Friday, 20 June 2014

HUKUMCIN AZUMIN YA MACE A SHARIA

BAYANI AKAN HUKUMCIN AZUMIN MACE A SHARI’A

Daga www.sautulazimiyyah.blogspot.com

Da sunan Allah mai yawan Rahama,  Mai yawan jin kai, tsira da Aminci su kara tabbata ga fiyayyan halitta Annabin rahama, tare da saabbansa da iyalan gidansa, da duk masu binsa da kyautatawa har zuwa ranar Alkiyama.

Bayan haka Azumin watan Ramadan wajibi ne akan kowanne musulmi Namiji da musulma mace, kuma yana daya daga cikin manya manyan ginshikan musulunci, kuma daya ne daga cikin rukunansa, kamar fadin Allah (SWT) cikin littafinSa Mai tsarki cewa: "Yaku wadanda kuka yi imani, an wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi ga wadanda suka gabace ku, don kuji tsoron Allah" (Bakara aya ta 283).

Kamar yadda shari'a ta dora yin azumi akan namiji, haka ta dorawa ya mace yinsa, na Ramadanne ko na nafila, amma kuma shari'a ta rwangwantawa mace game da yin azumin a wasu wurare ko kuma ace awasu lokuta, wannan saboda kasancewar mace mai rauni ta fanin shari'a da hankali,

Idan watan ramadan ya tsaya to ya wajaba akan ko wanne musulmi da musulma, baligai, kuma masu lafiya, mazauna gida su yi azumi, ma'ana su kame bakinsu daga ci ko sha ko saduwar aure daga fudowar alfijir har zuwa faduwar rana, wanda kuma ya kasance mara lafiya ko yazamo matafiyi acikin kwanakin azumin ramadan, to ya halata agare shi da ya sha azumin sa'annnan ya rama adadin kwanakin da ya sha acikin kwanakin da bana ramadanba.

Allah (SWT) yace: "Wanda ya riski wata dag a cikin ku, to sai ya azumce shi, wanda kuma ya zamo maras lafiya ko matafiyi, to sai ya rama a kwanaki na gaba..." (bakara aya ta 185).

Don haka duk wanda watan Ramadan ya riske shi amma ya tsufa tukuf, ko kuma mara lafiya dake a kwance, da ba'a sa ran zai warke daga rashin lafiyar, mace ko namiji, to ko wanne daga cikin wadannan zai sha azumin, amma sai ya ciyar da miskini daya rabin sa'i, ma'ana mudu biyu na galibin abincin kasar, amaimakon ko wace rana, wacce ya sha azumi acikin ta. kamar yadda Allah maigirma da daukaka ya bayyana cikin suratul bakara aya ta 184.

To anan mace ma shari'a ta bata damar shan azumi saboda wadansu uzururuka wadanda ke faruwa agareta wadanda basa faruwa ga da namiji, wadannan uzururruka sune kamar haka:-

1. JININ HAILA DA JINI BIKI:- 
Ya haramta ga mace mai jinin biki ko na haila tayi azumi, amma kuma wajibi ne ta rama azumin awasu kwanaki da ba na ramadana ba, sabanin salloli su baza ta rama su ba.
Saboda Nana A'isha (RA) tace:- "Mun kasan ce ana umurtar mu da rama azumi amma ba'a umurtar mu da mu rama salla. Awata ruwayar ta imam muslim yace, "Mu'azatu tace na tambayi Nana A'isha nace saboda me mai haila zata rama azumi amma bazata rama sallah ba, sai tace:- ke 'yar (khawarijawa ce) sai nace ni ba ita ba ce nadai tambaya ne kawai, sai tace dani hakan na samun mu, sai aka umurce mu da mu rama azumi, amma ba'a umurce mu da mu rama salla ba, kuma ta kara da cewar wadannan al'amura ne da mutum yake tsayawa inda aka tsai da shi, ba ra'ayi ake bi ba a’a nassi ake bi. idan kuma mace taga farar kassa, wato wani ruwa da mahaifa take fitarwa bayan karewar jinin haila, wacce mace ke gane samun tsarkinta idan ta gan ta, to sai ta daura  niyya don daukan azumi. idan kuwa bata da wata takamaimiyar hanyar samun tsarki sai tayi kunzugu da Auduga ta gargajiya ko 'yar kanti, ko dai wani abu makamancinta kamar tolet paper, idan ta cirota da ganta tsaf babu jini ta tsarkaka kenan, to sai ta dauki azumi, amma kuma idan bayan ta dauki azumi sai jinin ya dawo mata a wannan ranar, to sai ta sha azumin, amma idan bata sha ba sai jinin ya dauke kafin magariba, to azuminta ya ingan ta. sa'annan matar da taji alamar fitowar jinin haila amma sai bai fito ba, sai bayan magariba to ita ma azumin ta yayi.
Matar da take haila sai jinin ta ya dauke tun dare sai tayi niyar yin azumi, kuma ta kasance bata yi wanka ba har alfijir ya keto to azumin ta ya ingan ta, bisa mazhabar daukacin malamai.
matar da tasan cewar gobe ne jini zai zo mata, amma sai ta tashi da azumi to ba zata ci abinci ba har sai idan jinin ya zo mata, sannan sai ta sha azumin, idan kuma bai zo mataba sai taci gaba da azuminta.
Mai biki idan ta samu tsarki kafin kwanaki Arba'in da haihuwar ta, to sai tayi wanka tayi niyyar azumi, amma idan jinin ya haura kwana Arba'in bai dauke ba to sai ta dauki jinin a matsyin jinin istihada (wato jinin cuta) sai dai kuma idan jinin ya yi dai dai da lokacin al'adarta wadda take yi duk wata, to wannan kam sai ta dauke shi amatsayin jinin haila.

2. Mace mai ciki da mai shayarwa:- Itama mace mai ciki ko mai shayarwa idan har yin azumi gareta zai cuce ta, ko ya cuce jaririn ta, ko kuma duka su biyun zasu cutu, to ita ma anyi mata rangwame akan ta sha azumi a cikin halin cikin ko shayarwar.
Amma kuma idan yin azumin zai cutar da jaririn ta ne kawai ban da ita, to zata rama azumin kuma ta ciyar da miskini daya maimakon azumin da duk ta sha aduk lokacin da tazo ramawa, amma idan yin azumin zai cutar da ita ne ita kadai to zata rama azumin kawai banda ciyarwa.Top of Form Domin Ayar da ke yin bayani akan wanda ke iya yin azumi amma da kyar to lallai akwai mace mai ciki da mai shayarwa idan suka jiwa kansu ko jaririn su tsoron cutuwa.
Don haka zance mafi rinjaye anan shine anyiwa mace mai ciki da mai shayarwa kiyasin marar lafiya don haka ya halatta da su sha azumin kuma ba su da kaffara sai dai ramuwa, ya Alla suna jiwa kan su tsoro ko suna jiwa 'ya'yan su tsoro, hujjar wannan itace ruwayar Imamu Tirmizi yace: Annabi (SAW) yace: Allah madaukakin sarki ya daukewa matafiyi wani yanki na azumi (wanda ya sha alokacin tafiyar sa) da wani yanki na sallah (yana nufin yin kasaru) kuma ya daukawa mace mai ciki, da mai shayarwa yin azumi.

3. Jini rashin lafiya:- ko kuma jinin ISTIHADHA macen da jini yake zuwar mata bana haila ba, azumi wajibi ne akan ta, bai halatta ta sha azumi saboda wannan jinin domin shi jinin rashin lafiya ne kamar zuwan kumallo ne ko fitar jini saboda rauni, ko fitar ruwan kurji, duk wadannan abubuwa ne wadanda basu da lokaci kayadadde na zuwan su, balantana ace mace tabar azumi domin su, ma'ana zuwan su ba zai hana mata yin azumi ba. 4. Matar aure:- Bai Halata ga Macar aure tayi Azumin Nafila ba, alhali mijin ta na gida sai da izinin sa ko idan baya gari ya yi tafiya, amma kuma ban da na ramadan, macen da azumi ya wajaba akan ta idan ta dauki azumin ramadan sai mijinta ya tara da ita da rana alhali tana dauke da azumin ramadan, kuma bisa yardarta, to dukkan su zasu yi ramuwa da kaffara, amma idan tilasta mata ya yi, to tayi iyakar kokarin ta na hana shi, amma bata yi nasarar hana shi ba, to ita babu kaffara a kanta sai dai ta rama azumi. Amma idan mace tana barci acikin watan ramadan sai mijinta ya tara da ita, to malamai sunce ita ma babu kafara akan ta sai dai ta rama azumi.

Anaso ga mace budurwa ko wacce mijinta ya yi mata izinin yin Azumin da ta rika yawan yin azumin nafila, ko yin Azumin mustahabbi (wato abin da aka so) da kuma yin azumin a ranakun litinin da Alhamis, da kwanaki shida na watan shawal, (wato Sittu Shawwal) da kwanaki goman farko na zulhijja, (Wato Ashara Zulhijja) da azumtar ranar Arafat da ranar Tasu'a da Ashura, sai dai kuma bai kamata ba gareta da tayi azumin nafila ba, alhali ana binta ramuwar wani azumin, har sai ta rama azumin da ake bin ta. kuma ya kamata ga duk matar da ta san cewa mijin ta baya iya danne sha'war sa a duk lokacin da dama ta samu, to ta nisanci mijin ta acikin azumi, kuma ta daina yin ado ko kwalliya a cikin watan azumi.

Akarshe malamai sun ce wajibe ne akan mace ta ramuwa azumin da ake binta kafin kamawar wani azumin, sai dai idan da wani uzuri mai girma, amma idan bata rama ba har wani azumin ya kama, ba tare da wani uzuri ba, to duk yayin da tazo rama wa, bayan ta rama sai ta ciyar da miskini daya. Kamamalawa Abin da akeso agare ki ya ke 'yar'uwa Musulma, idan kina Jinin haila to ki zauna bisa al'adarki tayin jini a duk wata, ki yarda da abinda Allah (SWT) ya hukunta agareki, kada kiyi kokarin shan wani abu da zai hana jinin fitowa, ki karbi abin da Allah ya yarje miki, na shan azumin akwanakin haila da yin ramuwar su bayan salla, domin kuwa haka matan Annabi (SAW) iyayen muminnai, da matan salihan bayin Allah, suka hakura.Amma idan kika ki, kika sha wani magani domin hana fitar jinin haila a watan azumi, jinin kuwa ya dauke kika samu tsarki kika cika azumin ki cif cif, batare da kin sha ko daya ba, to babu kommai amma baki yi koyi da iyayen muminai ba, kuma baki samu ladan yin koyi da salihan bayi ba.

Wannan shine dan abi da ya sawwaka game da hukumcin da shari'a ta dorawa mace game da azumi, da fatan zamu amfana, abin da akji na daidai daga Allah ne na kuskure kuma daga gareni ne, ina sauraron gyara,

Akulu kauli hadha wa astagfilullaha li wa lakum Wassalamu alaikum warahamatullah.

ADDUA TAKOBIN MUMINI

Addu’a takobin mumini
Daga www.sautulazimiyyah.blogspot.com

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.  Dukkan yabo da godiya su tabbata ga  Allah, Ubagijin halittu baki daya.  Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu sallallaahu alaihi wasallam, tare da alayensa da sahabbansa  baki daya, da duk wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar karshe.   Bayan haka, a yau inaso in dan yi tsokaci ne a kan addu’a a matsayinta na takobin mumini.  Za mu ga ma’anarta da falalarta da lokuta da guraben da ake karbarta, sannan da ladubbanta.  Haka nan akwai nau’in wadanda ake karba musu addu’a da kuma wadanda ba a karba musu ko kuma ake jinkirta musu. Sannan da bayanan a kan dalilan dasuke sawa ba a karbar addu’a  duk daga abin da aka cirato daga zantuka da bayanan magabata na kwarai, Allah Ya jikansu da rahama.  Sai kuma wani waige a kan Istikharah. Bismillah! MA’ANARTA A Larabce addu’a na nufin kiran wani, ko neman miko wani abu.  Suna cewa: da’aa bil kitabi, ma’ana ya nemi a miko masa littafi.  A isdilahi  kuma addu’a tana nufin tarin kalmomin yabon Ubangiji, masu nuni ga neman wani abu daga gare Shi, ko neman tsarin wani abu (sharri) daga gare Shi. FALALARTA “An karbo daga dan Abbas, Allah Ya yarda da shi cewa Yahudawan Madina sun tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) suka ce: ‘Ta yaya Ubangijinmu Zai ji addu’armu, bayan kai kana zaton cewa tsakaninmu da sama kimanin tafiyar shekara dari biyar ne.  Kuma tsakanin kowace sama da ’yar uwarta ma haka ne ?’  Sai Allah Ya saukar da:  “Duk lokacin da bayiNa  suka tambaye ka game da Ni, to Ni Makusanci ne. ina amsa addu’ar mai roko in ya roke Ni.”  Bakara aya ta 186 ( daga Algunya ta Sidi Abdulkadir Shafi Na 373). Ma’aiki, sallallahu alaihi wasallam,  ya ce “Addu’a ita ce ibada.”  Kamar yadda aka fitar a littafin Riyadhussalihin na Imam Nawawi a Kitabul – da’awati . A wata riwayar kuma ya ce: “Hakika Ubangiji na mu’amala irin ta jin kunya.  Idan bawa ya buda hannu ya roke Shi, Ya ki amsa masa,  ko dai ya gaggauta masa a amsawar tun a duniya, ko ya jinkirta masa sai a ran kiyama.” LOKUTA DA GURABEN AMSA ADDU’A Ana karba (amsa) addu’a a wurare da lokuta da kuma guraben yanayi kamar haka: 1- Yayin sujjada. 2- Lokacin alwala. 3-Lailatul kadri. 4- Yayin saukar ruwan sama. 5- Tsakar dare. 6- Tsakanin kiran sallah da ikama. 7- Ranar Juma’a 8- Ranar  Arfa. 9- Yayin kiran sallah.        10- Bayan kiran sallah. 11- Bayan jifan shaidan.      12- A Safa da Marwa. 13- Sallolin farilla.        14- Watan Rajab. LADUBBAN ADDU’A Yana daga cikin ladubban addu’a mutum ya kasance yana da: 1- Ikhlas – wato ya kasance yana da tsarkin zuciya, ya fuskanci Allah kadai a cikin abin da yake bukata. 2- Kyakyawan zaton amsa ta. 3- kankan da kai da sassauta sauti. 4- Shiga (suturarsa) da ci da shansa su kasance na halal. 4- Fuskantar alkibla.   5- Naci a addu’ar. 6- Cudanyata da yabon Ubangiji da kirari gare Shi. 7- Salatin Annabi farko da tsakiya da karshe. 8- Fadada abin nema ga sauran musulmai. 9- Yin ta a tsanani da walwala. 10- Halarto zunubi da bayyana tuba. 11- Bijiro ni’imomi da bayyana godiya ga Allah. 12- daga hannu sama da shafar fuska da shi bayan addu’ar. WADANDA BA A KIN AMSA ADDU’ARSU 1- Mai azumi yayin buda baki.   2- Wanda aka zalinta. 3- Shugaba nagari.   4- Matafiyi kan yardar Allah. DALILIN kIN AMSA ADDU’A Wofintar addu’a ga ladaban amsa ta na jawo kin amsa ta.  An tambayi Shehi Ibrahim  dan Adhama, Allah Ya yi masa rahama, cewa ‘ko me ya sa muke rokon Allah ba Ya amsa mana?’ Sai ya ce saboda :- 1- Kun san sunnar Ma’aiki, sallallahu alaihi wasallam, ba ku bi. 2- Kun san Alkur’ani ba ku aiki da shi. 3- Kuna cin ni’imomin Ubangiji ba ku godiya. 4- Kun san Aljanna ba ku nemanta. 5- Kun san wuta ba ku tsoranta. 6- Kun san shaidan kuna binsa. 7- Kun san mutuwa ba ku yi mata tanadi ba. 8- Kun san mamata ba ku tunawa da su. 9- Kun bar abinku kun shagalta da na mutane. Haka nan Allah Yakan jinkirta wa bawa addu’rsa don soyayya, kamar yadda hadisi ya bayyana cewa, “Bawa kan roki Allah Ya biya masa da wuri, saboda ba Ya son jin muryarsa; wani (bawan kuma) ya roka a jinkirta masa, saboda son jin muryarsa da Allah Yake .” TSAWAITA  ADDU’A KO TAKAITA TA Nana A’ishah, Allah Ya yarda da ita, ta ce Manzon Allah,  sallallahu alaihi wasallam, yana son  dunkulalliyar addu’a, yana barin watanta (ma’ana ba ya tsawaita mai wuce haddi), kamar yadda aka fitar a littafin Riyadhussalihina a Kitabul da’awati shafi na 264). ISTIKHARAH Wannan na nufin neman zabin Allah kan wani al’amari da bawa yake so ko zai aikata. Sayyadina Jabir, Allah Ya kara masa yarda, ya ce “Ma’aikin Allah, sallallahu alaihi wasallam, ya kasance yana koya mana istikhara a duk al’amari , tamkar sura daga Alkur’ani.  Yana cewa, ‘idan dayanku ya nufi wani al’amari, sai ya yi sallar nafila raka’a biyu, sai ya ce: Allahumma inni astakhiruka bi ilmika wa astakdiruka bi kudratika wa as’aluka min fadlikal azim fa innaka  takdiru wala akdiru wa ta’alamu wala a’alamu wa anta allamul guyub; allahumma in kunta ta’alamu anna hazal amra khairun li fi dini wa ma’ashi  wa akibati amri fakdirhu li wa yassirhu li summa barik li fihi; wa in kunta ta’alamu anna hazal amra sharrun li fi dini wa ma’ashi wa akibati amri fasrifhu anni wasrifni anhu wakdir liyal khaira haisu kana summa ardhini bihi  (sai mutum ya ambaci bukatarsa) – Imamul Bhukari. Tabbas Allah na fushi da bawanSa in ba ya rokonSa.  Allah Ka daukaka Musulunci da musulmai, Ka rusa kafirci da kafirai.  Ka yalwata mu da soyayyar Ma’aikinmu, sallallahu alaihi wasallam, Ka sa al’amarinmu ya kasance a ranar mutuwarmu muna masu cikawa da kalmar la’ilaha illallah muhammadur rasulullah

Tuesday, 17 June 2014

Bayani akan Aikin Hajji a takaice

Takaitaccen bayani kan aikin Hajji
Daga: www.sautulazimiyyah.blogspot.com

Da sunan Allah mai yawan Rahama mai yawan jinkai, tsira da aminci sukara tabbata ga Shuhaban Halitta da dukkanin sabansa baki daya.

Bayan haka Shi dai aikin Hajji ya kasu kashi uku ne:
1. Hajjin Tamattu’i.
2. Hajjin Kirani.
3. Hajjin Ifradi.

1. Hajjin tamattu'i: Shi ne wajibin wanda yake zaune a nesa da garin Makkah, nisan da ya kai mil 48, yayin da Hajjin Kirani da Ifradi sune wajibin wanda yake zaune a garin Makkah da kewayenta, wato nesansu da garin Makkah bai kai mil 48 ba. To amma a aikin Hajjin bakance, ko na mustahabbi, ya halatta ga mazaunin Makkah da wanda ke nesa da Makka ya zabi duk aikin Hajjin da ya ga dama tsakanin raben-raben da aka ambata a sama.
To bisa la’akari da cewa aikin Hajjin Tamattu’i shi ne wajibin mafiya yawa mutane, musamman mutanenmu, don haka za mu yi bayani ne kan wannan nau’i na aikin Hajji.

Ga yadda ake yin Umurar Tamattu’i: Da farko mutumin da ya yi niyyar yin aikin Hajjin Tamattu’i zai fara ne da daura harami a daya daga cikin wararen da ake daura haramin guda biyar, ko kuma abin da ake ce wa ‘mikati,’ wato: 

(1) Zul Hulaifa 

(2) Akik 

(3) Juhfa 

(4) Yalamlam 

(5) Karnil Manazil.


1. Harami: Shi ne sanya kyallen tufafin nan guda biyu da Alhaji zai sa yayin aikin Hajjin. 

Yadda ake daura harami shi ne: Mutum zai yi niyyar yin harami da Umurar Tamattu’i na Hajjin wajibi, sannan ya sanya tufafin haraminsa guda biyu, zai daura guda, ya kuma yafa guda, wato ya yi mayafi da shi. Daga nan sai ya fara ‘talbiyya’ wato fadin: Labbaikallahumma labbaik, labbaika la sharika laka labbaik, innal hamda, wan ni’amata laka wal mulk, la sharika laka. To idan mutum ya yi haka ya zamanto muhrimi (wanda ya daura harami) kenan da aikata wasu abubuwa suka haramta masa kamar su kusantar mace, shafa turare, sanya kewayayyen tufafi ga namiji, farauta da makamantansu. Akwai kuma wasu ayyuka na mustahabi da ake so mutum ya aikata, misalin yin wanka kafin daura harami da makamantan hakan. 

2. Dawafi: Abu na biyu cikin aikin Umrar Tamattu’i shi ne Dawafi, wato kewaya Dakin Ka’aba. Yadda kuma ake yin sa shi ne: Mutum zai fara da yom niyyar Dawafin Umurar Tamattu’i ne,sai ya fara zagaya Dakin Ka’aba har sau bakwai, zai fara ne daga inda Hajrul Aswad yake, wato Dakin Ka’aba na hannunsa na hagun. Idan ya fara daga wajen Hajrul Aswad ya zagayo ya zo wajen da ya fara, to ya yi guda kenan, haka-haka har sau bakwai.

3. Sallar Dawafi: Idan mutum ya gama dawafi wato ya kewaye Dakin sau bakwai, sai ya yi sallar Dawafin raka’a biyu a Makama Ibrahim. Wannan shi ne wajibin Umura ta Tamattu’i.

4. Sa’ayi: Wajibi na hudu shi ne Sa'ayi, wato tafiya tsakanin Safa da Marwa, yadda ake yin ta kuwa shi ne: Mutum ya yi niyyar yin Sa'ayi na Umrar Tamattu’i na Hajjin wajibi, sai ya fara tafiya daga Safa ya zo Marwa, daya kenan, sannan daga Marwa ya zo Safa, biyu kenan har sau bakwai. Wato tafiya daga Safa zuwa Marwa sau hudu, daga Marwa kuma zuwa Safa sau uku, wanda karshen tafiyar za ta kare ne a Marwa.

5. Aski: Wajibi na biyar kuma na karshe a Umurar Tamattu’i shi ne: Aski, ko kuma saisaye, mutum ya aske wani abu daga cikin gashin kansa ko gemunsa, ko gashin bakinsa, ko kuma ya yanke farcensa. Da hakan ne ake kare aikin Umurar Hajjin Tamattu’i, wanda hakan na nufin kenan dukkan abubuwan da aka haramta masa saboda harami a halin yanzu ya halatta a gare shi, misali kusantar mace, sanya turare da sauransu. Daga nan sai mutum ya jira lokacin daura haramin Hajjin Tamattu’i.

HAJJIN TAMATTU'I: 

Ayyukan Hajjin Tamattu'i Su ne: 

1. Saka harami a Makka.

2. Tsayuwa a Arafa.

3. Tsayuwa a Mash'arul Haram.

4. Jifan Jamratul-Akaba (jifan shaidan).

5. Yin hadaya.

6. Aske gashin kai ko rage shi.

7. Kwana a Mina a dare na sha daya.

8. Jifan jamrori(shedanu) uku a rana ta sha daya.

9. Kwana a Mina a dare na sha biyu.

10. Jifan jamrori (shedanu) uku a rana ta sha biyu.

11. Dawafin hajji.

12. Sallar dawafi.

13. Sa'ayi (Safa da Marwa).

14. Dawafin mata.

15. Sallar dawafi.

HUKUNCE - HUKUNCEN HAJJIN TAMATTU'I

An shardanta wa hajjin tamattu'i abubuwa kamar haka:

Na daya: Niya, ita ce nufin aikata irin wannan nau'in hajjin yayin daura ihramin umarar. Idan ba haka ba, bai inganta ba.

Na biyu: Ya zama umrar da hajjin ya yi su a watannin aikin hajji.

Na uku: Tilas ya yi hajji da umrar a cikin shekara guda.

Na hudu: Ya zama mai yin hajjin da umrar mutum guda ne.

Da zai dauki hayar mutum biyu su yi wa mamaci hajjin tamattu'i, watau daya ya yi umra dayan kuma ya yi masa hajjin, bai isar masa ba.

CIN RUBA TANADIN YAKI DA ALLAH DA MANZON SANE

Cin Riba Tanadin yaki da Allah da Manzon sane
Daga Auwal Zakari Ayagi

Da suna Allah mai Rahama mai jinkai, tsira da aminci sukara tabbata ga fiyayyen halitta cikamakin Annabawa, shugabannin manzanni, tare da sahabbansa da suka taimaka masa wajen kafuwar  addini, da Ahalin gidansa da matayensa da dukkan wadanda suka bishi da kyautatawa har zuwa ranar Alkiyama.

Bayan haka Ubangiji mai girma da daukaka yana fada cikin Alkur’ani mai girma:

{ یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ ٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَذَرُوا۟ مَا بَقِیَ مِنَ ٱلرِّبَوٰۤا۟ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِینَ (278) فَإِن لَّمۡ تَفۡعَلُوا۟ فَأۡذَنُوا۟ بِحَرۡبࣲ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۖ وَإِن تُبۡتُمۡ فَلَكُمۡ رُءُوسُ أَمۡوَ ٰ⁠لِكُمۡ لَا تَظۡلِمُونَ وَلَا تُظۡلَمُونَ (279) }

[Surah Al-Baqarah: 278-279]

Ma'ana

“YAKU WADANDA KUKAYI IMANI KUJI TSORON ALLAH KU BAR ABIN DA YAYI SAURA DAGA RIBA IN KUN KASANCE MUMUNAI, IN HAR BAKU AIKATABA (barin cin ribar) INA MUKU IZINI DA YAKI DA ALLAH DA MANZONSA, IN KUKA TUBA ASALIN DUKIYARKU NA GAREKA BAKU YI ZALUNCI BA BA’A ZALINCE KUBA”  (Bukara Aya ta 272-279)
Wannan aya tana tsoratar damu game da Mu’amala da Riba, inda Allah da kansa yake cewa duk wanda bai bar cin Ruba ba yana masa izinin yin yaki dashi da Annabinsa (SAW), kamar yadda yazo a labari cewa: Ranar Alkiyama Ubangiji zai bawa masu cin Ruba makami ya umarce shi da yayi yaki da shi, Allah ya kiyayemu, Allah yace: amma in kuka tuba to sai ku debi asalin Dukiyarku (jarinku) ragowar kudin sai ku rabar in kukai haka bakuyi zalunci ba kuma ba’a zalunce kuba.

Menene Ruba?
Ruba tana nufin dadi abisa abubuwa da kebantar Karin kudi

Rabe-Raben Ruba
Ruba ta kasu izuwa kashi biyu wato:
* Rubar Dadi
* Rubar jinkiri

* Rubar Dadi: Rubar dadi tana nufin cinikin jinsi daya kamar (Gero da Gero, Dawa da Dawa, Naira da Naira da sauransu) amma tare da dadi akan cinikin, kamar asayi Gero kwano daya amma sai ace sai ka dada rabin kwano akan kwano dayan, ko sayan sababbin kudi, misali na Naira dari biyar amma ace sai an dada Naira Hamsin akai, da sauransu.

* Rubar Jinkiri: Rubar jinkiri ta kasu kashi biyu,:
* Ruba Ninkawa
* Ruba mai daduwa don dogon lokaci.

Ruba mai ninkawa: Ruba mai ninkawa itace ake cewa Rubar Jahiliyyah, wannan itace ubangiji ya haramtata da nassin Alkur’ani mai girma, inda yake cewa: “YAKU WADANDA KUKAYI IMANI KADA KUCI RUBA NINKIN-BANINKIN: (Ali Imram Aya ta 130).

Yanda wannan Ruba take, Shine a baiwa wani bashi zuwa wani lokaci abin ayyanawa, idan lokacin yayi bai samu damar biya ba, sai ace dashi ko ya biya ko kuma a karamasa kudi sannan a kara masa lokacin biyan, haka za’a rika karamasa kudi ana karamasa lokacin biyan, har kudin sun ninninka kansu.

Misali kan wannan shine kamar bashin da kasashe suke ciyowa bisa yarjejeniyar zasu biya zuwa Shekarun da aka ayyana, idan lokacin yayi basu biya ba, sai kudin suyi ta karuwa gwargwadon tsowon lokacin da kasar tayi bata biyaba, sai aga kudin sun ninka kansu ninkin ba ninkin. To wannan itace Rubar da wannan aya take Magana akai.

Ruba mai daduwa don dogon Lokaci; Wannan itace Rubar da ake bada bashi da kari don bashin zai dauki dogon lokaci, misali: abada bashin naira Dubu daya amma za’a biya dubu da dari daya a tsawon kwanaki ishirin.
Ko sayen wani abu da kari kan asalin kudin sa don daukan dogon lokaci, misali sayen Sha’ir ko Dabino ko kwaya kamar wake, masara, gero da makamantansu, amma da Karin kudi in zai kai wani lokaci, misali: ana sayar da Masara Naira 300 a ko wacce kasuwa, sai abada ita bashi akan Naira 350 don za'a biya a watanni biyu, ko biya biyu ga ma’aikata, da makamantansu.

HUKUMCIN RUBA
Ita dai Ruba haramunce, sabo da fadin Ubangiji madaukakin sarki cikin suratul Bakara Ayata 275 cewa:
“Allah ya halatta ciniki ya haramta ruba”
Da fadinsa “YAKU WADANDA KUKAYI IMANI KADA KUCI RUBA NINKIN-BANINKIN: (Ali Imram Ayata 130).

Ga kuma fadin Annabi Alaihissalam cewa:

1. “Allah ya tsinewa mai cin Ruba da wakili akan Ruba da masu shaida akan Ruba da marubucin Ruba” (As-habu Sinan)

2. “Sisi na Ruba da mutum yake cinsa yana sani shi yafi tsananin Azaba da Zina Talatin da mutum zaiyi" (Ahmad da Hakim)

3. “Ruba kofa Saba’in da Uku ce mafi saukinsu shine mutum ya auri mahaifiyarsa" (Hakim)

4. "Ku nisanci abubuwa bakwai mafiya ukuba, sai akace yarasulullahi menene? Sai yace: Yin tarayya da Allah, da sihiri da kashe ran da Allah ya haramta da cin Ruba, da cin dukiyar marayu da juya baya (Guduwa) Ranar yaki, da yin kazafi ga mumina katangaggiya” (Buhari da Muslim) 

UKUBAR MASU CI RUBA
Ubangiji madaukakin sarki yafada cikin Suratul Bakara Ayata 275:

“Wadannan da suke cin Ruba basa tashi (yayin tashi daga kaburbura) sai kamar misalin wadanda shaidanu suke bubbugewa (tashin su kamar na masu fyarfyadiya) da shafa (ta Aljanu) wadannan don cewa su suna cewa shi ciniki kamar Ruba ne”.

Idan Ubangiji ya tashi mutane ranar Alkiyama zasu fita suna masu gaggawa, sai masu cin Ruba su zasu tashi suna faduwa kamar masu fyarfyadiya, don cewa su yayin da suke cin Ruba Ubangiji yana tarata a cukkunansu har ta rinjayesu ranar Alkiyama duk yayin da suka tashi sai su fadi, suna son suyi gaggawa kamar sauran mutane amma baza su iyaba.

Katadatu yace Mai cin Ruba za’a tasheshi ranar Alkiyama yana mahaukaci.
An karbo daga Abi Sa’idul Khudri (RTA) cewa Manzon Allah (SAW) yace yayin da akai Isra’i dani, na shude ga wasu Jama’a cukkunansu yana gabansu ko wane mutum cikinsa kamar katon gida, cikin nasu yana karkatar dasu suna masu kururuwa a bisa kwararowar azabar Jama’ar Fir’auna ana bijiro musu da azaba safe da yamma, sai yace: sai a bijiro musu da Azaba kamar misalin gudajjen Rakumi basaji basa gani, yayin da wadannan masu cukkunan sukajisu sai su tashi, amma sai cikkunansu su rinjayesu bazasu iya tashi ba, har sai jama’ar fir’auna sun samesu sai subi ta kansu, suyi gaba dasu suyi baya da su, haka za’ai ta yi musu wannan Azaba. Sai Ma’aikin Allah yace su wnene wadannan ya dan’uwa Jibrilu? Sai yace sune masu cin Ruba.

An karbo daga Ibn Mas’ud daga mahaifinsa cewa: Idan zina da Ruba suka bayyana a Alkarya, sai Ubangiji yayi izinin halakar da ita.

Manzon Allah (SAW) yace: Ruba bazata bayyana a al’umma ba face hauka ya bayyana  a cikinsu. Zina bazata bayyana ga Al’umma ba face Mutuwa ta bayyana a garesu, Al’umma baza su tauye ma’auni da mudu ba face Allah ya hana su ruwan sama.

Har ilayau Manzon Allah Alaihissalam yace: Jama’a hudu Allah bazai shigar dasu Aljanna ba, ba zasu dandani Ni’imarta ba.
i. Mai narka Giya
ii. Mai cin Ruba
iii. Mai cin dukiyar marayu bada hakki ba.
iv. Mai sabawa iyayen sa.

An karbo daga Abubakar Siddik (RTA) yace: Mai dadi da wanda aka dadawa yan wuta ne, (ma’ana Mai bada Ruba da mai karbarta)

Wadannan Ayoyi da Hadisai suna nuna girman laifin Ruba, da irin Azabar da zata riski masu mu’amala da ita, da kuma mahimmancin barinta.

HIKIMAR HARAMTA RUBA
Haramcin mu’amala da Ruba na dauke da hikima kamar sauran ibadu, an haramta ta ne sabo da jarraba imanin bawa don ganin yayi biyayya a cikin aikatawa ko cikin hani, sannan yana daga cikin haramcin Ruba:

* Kiyaye wa abisa dukiyar Musulmi, don kada yaci dukiya yana mai barna.
* Fuskantowar musulmi cikin yaduwar dukiyarsa cikin hali madaukaki ba tare da cutar da sauran musulmi ba, cikin sana’arsa da Moman sa da Kasuwancin sa da sauransu.
* Toshe hanyoyin masu sa kiyayya ga musulmi, domin kiyayya ga musulmi tana wahalshe shi, sababinta kuma abin hani ne.
* Tseratar da musulmi bisa ga abin da zai kaishi ga halaka don cin Ruba zalunci ne kuma halakane.
* Bude kofofin biyayya ga musulmi don suyi guzuri sabo da lahira.

KAMMALAWA
Kamar yadda muka karanta Ayoyi da Hadisan Manzo Alaihissalam masu hani ga yin mu’amala da Ruba, don haka ya zama lallai a garemu da mu barta, domin in har bamu barta ba abubuwan da Allah zai yiwa musu mu’amala da ita lallai zasu tabbata ga masu mu’amala da ita daga cikin mu, domin  a yau akasarin mu’amalarmu da Ruba a ciki, a Bankuna ne, ko a Kasuwanni, ko a wuraren ayyukanmu na yau da kullum, ada mutum sai dai shi da kansa yakai kansa wajen mu’amala da Ruba, Amma a yanzu biyoshi ake har wajen kasuwancinsa ko wajen aikinsa ana tura masa bashi mai dauke da Ruba, tare da yi mata kwaskwarima, don haka ya zama wajibi mu rika tantancewa tsakanin cinikayya (Kasuwanci) da Ruba.
Domin zakaji wasu suna cewa ai lalurace tasa ni karbar bashin Banki mai dauke da Ruba don babu yanda zanyi, ko a’a gidana zan karasa ginawa, ko abin hawa zan siya da makamantan haka, to shima Ubangiji a lalurar zai hukun ta shi sabi da mu;amalar da yayi da Rubar.

Dafatan Allah Ta’ala zai datar damu, ya tsarkake mana hanyoyin neman mu daga Ruba da makamantanta, ya shiryar damu ya karamana tsoronsa da biyayya agareshi, ya karamana Lafiya da zaman Lafiya da kwanciyar hankali a garunmu da sauran garuruwan musulmi. Allah ka kara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi Muhammad da ahalin gidansa da dukkan sahabbansa, da wadanda suka bishi da kyautatawa har zuwa ranar karshe.

Alhamdulillah.

Auwal Zakaria Ayagi

Takaitaccen Tarihin Salman Alfarisi Allah yakara Yarda a gareshi

Tarihin Sahabi Salman Farisi (RTA)
Daga Auwal Zakari Muhammad Ayagi
Shugaban kungiyar Alazmiyyah Islamic Foundation

Takaitaccen tarihin sahabin Manzon Allah (SAW) mai girma wato Salman Farisi, to wasu ruwayoyi na tarihi sun bayyana cewar an haifi Salman al-Farisi ne a shekara ta 568 miladiyya ko kuma kusa da haka a wani gari na kasar Farisa da ake kira Jiyye da a halin yanzu yake kusa da garin Isfahan (a Iran). Asalin sunansa shi ne Rozeba, sai dai daga baya, bayan musuluntarsa Manzon Allah (s.a.w.a) ya sauya masa suna zuwa Salman, an ce a wasu lokuta a kan kira shi da Abu Abdullah. Mahaifin Salman dai attajiri ne sanann kuma mai fadi a ji a garin nasu da kewayensa. To sai dai duk da arzikin da yake da shi, Salman shi ne dansa kawai, don haka yake tsananin kaunarsa. A wancan lokacin mafi yawan al'ummar Farisa suna bin addinin bautan wuta ne, don haka cikin wannan addini ne Salman ma ya taso, inda mahaifinsa ya ware wasu malamai don koyar da shi akidu da koyarwar wannan addini, ta amma sakamakon irin hazakar da yake da ita ya zamanto ya sami ilmi mai yawan gaske sama da malaman da suke koyar da shi. A wancan lokacin babban abin alfahari ne ace mutum ya zamanto daya daga cikin malaman addini kuma mai hidima wa daya daga cikin dakunan bautan wutan a kasar Farisan, hakan na kawo wa mutum daukaka da girmamawa. Don haka ne mahaifin Salman yayi kokarin ganin dansa ya zamanto daya daga cikin irin wadannan mutane tun yana dan shekara sha shida a duniya. Salman yayi shekaru uku yana aiki a dakin bautan wuta na Jiyye, to sai dai ba a jima ba sai ya fara kosawa da wannan aiki da malaman dake karantar da shi saboda kasantuwansu mutane masu karancin tunani da ilimi. A mafi yawan lokuta ba sa iya amsa tambayoyin da yake musu ko kuma su ba shi amsa maras gamsarwa. Don haka tun daga lokacin ya fara tunanin yadda zai sami wata mafita. Salman ya fara samun damar ficewa daga wannan addini ne lokacin da mahaifinsa ya tura shi wani gari don ya wakilce shi a wajen. A hanyarsa ta zuwa wannan gari ne ya ci karo da wasu ma'abota addinin kirista da suka fito daga kasar Siriya, inda suka yi masa bayanin akidun addininsu, daga karshe dai Salman ya zama Kirista. Bayan da ya dawo gida, Salman ya shaida wa mahaifinsa ganawarsa da wadannan kiristocin da kuma karbar addinin kiristancin da ya yi. Hankalin mahaifin Salman ya kara tashi kwarai, nan take ya bukaci ya yi da wannan sabon addini amma Salman yaki, don haka sai ya sa aka ta dukansa aka kuma tsare shi kwana da kwanaki ba tare da abinci ko ruwan sha ba. Bayan zama a gidan yari na wani lokaci, Salman ya samu nasarar tserewa daga inda ake tsare da shi ta hanyar taimakon daya daga cikin bayin babansa mai suna Mehran wanda yake tsananin kaunar Salman saboda shi yake kula da shi tun yana yaro. Bayan da ya gudu Salman ya koma wajen wadannan kiristocin inda su kuma suka tura shi kasar Siriya tare da wani ayari. A lokacin da ya isa kasar Siriyan a nan ma ya ci gaba da karatu da neman ilimi ta haka ne ya tara dimbin ilimi mai yawa. To sai dai a wannan karon ma ya sake shiga wata damuwar, yana jin cewa lalle abin da yake kai ba shi ne hakikanin gaskiya ba, akwai gaskiya ta hakika da har yanzu bai same ta ba. Lokacin da wannan tunani ya dame shi sosai sai ya mika komai ga Allah Madaukakin Sarki Yana mai addu'ar cewa Allah Ya nuna masa hakikanin gaskiya. Allah Mai karban, Salman bai san cewa ya kusa kai wa ga gaskiyar da yake bukata ba. . Bayan da ya bar garinsu Salman ya zauna a kimanin garuruwa guda hudu, gari na karshe da ya zauna shi ne Ammuriya dake karkashin daular Rumawa. A nan ne a karon farko ya sami labarin bayyanar wani Annabi a garin Makka da yazo da sakon bautan Allah Shi kadai da yin watsi da bautan gumaka. Nan take Salman ya fara tunanin cewa watakila wannan haske da ya bayyana a Makka shi ne shiriyar da yake bukata. Don haka ya fara shirye-shiryen tafiya Makka don ganawa da wannan sabon Annabi don jin ta bakinsa. To sai dai a hanyarsa ta tafiya Madina nan ya fuskanci matsala inda ayarin 'yan kasuwan da yake tare da su suka ha'ince suka sayar da shi ga wasu yahudawa. Su ma wadannan yahudawan sai suka sayar da shi ga wani attajiri mutumin Madina wanda yake zuwa wajen don kasuwanci. Duk da irin wahalhalun da ya fuskanta a matsayin bawa a Madina amma hakan bai hana shi ci gaba da binciken yadda zai sadu da Manzon Allah (s.a.w.a), duk da cewa a lokacin Manzo bai riga da ya yi hijira zuwa Madina ba. Wata rana Salman yana cikin aiki sai ya ji mai gidansa yana tattaunawa da wani mutum wanda yake bayyana masa cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi hijira zuwa garin Yathrib (Madina), nan take Salman ya fara tunanin yadda zai sami damar ganawa da wannan Annabin. Wata rana kuwa sai mai gidan nasa ya yi tafiya don haka sai ya nufi gidan Abu Ayyub al-Ansari (r.a) wanda Manzon Allah (s.a.w.a) yake zaune a gidansa a lokacin. Ko da suka yi ido biyu da Manzon Allah (s.a.w.a) nan take sai ya ji zuciyarsa ta cika da kaunar wannan Annabi yana gaya wa kansa cewa lalle wannan mutumi ba makaryaci ba ne. Bayan wani lokaci na tattaunawa a tsakaninsu, Salman ya karbi Musulunci, yayi imani da cewa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu bawansa ne kuma ManzonSa. A nan ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya sake masa suna zuwa Salman, wanda da hakan ne aka sanshi tsawon tarihi. Tun daga wannan lokaci Salman ya ci gaba da zuwa wajen Ma'aiki (s.a.w.a) a kai a kai. Da haka ne Salman ya cimma burinsa, wato ya samu tafarkin da zai amsa masa tambayoyin da yake da su da magance masa matsalolin da yake fama da su, baya ga samun darajar kasancewa daya daga cikin sahabban Ma'aikin Allah (s.a.w.a). Matsala guda da Salman yake fama da ita, ita ce bautan da ya ke yi don shi bawa ne. Don haka wata rana Manzon Allah (s.a.w.a) ya bukaci mai gidan Salman ya sayar masa da shi don ya 'yantar da shi daga bauta. Mai gidan Salman ya kafa sharadin cewa wajibi ne Salman ya shuka masa bishiyar dabino 300 sannan kuma ya biya oza arba'in na zinare a matsayin kudin fansarsa. Lokacin da Salman ya gabatar wa Manzon Allah (s.a.w.a) da wannan bukata ta mai gidansa, sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya juya ga sahabbansa ya ce musu: "ku taimaki dan'uwanku". Nan take Sahabbai suka mike suka hada wadannan bishiyoyi da bayahuden yake bukata, sannan Annabi (s.a.w.a) ya bukace su da su tona ramukan da za a shuka su, bayan da aka gama tona ramin sai Manzo (s) ya zo da kansa ya shuka bishiyar farko sannan sauran sahabbai suka biyo sahu. To an gama shuka bishiyoyi amma abu guda ya rage shi ne zinare, don haka har ya zuwa yanzu Salman yana a matsayin bawa. Bayan wani lokacin kuma Manzon Allah (s.a.w.a) ya tara wadanann zinare da ake bukata inda ya ba wa Salman don ya kai wa mai gidansa don cika wannan sharadi na 'yantar da shi. Ta haka ne Musulunci ya ‘yantar da Salman Al-Farisi. Daya daga cikin gagarumar hidimar da Salman yayi wa Musulunci shi ne lokacin da kafiran Makka suka shirya makircin kawo hari birnin Madina da mamaye shi gaba daya. A wannan lokaci ne Salman ya ba wa Ma'aiki (s.a.w.a) shawarar a tona rami mai zurfin gaske a kewaye garin Madina da shi don hana makiyan shigowa. Bayan gama tonun ramin sahabbai sun yi farin ciki da jinjina wa Salman kowani bangare naso ya janyo shi zuwa ga bangarensa, hakan ne ma ya sanya wani daga cikin Muhajirai (mutanen Makka da suka yi hijira zuwa Madina) ya ce: "Salman daya ne daga cikinmu mu Muhajirai", nan take sai wani Ba'ansare (mutumin Madina) ya yi caraf yace: ‘A'a Salmanu daya ne daga cikinmu, mu Ansarawa". Haka dai aka ci gaba da kace nace tsakanin bangarorin biyu. Bayan wani lokaci sai ga Manzon Allah (s.a.w.a) ya iso, yayin da yaji su suna wannan musu, sai yayi murmushi ya kawo karshen musun da cewa: "Salmanu ba Muhajiri ba ne ba kuma Ba'ansare ba ne, Salman yana daga cikin(mu) Ahlulbaiti". Wannan babban matsayi ne da Manzon Allah (s.a.w.a) bai taba ba wa wani mutum in ba Salman ba, wato Salmanu ya zamanto daga cikin Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a), zababbiyar zuriya daga wajen Allah Madaukakin Sarki. A tarihin Musulunci babu wani mutum da ya taba samun irin wannan gagarumin matsayi in ba Salman al-Farisi ba. Salman al-Farisi ya bar duniya ne yana da shekaru 88 a duniya. Salman al-Farisi ya rasu ne a lokacin halifancin Sayyadina Ali (RTA) a garin Mada'in, wajen da Sayyadina Ali ya nada shi a matsayin gwamnan wajen.