAMAKON MAI WASA DA SALLAH

BAYANI A KAN SAKAMAKON MAI WASA DA SALAH
Daga Auwal Zakari Muhammad Ayagi GSM 07090987314, 07038775781,
Website: www.sautulazimiyyah.blogspot.com

Da sunan Allah mai yawan Rahama mai yawan jinkai, tsira da Aminci su kara tabbata ga Shugaban Halitta, Annabin da Ubangijin Sa ya gayyace shi fadarsa su ka gana, ya ba shi Salloli biyar, kuma ya umarce mu da mu rinka aikatasu a kowacce rana, tare da kiyayesu ba tare da tauyesu ba balle a barsu dungurumgun, sannan Ubangiji ya tanadi babban rabo ga mai kulawa da su kamar yadda ya yi umarni, haka-zalika ya yi tanadin azaba ga wanda baya zuwa da su kamar yadda ya yi umarni, tsiran Ubangiji ka hada da sahabbansa da suka bishi da kyautatawa tare da kiyaye Sallah, da yinta a kan lokacinta cikin jam’i ba tare da sun tauye ta da komai ba, da matayensa da yayayensa da dukkan wadanda suka bishi da kyautatawa tare da kiyaye hukumce-hukumcen Sallah har zuwa ranar Alkiyama.
Bayan haka, da yardarm Allah zan gabatar da Muhadara Maitaken: SAKAMAKON MAI WASA DA SALAH da fatan Allah yayi mana jagoranci, yasa mu fadaka mukiyaye, abin da akji na daidai daga Allah ne, na Kuskure kuwa daga gare nine, WAMA FAUFIQI ILLA BILLAH, WALAHAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH.

SALLAH GINSHIKIN ADDINI
Ya yan uwa Musulmi, mu sani cewa Sallah ita ce ginshikin Addini, duk wanda ya tsayar da ita, tare da ba da hakkokinta, to hakika ya tsayar da addini, wanda kuwa ya tauyeta, to ya tauye addini, domin yana daga manya-manyan musiba wulakantu Sallah, da tauyeta da rashin yinta a cikin jam’i.

MAI TOZARTA SALLAH DA SANNU ZAI HADU DA AZABA
Ubangiji mai girma da daukaka yana cewa cikin Littafi mai girma, a cikin Suratul Maryam aya ta Hamsin da tara zuwa sittin (59- 60)

SAI WADANSU YAN BAYA SUKA MAYE A BAYANSU SUKA TOZARTA SALLAH, KUMA SUKA BI SHA’AWOWINSU, TO DA SANNU ZASU HADU DA AZABA, FACE WANDA YA TUBA, KUMA YA YI IMANI, KUMA YA AIKATA AIKI NA KWARAI TO WADANNAN ZA SU SHIGA ALJANNA KUMA BA ZA A ZALUNCESU DA KOMAI BA.
MENENE TOZARTAR SALLAH
Ibn Abbas (RTA) ya ce, ba ana nufin tozarta sallah shi ne barin sallah baki daya ba, a’a ana nufin jinkirtata daga lokacinta.
Sa’id Ibn Musayyib Allah ya kara yarda a gareshi, shugaban tabi’ai ya ce, tozartar sallah shi ne kin sallar azahar har lokacin sallar la’asar ya shiga, ko kin sallar la’asar har lokcin sallar magariba ya shiga, ko kin sallar magariba har lokacin sallar isha’i ya shiga, ko kin sallar isha’i har ketowar  alfijir.
MASU SHAGALA DA GA SALLARSU ZA SU HADU DA AZABA
Har ila yau, Ubangiji mai girma da daukaka yana fada cikin wata ayar daban cewa:
"TSANANIN AZABA YA TABBATA GA MASALLATA WADANDA SUKE MASU SHAGALA DAGA SALALRSU" (Ai masu gafala daga gareta masu wulakanta ta) suratul ma’un Aya ta Hudu.
Sa’ad Ibn Abi Wakkas (RTA) ya ce: na tambayi Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi, a kan wadanda suke masu shgala daga sallarsu, ya ce shagala daga sallah shi ne jinkirta lokaci, ma’ana kin yin sallah a kan lokacin har lokacin sallar gabe ya shiga.
An kirasu masallata sai dai kuma ga shi suna wulakanta ta, tare da jinkirta ta daga lokacin ta, Allah ya yi musu alkawarin ‘WAILU’ shi wailu  wata Tsananin Azaba ce, a wata fadar kuma an ce wani rami ne a  cikin wutar Jahannama da za a saka dukkan duwatsun duniya a cikin sa da sun narke saboda tsananin zafin da yake cikinsa. To nan ne mazaunin masu wulakanta Sallah ko jinkirta ta daga barin lokacinta, sai dai wanda ya tuba ya yi nadama a bisa aikinsa na baya.

DUKIYA DA ‘YA’YA SUKAN SA MUTUM YA ZAMA HASARARRE
Ubangiji mai girma da daukaka ya fada a cikin wata aya cewa:
 “YA KU WADANDA KUKA YI IMANI, KADA DUKIYOYINKU DA ‘YA’YANKU SU SHAGALTAR DA KU DAGA AMBATON ALLAH, WANDA YA YI HAKA YA NA DAGA MASU HASARA (Suratul Munafikun aya ta 9).
Masu fassara suka ce: Abin da ake nufi da ambaton Allah a cikin wannan ayar shi ne Salloli biyar, duk wanda dukiyarsa da kasuwancinsa, ko tarin ‘ya’yansa suka shagaltar da shi daga sallah, to ya zama hasararre, yana tare da masu hasara.

SALLAH ITA CE FARKON HISABI
Manzon Allah Alaihis-salam ya fada cikin hadisin da Tirmizi ya rawaito cewa:
“FARKON ABIN DA ZA A YI WA BAWA HISABI DA SHI A RANAR ALKIYAMA DAGA AYYUKANSA SHI NE SALLAH, IDAN TA INGANTA, TO HAKIKA YA RABAUTA YA TSIRA, AMMA IN TA TAWAYA TO HAKIKA YA TABE YA YI HASARA.

KIN SALLAH DA KIN CIYARWA KAN TSUNDIMA BAWA WUTAR SAKAR
Ubangiji ya fada cikin Suratul Mudassir aya ta 42-48, yana mai bayar da labarin ‘yan wuta cewa:
“ME YA SHIGAR DA KU CIKIN SAKAR? SAI SUKA CE ‘BA MU KASANCE CIKIN MASU SALLAH BA, KUMA BA MU ZAMO CIKIN MASU CIYAR DA MATALAUTA BA, KUMA MUN KASANCE MUNA KUTSAWA TARE DA MASU KUTSAWA, MUN KASANCE MUNA KARYATA RANAR SAKAMAKO HAR GASKIYA (wato mutuwa) TA ZO MANA, SABODA HAKA, CETON MAI CETON MASU CETO BA ZAI AMFANE SU BA!

BARIN SALLAH KAFIRCI NE
Manzon Allah tsira da Aminci ya kara tabbata a gareshi ya ce: “ALKAWARIN DAKE TSAKANINMU DA TAKANINSU SHI NE SALLAH, WANDA YA BARTA HAKIKA YA KAFURTA (Iman Ahmad da wadansu). Ya zo a cikin Sahihu Buhari cewa, Manzon Allah, (SAW) ya ce: Wanda sallar la’asar ta kuburce masa, hakika ayyukansa sun baci”.
Har ila yau, Shugaba Alaihis salam ya ce: An umarceni in yaki mutane har sai sun tabbatar babu abin bauta wa sai Allah, sannan su tsayar da sallah, su bayar da zakka, idan har suka aikata haka, jininsu ya kubuta daga gareni, da dukiyoyinsu sai da hakkinta (hakkinta shi ne wanda ya kashe shi ma a kashe shi, ko bazawari matsinaci; ko wanda ya bar addini duk za a kashesu) sakamakon yana gun Ubangiji (Buhari da Muslim).

MAI WASA DA SALLAH ZA A TASHE SHI TARE DA FIR’AUNA
Manzon Rahama Alaihissalam ya ce: “Wanda ya kiyaye sallah za ta zamo haske da kubuta a gareshi ranar alkiyama, wanda baya kiyayeta kuwa ba za ta zamo haske ba agare shi; ba za ta zamo kubuta agershi ba, Ranar Alikiyama zai zamo tare da Fir’auna da Hamana da Ubayyid Dan Kha’ab. Ma’ana zai tashi ranar Alkiyama tare da wanda aikinsa ya zamo makamancin ayyukansu, zai zamo kamar mai bin su ne.
Sashin Malamai sun ce: Hakika za a tashi mai barin Sallah tare da mutanan Hudu, domin cewa yana shagaltuwa ga barin sallar ne bisa dalilin tarin dukiyarsa, ko mulkinsa ko bisa taimakawa mai mulki (Wazirci) ko kasuwancinsa. Wanda dukiyarsa ta shagaltar da shi da barin sallah za a tasheshi tare da Karuna, wanda kuwa mulkinsa ya shagaltar da shi ga barin sallah,i za a tasheshi da Fir’auna. Wanda wazircinsa ya shagaltar dashi ga barin sallah, shi kuma za a tasheshi da Hamana, amma wanda kasuwancinsa ya shagaltar da shi har yake barin sallah, za a tashe shi da Ubayyi da khalaf, (Attajirin kafirinnan na maka).
Imam Baihaki (RTA) ya rawaito cewa Umar Dan Khaddab (RTA) ya ce: “wani mutum ya zo wajen shugaba Annabi Alaihis Salam ya ce: Ya rasululahi, wanne aiki ne mafi soyuwa a wajen Allah a musulunci? Sai Manzon ya ce: SALLAH A KAN LOKACINTA, wanda ya bar sallah babu addini a gareshi, sallah ginshikin addini ce”.

JINKIRTA SALLAH BABBAN LAIFI NE
Jinkirta sallah ga barin lokacinta da gangan alhali mutum yana da ikon da zai yi ta a lokacinta, kuma ba tare da wani Uziri ba, ko wani rangwame da aka yi masa na jinkirta ta ko gabatar da ita ba, misali kamar matafiyi da makamantansu, babban laifi ne wanda shirka ce kadai ta fishi. Domin Annabi Alaihis-salam y ace: ‘Wanda ya hadu da Ubangiji yana mai tozarta Sallah, Allah ba zai karbi dukkan kyawawan ayyukansaba” Ibn Jauzi (RTA) ya ce: “BABU WANI ZUNUBI Mafi girma bayan shirka kamar jinkirta sallah ga barin lokacinta, da kashe mumini ba tare da hakki ba”.
Sahabban shugaba alaihis-salam sun kasance basa ganin wani abu da barinsa kafirci ne kamar sallah. An tambayi Imam Aliyu (RTA) game da wata mace da bata yin sallah, sai y ace: wanda baya sallah kafiri ne. shi kuma Ibn Mas’ud (RTA) ya ce: ‘wanda baya sallah babu addine tare da shi”. Shi kuma Ibn Abbas (RTA) cewa yayi: ‘wanda ya bar Sallah daya da gangam zai hadu da Ubangiji yana mai fushi das hi, Ibrahimul-Nakha’iyyu (RTA) ya ce: wanda ya bar sallah hakika ya kafirta.

FARKON TAMBAYA A KABIRI SALLAH
Aunu dan Abdullah (RTA) ya ce: idan aka shgiar da bawa kabarinsa farkon abin da za a tambaya shi shi ne sallah. Idan ta kyautata sai a duba sauran ayyukansa, amma idan ba ta kyautata ba, ba za a duba sauran ayyukansa ba, don haka yana da kyau mu zamo masu kyautata sallolinmu domin duk kyawun ayyukan mutum, in har ba ya kyautata sallarsa, a lahira, ko kallon ayyukan ba za a yi ba, sallar dai ita ce farkon abin duba in ta inganta to ya haye in kuwa bata inganta ba, duk kyawun ayyukansa baza su amfane shi da komai ba.
Shugaba Annabi (SAW) ya ce: Idan bawa ya yi sallah a farkon lokacinta za a hau da ita sama tana haske, har sai ta isa ga al’arshi, sai ta yi ta nema wa mai ita gafara har zuwa ranar Alkiyama,a tana mai fadi: Allah ya kiyaye ka kamar yadda ka kiyayeni. Amma idan ya yi sallar ba a cikin lokacinta ba, za a hau da ita sama tana mai duhu, idan taje ga al’arshi za’a cukur-kudeta a jefi fuskar mai ita da sallar, tana mai cewa Allah ya tozartaka kamar yadda ka tozartani”.

MUTANE UKU ALLAH BA YA KARBAR SALLARSU
Mutane uku Ubangiji ba ya karbar sallolinsu, kamar yadda Abu Dawud ya rawaito cikin sunnaninsa daga Abdullahi dan Amru dan Asin (RTA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: ‘uku Allah ba ya karbar sallolinsu
1.      Wanda ya jagoranci jama’a suna masu kinsa (kuma ba za su iya fada masa ba don tsoronsa)
2.      Wanda ya bautar da ‘yantacce   3.      Mutumin da yake sallah bayan lokacinta ya wuce;.
Ya zo daga gare shi har ila yau ya ce: ‘wanda ya hada tsakanin salloli biyu ba tare da wani uziri ba, to Hakika ya zo da wata kofa mai girma daga kofofin manya-manyan laifuka.
Allah ya gafarta mana ya shiryemu, domin ya zama wajibi a garemu mu tsaya mu yi duba cikin yadda muke salloli domin mu kawo gyara cikin gaggawa kafin lokaci ya kure mana. Allah ya sa mu dace.

YAUSHE ZA A UMARCI KANANAN YARA YIN SALLAH
Abu Dawud ya rawaito Hadisi cikin Sunan cewa Manzon Allah (SAW) ya ce: ‘KU UMARCI YARA DA YIN SALLAH IDAN SUKA ISA SHEKARA BAKWAI; IDAN SUKA KAI SHEKARA GOMA KU DAKESU A KANTA’.
Umarni da yin Sallah a shekara bakwai shi zai sa su kiyayeta tare lura da lokutanta, tare da sanin girman Sallar tun suna kanana; amma sai Ma’aiki ya ce, idan sun kai shekara goma za a dokesu idan suka ki yin Sallar. Ya zo cikin wata ruwayar cewa: Ku UMARCI ‘YA’YANKU DA YIN SALLAH TUN SUNA SHEKARA BAKWAI, KU DOKESU A KANTA IN SUN KAI SHEKARA GOMA, KU KUMA RABA TSAKANINSU A WAJEN KWANCIYA’. Raba wajen kwanciya shi ne kada yaro namiji ya kwanta tare da ‘yar uwarsa mace a kan shinfida daya, idan suka kusanci balaga.
Imam Abu Sulaiman Haddabi (RTA) ya ce: wannan Hadisi yana shiryatarwa a kan tsanantawa a gare shi, idan ya balaga, idan har ya bar Sallar.
Sashin Abokan Imamu shafi’i Allah ya kara yarda a garesu sun kasance suna ganin za a kashe wanda ya bar Sallah da gangan in har ya balaga, amma idan bai kai lokacin balaga ba ya cancanci duka, wannan yana shiyatarwa kan cewa za a umarci kananan yara da Sallah lokacin da suka kai shekara bakwai. In kuma suka kai goma za a dokesu in suka ki yin Sallah.

SABANIN MALAMAI KAN HUKUMCIN MAI BARIN SALLAH 

Malamai sun yi sabani kan hukumcin mai barin Sallah. Imam Malik da Imam Shafi’I da Imam Ahmad sun ce, za a zare ran mai barin Sallah da takobi, sannan sai suka yi sabani a kan kafircinsa idan har ya bar Sallar ne ba tare da uziri ba har lokacinta ya fita. Malam Ibrahimal Naha’iyyu da Malam Ayyubal Sahatinayi da Malam Abdullah Dan Mubarak da Iman Ahmad Dan Hambali da Imam Ishak da Dan Rahawayah sun ce: shi kafiri ne, suna masu kafa hujja da fadin Manzo Alaihis-salam cewa: Alkawarin dake tsakaninmu da su (kafirai) Sallah, wanda ya barta hakika ya kafirta, da fadin Alaihis-salam cewa: ‘Tsakanin Mutum da kafirci barin Sallah”.

MAI KIYAYE SALLAH UBANGIJI ZAI GIRMAMA SHI DA KARAMOMI GUDA BIYAR
Hakika an rawaito a cikin Hadisi: ‘cewa wanda ya kiyaye Salloli ababen Rubutawa, Ubangiji zai girmama shi da karamomi biyar:

1.                  Za a dauke masa kuncin rayuwa
2.                  Za a dauke masa Azabar Kabari
3.                  Za a ba shi littafinsa a hannun dama
4.                  Zai shude siradi kamar walkiya mai bicewa
5.                  Zai shiga Aljanna ba tare da Hisabi ba.


MAI WASA DA SALLAH ZAI HADU DA UKUBOBI GOMA SHA HUDU
Amma shi kuma mai wasa da Sallah zai hadu da ukubobi har goma sha hudu, ukubobi biyar a duniya, uku a lokacin mutawa, uku a cikin kabari, uku lokacin da zai fita daga kabari. Amma Ukubobin da zai hadu da su tun a Duniya
1.                  Za a cire albarka a cikin Rayuwarsa
2.                  Za a shafe kamannin Salihai daga fuskarsa
3.                  Duk aikin da zai aikata ba za a ba shi lada ba
4.                  Addu’arsa ba zata daukaku ba (ma’ana ba za a karbi addu’arsa ba)
5.                  Ba shi da rabo a cikin addu’o’in bayi nagari

Ukubobin da za su same shi a lokacin mutuwarsa sune:
6.                  Zai mutu wulakantacce (wanda azaba da fitinar kabari suke jiransa)
7.                  Zai mutu yana mai jin yunwa,
8.                   Zai mutu yana mai jin kishirwa koda za a shayar da shi da kogunan Duniya ba za su raba shi da kishirwa ba
Ukubobin da za su same shi a cikin kabarinsa sune:
9.                  Za a kuntata kabarinsa har sai hakarkaninsa sun saba wa juna
10.             Za a kunna wuta akabarinsa yana jujjuyawa a kan garwashin wutar safe da dare
11.             Za a sanya macijiya a cikin kabarinsa, mai suna Shuja’ul Akara’u.
Shuja’ul Akara’u: Idanunta na wuta ne, faratanta na bakin karfe, tsawon kowanne farce kwatankwacin tsawon tafiyar kwana daya, za ta yi magana da mataccen tana cewa ni ce Shuja’ul Akara’u, muryarta kamar tsawa, ta ce da shi: Ubangijina ya umarce ni da in dokeka bisa ga tozarta Sallar Asuba da ka yi har rana ta fito, in dokeka bisa ga tozarta Sallar Azahar da ka yi har lokacin La’asar ya shiga, in dokeka bisa ga tozarta Sallar La’asar da ka yi har Sallar Magariba ta shiga. Har ila yau, in dokeka bisa ga tozartar Sallar Magariba da ka yi har lokacin Sallar Isha’i ya shiga, in kuma doke ka bisa ga tozartar Sallar Isha’i da ka yi har lokacin Sallar Asubahi ta shiga, duk lokaciin da ta doke shi zai nitse a kasa tsawon zira’i saba’in, ba zai gushe ba a cikin kasa ana mai yi masa azaba har zuwa ranar Alkiyama.
Amma musibu ukun da za su same shi a lokacin fitarsa daga kabarinsa sune
12.             Za a tsananta bincike a gare shi
13.             Zai hadu da fushin Ubangiji
14.             Zai shiga wuta
A wata ruwayar ya zo cewa: zai zo ranar Alkiyama a fuskarsa an yi rubutu layi uku, layi na farko an rubuta ya mai tozarta hakkin Ubangiji, layi na biyu kuma an rubuta, ya wanda ya kebanta da fushin Ubangiji, a layi na uku kuma an rubuta kamar yadda ka tozarta hakki Allah a Duniya a yau ka fita daga rahamar Ubangiji.
An rawaito daga Ibn Abbas Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: ranar Alkiyama za a zo da wani mutum a tsayar da shi gaban Ubangiji, sai yace: a kaishi wuta, sai ya ce ya Ubangiji saboda me? Sai Ubangiji yace: Saboda Jinkirta Sallah da kake yi ga barin lokacinta, kuma ka hadu da ni kana makaryaci.

WANE NE SHAKIYYI ABIN HARAMTAWA?
Daga Shugaba Annabi Alaihis-Salam, wata rana yace da Sahabbansa ‘Ya Ubangiji kada ka bar Shakiyyi ko abin Haramtawa a cikinmu, sannan ya ce: shin kun san wane ne Shakiyyi abin Haramtawa? Sai sukace wane ne ya Ma’aikin Allah, sai ya ce: MAI BARIN SALLAH”
An rawaito cewa farkon wanda a ranar Alkiyama za a fara bakanta fuskarsa shi ne mai barin Sallah. A cikin wutar Jahannama da akwai wani kogo mai suna Mulkimu, cikinsa akwai macizai, kowacce macijiya kaurinta ya yi girman wuyan rakumi, tsawonta kwatankwacin tafiyar shekara, zata sari mai barin Sallah, dafinta zai rika yawo a cikin jikinsa har shekaru saba’in, sannan namansa ya zagwanye.

BARIN SALLAH SHI NE MAFI SHARRI FIYE DA ZINA DA KISAN KAI
Barin Sallah shi ne laifi mafi girman sharri fiye da zina da kisan kai, kamar yadda ya zo cikin wata Hikaya, cewa wata mata daga bani Isra’ila ta je wajen Annabi Musa Alaihis-salam, sai ta ce da shi, ya Ma’aikin Allah ni na aikata laifi mai girman gaske, ina mai tuba ga Allah, ina rokonka da ka rokamin Ubangiji da ya gafartamin laifin da na yi ya karfi tubana, sai Annabi Musa ya ce da ita, wane laifi kika aikata? Sai ta ce ya Annabin Allah Hakika ni na yi zina har na haihu, da na haihu sai na kashe jaririn, sai Annabi Musa ya ce da ita, maza ki fita ya fajira kada wuta ta sauko daga sama ta konemu saboda wannan babban laifi naki, sai ta fita daga gare shi tana mai karyayyar zuciya. Sai Mala’ika Jibrilu ya sauka, yace Ya Musa: Ubangiji yace da kai me ya sa ka juyar da mai tuba. Shin ka san mafi sharri daga laifinta? Sai Annabi Musa yace: Ya Jibrilu shin wane ne mafi sharri daga gareta? Sai ya ce: MAI BARIN SALLAH DA GANGAN

MAI WULAKANTA SALLAH DA SANNU ZAI HADU DA AZABA

 Mai wulakanta Sallah da jinkirtata ga barin lokacinta da sannu zai hadu da Azabar Ubangiji da zarar an sanya shi a kabari. Kamar yadda ya zo cikin Hikayar wata mata da ta rasu, wani dan Uwanta ya halarci binne ta, bai sani ba sai jakar kudinsa ta fada cikin kabarin, kuma babu wanda ya lura har aka rufe kabarin, sai daga baya ya tuna, sai ya juya ya koma wajen kabarin bayan kowa ya tafi, sai ya hake kabarin yana hake shi sai ya ga kabarin yana ci da wuta, sai ya yi sauri ya mayar da kasar ya rufe ya komo gida yana mai kuka ya ce da mahaifiyarsu a halin damuwa: ya uwarmu bani labari game da yar’uwata, me take aikatawa a lokacin rayuwarta na barna, sai ta ce: mene ne ya sa kake tambaya? Sai ya ce: Ya mahaifiyarmu na ga kabarinta yana ci da wuta. Sai ta fashe da kuka tana mai cewa ya Dana ‘yar uwarka ta kasance tana wulakanta Sallah, tana jinkirtata ga barin lokacinta.
            Wannan shi ne halin mai jinkirta Sallah ina kuma ga wanda ba ya yin Sallah kacokan? Muna rokan Allah ya taimakemu, mu zama masu kiyaye Sallah a kan lokacinta.

SAKAMAKON MASU TAUYE SALLAH BA SA CIKA RUKU’U KO SUJJADA
            Tauye Sallah, shi ne kin cika wani aiki na Sallah kamar kin cika ruku’u, ko kin cika sujjada da sauransu. Hakika ya zo cikin fassarar fadin Ubangiji Madaukakin Sarki cikin Suratul Ma’un aya ta biyar, cewa:
‘Tsananin Azaba ya tabbata ga masallata, wadanda suke masu shagala a Sallarsu” shagala a Sallah shi ne tauye Sallah wajen kin yin cikakken ruku’u da cikakkiyar sujjada. Ita ce Sallar da a zamanance ake cewa ‘YAR FAKI’.
Ya zo cikin Buhari da Muslim an rawaito daga Abi Huraira Allah ya kara yarda a gare shi, cewa, wani mutum ya shiga masallaci, Manzon Allah yana zaune a ciki, sai mutumin ya yi Sallah, sannan ya zo ya yi sallama ga Manzo SAW sai ya juyar da sallama a gare shi, sannan ya ce da shi koma ka yi Sallah don cewa ba ka yi Sallah ba, sai ya koma ya sake Sallah kamar ta baya ya sake zuwa ya yi sallama ga Shugaba Alaihis’salam, ya amsa sallamar ya sake cewa koma ka yi Sallah ba ka yi Sallah ba, ya sake komawa ya yi Sallah kamar ta baya, ya sake sallama ga Shugaba, har ila yau ya sake cewa koma ka yi Sallah ba ka yi Sallah, har sau uku, sai ya ce a ta ukun, Na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ya Ma’aikin Allah, ba zan iya yin fiye da wannan ba, ka ilimantar da ni, sai Manzo ya ce: ‘idan ka tashi don yin Sallah ka yi kabbara, sannan ka karanta abin da ya sauwaka daga Alkur’ani, sai ka yi ruku’u har sai ka nutsu kana mai ruku’u, sai ka dago har sai ka daidaita a tsaye, sai ka yi sujjada har sai ka nutsu kana mai sujjada, sannan ka zauna har sai ka nutsu kana zaune, sai ka yi sujjada har sai ka nutsu kana mai sujjada ka aikata haka a cikin dukkan Sallarka”.

BA A KARBAR SALLAR WANDA BA YA CIKA RUKU’U KO SUJJADA
Imam Ahmad Allah ya kara yarda a gare shi ya rawaito daga Badariy (RTA) ya ce: Manzo Alaihis-Salam ya ce: Ba a karbar Sallah ga wanda a cikin ruku’u da sujjada bayansa ba ya daidaituwa.
Abu Dawud da Tirmizi sun rawaito har ila yau, ya ce: Wannan Hadisi ne kyakkyawa ingantacce. Ya zo a wata ruwayar cewa: ‘Har sai bayansa ya daidaitu a cikin ruku’u da sujjada’.
Wannan nassi ne daga Shugaba Annabi Alaihis-salam cewa: wanda yake Sallah bayansa ba ya daidaituwa a ruku’u da sujjada, Sallarsa batacciya ce, wannan cikin Sallar farilla, hakan nan da nutsuwa shi ne sanya kowacce gaba a birgenta.

WANE NE BARAWON DA YAKE SATA A CIKIN SALLAH?
Ya tabbata daga Annabi Alaihis-salam, ya ce: mafi tsananin mutane sata shi ne wanda yake sata a cikin Sallarsa, sai aka ce, ta ya ya zai yi sata a cikin Sallarsa? Sai ya ce: Wanda ba ya cika ruku’unta ko sujjadarta, ba ya karatu a cikinta”.
Imam Ahmad ya rawiato Hadisi daga Ahmad Ibn Hambali daga Hadisin Abi Huraira Allah ya kara yarda a gare shi, cewa, Shugaba Alaihis-Salam ya ce: Ubangiji ba ya duba izuwa mutumin da bayansa ba ya mikewa tsakanin ruku’u da sujjada (Ubangiji ba Ya karbar Sallarsa).

ZA’A BUGI FUSKAR MAI TAUYE SALLAH DA SALLARSA
An karbo daga Umar dan haddabi (RTA) cewa shugaba Alahis-salam, ya ce: ‘Babu wai mai yin sallah face yana tare da mala’iku guda biyu daya a damansa daya a hagunsa. Ida ya cika sallarsa, sai a daukakata zuwa ga Ubangiji madaukakin saki, amma idan ya tauyeta bai aika ta ba sai a doki fuskara da ita.
Har ila yau shi ma Imam Baihaki ya rawaito Hadisi da sanadinsa daga Ubadatu dan Samit, cewa Annabi Shugaba Alaihis-Salam ya ce: wanda ya yi Alwala ya kayutata alwalars,a sannan ya tashi domin ya yi sallah ya cika Ruku’un ta da sujjadar ta, ya kyautata karatunta, wanan sallar za ta ce: Ubangiji ka kiyayeshi, kamar yadda ka kiyayeni, sannan sai a daukakata zuwa sama tana mai haske da kyalkyali, za’a bude mata kufofin sama, har sai ta isa ga ubangiji sannan ta nemi ceton mai ita (wanda ya cika sallar). Amma idan bai cika ruku’unta ba, bai cika sujjadar ta ba, kuma  bai kyautata karatun ta ba, sai Sallar ya ce: Ubajgiji ka tozartashi kamar yanda ya tozartani, sannan a daukaka ta zuwa sama tana mai tsananin duhu, sai a kulle kofafin sama sai a ninninketa kamar yadda ake nannade tufafi sai bugi fuskar mai ita da ita (sallar).
MAI TAUYE SALLAH A ZABA NA JIRANSA
An karbo daga Salmanal farisi Allah ya kara yarda a gareshi ya ce: Annabi shugaba AlaihisSalam ya ce: Sallah tana da ma’aunai guda biyu, wanda ya cikata za’a cika masu ma’uninsa, amma wanda ya tauye ta hakika munsan sa cewa Ubangiji ya fada cikin Suratul mudaffifin ayata (2) cewa:
Tsananin azaba ya tabbata ga masu tauyewa (masu tauye ma’auni, ko mudu, ko Sallah) Allah ya tanadar musu (wailu) shi wani rami ne a cikin wutar jahannama, wanda ita kanta jahannamar tana neman tsari da zafin sa, Allah ya kiyayemu.

ANA SUJJADU A KAN GABOBI GUDA BAKWAI
An karbo daga Ibn Abbas Allah ya kare yarda agareshi, cewa: Annabi Shugaba Alaihis-Salam yace: idan dayanku zai yi sujjada ya sanya fuskarsa, da hancinsa da hannunsa a kasa, doin cewa Ubagiji ya yi wahayi gareni da inyi sujjada a kan gabbai guda bakwai, goshi, da hanci, da tafika biyu da guyoyi guda biyu da cikin duga-dugai biyu.
Wanda ya yi Sallah ba tare da bawa kowacce gaba hakkinta ba, wannan gabar za tai ta la’antarsa har ya idar da Sallar.

RASHIN CIKA SALLAH BABBAR HASARACI
Wanda baya cika sallah ya zama mai babbar hasara, domin duk shekarun da ya yi yana sallah ba ta karbuwa, kamar yadda buhari ya rawaito daga Huzaifatul yaman Allah ya kara yarda Agareshi cewa yayi ga wani mutum yana sallah baya cika ruku’un Sallarsa, baya cika sujjadrta, sai Huzaifa ya ce da shi. Baka sallah da za ka mutu kana wannan Sallar daka mutu ba akan ta farkin Annabi (SAW) ba, a wata ruwayar kuma ta Abi Dawud cewa ya yi; Tin yaushe kake wannan Sallar? Sai ya ce: tin tsawon shekaru Arba’in, sai ya ce tsawon shekaru Arba’in dinnan baka yin sallah da dai, da zaka mutu da ka mutu ba kan tafarkin Annabi Alaihis salam ba.

SALLAH ITAC E FARKON HISABI
Hasanun basar ya kasance yana cewa: Ya kai Dan Adam shin wanne abune mafi girma a gareka, da Addininka, idan ka walakanta sallarka, ai ita ce farkon abin da za’a tambaya daga ayyukanka ranar Alkiyama. Kamar yadda ya gabata daga fadin Manzo Alaihis Salam cew: farkon abin da za’a fara yiwa bawa Hisabi dashi a Ranar Alkiyama daga ayyukansa Sallah, in ta kyautatu, ya tsira ya rabauta, in kuma ta baci ya tabe yayi hasara.
Idan wani abu ya tawaya daga farillan bawa, Sai Ubangiji yace idan yana da wani abu daga nafil-fili a cike masa inda ya tauye na daga farillarsa, haka ma sauran ayyukansa za’a yi masa, don haka ake son mutum ya yawaita nafil-fili.

WANDA BAYA YIN SALLAH TARE DA JAMA’A YANA CIKIN NARKO MAI TSANANI
A nan zamu ji abin da Allah ya tanada ga wanda baya halartar Sallar jami’i alhali yana da ikon da zai halarta. Ubangiji mai girma da daukaka yana cewa:


‘RANAR DA ZA’A YAYE KWAURI, KUMA A KIRASU ZUWA GAYIN SUJJADA, BAZASU IYA YIBA. SU FITO DA IDANU KASKANTATTU, WULAKANCI YANA RUFESU LALLAI NE ADA SUN KASNACE ANA KIRANSU ZUWA YIN SUJJADA, ALHALI KUWA SUNA LAFIYA LAU (SUKA KI YI)
Suratul Kalam Aya ta 42-43).
Ibrahimal tainiyyu yace: Abin da ake nufi a wannan aya shi ne kiransu zuwa Sallolin farilla ta kiran Sallah da ikama. Sa’id bn Musayyib shi kuma ya ce: Sun zamo suna jin fadin ‘HAYYA ALAS-SALA HAYYA ALAL FALAH’ wato ku yi gaggawa zuwa sallah, ku yi gaggawa zuwa babban rabo, basa amsawa alhali suna lafiyyayyu.
Ka’abul ahabar ya ce: wannan aya bata sauka ba face ga wadnada suke kin halartar Sallah tare da jama’a, shin wane narko ne mafi tsanani fiye da kin yin Sallah tare da jama’a alhali da haliin yin hakan?
Yazo cikin Sahihun muslim, cewa wani makaho ya je wajen manzon Allah (saw) Yace: ya ma’aikin Allah, bani da dan jagora da zai yi min jagoranci zuwa masallaci sai ya roki Manzon Allah da ya yi masa rangwame don ya rika yin sallarsa a gida, sai Manzon Allah ya yi masa, yayin da ya bada baya sai Manzon Allah ya kirashi ya ce masa, shin kana jin kiran sallah sai ya ce Na’am yana ji, sai Manzon Allah ya ce ka amsa kiran, wato ya rinka zuwa masallacin babu rangwame. Abu Dawud ya rawaito daga Amru dan Ummul maktum cewa shi yaje wajen Manzon Allah tsira da amince su tabbata a gareshi ya ce ya ma’aikin Allah cewa madina tana da yawan halittun kasa masu cutarwa kamar macizai da kunamai da makamantansu, ga kuma dabbobi masu cutarwa, ni kuma ina da matsalar ido (bana gani) gidana kuma yana nesa daga Masallci shin za’a min rangwame inyi Sallah a gida? Sai Manzon Allah SAW yace: Shin kana jin kiran sallah? Sia yace yana ji sai Manzon Allah ya ce: ka amsa domin ba zan iya yi maka rangwame ba?
To wannan fa makaho ne yayi kukan bashi da dan jagora zai wahala zuwa masallaci don Sallar jam’i, amma duk da wannan bai samu rangwamen yin ya yi sallar a cikin gidansa ba, to ina kuma ga wnada yake gani sarai, to a nan babu wani uzuri a tare da shi da har zai hanashi halartar Masallaci don yin sallar jam’i, a kan wannan ne aka tambayi Ibn Abbas Allah ya kara yarda a gareshi, Kan wanda yake tsayuwar dare, amma baya Sallah a cikin jama’a, baya sallar Jam’i, sai yace: in har  ya mutu a wannan halin to shi dan wutane.
Abu Huriara Allah ya kara yarda a gareshi yace: a cika kunnuwan mutum da narkarkiyar dalma shi ya fi sauki a gareshi da yaji kiran Sallah ya ki amsawa.
Yan’uwa mu duba Azabar da za’a ji yayin da aka sami dalma harkakkiya aka dura a kunnen mutum, amma duk wannan mai sauki ce a kan azabar da za’ayi wa wanda ya ke jin karan sallah amma baya tashi ya tafi Masallci don amsa kiran Allah.

BAZA A KARBI UZURIN TSORO KO RAHIN LAFIYA BA WAJEN ZUWA MASALLACI
Haka zilaka wanda yake fakewa da tsaron ko rashin lafiya yaki zuwa masallaci don sallar jam’i shi ma ubangiji bazai karbi sallar da yayi a gida ba. Kamar yadda aka rawaita daga Ibn Abbas Allah ya kara yarda a gareshi yace: Manzon Allah tsira da Aminci su kara tabbata a gareshi ya ce: Wanda ya ji kiran Sallah sai wani uzuri ya hane shi da ya amsa kiran (ya ki ya tafi masallaci don Sallar jam’in) sai aka ce ya Ma’aikin Allah wanne uzuri? Sai yace tsoro ko rashin lafiya, baza a karbi sallar da ya yi a gida ba.

MUTANE UKU ALLAH YA LA’ANCESU
Hakim ya fita da hadisi daga Ibn abbas Allah ya kara yarda a tare da shi ya ce Manzon Allah tsira da aminci tabbata a gareshi ya ce mutane uku Allah ya la’nace su:
1.      Wanda ya jagoranci mutane alhali basa kaunarsu.
2.      Macen da ta kwana mijinta yana fushi da ita.
3.      Sai kuma mutumin da yaji kiran sallah yaki amsa kiran, wato yaki tafiya inda ake kiran sallar donyin slalar jam’i).

BABU SALLAH GA MAKWABCIN MASALLACI
Sayyadi Aliyu Allah ya girmama fuskarsa yace: babu sallah ga makocin masallaci face a cikin masallacin, sai akace masa wanene makocin masallaci sai ya ce wanda ya ke jin kiran sallah.
Idan makai duba da wadannan hadisai zamu fahinci cewa babu wani uzuri ga mutumin da yake jiyo sautin mai kiran Sallah yana kira zuwa ga babban rabo, wato sallah, sannan ya toge a kofar gida, ko a cikin gidansa ba tare da ya tafi masallaci ba, abin da ake so shi ne da zarar mutum ya ji kiran Sallah tafiya zuwa masallaci.
Kamar yadda Imam Rabi’u dan Haisam ya ke yi, domin shi mutum ne wanda barin jikinsa daya ya shanye amma duk da haka sai ya dogara ya tafi zuwa Masallaci don samaun Sallar jam’i, sai akace da shi, ya Aba Muhammad bisa ga irin lalurar da take tare daka,i ai kai an maka rangwame ka iya yin sallar ka a gidanka sai yace: wannan abin da kuke cewa ne, ammai ni tayaya zanji mai kiran Sallah yana cewa, ‘kutaho zuwa Sallah, ku taho zuwa ga babban rabo’. Ai duk wanda yake da ikon amsa wannan kiran, to lallai ya aikata ko da kuwa dan jan cikine.
Wannan shi ne halin manyan bayanin Allah in har zasu iya ko da a wanne hali suke, za kage sun kokarta sun tafi masallaci sashin salaf suna cewa; Babu wani mutum da Sallar Jam’I zata tsere masa face akwai zunibi da zai same shi.
Abdullahi dan Umar ya ce: wata rana Amru (RTA) ya tafi gonarsa, yayin da ya dawo sai ya tarar mutane sun idar da sallar la’asar, a nan take sai Amru ya ce: ‘INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR-RAJIUN’ yana fadi, yana cewa yau Sallar la’asar ta kubuce min a cikin jam’i, saboda haka jama’a ku shaida na bayar da gonar sadaka ga muskinai (mabukata don ina fatan ta zamo kaffara ga abin da na aikata na rashin samun sallar la’asar a cikin jam’i.
To ‘yan Uwa Musulmi Hakika ya zama wajibi a garemu mu zamo masu kaucewa kin halartar sallar jam’i, ya zama tilas a garemu, mu lazimci Masallatai, domin akwai dan karamin misali, mudubi yanda a lokacin Azumi muke cika Masallatai babu masa ka tsinke, amma da zaran watan ya wuce sai masallatai su yi sako-sako, an dai na zuwa, shin me yake jawo haka?
Lallai ne mu koma ga Ubangiji mu tuba mazamo masu kiyayye dukkan hukumce-hukumcen Sallah.

KAMMALAWA
Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Ubangiji da ya bani ikon kawo karanshen wadannan bayannan da suka shafi Mas’aloli da hukunce hukuncen wadanda suke wasa da Sallah, da kuma wadanda basa yin sallah a Jam’i.
Ina rokon Allah Mai girma da Daukaka dukkan abin da nayi na kuskure ya gafarta min, abin da nayi na daidai ladan yasa a mazanin Sayyadina Rasululallah, marasa lafiya na musulmi Allah ya basu lafiya, wadanda muka rasa daga iyaye da yan’uwa da dukkan ak’ummar Musulmi allah ya gafarta musu, dukkan masu bukatu na alheri Allah ya biya musu, Allah ya samu cikin ceton sayyadina rasululalhi ranan Alkiyama. Amin.
‘AKULU KAULI HAZA, WA ASTAGFIRULLAH UWA LAKUM WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI TA’ALA WA BARAKATUHU

No comments:

Post a Comment