HAKKOKIN MAKWABTAKA A
MUSULUNCI
Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan
jinkai, tsira da aminci su kara tabbata ga Shugaban halitta da Ahlin gidansa da
Sahabansa, da dukkan wadanda suka bi shi da kyautatawa har zuwa Ranar Karshe.
Bayan
haka, a yau jama'a da dama ba sa kulawa da hakkokin da Musulunci ya shimfida wa
makwabtaka da irin yadda ya tsarawa kowane makwabci ya zauna da makwabcinsa da yadda
zai girmama shi da kuma yadda zai gujewa cutar da shi.Don haka, na ga ya dace
in dan fadakar ko in tunatar da 'yan uwana Musulmi da suka rafkana ga irin wadannan
Hakkoki tare da fatan wannan rubutu zai amfanar da masu karatu.
Da farko,
wajibi ne kowane Musulmi ya san hakkokin makwabcinsa da suke kansa,
tare da
sanin ladaban zama da shi, idan ya san hakan, shi zai sa ya zauna da
makwabtansa kamar yadda addini ya tsara.Domin Ubangiji mai
girma da daukaka
ya fada cikin littafinSa mai girma, cikin suratul
Nisa'i aya ta 36 cewa:
"GA IYAYE A KYAUTATA MUSU, DA MAKUSANTA, DA MARAYU, DA
MABUKATA, DA MAKWABCI NA KUSA".
Da kuma fadin Manzon Allah, Sallallahu Alaihi
wasallam cewa; "JIBRILU BAI GUSHE
BA YANA YI
MIN WASIYYA KAN MAKWABCI HAR NA ZACI ZAI GAJENI" (Buhari
da
Muslim).
Har ila yau,
da fadinsa Alaihis-salam "WANDA
YA KASANCE YA BAYAR DA GASKIYA DA ALLAH DA RANAR LAHIRA YA GIRMAMA MAKWABCINSA"
(Buhari da Muslim).
Idan muka
yi duba ga wannan Aya da wadannan Hadisai za mu fahimci girman
kyautata
wa makwabci da girmama shi, domin girmama shi ma yana nuna cewa
mutum ya
bayar da gaskiya da Allah da ranar Lahira.
WANENE
MAKWABCI
Malamai
sun bayyana makwabci cewa shi ne wanda in ka kidaya gidaje arbain daga jikin
gidanka hagu da dama gaba da baya.
RABE-RABEN
MAKWABTA DA HAKKOKIN KOWANE
A tsarin Musulunci makwabta sun kasu
zuwa kashi uku, kowanne da
irin
hakkokin da ke kansa, akwai mai hakki daya da mai hakkoki biyu da kuma mai
hakkoki
uku.
1. Makwabci Musulmi, makusanci
(Dan'uwa): Shi wannan yana da hakkoki uku, hakkin Musulunci ga hakkin
makwabtaka, ga kuma hakkin 'yanuwantaka, wanda yake tsan-tsan ya ga ya auke
dukkan wadannan hakkoki.
2. Makwabci Musulmi: shi wannan yana da hakkoki biyu ne kawai, wato
hakkin makwabtaka, sai kuma hakkin Musulunci.
3. Makwabci wanda ba musulmi ba:
shi ma nan yana da hakki daya ne kawai wato hakkin makwabtaka.
HAKKOKIN
MAKWABTAKA
Akwai hakkokin makwabtaka da dama, amma za mu dauko
wasu daga
ciki mu yi bayaninsu.
KAYUTATA
MASA: Yana daga cikin hakkokin makwabtaka a kyautata masa
ta kowanne hali, kamar aika masa da abin da ka dafa, bashi shawarwari da za su amfane
shi, a kansa ko iyalansa, ko 'ya'yansa, tsawatarwa 'ya'yansa a kan abin da aka
ga zai cuce su, domin kyautata wa makwabci yana kai mutum zuwa Aljanna "wani
mutum ya je wajen Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: "Ya Ma'aikin
Allah shiryar da ni a bisa wani aiki, idan na tabbata a kansa zan shiga Aljanna,
sai ya ce: Ya Ma'aikin Allah ta ya ya zan san ni mai kyautatawa ne? Sai ya ce:
Tambayi makwabtanka idan suka ce kai mai kayutatawa ne to shi ne, amma idan
suka ce kai ba mai kayuatatawa ba ne, to ba shi ba ne". Wannan Hadisi
yana
nuna mana
cewa idan mutum yana son ya san matsayinsa, to ya tambayi makotansa sune
shaidarsa a kan shi mai kyautatawa ne ko a'a, don haka wajibi ne mu zamo masu
kyautata musu don mu samu kyakkyawar shaidar cewa mu masu kyautatawa ne, don in
muka zamo masu kyautatawa, to mun kama hanyar zuwa Aljanna.
Ibn Umar
ya kasance yana da makwabci Bayahude, idan ya yanka akuya sai ya ce: ku kai wa
makwabcina Bayahude wannan (Abu Dawud da Tirmizi).
Har ila yau, ki ya ye
mutuncinsa da na iyalinsa da dukiyarsa suna daga cikin kyautatawa, domin Annabi
Alaihissalam ya ce: "Mutum ya yi zina da mataye goma shi ya fi sauki a
gare shi da yin zina da matar makwabcinsa, mutum ya yi sata a gidaje goma shi
ya fi sauki a gare shi da ya yi sata a gidan makwabcinsa" (Ahmad).
Ya zo
cikin sunani Abu Dawud daga Aba Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: "wani
mutum ya zo wajen Ma'aikin Allah ya kawo karar makwabcinsa, sai ya ce da shi, ka je ka yi
hakuri, sai ya sake zuwa na biyu ko na uku, sai Manzon Alla ya ce: jeka ka debo
kayanka ka zuba a kan hanya, sai ya je ya sanya duk lokacin da mutane suka
zo wucewa sai suka tambaye shi bisa
halin da ya ke aiki, sai ya basu labarin irin cutar da makwabcinsa yake yi
masa. Sai suka rinka la'antar makwabcin, sai makwabcin ya zo gare shi ya ce: ya
dan uwana mayar da kayanka gidanka ba za ka kara ganin wani abu na rashin
kyautatawa ba daga
gareni
har abada".
2. RASHIN CUTAR DA SHI: Har ila yau, yana daga hakkin
makwabcin a kan makwabci kada ya cutar da shi ta kowanne hali, wurin magana ne,
ko a wani aiki ko a katangarsa, ko ya sa indararon ruwan gidansa, ya rika zuba
musu ruwa cikin gidansa, ko saka murhun girki a jikin bangonsa ya rika zafafa
masa bango, ko hayakin girki ya rika
shiga gidansa yana tirara masa daki. Ko rariyar sa ta biyo ta gidan ka ka toshe
ta, ko ya rinka kora masa kazanta, ko yaki tsaftace ta wurinta ya rika cutarsa,
ko ya daure dabbobi a cikin kadangarsa su rinka bugun bangonsa. Ko ya rika
kiwon kaji a jikin gidansa warinsu ya rika cutarsa. Da dai sauran cutarwa ta kowane
hali. Domin Manzon Allah sallallahu Alaihi wassalam ya ce : Bai
yi imani ba! Aka ce wane ne ya Ma'aikin Allah? Sai ya ce: wanda
makwabcinsa bai aminta daga cutarwarsa ba". A cikin
wata ruwayar ya ce: "Ba zai shiga Aljanna ba wanda makwabcinsa bai
aminta daga cutarwarsa ba (Muslim) da fadin Manzon Allah Alaihis Salam "Wanda
ya kasance ya bayar da gaskiya da Allah da ranar Lahira, kada ya cuci
makwabcinsa (Buhari da Muslim). Da kuma fadinsa (SAW). "Ita tana
wuta gashi ita tana azumtar yini, tana tashi da daddare amma tana cutar
makwabtanta" (Ahmad da Hakim). Wadannan Hadisai duk suna zuwa ga guje
wa cutar da makoci.
3. GIRMAMA
SHI: Girmama makoci shi ma yana daga cikin hakkokin
makwabtaka. Kada ka wulakanta shi, ko ka yi masa kallon banza aa ka girmama shi
da duk wani sanadi da ka sani, ka yi alheri a gare shi, domin Manzon Allah
Alaihis Salam ya ce: "YA KU
MATAN MUSULMI KADA MAKWABCIYA TA WULAKANTA MAKWABCIYARTA" da fadinsa
ga Abi Zarrin: YA ABA ZARRIN IDAN ZA KA DAFA MIYA KA KARA YAWAN RUWANTA KA
AIKA WA MAKWABTANKA". Da kuma fadinsa (SAW) ga Aisha lokacin da ta ce
ina da makwabta biyu ga wanne daga ciki zan shiyar? Sai ya ce zuwa wanda
kofarsa tafi kusa gareki (Buhari da Muslim).
Yana daga
cikin girmama shi da karrama shi, kada ka hana shi jingina gini a gininka, ko
dora wani abu a kan katangarka, kamar rumfa, ko azara da sauransu, kuma kada ka
sayar da wani abu naka ko ka bayar da jinginarsa face ka fara tuntubarsa, in ba
ya bukata, sannan sai ka sayar wa da wani domin fadin Annabi Alaihis Salam
cikin Hadisin Buhari da Muslim cewa: 'WANDA
YA KASANCE YANA DA MAKWABCI KO ABOKIN MU'AMMALA KADA YA SAYAR DA WANI ABU NASA
HAR SAI YA BUJURO GARE SHI (Ma'ana sai ya tambaye shi ko zai saya in
ba zai saya ba sannan ya kai wa wani). (Buhari da Muslim).
4. JURIYA
GA CUTARSA: Yana da kyau ga makwabcin da Allah ya jarrabe shi da
makwabci mara kirki da ya jure ya yi hakuri kamar yadda muka ambata a Hadisin
da ya gabata na Aba Huraira na mutumin da ya kai karar makwabcinsa wurin Manzon
Allah, sai ya ce da shi ya yi hakuri
daga cutar makwbcin nasa, yin hakuri daga cutar makwabci bin umarnin Manzon
Allah ne, kuma rashin hakuri daga cutar tasa, da daka ta tasa kullum rigingimu
iri-iri to wannan saba Umarnin Annabi Alaihis-salam ne, rashin bin umarninsa
kuwa babban laifi ne kuma halaka ne. Wajibi ne ga makwabci ya hakura da cutar
makwabcinsa ko da kuwa ba Musulmi ba ne, domin an rawaito daga Sahih dan
Abdullahi Attusturi (Allah ya yi masa rahama) cewa shi ya kasance yana da
makoci wanda yake zuba ruwan kazanta daga gidansa zuwa gidan Sahih, sai shi
Sahih ya sanya wani daro duk lokacin da ya zubo wannan kazantar sai ya tare a
daron, idan dare ya yi sai ya je ya zubar yadda babu wanda zai gani.
Haka ya
zauna cikin wannan hali har lokaci mai tsawo, har lokacin da ajalinsa ya
tabbata, sai ya kira wannan makocin nasa kafiri ya ce da shi, zo ka shiga
gidana ka ga abin da yake cikinsa, da ya shiga sai ya ga daro cike da kazanta a
ciki, sai ya ce da shi mene ne wannan nake gani? Sai Salihu ya ce ai wannan ya
dade yana zuba gidana sai na tare shi da rana, in dare ya yi sai in zubar, to
kuma yanzu ajali ne ya gabato ina jin tsoron in na rasu kada ku samu sabani da
wani ba ni ba, in ka aikata masa wannan abu, sai kafurin ya ce; ya kai wannan
malami yanzu haka ka yi hakuri da ni na tsawon lokaci ga shi kuma ni kafuri ne?
To miko min hannunka, take ya yi kalmar shahada ya musulunta.
In muka duba ga wannan kissar za mu
fahimci darusa da dama, kamar juriya da hakuri da wannan malami ya yi da cutar
makocinsa kafiri, har tasa ya ranauta zuciyar kafirin, ya musulunta.
Ina rokon
Allah Subhanahu wata'ala da ya gyara halayenmu, ya sanya mu cikin masu kyautata
wa makotanmu, da girmamasu da kauce wa cutar da su Ya Ubangiji ka kara mana
juriya daga cutar makota, ka sanyamu cikin masu babban rabo Duniya da Lahira.
Ka kara tsira da aminci ga Shugaban halitta Annabin rahama sallallahu alaihi
wasallam.
Wassalamu
Alaikum warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu
Dan
uwanku a Musulunci
Auwalu
Zakari Muhd Ayagi
E-Mail
auwalzakari@yahoo.com
Tel: 07038775781,
08023615685
No comments:
Post a Comment