Thursday, 28 August 2014

Ciwon Sarke Hakora (Tetanus)

Ciwon sarke hakora ko tatanas kamar yadda wasu suka fi sanin sa da shi, shi ma nau’in ciwo ne da kan iya kama kowa, manya da yara, kuma kwayoyin cuta na bacteria da ake kira Clostridium tetani ke haddasa shi, kuma suna nan a kowane yanki na duniya.

Su wadannan kwayoyin cuta a cikin kasa suka fi rayuwa, amma iska kan kwashe su su bazu, wasu su hau fatar jiki. Idan suka samu suka shiga jiki sai su rika samar da wata guba da kan kama jijiyoyin jiki, su hana wurin motsi.

An yi kiyasin cewa duk shekara wannan ciwo na halaka mutane kusan dubu dari uku, yawancinsu jarirai, musamman a kasashe irin namu.

Yadda ake kamuwa da ciwon sarke hakora:
kwayoyin za su iya shiga jiki ne yayin da mutum ya ji rauni komi kan kantarsa (ko yanka ko kujewa ko gyambo ko kuna ko cizon wata dabba), idan  ba a dauki matakin kariya ba.

Jariri kan iya dauka a jikin abin da aka yanke cibi da shi, in ba mai tsabtaba ne. Bayan kamar kwanaki hudu zuwa mako biyu da yankan cibi ko yin rauni, gubar da kwayoyin cutar ke saki ta fara barna, za a ga jariri yana ta amai da zazzabi da yawan kuka da kin karbar mama. Wadannan su ne alamu na farko, in ba a dau matakin kai wa asibiti ba, za a ga wani bangare na jikin jariri ko kuma duk jikin gaba daya yana jijjiga, ko yana sandarewa.

A manya kuwa za a fara jin mukamukai sun cije, hakora sun sarke, sai wuya ya sandare, a kasa hadiyar ruwa ko abinci, sanadiyar wannan guba ta kwayoyin cutar. In ba a dauki mataki ba, haka za a ga duk jiki ya sandare daga sama zuwa kasa, wato daga kai har zuwa kafa, mara lafiya na bankarewa.

Kashi 40 zuwa 80 cikin dari na masu wannan karkarwa da sandarewa ba sa kai labari ko an je asibiti.

Hanyoyin kariya daga wannan ciwo: Allurar riga-kafin kamuwa da ciwon sarke hakora ita ce hanyar da aka tabbatar za ta kare kamuwa daga wannan ciwo.
Saboda haka:

1. Kowa da kowa ya samu a yi masa allurar riga-kafin sarke hakora akalla sau daya a cikin shekaru goma.

2. Mata masu ciki su rika zuwa awo domin a wurin ne ake ba da allurar riga-kafin wannan ciwo. Jaririn da ke ciki kan samu nasa rabon ta mahaifa.

3. A kai yara daga wata biyu ga cibiyoyin riga-kafi, a basu wannan allura, a sake komawa in sun kai wata hudu da wata shida, sannan duk yara daga shekaru 3-7 domin su suka fi yin rauni a yau da kullum ba tare da iyaye sun sani ba.

4. Idan yaro ko wani babba ya yi rauni, bayan zuwa asibiti an wanke ciwon, an ba da magunguna, to a tabbata an karbi allurar tatanas don yin riga-kafi.

5. A tabbatar ungozoma mai karbar haihuwa a gida tana amfani da sabuwar reza ko aska wajen yanke cibi, ba tsohuwar reza ko aska ba, domin ko tafasa reza da askar baya kashe kwayar cutar tatanas.

6. Manoma su yawaita zuwa karbar wannan allura, su kuma rika amfani da takalmin ruwa irin na roba domin wani zubin sukan yi rauni da lauje ko fartanya ba tare da ma sun sani ba.

7. A yi hanzarin kai jariri mai yin jijjiga ko mai nuna alamomin da aka zayyana a sama asibiti mafi kusa, ko da mai gida ba ya kusa, musamman in a gida aka haifi jaririn.

8. A yi hanzarin kai duk wani babba da hakoransa ko mukamukansa suka cije, ya kasa magana ko cin abinci asibiti mafi kusa.

Allah ya kara mana lafiya.

1 comment: